AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 8
Zahra na komawa ɗakin ta, ta faɗa kan gado cike da kuka da ɓacin rai.
"Wannan wane irin rayuwa ce na tsinci kaina a ciki? Me na yi wa Mama da ta tsani ganina haka, ko don ni ba ƴar cikinta ba ce? Ya Allah, dukkan al'amura hannunka suke, kai ne mafi sanin mafita. Ka shiryar da zuciyata, ka bani ƙarfin gwiwa," ta faɗa cikin kuka, tana juyi a kan gado.
A hankali ta tashi, ta shige banɗaki, tana ƙoƙarin daurewa kamar ba komai. Alwala ta yi, ta fito don sallar nafila. Ta tsaya cikin nutsuwa, ta kai kuka da addu’a ga Ubangiji Mai iko da komai. Bayan ta idar, ta zauna har wani lokaci tana sabbatu da roƙo cikin sanyi da tawakkali. Daga nan ta wuce ta yi wanka, sannan ta zauna a reading corner ɗinta.
Duk yadda zuciyarta ke nauyi, Zahra ta san Mama ba ta taɓa goyon bayan karatunta ba. Amma hakan ba zai hana ta cika burinta ba. Tuni ta saka a zuciya cewa, duk da tsangwama da ƙiyayya, baza ta bari su hana ta cimma burinta ba. Karatu ta ɗora da shi, saboda ta san Allah kawai zai iya kawo mata ɗauki.
A ɓangaren su Mama...
Mama na zaune a falo, tare da ɗiyanta mata; Habibah, Farida da Laurat. Hira suke game da gaisuwar da za a kawo daga gidan saurayin Habibah.
Habibah ta ɗaga kai daga wayarta ta ce da mamarta
"Mama kin san gaskiya? Wallahi bana so idan suka zo su ga Zahra. Yana ɓata min ƙima idan an ce ƴar’uwata ce. Ta ƙi aure, taƙi komai, sai dai girman kai."
Mama ta harareta da dariyar mugunta, sannan ta ce,
"Ai da la’asar zaki ce su zo. A lokacin tana cikin karatunta marar amfani, wannan bokon da baza ta kai ko ina ba."
Abdul Hakeem da ke zaune a gefe ya ɗaga kai, ya ce da nutsuwa,
"Gaskiya Mama, ku daina wahalar da Zahra. Yarinyar nan ta fi kowa innocence a cikin mu. She doesn’t deserve this hatred. Da zaku duba zuciyoyinku da adalci, za ku gane cewa ita ba laifi gareta ba."
Mama ta juya masa da tsawa,
"Ka gama? Idan ka gama sai ka tashi ka wuce ɗakin ka. Idan kuma baka gama ba, sai ka ɗauko bulala ka zazane mu duka. Anan ne Zan ga karfin ikon ka, Abdul!"
Abdul ya yi murmushi mai ɗaci.
"Allah ya huci zuciyar ki, Mama." Ya miƙe ya fita daga ɗakin.
Mama da Habibah suka ci gaba da hirar su.
"Wallahi Habibah, na fi jin daɗin cewa ke za ki yi aure kafin Zahra. Farida da Laurat ma suna nan a layi. Ita kuma waccan... bokon sai dai na lalata shi gaba ɗaya."
"Mama, ke ce burina. Ina sonki fiye da yadda kike tunani, saboda kullum so kike ki ga muna cikin farin ciki."
Suka cigaba da hirarsu cikin mugun nufin zuciya.
A ɓangaren Musharraf...
Musharraf na kwance a gadon sa, bai iya yin komai ba sai tunani. Zuciyarsa cike da damuwa da ɓacin rai.
"Ya Allah, me Zahra ta yi da ta kasa samun kwanciyar hankali? Shin babu farin ciki a ƙaddararta ne? Wace irin adalci ce haka?"
Ya jawo wayarsa daga gefensa, ya kira Zahra.
Zahra da ke cikin karatu ta kusa gama handout ɗinta lokacin da taga kiran Musharraf. Gaban ta ya faɗi.
“Me ya faru kuma?” Ta tambayi kanta. Sai ta ɗaga wayar a hankali.
"Hello Yaya."
"Na'am, Zahra kina jina?"
"Eh, ina ji."
"Kar ki saka damuwa a ranki, please. Ki maida hankali a karatunki. I'm working on the matter with Mama. And please, don't mention anything to Mommy. Bamu so ta sa damuwa akan maganar nan yanzu."
"To Yaya. In shaa Allah, zan yi ƙoƙari. Na yarda da ƙaddarar Allah, kuma na yarda cewa duk da wahala, akwai hikima a cikin hakan. Allah ya fi mu sanin abin da ya fi dacewa."
"Allah ya ƙara miki hakuri da tawakkali, Zahra. Gaskiya Jameel ya yi sa'ar mace."
"Yaya..." Ta faɗa a kunyace.
"Menene?"
"Ni dai ka bari."
"Toh, na bari kafin ki saka kuka!" Suka yi dariya a tare, sannan suka katse wayar.
Zahra ta cigaba da karatunta. Musharraf ya cigaba da tunani, yana sa da warware a zuciyarsa.
---
Mommy na gyara labaran rediyo da za a karanta cikin awa biyu. Musharraf ya shigo da sallama.
Mommy ta ɗago kai,
"Kamar kana da magana a bakin ka."
"Eh fa Mommy. Ina da magana da nake so mu tattauna."
"Okay. Bari na ƙarasa wannan aikin. Just give me few minutes."
Ya zauna yana latsawa waya, ita kuma ta gama aikin nata. Tana cire glasses, ta ce
"To, ina sauraron ka yanzu."
"Mommy, iyayen Salma sun ce na turo magabata. So nace bari in fara faɗa mi ki kafin Daddy."
"Alhamdulillah! Finally, ɗaya daga cikin yara na zai yi aure." Mommy ta faɗa cikin farinciki.
"Mommy..."
"Na’am, ango mai jiran gado?"
"Ke kuma da zolaya." Suka yi dariya.
"Amma gaskiya," ya cigaba. "Why not mu sa Jameel na Zahra da ya Turi yanzu tunda karatunta ya kusa ƙarewa?"
"Eh, shawara ce mai kyau. Zan sanar da Daddy idan ya dawo."
---
Bayan fitarsa...
Musharraf ya nufi shashin Mama.
"Assalamu alaikum."
Mama ta juya kamar ba ta ji ba. Farida da Laurat suka amsa. Habiba kuwa ta kau da kai.
"Ina kwana," Laurat ta gaishe shi.
"Lafiya lau, Laure. Ya kike?"
"Lafiya ƙalau Yaya."
Ya juyo ga Mama,
"Ina kwana Mama? Da fatan kina lafiya?"
"Lafiya ƙalau," ta amsa a taƙaice.
"Mama na zo mu yi magana ne."
"Ina jin ka."
Ya ce wa su Habiba, Farida da Laurat,
"Ku bamu waje mu tattauna."
Farida da Laurat suka fita. Habiba ta ƙi tashi.
"Habiba, zaki fita ko sai na tattaka ki a nan?"
Ta miƙe tana maganganu ƙasa ƙasa ta fice.
Musharraf ya zauna yana kallon Mama cikin ido.
"Mama, daman na zo ne mu yi magana game da Zahra. Na lura da yadda kike tsanar ta, har da ni ma. Amma me ya sa? Muna da laifi ne?"
Mama ta dafe ƙafafu, ta ce da isa,
"Kai Musharraf kenan. Ai ba laifi ɗaya kuka yi min ba. Tun daga lokacin da Zuwaira ta aure min miji, ta asirce shi. Sai kuma ita Amina, ta zo ta kama da asiri. Daga nan kai da Abdul Alhaji ya nuna bambanci a tsakanin ki ku. Sannan ita Zahra munafuka ta karkatar da hankalin mahaifinku. Ya fi ƙaunar ta fiye da dukkan ku. Ai ban taɓa son Amina ba, kuma duk ɗan da ta haifa ba zan taɓa son sa ba. Don haka ba zan taɓa son Zahra ba!"
Musharraf ya ɗaga kai yana kallon Mama cikin jin mamakin furucinta.
"Mama, wannan kuskure ne. Zahra bata cancanci wannan ƙiyayya ba. She's just a girl trying to survive. Ki yi ƙoƙarin cire son zuciya, ki kalli Zahra da idon tausayi. Ki fahimce ta..."
"Dakata! Idan wannan ne ka zo faɗa, to ka iya barin ɗakin."
"Mama don Allah ki fahimce ni..."
"Naƙi na fahimce ka ɗin. Tashi ka fita malam!" Mama ta faɗa cikin fushi.
"Zan tafi, amma ki sani... rana ɗaya zaki yi nadamar abubuwan da kike yi. Ki bar Zahra saboda Allah. Ta sha wahala da yawa."
Ya miƙe ya fice. Mama ta bi shi da kallo, tana rawar murya.
"Ah lallai Kam! To bari in gama da Zahra, sai in wai waye ka Musharraf. Ai kaima ba barinka zan yi ba. Shashasha kawai."
Wannan page ɗin ta ki ce shugaba mai capacity; Na'ima Sarauta(Nimcy)😍. Allah ya ƙara miki ɗaukaka.