AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 24

by @jikargarba001

Alhaji Bashir ya koma masallaci, ya yi wa limamin bayani a takaice kan abinda ke faruwa. Baba Liman ya gyara zama, yana kallon Alhaji Bashir cikin kulawa ya ce, "Alhaji Bashir, ina ganin kawai ka yarda wa yaron, a daura auren da shi. Idan akwai wani abu da zai taso daga baya, sai mu bincika asalin sa da duk abin da ya shafe shi."

Alhaji Bashir ya jinjina kai cikin gamsuwa. "Shikenan Malam. Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi."

Daddy ne ya kasance wakilin Kassim. Aka daura auren Zahra da Kassim akan sadaki naira dubu ɗari, wanda shi Daddy ne ya biya.

Baba Liman ya gyara murya ya ce, "Alhamdulillah. Wannan aure mu ɗauke shi a matsayin wani darasi na rayuwa. Yanzu dai abinda yake akwai shine, kai Kassim, gobe da safe zamu zo mu gan iyayenka da kuma inda kake zama. Ba zai yiwu mu ɗauki ƴar mu, mu ba ka sakaka ba, ba tare da sanin asalin ka ba. Daga ƙarshe, muna godiya matuƙa da irin karamcin da ka nuna."

Ya juyo zuwa ga Daddy ya ce, "Alhaji, ya kamata ka je ka ji da jama'a. Allah ya daɗa rufa asiri, ya kara mana lafiya da zaman lafiya."

"Aameen Malam. Na gode sosai," Daddy ya ce, suna musabaha da Liman. Ya karbi lambar wayar Kassim don tuntubar sa gobe, sannan ya nemi da ya bi shi ɗaurin auren su Musharraf.

A waje kuwa, Musharraf da Abdul Hakim sun kasa fahimtar abin da ke faruwa a masallacin. Suna tsaye a gefen mota suna jiran Daddy. "Wai tsaya, yaushe sunan Jameel ya koma Kassim ban sani ba?" Abdul Hakim ya tambaya, yana bin Musharraf da ido.

Musharraf ya ja dogon numfashi. "Wannan sai Daddy ya fito zai mana bayani, domin wallahi I’m very confused right now."

Daga nan suka hango Daddy yana fitowa daga cikin masallaci yana gaisawa da mutane. Bayan gaishe-gaishe, Daddy ya karaso inda suke da Kassim a biye da shi.

"Mu tafi ko?" Ya tambaye su, yana kallon Abdul, wanda shine dreban su a yau.

Abdul Hakim ya shiga driver’s seat. Musharraf ya buɗe wa Daddy kofar baya ya shiga. "Shigo mana Kassim," Daddy ya fada, yana yafito Kassim da ke tsaye. Kassim ya karaso ya shiga motar. Musharraf ya bishi da kallo. "Could this be the Kassim?" Ya tambayi kansa. Abdul Hakim ya dubi Kassim ta madubi yana nazarin shi.

Musharraf ya rufe ƙofar ya koma gaba ya zauna. Abdul Hakim ya ja mota suka nufi masallacin da za a ɗaura auren Musharraf da amaryarsa Zainab. Kowa cikin natsuwa da tunani ya ke. Daddy na tunanin yanda zai fuskanci Zahra, Mommy da Iya kan yadda aka ɗaura auren Zahra da wani daban ba Jameel ba. Musharraf na tunanin dalilin da yasa mijin Zahra ya koma Kassim. Abdul Hakim kuma na mamakin sauyin mijin da aka samu all of a sudden. A ɓangaren Kassim kuwa, tun da suka karaso bakin mota, yake mamakin irin arzikin waɗannan mutane, ganin irin motar da suka shigo.

---

Alhaji Usman yana barin masallaci ya tafi gidan su Jameel direct. Tun daga bakin get ya ji maganar mata kan yadda aka fasa auren. Suna cewa yarinyar ce ke bin maza, shi yasa ta dade ba ta yi aure ba, shine ake son a cuce Jameel a cusa masa ita, sai Allah ya kiyaye. Ya nufi shashin Alhaji Dawood kai tsaye ba tare da ya amsa gaisuwar kowa ba. Yana zuwa bakin kofar, ya tura, ya tarar da ita a rufe. Ya ciro wayarsa ya kira layin Alhaji Dawood, amma babu amsa. Har ya juya zai tafi sai ya ji kamar ana buga ƙofa ta ciki. Ya kara jin kunnensa, ya tabbatar da ana buga kofa.

Zagayowa yayi ta bangaren windo, ya hau wani dutse ya ɗan buga glass ɗin yana cewa, "Waye a ciki?"

"Ni ne, Dawood," ya ji muryar ƙanin sa daga ciki.

"Dawood lafiya ka ke buga ƙofa haka? Ka rasa key ne?"

"Key ɗin na wajen Saudatu. Ita ta rufe ni daga waje ta tafi da key."

"Ban gane ba, ita Saudatu din tana da taɓin hankali ne?"

"Wata kila."

"Barin aika a kirawo ta," Alhaji Usman ya ce yana zagayowa. Ya kira wata yarinya daga gaban shashin.

"Kin san Maman Jameel?"

"Eh na santa."

"To ki je ki ce mata Yaya Usman na nemanta."

"Toh," yarinyar ta ce. Ta kwasa a guje. Wajen da ta gan mata sun taru ana rabon abinci ta tsaya.

Ta ce, "Ana neman Maman Jameel "

"Waye ya ce ki kira ta?" Murja ƙanwar Jameel da ke cikin masu rabon abincin ta tambayeta

"Wani mutum ne. Wai na ce Yaya Usman."

"A ina yake?"

"Can kusa da furanni."ta faɗa ta nuna mata part ɗin Alhaji Dawood da aka ƙawata gaban da flowers masu kyau da ɗaukar ido.

"To kije ki ce tana zuwa."

Yarinyar ta koma ta isar da sako. Murja, kanwar Jameel ta shiga dakin inda ta tarar da Mommy ta yi tagumi, tana tunani halin da Jameel zai shiga ta dalilin fasa auren nan.

"Mama ki daina tunani haka, kar ki janyo wa kanki ciwo."

"Ba za ki gane bane Murja. Halin da Jameel ke ciki ya dame ni."

"Na ɗan lokaci ne, duk zai wuce. Yanzu dai Baba Usman na waje yana jiranki, a ɓangaren Daddy."

"A bangaren Alhaji?"

"Eh. Daga waje."

"To dauko mini mayafi a wardrobe."

Murja ta miko mata mayafin, ta fita daga ɗakin, ta koma bakin abinci. Hajiya Saudatu ta yafa mayafi, ta ɗauki key da wayar mijinta ta fito.

A tsaye ta tarar da shi ya goya hannu a baya yana zagaya wajen a hankali.

"Assalamualaikum Yaya."

"Wa’alaikumus Salam. Bani key ɗin."

Ta mika masa key ɗin kamar wacce aka kama da laifi. Ya karbi key ya buɗe kofa.

"Ki shigo," ya ce.

Ta biyo bayansa suma-sumai. Ya mika mata bunch na key, ya ce, "Ungo, je ki bude ɗakin da kika rufe ɗan ki."

Mommy ta kalli Yaya Usman da mamakin, ta yaya ya san ta rufe mutum a ɗakin. Amma ba ta da zaɓi, ta karɓi key din, ta bude kofar dakin. Alhaji Dawood ya ɗauki rigarsa da ke kan gado ya dora akan singlet ɗin jikinsa, ya raɓa ta gefen ta ya fita daga dakin, ba tare da ya ce da ita uffan.

A falon suka zauna. Alhaji Dawood ya ce, "Yaya ina wuni? Ya kukaji da jama’a?"

"Lafiya. Yanzu dai kafin jin dalilin rufe ka a ɗaki, na fi son jin dalilin fasa auren."

Dawood ya ce, "Fasa aure kuma? Ai ba a fasa aure ba."

"Ban gane ba? Kai fa ka ce a fasa auren. Na kira ka baka dauka ba. Na kira Jameel shima bai ɗauka ba. Sai Saudatu ce ta ɗauka ta ce kun fita tare. Da haka na ce a fasa, kada Jameel ya zo ya wulaƙanta ƴar mutane, tunda gashi har ya fara ƙi tun yanzu. Amma Ka sani, wannan abin da ku ka yi, ka zubar da darajata a gaban Alhaji Bashir."

"Innalillahi... Tabbas idan har mutum ya yi rashin sa'ar mata to fa kana cikin bala'i. Yaya wallahi Saudatu ce ta kitsa komai. Ni ma ban san me ke faruwa ba. Ina shirin fita ne ta zo da maganar fasa aure saboda wani bidiyo na zahrar da aka turo mata. Na nuna rashin amincewa, na shiga wanka, sai kawai ta dauki wayata, ta rufe ni, ta tafi."

Alhaji Usman ya juya ya kalli Saudatu, with all strictness ya ce "Ke ce kika mini tura saƙon a fasa aure?"

"Eh... Ni ce. Ka yi haƙuri."

"To kin kyauta. Dawood..."

"Na’am Yaya."

"Yanzu za mu tafi gidan su Zahra, mu nemi afuwa, a ɗaura auren, saboda wallahi yanayin da Alhaji Bashir ya shiga da nace masa mun fasa auren, babu kyaun gani, na tausaya ma shi matuƙa,but I have nothing to do, tunda wakilta Ni aka yi. Wanda ya wakilta ni kuma ya ce ya fasa ."

Saudatu cikin karancin murya ta ce, "Don Allah a basu haƙuri amma kar a ɗaura auren nan. Wallahi Yaya saboda ba ka gan bidiyon bane, ya munana sosai fa."

"Yi min shiru! Ko da a zahiri na gan ta da wani, sai an ɗaura. Wannan lokacin ba na bincike bane. Me ya hana ki bincikar halayen ta tun farko?"

Alhaji Dawood ya ce, "Yaya na yi bincike. Duk inda aka ce zan je, na je. Yarinyar da kyaun sheda na sameta. Sai dai wasu mata ke zarginta ba tare da hujja ba. Wannan dalilin ya sa da ta zo min da maganar bidiyon na ƙi a fasa auren, saboda na san zai iya kasancewa ɗaya daga cikin kurakuren ta na baya wani ke son ya using don wargaza wannan auren wataƙila, it might even be a setup, amma ta ƙi saurarata."

"To shikenan. Dawood ka kwantar da hankalinka. Nima na yi bincike akan yarinyar, kuma na tabbatar da tarbiyyar ta. Yanzu dai kira shi Jameel ɗin mu koma gidan su before it's too late. Ke kuma Saudatu ki jira hukunci na a gare ki.