AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 23

by @jikargarba001

Master's side na gidan mahaifiyar Jameel ta nufa cikin hanzari kamar wadda gobara ke bin ta. Da ƙarfi ta turo ƙofa ta shiga ciki cike da fushi da tashin hankali, tana kiran suna da ƙarfi, "Alhaji! Alhaji!"

Alhaji Dawood, mahaifin Jameel, yana ɗaki yana shirin shiga wanka. Jin kiran da Saudatu ke yi masa da muryar tashin hankali ya sa ya fito da sauri daga ɗakin, har sun kusan ci karo da juna a ƙofar. Ya ja da baya yana tambaya da damuwa, "Lafiya?"

"Alhaji babu Lafiya! You need to call off this wedding right now!"

"Wane auren?"

"Auren Jameel."

"Ban gane ba? Kina cikin hankalin ki kuwa, Saudatu?"

"Ni ko nake cikin hankalina! Wallahi sai an fasa auren nan. Just take a look at this." Ta miƙa masa wayarta hannunta na rawa saboda tsananin fushi.

Ya karɓa da rashin fahimta, ya kalli screen din wayar. Idanunsa suka cika da mamaki da takaici yayin da yake kallon bidiyon da ke wayar. Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi.

"Uhmm... Saudatu, koma dai menene ya faru, ina ganin ki yi haƙuri. Auren ya kusa sosai, we can’t just call it off an hour to ɗaurin aure. Idan muka fasa aure yanzu, ba mu yi mu su dalci ba."

"Wane irin adalci kake magana akai? Mu da suka rufa mana asirin ƴar su, sun yi mana adalci ba? Sun yaudare mu da kyawawan kalmomi, ba su faɗa mana cewa ƴar su balagaza ce ba. Kuma kai kana son mu ci gaba da wannan, kana wani maganar adalci."

"Kin ga Saudatu, it might be a mistake from her past. Ƙila ta tuba zuwa ga Allah. Who are we to judge her when we all are sinners."

Saudatu ta yi murmushin takaice.cikin ɓacin rai ta ce "Are you for real? Ka ce ƙila ne ka, What if this is not her past but her present lifestyle?"

Alhaji Dawood ya ce da gajiyawa, "Kinga Saudatu, mu bar maganar nan. Bari na shiga wanka na shirya. Kar ayi ta jira na. Idan ma halin ta ne, bayan bikin sai mu san yadda za a gyara ta." Ya juya ya shige bathroom ba tare da wata damuwa ba.

Kallo Saudatu ta bi shi da shi baki a buɗe. Hankalinta ya tashi, ta rasa yadda za ta yi. Dukkan tunaninta ya ɗaure. Can ta hango wayarsa a gado. Da sauri ta ɗauke ta, ta cire key ɗin ƙofa, ta fita ta rufe ƙofar daga waje, tana fadin, "Wallahi ɗa na ba zai aure ƴar iska mara tarbiyya ba. Akan me na gama tarbiyyantar da ɗana a zo a cuce shi"

Kai tsaye ta nufi ɗakin Jameel. Angon da aka gama shirya wa cikin fararen shadda mai ƙyalli, yana sheƙar kamshi, abokansa na zolayar sa da dariya.

Saudatu na shigowa, ɗakin ya dauki shiru. Kowa ya juya ya kalleta ganin yadda ta haɗe fuska, sai suka gaishe ta cikin ɗar-ɗar. Ta amsa gaisuwarsu ba tare da walwala ba. Ta kalli Jameel da ido kai tsaye tace, "Where do you think you're going to?"

Jameel ya yi murmushi yana kallon abokansa, yana tunanin zolayarta ce ya tashi. "Zan tafi ɗaurin aure na, of course," ya faɗa yana buɗe hannaye, yana nuni da ta kalli shigar da ya yi.

Amma murtuƙe fuska Saudatu ta yi, tace da ƙarfin murya, "Babu inda za ka je, Jameel. Auren nan an fasa!"

Jameel ya ja da baya, ya ɗan kalli abokansa da suka yi shiru suna kallon ta da mamaki a fuskokin su.Sai ya juya da damuwa ya ce, "Mama kenan, don Allah ki bar wasa haka. Just get ready, in the next few hours I will bring your daughter-in-law home."

"Jameel, ba wasa nake ba. I’m damn serious. Wallahi idan ka gan ka auri yarinyar nan yau, sai dai in ba na numfashi."

"Wait, Mama... But why? Me ta miki?" Ya tambaya cikin damuwa, ganin cewa tabbas da gaske fa take.

Ta miƙa masa wayarta. Da hannu mai rawa ya karɓa, ya kalla. Wani sanyi ya ratsa jikinsa yayin da zuciyarsa ta karye. Bidiyon Zahra ce kwance a hotel room a ƙirjin Wani saurayi tsirara, daga ita sai pant, da karar sigari a bakinta, ta kumshe ido. Bidiyon ya kashe masa dukkan farin ciki.

"No! This can’t be Zahra. Wannan ba ita ba ce!" Ya faɗa a ruɗe, jikinsa ya ɗauki rawa.

"Idan ba ita ba ce, wacece? Ni ce kenan, huh!?Jameel, forget it. Ba za ka auri wannan yarinyar ba. That’s final."

"Please Mama, kar ki ce haka. Bari na yi magana da ita tukuna. Maybe there’s an explanation. Maybe it’s even a mistake."

"Jameel na riga da na yanke hukunci. Auren nan ba zai yiwu ba. Idan kuma kana ganin za ka ci gaba da gardama da ni, fine continue. Amma ka sani wallahi idan ka yi auren nan, ban yafe maka ba!."

Tana faɗin haka ta nufi ƙofa. Jameel ya ruga ya riƙe ƙafarta, yana kuka kamar yaro, "Mama please! Wallahi Zahra ba haka take ba. I trust her. Maybe it was a mistake. Maybe someone set her up."

Saudatu ta yi ɗan dariyar takaici, ta ce, "Aure an fasa. Idan kuma ka dage, ka je ka aure ta. Amma daga yau na yafe ka daga cikin ƴaƴana. Ba zan yarda na a haɗa zuri'a da karuwa ba."

Ta fizge ƙafarta daga hannunsa ta fice, ta bar Jameel a tsugunne kamar gunki. Jameel ya fashe da kuka mai taɓa zuciya, yana furta, "Me yasa za ki yi mini haka Zahra? Me ya sa a yanzu ne?"

Abokansa suka taru kusa da shi, kowa da nasa ƙoƙarin kwantar masa da hankali.

Saudatu na fitowa daga ɗakin ta nufi inda ake girki. Mutane na ta aikin abinci. Ta tsaya tsayin daka, ta ɗan ja numfashi tace, "Kuyi stopping komai. An fasa auren."

Matar da ke motsa miya ta juyo cikin mamaki, "Ban gane an fasa aure ba?"

"Eh an fasa. Saboda an kama matar da ɓatanci."

Matar nan ta saki cokali, tana faɗin, "Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Jama’a ku zo ku ji!"

Nan fa labari ya baza. Mutane suka taru suna tattaunawa, wasu da mamaki, wasu da tausayi, wasu da jin kunya. Saudatu ta bar wajen cikin natsuwa kamar wadda ta gama nasara.

Ta shiga ɗakinta, ta faɗa kan gado. Hawaye suka gangaro daga idonta. Ba saboda jin daɗi ba, amma saboda baƙin ciki. Ta fi kowa sanin yadda ɗanta Jameel ya ɗora zuciyarsa akan Zahra. Amma ba za ta iya barin shi ya auri ƴar da ta rasa kunya da mutunci ba.

Ta share hawayenta, ta janyo wayar mijinta ta tura saƙo ga yayansa wanda shi ne waliyyin auren Jameel, ta faɗa masa auren an fasa.

A gefe guda kuma, Alhaji Dawood yana fitowa daga wanka, yana shiri cikin hanzari. Yana cikin shirinsa sai ya fara tunanin videon da ya gani a wayar Saudatu. Bai taɓa zargin Zahra da irin hakan ba, saboda yayi bincike sosai a kanta kuma bai same ta da rashin tarbiyya ba, definitely this might be a setup.

Yana duba wayarsa don ya tafi wajen ɗaurin aure amma bai ganta ba. "Ina na ajiye wayar? Ko dai na bar ta a mota ne?" Ya kama hanyar fita sai ya ji ƙofa a rufe.

"Kar dai Saudatu ta rufe ni ta waje? Lallai, wannan mata."

Ya dawo ya zauna, ya sake duba gado amma bai ga wayar ba. "Kar dai ta ɗauke mini waya. Da kuwa ranta in yayi dubu sai ya ɓaci."

Ya bugi ƙofa da ƙarfi amma babu wanda ya ji shi. Cikin damuwa ya ci gaba da jira.

...

A masallaci kuwa, an ɗaura auren Habibah da Lawal. Saura na Zahra da Jameel. Liman ya kira waliyyin Jameel har sau uku amma shiru.

Malam Usman, wakilin Jameel ya fita daga masallacin bayan ya karanta saƙon da Saudatu ta turo masa ta wayar ƙaninsa. ya ɗan tsaya daga gefe, ya kira Alhaji Dawood, babu amsa. Ya kira Jameel, shiru. Ya kira Hajiya Saudatu, the same.

Sai ya kira matarsa, ya ce ta miƙa wayar ga Saudatu. Bayan ƴan daƙikoki, ta kira ta ce, "Ga ta nan."

Ya ce, "Hello, Saudatu. Ina Dawood?"

"Ya fita."

"Jameel fa?"

"Tare suka fita."

"Ina suka tafi?"

"Gaskiya bai faɗa mini ba Yaya."

"Me ke faruwa ne?"

"Auren ya ce a fasa. Saboda an samu yarinyar da rashin tarbiyya, bin maza ta ke yi."

"Subhanallahi! Amma..."

Bai kai ga ƙarasawa ba sai ya ji an taɓa shi, juyowar da zai yi yayi ido huɗu da Alhaji Bashir. Katse kiran yayi yana faɗin "I will call you back."

"Malam Usman kai a ke jira a masallaci." Daddy ya faɗa

"Alhaji akwai matsala."

"Wace irin matsala?"

"Mun fasa aure."

"Ban gane kun fasa auren ba?"

"Eh mun fasa, saboda mun sami ƴar ku da rashin tarbiyya."

"Ban gane ba. Me ya hana ku gano hakan tun da farko, sai yanzu a wannan lokacin za ku kawo wani magana mara tushe?"

"Ai da kun faɗa mana gaskiya cewa ƴar ku mara tarbiyya da kamun kai ne da ba akai wannan gaɓar ba "

"Don Allah Alhaji kada ka kuskura ka yi ɓatanci ga ƴata. Kun fasa auren kenan, shikenan, don't upset me!"

"Eh mun fasa auren." Alhaji Usman ya daɗa jaddadawa.

"To Allah ya saka. Za ku gane illar abin da kuka yi, idan kun zalunci ƴar nan za ku gani."

Alhaji Usman bai kuma cewa komai ba, ya tafi wajen motarsa, ya shiga motar cikin ɓacin rai.

Alhaji Bashir ya yi baya baya kamar zai faɗi. wani saurayi da ke zaune daga gefen su lokacin da suke maganar, ya yi saurin tare shi yana ce, "Alhaji don Allah ka kwantar da hankalinka. Idan ƴar ka ta ji an fasa auren ta ba zai mata ciwo irin ta ji cewa wani abu ya sameka ba. Zauna Alhaji." Ya ƙarasa yana zaunar da daddy."

"Ɗan saurayi ba za ka gane me na ke ji ba. Na rasa ta yaya zan faɗawa Zahra wannan mummunar labarin. Yarinyar nan ta sha wahala, duniya na zargin ta akan ta ƙi yin aure, a lokacin da muke tunanin komai ya zo ƙarshe, sai wannan ƙaddarar ta afku." Daddy ya faɗa cikin hawaye."

"Alhaji ka daina kuka. Idan ka amince, zan auri Zahra don na wanke ta daga zargi na kuma fitar da kai kunya."

"Kai wanene? Kuma me ya sa zaka yi haka? Me yasa kake tunanin cewa zan aurar maka da ƴata sukutun ba tare da na san ko waye kai ba, ba tare da amincewar ta ba, ba kuma domin kana sonta tana sonka ba, sai don taimako da tausayi."

"Alhaji idan har ƴar ka mai biyayya ce ba za ta ƙi auren nan ba. Soyayya kuma wannan zai zo daga baya, a lokacin da aka yi auren muka zauna tare a cikin gida ɗaya na tabbata soyayya zai ƙulu, ai shi so gina shi ake yi. Maganar sani na kuma, zan bayyana maka komai. Ga ID card dina, zaka samu dukan basic information akaina a ciki, sauran bayanai kuma zai biyo bayan auren idan ka amince."

Alhaji ya karɓa ya duba. Ya ce, "Kana ganin iyayenka za su amince?"

"Babu matsala. Mahaifina ya rasu. Mahaifiyata kuma, daman ba ta da burin da ya wuce ta gan aure na, ta daɗe tana son na yi aure, don haka na tabbatar sai ta fi kowa farin ciki da wannan auren."

"Na gode sosai ɗan nan, Allah ya saka da alheri. Yadda ka rufa mana asiri, Allah ya rufe naka, Allah ya sa ku so juna da Zahra." Daddy ya rinƙa yi masa addu'a ido cike taf da kwalla.

"Aameen Baba. Mu tafi kar liman ya gaji da jira.