AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 28
Bayan Abdul ya bude taro da addu’a, falon ya dauki shiru. Kowa ya nutsu, zuciya cike da jiran jin dalilin wannan taron.
Iya ta kalli Alhaji Bashir da yake zaune shiru a gefenta ta ce,
“Bashir, kayi magana mana. Ka tara mu, ka bar mu cikin zullumi.”
Numfashi mai nauyi Alhaji Bashir ya sauke.
“Iya, ban san yadda zan fara ba.”
“Ka fara dai, ko ta yaya ne,” Iya ta ce.
Ya gyara murya, sannan ya fara;
“Bismillah, da farko, zan tunatar da mu abinda duk muka sani. Mu bayin Allah ne, kuma bamu da iko da kanmu face abinda Mahaliccinmu ya tsara mana. Don haka mu kasance masu karɓar kaddarar mu hannu bibbiyu, sannan mu yi fatan hakan shi ne mafi alkhairi, koda kuwa ba haka muka so ba.”
Shiru kowa yayi, yana sauraren sa cikin nutsuwa. Ya ɗan tsaya na wasu daƙiƙai, kafin ya ci gaba;
“Zahra, ki kara hakuri da yadda rayuwa ke ta juyawa a kanki. Ki sa a zuciyarki cewa duk alkhairi ne, wataƙila ma wata hanyar ɗaukaka ce, In Sha Allah. Kar kiyi tunanin wani mutum ko wani aljani ne ke sa miki hannu. A’a, jarabtar imanin ki ne Allah yake yi. Don haka ki daure, ki cinye wannan jarabawar.”
Musharraf da Abdul ne suka riga suka fahimci inda maganar ta dosa. Sauran mutanen falon suka bi Alhaji Bashir da kallon mamaki, tamkar suna tambaya da ido.
Mommy ta fara jin wani irin tashin hankali, tun ma kafin ta san me ya faru da Zahra a wannan karon.
Zahra kuwa, shiru tayi, ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsunta, zuciyarta na jiran taji me kaddara ta zo mata da shi a wannan lokaci.
“Zahra…” Daddy ya kira.
“Na’am, Daddy,” ta amsa a hankali, cike da nutsuwa, ba tare da wani alamar tsoro a fuska ba.
“Na yanke wani babban hukunci a rayuwarki ba tare da neman izinin ki ba. Ina fatan zaki yafe min, ki kuma yi min biyayya.”
“Daddy, kana da damar ka yanke kowanne irin hukunci a rayuwata, ba tare da sanina ba. In Sha Allah, zan kasance mai biyayya gare ka har karshen rayuwata.”
“Allah ya yi miki albarka. Ya baki ‘ya’ya masu yi miki biyayya fiye da yadda kika yi mini.”
“Ameen, ya Rabbi,” ta amsa.
Iya ta katse da cewa; “Bashir, ka faɗa mana me ya faru. Wallahi na fara tsurewa.”
“Na aurar da Zahra ga wani bawan Allah mai suna Kassim, lokacin da iyayen Jameel suka zo mini da labarin cewa Jameel ya fasa auren Zahra,” Daddy ya faɗa hankali, kamar bai son faɗin.
“Ban gane ya fasa aurenta ba…” Iya ta tambaya, cikin rashin fahimta.
Sai Alhaji Bashir ya yi musu takaitaccen bayani akan yadda a ranar ɗaurin aure aka rasa waliyin ango, shi da kansa ya fita neman sa, har ya gano Alhaji Usman ya fice yana waya… sannan komai ya canza.
“Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’un! Bashir, sai ka aurar da ɗiyarka ga wanda baka ma san ko waye ba? Wannan wane irin rashin tunani ne?” Iya ta faɗa cikin masifa.
Sunkuyar da kai Alhaji Bashir yayi. “Iya, ban da wani zaɓi a lokacin. Na aurar da Zahra ne da fatan zata samu sassauci daga wannan ƙuncin rayuwa da ke biyo bayanta lokaci-lokaci. Sau da dama muna jin aure na iya zama maganin matsaloli idan an dace. Ku taya ta da addu’ar dacewa.”
“Kar ka gaya min wannan maganar banza! Ta yaya za ka aurar da yarinya da wanda ba son shi take yi ba? Ai da hakan gwara ta zauna babu aure!”
“Iya, kiyi hakuri. Amma a ganina wannan shine daidai a irin wannan yanayi. Ki kalli irin tsangwama da ake mata akan batun aure. Idan kuma aka kara jin an fasa aurenta a ranar aure, me kike tunanin zai faru? Ban ma yarda da yaron nan ba har sai da na ga ID card dinsa, na san gurin aikinsa, muka je har gidansu tare da Liman. Mahaifiyarsa ta amince, ta kuma yarda cewa wannan ne kaddarar su. Akan me mu baza mu yarda da wannan ƙaddarar ba?”
Iya ta karkada kai cikin takaici. Falon ya sake yin shiru.
“Ka koma gidansu yaron, ka karbo takardar sakin jikata, domin ban aminta da auren nan ba,” Iya ta dage.
“A’a, maganar saki bata taso ba,” Baaba Tani ta shiga maganar.“Tunda an riga da an ɗaura aure, a bari idan Zahra ta ga zata iya zama da shi, a barsu. Amma sai a rinƙa sa musu ido sosai.”
“Yo, hauka Zahran take da zata yarda ta zauna da shi? Ai ko da kika ji tace zata yi biyayya bata san cewa wannan zancen tebur ba giya ba ne” Iya ta dage.
"Da dai an kuma tambayarta."
“Ke Zahra, kin amince da wannan auren?” Iya ta tambayeta tana wani zazzare mata ido
Zahra bata ɗago ba tace. “Kamar yadda na faɗa tun farko, zan zama mai biyayya ga mahaifina. Na san ba zai cutar da ni ba.”
“Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un! Zahra, baki da hankali ne? Baki san yaron ba fa!”
Zahra ta ɗan yi murmushi na ƙarfin hali. “Iya kenan, zan iya zama da shi. Ke ma ai kika ce baki san mijinki ba sai da aka kaiki ɗakinsa, amma kika zauna, me yasa kike tunanin Ni ba zan iya ba?.”
Mommy ta fashe da kuka. Anty Salima ta rungume ta tana lallashi.
“Yauwa, Amina, kar ki yarda a yi wannan lalaci da ke,” Iya ta ce tana share kwalla.
Mommy ta girgiza kai cikin kuka. “Bani da zaɓi, Iya. Abinda ya faru ya riga da ya faru. Fata na shi ne Allah ya ba ta salama a gidan aurenta , kuma wannan ya zama karshen wahalarta.”
Iya ta yi iya kokarinta don ganin a soke auren, amma kowa ya ƙi yarda. A karshe ta tashi a fusace ta bar falon.
Daddy ya sa aka rufe taron da addu’a, sannan ya bi bayan Iya.
Zahra ta biyo Mommy ɗaki. Ta na so tayi kuka amma hawayen sun kafe. Zuciyarta na zafi, makogwaronta daci, duniya na juyawa.
Mommy ta matso kusa da ita cikin kuka. “Zahra, In Sha Allah wannan aure alkhairi ne. Saboda biyayyar da kika yi wa mahaifinki, Allah ba zai taɓa barin ki haka ba.”
Zahra ta yi murmushi kawai ta kwanta a cinyar Mommy tana sauke numfashi. Anty Salima, Farhana, da Anty Ramlat suka rika bata baki suna lallashi.
Musharraf ya tsaya a gefe yana kallonta, zuciyarsa cike da tausayawa. Daga ƙarshe ya juya ya fita zuwa falo, shiru kawai ya zauna.
Bayan kusan awa guda Daddy ya fito daga ɗakin Iya. Da kyar shi da Baaba Asabe suka shawo kanta ta amince da auren. A falo ya tarar da Musharraf da Abdulhakim suna zaune, kowannensu cikin zurfin tunani.
“What are you still doing here?” ya tambaye su.
Shiru suka yi duka.
“My friends, ku tashi ku tafi gida. Kun bar ƴaƴan mutane a gida, kun zo kun zauna a nan.”
Musharraf ya ce
“Zan tafi da Zahra, please.”
“No. Zahra will be here with us. Ku wuce gida.”
"Daddy, kayi hakuri. Zan tafi da ita. Wallahi Gobe da sassafe zan dawo da ita.”
"A’a, Musharraf—”
A nan suka ji sawun tafiya. Zahra ce ke sauka daga matakala a hankali, tana tafiya kamar mai shirin faɗuwa. Farhana na biye da ita tana rike da hannunta. Daddy ya yi saurin karasawa ya tallabe ta.
“Baki kwanta ba? Me kike so?”
Murmushin karfin hali ta yi tace;
" I just want to be with Yaya.”
Daddy ya tsaya yana kallonta. Ya san irin bond ɗin dake tsakaninta da Musharraf, irin wannan soyayyar ’yan uwa ba kasafai ake samu ba. Ya san dalilin da yasa yake kaucewa buƙatar Musharraf na tafiya da ita gidan sa—don kada su shiga haƙƙin matarsa, amma yanzu, bai da zaɓin da ya fi barin ta tafi da shi.
“You can go with her,” Daddy ya ce a karshe. Ya shafa kanta. “Take care of yourself, dear.”
Ya juya ya haura ɗakinsa, zuciyarsa cike da nauyin tunani.
Farhana ta ce;
"Zan bi ku, please.”
"Jeki ki dauko mata hula, sai mu tafi,” Musharraf ya amsa.
---
A gidan Musharraf
Suka sauka a wani daki kusa da na Zainab. Musharraf ya shiga kitchen tare da Zainab suka haɗa mata watermelon juice mai sanyi.
Suka turo kofar dakin, suka tarar da Zahra kwance akan darduman da tayi sallah, ta sa pillow ta jingina, idonta a lumshe, Farhana na yi mata tausa.
Zainab ta kalle ta cikin tausayi, tace;
“Zahra, tashi ki hau gado, kar sanyin tiles ya miki illa.”
Shiru tayi mata. Zainab ta matsa kusa da ita tana ƙara faɗin;
"Tashi mana.”
A hankali ta bude ido, ta kalli hannun da Zainab ta miƙa mata, kafin a hankali ta dora nata kamar mai tsoron taɓa wuta. Zainab ta miƙar da ita zuwa bakin gado.
Musharraf ya zauna kusa da ita, ya mika mata glass.
"Drink.” ya furta a hankali.
Kai ta girgiza tace;
"Bakina babu daɗi.”
“Daurewa zaki yi. Please, drink.”
Ta karɓa a hankali, ta kurɓa kaɗan, ta mika masa sauran. Ya mika wa Zainab. Sai ya kwantar da kanta a kafadarsa, yana bubuga shoulder ɗinta a hankali;
"Cry, Zahra.”
“Ban son nayi kuka. I’m tired of being weak. I want to be strong.”
"Who told you only weak people cry? Even strong people cry. The difference is; weak people cry and crumble, while strong people cry and rise up with more strength.”
Da wannan, ta fashe da kuka mai sauti, kamar dama tana jiran kalmar. Farhana da Zainab suka tsaya suna kallonta cike da tausayawa, Musharraf na patting ɗinta har ta gama. Ta kai mintina talatin tana kuka, da kanta tayi shiru ba tare da wani yace tayi shiru ba,.
'Yaya, na yarda da kai amma kayi min karya… why did you lie to me?”
“I’m sorry, princess. Dole ce tasa. Na san ba Jameel ne mijinki ba, amma Daddy bai bani damar sanar da ke ba.”
Shiru. Sai ta tambaya a hankali:
"Anya akwai farinciki a ƙaddarata?”
“Don’t say that. InSha Allah akwai, kuma na dindindin. Just remain strong for now. Princess are you sure kin amince da auren nan ko dai kawai tirsasa kanki kike yi?"
"A shirye nake nayi wa Daddy biyayya duk da ban san shi Kassim ba. No matter who he is, I will stay with him.”
"Na taba ganin shi. He doesn’t look bad,” Musharraf ya ce.
Ta daga ido ta ɗan yi masa kallon tambaya. Kai ya gyaɗa mata, yace;
"Na gan shi ranar ɗaurin aure. Mu muka sauke shi gida. Fine young man, dogo, baki… I’m sure you’ll like him.”
Kai kawai ta jingina kan kafadarsa, idonta a lumshe.
"Bacci kike ji?”
Kai ta gyaɗa. Ya ce wa Zainab;
"Haɗa mata ruwan zafi ta watsa.”
Bayan ta fito daga wanka ta saka nightie da Zainab ta kawo mata, ta sha paracetamol, ta kwanta. Farhana ta kwanta daga gefenta tana shafa kanta. Zainab ta musu “Sai da safe,” ta kashe wuta.
---
A gidan Inna Wuro
Drama yake tashi. Kassim ya nace zai koma wajen iyalinsa saboda matarsa ta dame shi da kira, yaro ba lafiya. Duk yadda Inna Wuro ta roƙe shi ya dakata har aikin ya kamala, ya ƙi. Ta kira Hajiya Turai ta sanar da ita abinda ke faruwa. Turai ta tura musu part-payment ɗin aikin su, ta ce ya aika wa matarsa domin ta kai yaron asibiti, sannan ya ƙara haƙuri, sati ɗaya saura komai ya kammala.
Da kyar suka shawo kansa. Amma Inna Wuro na ta masifa;
“Wallahi, ita dai Laure duk hanyar samun arzikin ka ita ke toshewa. Idan ba haka ba, me zai sa tayi ta kiran ka wai yaro bai da lafiya, kamar kai ɗin zaka iya ba shi lafiya, duk tabi ta dame ka bayan ta san neman kuɗi ka fito! Allah ya wadaran hali irin nata.”
Shi dai Kassim bai ce komai ba, sai ci gaba da latsa wayarsa da yayi