AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 17

by @jikargarba001

Iya ta bi su da kallo, sai ta ce, "Ina za ku tafi?"

Habiba ta kyaɓe baki tana mai nuna rashin jin daɗi, ta tsaya cak a wuri guda. Farida ce ta amsa, "Gidan su ƙawar Habiba zan rakata."

"Babu inda za ku je! Haba don Allah, yara ba za ku koyi zaman gida ba? Sai yawoce-yawocen banza da wofi? Ke Habiba da za ki yi aure nan da ‘yan watanni, wannan baƙin halin ne za ki kai wa mijinki? Amma lallai da kuwa kin dawo gida..." Iya na cikin faɗa kamar ta ke a ɗakin mahaifa. Habiba ta ja hannun Farida suka fita daga falon, suna mai kau da kai.

Iya ta bi su da ido tana faɗin, "Ina magana shine za ku fita? Ke Habiba, ba ki san tsautsayi na kan amarya ba ko?"

Suka yi kamar ba su jinta ba, suka cigaba da tafiya cikin natsuwa har suka zuwa bakin gate.

Iya ta buɗe baki cike da mamaki tana kallon su, sai ta ce, "Wallahi idan kuka fita daga gidan nan, ba za ku ji daɗin abinda zai biyo baya ba."

Haka suka fita daga gate abinsu, suka bar Iya tsaye cikin mamaki da ɓacin rai. Ta juya da sauri ta koma cikin falo tana faɗin, "Sahura! Sahura! Sahura!" tana ta kwaɗawa Mama kira da ɗaga murya.

Mama da ke zaune a ɗaki ta ji yanda Iya ke kwala mata kira. Gabanta ya faɗi tamkar ana watsa mata ruwan sanyi. Allah ya ɗora mata azababben tsoron Iya, tun lokacin da take 'yar aiki a gidan.

Mommy ma da ke duba wani littafi sai da ta ajiye shi gefe, tana mai tunanin me kuma Mama ta sake yi wannan karon.

"Sahura! Ba ki ji ina kiran ki ba!" Iya ta ƙara faɗa da ƙarfi.

A tare Mama da Mommy suka fito daga ɗakin, suka haɗe a staircase, Mommy ta dan ba wa Mama hanya ta wuce gaba, ita kuma ta biyo ta a baya.

Zahra, da ke ɗaki tana karatu, ta so ta yi kamar ba ta ji ihun Iya ba, amma saboda yawan hayaniyar da Iya ke yi, dole ta fito domin ganin me ke faruwa.

Mama na sauka daga matakala ta nufi inda Iya ke tsaye. Tana isa ta ce, "Yi haƙuri Iya, ina banɗaki ne lokacin da kika fara kiran."

Iya ta kalle ta sosai kamar mai nazarin ta, kafin ta ce da ita, "Sahura, me matsayi na a gidan nan? Akwai wanda ke gaba da ni a gidan nan? Akwai wanda ya isa in ba da umurni a gidan nan ya ƙi bi?"

Kowa ya yi shiru, yana kallon juna cikin mamakin me ya kawo irin wannan maganar.

"Ina tambayar ki!" Iya ta faɗa da murya mai cike da fushi.

Mama ta sunkuyar da kai, sannan ta ce, "Babu Iya, ke ce ke gaba da kowa a gidan nan. Dole ne mu bi umarninki."

"To kin fa sanar da ‘ya’yanki haka?"

"Iya, babu wanda bai san hakan ba a gidan nan."

"Shine suka zaɓi su taka min ƙa’ida su yi abin da zuciyarsu ta raya musu?"

"Iya ki yi haƙuri. Duk da ban san me suka miki ba, na ɗau alkawarin zan ɗauki mummunan mataki a kansu."

"Dalla! Yi min shiru. Mataki fa za ki ɗauka? Ai baƙin halinki ne su ka gada! Wai ace ni Iya ina magana da yara, suka yi min banza, suka fita su ka je su yawo."

Ta juyo ta kalli Mommy da Zahra, ta ce, "To ku kiyaye. Domin wannan isa da rashin kunya da yaran nan ke nunawa ba haka kawai ba ne, akwai wani abu a ƙasa. Ku buɗe idanu sosai, ku kuma dage da addu’a."

Sannan ta kalli Mama ta ce, "Ke kuma, ki kira min su, su dawo gida yanzu-nan."

Mama ta ce, "Iya, da wace waya zan kira su? Wayata na hannunki fa."

Iya ta ce, "Ke Zahra, kira min su da wayarki."

Zahra ta taɓe baki ta ce, "Bani da kati."

Iya ta juya ta ce, "Ke fa Amina?"

"Wayata ta samu matsala; ba ya ɗaukar kira."

Iya ta bisu da kallo mai cike da tuhuma, sannan ta ce, "Ya muku kyau."

Ta wuce ɗakinta, ta ciro wayar Mama daga ƙasan kayan ta, ta taho da ita tana cewa, "Gashi! Ki kirawo su da wannan, sai ki mayar min. Ni ba zan yarda a cinye min kati saboda waɗannan yara ba."

Mama ta karɓi wayar daga hannunta, ta kunna. Lambar Hajiya Turai ta fara turawa mata saƙo, tura mata saƙon cewa ta kira ta, ta layin da ta turo mata yanzu. kafin ta kira lambar Habiba kai tsaye.

"Hello, Habiba, kina ina?"

Habiba, da su ka sauka daga adaidaita sahu kenan, ta ce, "Muna kofar gidan, yanzu muka sauka."

"To ku dawo gida yanzu."

"Mu dawo kuma Mama? Ba mu ma shiga gidan ba."

"Na ce ku dawo gida yanzu!" Mama ta maimaita cikin faɗa.

A wannan rana su Habiba suka gane cewa tabbas shayin ruwa ne.Domin kuwa Iya ta tara kowa a gidan, ta bayyana hukuncin su kamar haka;

"Daga yau, ku za ku riƙa share ko ina a gidan nan da goge. Idan na ga ba a yi da kyau ba, zan kirawo ku ku sake. Babu amfani da inji wank, da hannunku za ku riƙa wanke kayan ku. Kuma wayoyinku za su riƙa kwana a hannuna. Da safe ƙarfe shida zan baku, da yamma kuma zan amsa. Domin jin daɗin da ɗa na ya samar muku shi ne ya sa kuke jin ba kowa da ke da ƙima sai ku."

Kowa ya yi shiru, ba wanda ya yi musu. Domin kuwa babu wanda ya isa ya ja da Iya.

Rayuwa ta cigaba da tafiya da sabani da sauyin hali. Yau daɗi, gobe babu daɗi. Mommy ta cigaba da shirye-shiryen biki na ‘ya’yanta. Iya kuwa ta dage wajen yi wa Zahra gyaran amare, amma ta ce, Ba ruwata da Habiba. Ita ba ta da kunya.

Mama kuma ta samu wata dama, ta haɗu da Hajiya Turai, suka fara tsara yadda za su ruguza auren Zahra.

Yau, Zahra ta fita da motar Mommy domin siyayya na abubuwan dinner party. Tana fitowa daga layin su ta hango maƙwabciyarsu, Haulatu, tana neman abin hawa. Sai ta danna mata horn.

Haulatu ta juyo tana dubawa. "Haulatu, shigo na sauke ki a bakin titi." Zahra ta faɗa tana sauke glass na motar.

"Zahra, ashe ke ce?"

"Eh, ni ce, shigo."

"Tare muke da Mama."

"Ina Maman take?"

"Ta tsaya siyan abu a shagon can," ta faɗa tana nuna wani shago.

Daidai lokacin, Maman Haulatu ta fito daga shagon. Tana zuwa bakin mota ta leƙa ciki ta ga Zahra ce. Fuskarta ta canza nan take. Ta ce, "Ke Haulatu, ba na hana ki tsayuwan da yarinyar nan ba?"

Haulatu ta sunkuyar da kai, "Mama, kawai ce ta yi za ta rage mana hanya."

"Bama so! Ki ƙyale ta kada ta ɗora ki a hanyar banza kamar yadda ita ta bi. Kin ga dai yadda ta gagara aure, ki cigaba da binta idan kina son ki ƙare kamar ta."

Zahra ta kalli Maman Haulatu da takaici, ta ce, "Ina kwana Mama." Bata jira amsarta ba ta ja motarta cikin ɓacin rai.

Ta wuce makaranta ta ɗauki Sofi suka nufi fashion house inda za a ɗinka mata dinner gown.

Receptionist ta tarbe su da fara’a, "Welcome ma, how may I help you?"

Sofi ce ta ce, "We're here to see your manager."

"Do you have an appointment with her?"

"Yes, we do."

"May I know the name?"

"Fatima Bashir."

Receptionist ɗin ta ɗauki waya ta kira manager. "Madam, baƙuwa na nan, sunanta Fatima Bashir. Ta ce tana da appointment da ke."

"Lead her in."

Suka biyo ta har ofishin manager. Bayan an shiga, receptionist ɗin ta ce, "Here they are, madam."

Manager ta ɗaga kai ta ce, "A kawo musu abin motsa baki." Sannan ta kalli su, ta ce, "Sit please."

Suka zauna. Sofi ta ce, "Thanks."

Bayan an kawo snacks, Madam ta ce, "Wacece amaryar?"

Sofi ta nuna Zahra da ke ta danna waya.

"Amarya, zan iya tambayarki wasu tambayoyi?"

"Go on," Zahra ta bata amsa kai tsaye ba tare da ta ɗago kai ba.

"Wanne irin gown kike so? Mai faɗi ne ko ɗamamme?"

"Kawai ki yi wanda ya dace da addini da al’ada."

"Ok, just a free gown kenan. Wane launi?"

Zahra ta ce, "Madam please, I'm not in a good mood. Can we reschedule this meeting?"

"Of course. That will even be better, because now that you're not in a good mood it may affect the outcome."

"Na gode. Sofi mu tafi."

A hanyar komawa gida, Sofi ta ce, "Zahra, I don't think what happened deserves this much anger."

"Baza ki gane ba."

"Zahra, ba yau ake faɗa miki irin wannan ba. Me ya sa ya dame ki haka?"

"Baza ki fahimta ba. We're not from the same culture, and you're even younger. Ba za ki gane irin wahalhalun da nake fuskanta ba."

Sofi ta kyaɓe baki, ta yi shiru, ba ta ce komai ba har suka isa makaranta. Zahra ta sauke ta, ta wuce gida.

Zahra na shiga falon gida ta ga kowa a tsaye. Saude mai aiki na kuka, Iya na faɗa har da hawaye.

Kusa da Musharraf ta je ta tsaya, ta ce, "Me ke faruwa?"

Iya ta juyo cikin yanayin fushi ta ce, "Zahra, kashe ni aka shirya yi a gidan nan yau. Wallahi da yanzu, sai dai a ji ana jana'izata, da ba don Allah ya tsare ba!"

"Ban gane kashe ki ba, Iya...?"