AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 22
Gobe za a ɗaura auren Zahra da Jameel. Gidan Mommy cike yake da motsin alhini da fatan alheri. Mommy ta yi duk mai yiwuwa don ganin Zahra da mahaifinta sun fahimci juna, sun ɗinke ɓarakar da ta shiga tsakaninsu. Ta dage sosai wajen sa Daddy ya sassauta zuciyarsa, ya bar Mama Sahura ta dawo ɗakinta don a gudanar da bikin yaransu cikin mutunci da martaba.
"Wallahi Alhaji, hakan babu daɗi. Ace za a yi bikin ƴarta guda amma ita ba ta nan? Don Allah ka duba lamarin da idon adalci," Mommy ta faɗa da murya mai rauni, cike da neman fahimta.
Alhaji ya jinjina kai da guntun numfashi. "Amina kenan. Ke kullum cikin sanya kanki a cikin al’amuran Sahura kike. Ita kuwa ko a jikinta. Yaushe za yi haƙuri ki yafe ki fita harkarta?"
"Alhaji, babu wannan ranan. Ba fa don ita nake ba, sai don Allah. Ina saka kaina a shoes ɗinta ne. Ka duba, idan ni ce za a yi bikin ƴata, amma a hanani halarta duk da ina da rai, yaya zan ji? Tabbas ba zan ji daɗi ba. Don haka, don Ma'aiki, kayi haƙuri. Bayan biki sai ka yanke duk hukuncin da ya dace."
Alhaji ya nisa. "Na ji, kuma na amince. Amma da sharaɗi, ana gama biki, Sahura za ta bar min gida na."
"Hakan ma an gode. Allah ya saka da alheri, ya ƙara girma da mutunci."
---
ƅangaren Zahra kuwa sai shirin biki su ke yi da murna. Farhana da Sofi, abokan zaman ta na kusa, sun tsaya tsayin daka wajen ganin amarya ta yi kyau kamar sarauniyar kyau. Jiya aka yi mata ƙunshi, yau kuma ana mata kitso mai kyau da birgewa. Kitso ne ƙananu masu kyau. sun fito mata da kyawun ta sosai.
Farhana ta shigo garden inda a ke kitson Zahra, riƙe da cup ɗin custard tana motsawa, ta ce; "Zahra amma kin san ba ki ci komai tun safe ba ko?"
"Bana jin yunwa," Zahra ta amsa a gajiye.
"Ai ba sai ana jin yunwa ba ake cin abinci, wasu lokutan ana ci ne saboda haƙƙin jiki. Na haɗo miki custard, na san za ki buƙaci hakan ."
"Ki ajiye, idan an gama kitson zan sha."
"A'a wallahi. Kitson da ko rabinsa ba a kai ba, kin san yaushe za a gama? Sha biyu yayi fa. Kin fiye gardama, kuma ba komai a cikin ki." Ta juya ta kalli mai kitson "Don Allah ki ɗan tsaya ta ci abinci na mintuna ƙalilan."
Mai kitson ta ce, "Babu matsala Hajiya, ki sha mana ko da kaɗan ne."
Zahra ta girgiza kai. "A'a, a ci gaba, na gaji sosai, I can't wait a ƙarasa kitson nan so that I can rest."
Farhana ta zauna ta motsa custard ɗin, ta ce; "To buɗe bakin ki, zan rinƙa baki a baki kamar baby."
Zahra ta kalleta, suka sakar wa juna murmushi mai cike da ƙauna. Sai ta buɗe baki. Farhana ta rinƙa bata custard kamar ƴar yarinya. Haka ta sha har ta shanye.
"Yauwa ko ke fa. Ko dai na ƙara miki ne?"
"A'a na ƙoshi. Yanzu dai ki bani wayarki."
"Me za ki yi da ita?"
"Ina son in kira Jameel. Sofia ta fita da tawa."
"Ina ta je?"
"Ta je siyo min pad."
"Wait... Don't tell me baƙonki ya zo ne?"
"Wallahi, not long ago."
"Oh my gosh, wrong timing," Farhana ta ce tana buga goshinta. Ta mikawa Zahra wayarta, ta shige cikin gida.
Zahra ta danna lambar Jameel, da Farha ta saving as in-law. Tana sa wayar a kunne, zuciyarta na bugawa.
"Hello..." Muryar Jameel ta fito, ta gyara zama tana jan numfashi.
"Hello Jameel... Zahra ce."
Cikin murya mai kauri da shauƙi, Jameel ya ce "My sunshine... amaryata ta gobe."
Zahra ta yi ɗan murmushi. "I can't believe gobe ne. I feel like I'm dreaming."
"Nima wallahi. Daga gobe fa, za ki zama tagwayen zuciyata. You will always be with me, a zuciyata da kuma zahiri."
"Jameel... Ina jin wani irin abu. Ba tsoro ba, ba damuwa ba. Sai dai wani nauyi a zuciya."
Cikin nutsuwa ya ce; "Ki dena jin nauyi. Daga gobe ni zan riƙe miki nauyin rayuwa. Your only duty is to love me more."
"Na gama ba ka zuciyata tun tuni. Pls, Jameel, ka saka ni jin daɗin da ban taɓa sani ba, kar ka juya mini baya duk rintsi please."
"Na rantse, Zahra, zan kula da ke kamar gilashi a hannun jariri. I’ll love you with softness, patience, and du’a."
Zahra ta lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya.
"Ka shirya jure halina, I’m not perfect."
"I can handle all of it. Just promise me za ki bar min zuciyarki gaba ɗaya."
"Tuni ta dawo taka. Don kai kawai take bugawa."
"Allahu ya kaimu gobe lafiya. Na kasa jiran ganin ki cikin farin shadda kamar amarya daga Aljanna, kina takowa zuwa gare ni a matsayin mata ta"
"Jameel... thank you for loving me this deep."
"No, I should thank you. Yanzu ki huta. Gobe na zo na dauke ki gida na mu sha soyayya mai daɗi da zurfi."
Zahra ta katse kiran da jin kunya, tana dariya.
"Munafuka," Farhana da ta ɗan daɗe da dawowa, ta ce tana kallonta. Zahra ta yi kamar ba da ita ake ba.
Farhana ta zauna kusa da ita. "Keep ignoring me.
"To me kike so na ce Miki fissabilillah? Kin fiye neman magana. Ba dai kin zage Ni ba, jeki na bar ki da halin ki."
"Bestie... listen to me."
"Ina ji."
"Shawara ce, idan kin ɗauka fine, idan ba ki ɗauka ba kin yi wa kanki. Kinga wannan kunyar da kike yi? Ajiye ta gefe daga gobe. Ki bayyana masa soyayyarki da gaskiya. Ki zama wadda zai daina kallon kowace mace saboda ke ɗaya, and the only way to do that shine ki bayyana masa azababben ƙauna mai tsaya a rai. Life is short. Na yi kuskure da ban nuna wa mijina irin son da nake mishi ba kafin ya mutu, na tsaya wai ni ina kunya. I deeply regret my action, ga shi yanzu he's no more.Ya Allah ka jaddada masa rahma." Ta ƙarasa cikin hawaye
Zahra ta riƙe hannunta, ta ce "Allah ya jikansa. Allah kuma ya kawo miki wanda zai so ki saboda Allah."
"Ameen."
"Cheer up joor, don't spoil my mood."
Farhana ta kwashe da dariya, ganin yanda Zahra ta yi maganar kamar wata ƴar baby.
Sofia ta dawo. Zahra ta canza pad, aka ci gaba da kitson. Har zuwa karfe uku kitson ya kammala. Ya fito kamar da inji aka yi. Gashinta ya sauko har gadon bayanta. Gaban goshinta sai Walƙiya ya ke.
"Wow! Sis your hair looks gorgeous just as you are."
"Farhana, ba ki gajiya da zolaya."
"Zolaya ko gaskiya?"
"Na gode, amma ya fi kyau wanda nayi kitson domin sa ya fara yabawa."
Sofia ta bita da mamaki. Zahra ba ta taɓa zama free da ita irin haka ba. She still can't believe Zahra is this jovial.
"Afuwan amaryar Jameel," Farhana ta ce. Duk suka yi dariya.
Zahra ta ce, "Sofi mu shiga ciki."
Sun tarar da su Anty Raflah da cousins ɗinsu sun iso. Sabon babin hira ya buɗe.
---
A ɓangaren Mama Sahura kuwa, suna tare da wata tsohuwa mai suna Wuro suna tasu shirye-shiryen.
"Kin tabbatar za ku iya aikin nan?" Hajiya Turai ta tambaya.
"Wallahi zamu iya, in har biya da kyau," Wuro ta amsa cikin biyayya.
"Biya ba matsala ba ne. Idan aikin ya yi kyau ki tabbata cewa kun fita daga talauci," Mama ta faɗa tana kallon ta.
"To ai shikenan kar ki ji komai, aiki zai yi matuƙar kyau."
Turai ta ci gaba da faɗin; "Mun kama haya a anguwar Kanawa, nan ɗanki zai kawo su a matsayin gidan ku idan sun buƙaci hakan. Idan aka gama komai sai ku koma ƙauyen ku. A Ibadan ma za mu kama gida, sai a ce can ne gidan da zata zauna.Bayan sun kawo ta sun juya baya sai ya a tattara ya bar Ibadan ɗin ya koma wajen sana'ar sa a Legas."
"Kina nufin ba a son kowa ya san ainihin inda muke?"
"Haka nake nufi."
"To shikenan. Zan tura miki ɗana sai ki daɗa yin ma sa bayanin yadda komai zai kasance."
"Hakan ma ya yi. Yanzu za ki iya tafiya, idan wani abu ya taso zan neme ki. Ga wannan ki hau adaidaita." Ta faɗa tana jefa mata kuɗi ƴan dubu-dubu.
"Na gode sosai Hajiya, Allah ya ƙara girma da ɗaukaka, Allah ya biya Miki dukkan buƙatun ki."
Ta fita tana godiya da hawaye.
Mama ta ce, "Zan koma ɗakina gobe. Alhaji ya turo saƙo ya ce in dawo ayi biki da ni kafin ya yanke hukunci a kai na."
"Kawata kenan. Ki miƙe neman taimako kin ƙi. Ai ga irinta nan sai wulaƙanta ki yake yi yanda ya ga dama."
"Turai yanzu ba wannan ba. Don Allah ki yi min alfarma ki biya mutanen nan da kyau, yanzu ba ni da kuɗi amma idan na koma gida zan samo a wajen shi Alhajin ko Abdul In Sha Allah, sai na biya ki."
"Ga irinta ai, da kina bin shawara da kuɗi yanzu ba matsalar ki ba ce."
Mama bata ce komai ba. Ta maida hankalinta kan TV.
---
RANAR AURE
Gidan su Jameel cike ya ke da hayaniya, mutane na ta shirin tafiya ɗaurin aure. Maman Jameel na shafa mai bayan ta wanka, sai wayarta ta fara ruri.
"Jameel ba zai bar Ni na huta ba, ko me ya ke buƙata yanzu?." Ta duba wayar, ba shi ba ne, sai dai wata lamba da ta ɗan saba gani. Ta ɗauka.
"Na ce miki kar ɗanki ya aura min budurwa amma kin ƙi. To wallahi ko sun yi aure, ba zai hana mu ci gaba da harka da Zahra ba. Saboda Zahra tawa ce kuma da ni ta saba."
"Kai sheɗan nebda ke son ya wargaza wannan auren. Amma ba za ka yi nasara ba."
"Hajiya ɗanki ne sheɗan, da yake son ya shiga tsakanin masoya."
"Kai saurara. Nan da few hours zahra za ta zama mallakin ɗa na. Mtseeew."
Ta kashe. Sai ga saƙo ya shigo. Ta duba. Tashi tsaye ta yi cikin firgici.
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un. Na shiga uku."
Kira ne ya sake shigowa wayar, ta ɗauka.
"Yanzu kin tabbatar cewa Zahra tawa ce ko kina kan kokonto?"
Ta kasa amsa. Ta katse kiran ta fito da sauri. Cikin zuciyarta, ta tabbatar cewa Zahra ba yar mutunci bace, ko da kuwa bata taɓa yarda da zargin ba a baya. An daɗe ana kiran ta da tura mata saƙonni akan kar ta bari ɗanta ya auri Zahra, saboda ba ta da kamun kai, ba ta yarda ba, Amma yanzu abinda ta gani ya tabbatar mata da Zahra ba ƴar mutunci bace.