AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 4

by @jikargarba001

Zahra na shiga ɗaki ta nufi bayi, ta watsa ruwa a jikinta. Da ta fito tana shafa mai, tunani ya mamaye mata zuciya. Gidan da ta taso ba kamar kowanne gida bane. Kamar wasan kwaikwayo ne, da kowanne ɗan wasa ke ɗaukar rawar da ba lallai ya so ba.

Asalin mahaifinta, Alhaji Bashir, haifaffen Kaduna ne. Shi ne ɗa na uku a jerin ‘ya’yan mahaifinsa. Ya shahara a sana’ar sayar da motoci da kuma canjin kuɗi. Matarsa ta farko ita ce Hajiya Hadiza, wadda ta haifa masa yara biyu—Raflah da Rauda. Amma Allah ya karɓi ranta a lokacin haihuwar Rauda.

Daga baya Alhaji ya auri yar aikinta Sahura, don ta ci gaba da kula da yaran da Hadiza ta bari. Sai dai daga baya Sahura ta gaji, ta ƙi ci gaba da kulawa da yaran. A karshe aka mayar da su wajen kakarsu daga ɓangaren uwa, Inna Habi,wacce ta riƙe su da kulawa da tausayi.

Sahura ta haifi ɗa guda, Abdul Hakim. Amma zaman ta da Alhaji ya gaza ɗorewa. Alhaji ya auri wata Bafulatana mai suna Zuwaira. Sahura ta ƙi zaman lafiya da ita, har hakan ya jawo rugujewar aurenta. Kafin nan Sahura ta sake haihuwar yarinya mai suna Halima.

Zuwaira ta zauna da Alhaji Bashir na tsawon shekara biyu kafin ta rasu a hatsarin mota. Ta bar jariri Musharraf, yana da wata bakwai kacal. Bayan Musharraf ya kai shekara ɗaya, Alhaji Bashir ya nemi auren Amina, kanwar Zuwaira, wacce yanzu suke kira da Mommy. Amina ta karɓi kulawar Musharraf da cikakken tausayi.

Daga baya Sahura ta sake aure ta haifi Safiya. Amma halayenta da rashin jituwa da kishiyoyi ya hana zaman lafiya, mijinta Murtala ya sake ta. Daga bisani Mommy ta roƙi Alhaji Bashir da ya dawo da Sahura ta zauna da ‘ya’yanta, amma har ila yau, babu canji a ɗabi’unta.

Bayan shekaru bakwai da auren Mommy, Allah ya azurta ta da Zahra. Wannan haihuwa ta zo ne a lokacin da ba ta tsammata ba,bayan dogon lokaci da Mama ke mata gorin rashin haihuwa. Zahra ta ci sunan Mommy da Daddy—an kashe tsuntsu biyu da dutse ɗaya.

Bayan wata biyar da haihuwarta, Mama ta haifi Safina, sai Habiba, Laurat, Farida, sannan auta—Ibrahim Khalil. Mommy ba ta ƙara haihuwa ba daga nan.

---

Ƙofar ɗakin Zahra aka buɗe, hakan ya fargar da ita daga duniyar tunani. Mommy ce ta shigo, ta zauna a bakin gadonta.

"Zahra, ki ji tausayi na a gidan nan. Ki daina jan magana. Wai me ya shafi ki da irin shigar Farida? Ko da kuwa tsirara za ta yi yawo a gari ba ruwanki."

"Farida ƙanwata ce. Bazan zuba ido in ga tarbiyyarta ta ɓaci ba. Komai da ta aikata, gidan nan za a danganta," cewar Zahra acikin tausashen harshe.

"Nufinki uwarta bata ba ta tarbiyya ba sai ke? Na sha faɗa miki; Ki gani kamar ba ki gani ba, ki ji kamar ba ki ji ba. Har Allah ya rabaku lafiya."

"Toh shikenan, Mommy."

Amsarta ta zo da sanyin murya, amma ba tare da ta yarda da maganar ba.

Mommy ta ɗauki charger laptop ɗinta da Zahra ta yi aro ta fice zuwa ɗakinta, Zahra kuma ta nufi bayi don yin wanka.

---

A ɓangare guda, Farida ta haura sama, ta tunkari ɗakin Mama tana kuka kamar wacce aka yi wa mutuwa. Mama ta shigo da sauri.

"Ke kuma kukan me ki ke yi kamar wacce ta rasa komai?"

"Mama, wannan test ɗin carry-over ne fa. Zahra ce ta hana ni fita makaranta. Malam ya ce duk wanda bai yi test ɗin yau ba—C.O zai dawo! Daddy zai zo ya yi min faɗa ya ce yana asarar kuɗin sa.

"Kar ki damu. Ni zan sami malamin ya baki makeup test. Zahra kuma zan yi maganinta da salo da ba ta zata ba. Tashi, ki shirya ki fita. Ko gidan kawarki ne, ki sha iska."

Farida ta share hawayenta ta tafi ɗakinta don canza kaya. Mama ta ɗauki wayarta, ta kira ƙawarta.

"Hello Hajia Kubra?"

"Na'am, Hajia Sahura."

"Ina so mu haɗu da ke. Kubra, kinga abin da ke faruwa? Yar kallo ake son a mayar da ni da ‘ya’yana a gidan nan. Yakamata na ɗauki mataki tun kafin abin ya kai ga rigima."

" kin faɗi gaskiya. Zan shigo nan ba da jimawa ba."

---

A wancan ɓangaren kuma, Zahra ta fito daga wanka, ta shirya, ta nufi reading corner ɗinta domin karatu. Amma kafin ta fara, ta duba wayarta. Tarin missed calls ta gani daga Mommy, da biyu daga Jameel.

Ta ƙira Jameel. ya katse. Sai ya ƙira.

"Haba masoyiyata, ina yin ki sosai ne shine kike min haka?"

"Ka yi hakuri wallahi. Wanka na yi. Sai yanzu na samu sarari."

"Lafiya kuwa? Kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah. Lafiya ƙalau."

"Masha Allah, za ki je makaranta yau?"

"A’a, yau zan huta a gida."

"Toh ko zan iya zuwa na ganki, na gaishe da Mommy?"

"Okay. Zan faɗa mata, duk abinda ta ce, zan sanar da kai."

"shikenan. Ki kula min da kanki, amaryar Jameel."

Zahra ta murmusa ta kashe wayar. Ta miƙe ta tafi ɗakin Mommy domin sanar da ita zuwan Jameel.

"Mommy."

"Na’am, Zahra."

"Uhm, Jameel ne ya ce zai zo ya gaishe ki yau. Shine na ce bari in sanar da ke."

"Okay. Ki ce ya zo bayan la’asar. Zan fita aiki yanzu."

Mommy editor ce a wani gidan rediyo. Tana da matsayi mai girma a fannin sadarwa.

Zahra ta raƙa Mommy har bakin mota, sannan ta dawo ɗakinta. Ta kira Jameel ta faɗa masa abin da Mommy ta ce. Bayan haka ta koma reading corner ɗinta ta buɗe littafi domin ci gaba da karatunta. Sai dai karatun na zuwa ne cikin nauyi. Zuciyarta ta cika da damuwa.

“Ina wannan gidan zai dosa da irin wannan halaye?” Ta tambayi kanta a ranta, idonta na kallon fitilar ɗakin da ke raɗa mata haske mai sanyi.