AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 32
Ja da baya ta fara yi da sauri, shi kuwa yana binta har ta kai bakin gado. Da sauri ta miƙe tana shirin sauka daga kan gadon, sai kawai ya fizge ta, ta faɗa jikinsa. Ya riƙe ta da ƙarfi.
Cikin ɓacin rai tace;
“Menene haka?”
“Haƙƙin aure.” Ya amsa kai tsaye.
Tana buɗe baki za ta yi martani, sai kawai ya sanya bakinsa cikin nata, ya fara kissing ɗinta da ƙarfi. Zahra ta fara ƙoƙarin kwace kanta. Da ƙyar ta samu ta kwace bakinta daga nasa, ta yamutsa fuska cikin ƙyama da mamaki. Bata gama processing abinda ke faruwa ba, ya sake juyar da ita ƙasa, shi kuma ya hau kanta. Ya dannata da nauyinsa yana ƙoƙarin sake haɗa bakinsu, amma ita ta haɗe haƙoranta gam-gam. Da haka ya saki bakinta, sai ya kai hannunsa ya fara wasa da boobs ɗinta. Cikin razana ta fashe da kuka.
Amma shi bai ji kukan nata ba, burinsa kawai ya biya buƙatarsa da ita. Duk da ƙoƙari, kuka, da yunƙurin kare kanta, Kassim ya cire mata rigar bacci. Zahra ta rufe kirjinta tana kuka sosai. A zuciyarta ta san abin da yake shirin yi ba laifi ba ne, amma ba ta shirya ba. Tsoro da fargaba ne suka mamaye ta.
Kassim ya kai maƙura wajen bukata, ya kasa haƙuri. Yana ta romancing ɗinta da ƙarfi kamar rayuwarsa tana rataye a kan hakan. Zahra ta yi ƙoƙarin ƙwacewa, ta gaji. Daga ƙarshe ta miƙa wuya.
Ya ci gaba da kissing nata a hankali, yana neman hanyar shiga. Amma a ƙarshe sai abin ya gagara. Ya daina ya juya ya ɗauki wayarsa, ya duba, yana mamakin yadda ɗan mintuna da suka wuce jikinsa yake da ƙarfi, amma yanzu kuma shiru, kamar jiƙaƙen tsumma.
Ya yi ƙoƙari sosai ya sake farfaɗowa amma abin ya faskara. Zuciyarsa na matuƙar ƙonewa, ciki na murɗawa. Har kuka Kassim ya yi a wannan dare. Bai runtsa ba, yana ta juye-juye, riƙe da mararsa. Zahra ma bata iya bacci ba, tsoro da damuwa suka mamaye ta.
Da safe bayan sallar Asuba ya sake gwadawa, amma shiru. Zahra ta lallaɓa ta yi sallah, shi kuwa bai iya tashi ba. Ganin irin wahalar da yake ciki har ta fara jin tausayinsa sosai, tana jin kamar ta amince masa kawai, amma duk da haka abin ya gagara.
Misalin tara na safe, Kassim ya rarrafa da kyar zuwa ɗakin Laure. Ya ce ta bashi paracetamol. Laure ta kalle shi cikin mamaki;
“Subhanallah, Kassim, ita matar taka ce ta jefa ka cikin wannan halin?”
“Don Allah ki bani paracetamol, zan mutu.” Ya ce cikin wahala.
Ta bashi maganin da ruwa. Bayan ya sha, ya kwanta. Laure ta fara shafa masa kai a hankali, har zuwa bayan kunnensa da gemu. Nan take jikinsa ya amsa, ya janyo ta jikinsa, ba tare da wata soyayya ba ya far mata. To amma abin da ya gagara a wajen Zahra, sai ya yi nasara da ita nan take.
Ran nan gaba ɗaya Kassim ya wuni cikin tunani. Bai taɓa fuskantar irin wannan ba a rayuwarsa. Har ya tafi wajen likita, aka ce babu matsala da shi. Sai ya ƙara zuwa wajen masu yin jiƙo wa maza a kasuwa, ya sha har kofi biyu. Amma zuciyarsa ta kasa hucewa, tunani Zahra kawai yake yi.
Daddare, abin ya sake maimaituwa. A wajen Zahra ya kasa, amma a wajen Laure sai ya yi.
Bayan ya yi wanka ya zauna bakin gado ya riƙe kansa, cikin damuwa. Laure ta zauna a gefensa ta ce;
“Kassim, gaya min gaskiya, ko dai matarka ba ta da lafiya ne? Saboda sai dai ka kunnu a dakinta, sai kazo wajensa ka sauke.”
“Babu ruwanki! Ki bar ni da damuwata.” Ya ce cikin haushi.
Laure ta tabe baki; “To, idan tayi wari zamu ji.” Ta tashi ta bar ɗakin.
A bangaren Zahra kuwa, ta kasa gane me ke faruwa. Duk tunaninta shi Kassim yana tausayinta ne ya bar ta. Hakan yasa zuciyarta ta fara cike da nadama da baƙin ciki, ganin irin halin da yake shiga a sanadiyar ta.
---
Back to Kaduna…
A Kaduna kuwa, hankalin Mommy ya tashi ƙwarai ganin babu labari daga Zahra. Wayarta ba ta shiga, lambar Kassim ma da ya bawa Daddy ta daina shiga. Har suka tafi gidan Inna Wuro, amma maƙwabta suka ce kwana hudu da barin unguwar.
Mommy ta shiga damuwa sosai, kullum cikin kuka da addu’a. Anty Salima da Musharraf suke ta kwantar mata da hankali, duk da su ma zuciyarsu cike take da damuwa.
Iya ce ta bada shawara a je Lagos domin a duba lafiyar su Zahra.
“Bashir, gaskiya bai kamata ya wuce gobe ba. Kana ganin halin da Amina ke ciki? Gaskiya gwara a je can ɗin a duba ko suna nan lafiya, ko hankalin mu zai kwanta.” Ta ce wa Daddy.
“In sha Allah, gobe zasu tafi. Har Musharraf ya yi musu booking flight.” Daddy ya ce.
“Yauwa, wannan ya fi.”
Washegari da sassafe Musharraf da Anty Salima suka shirya tafiya, kasancewar flight ɗin bakwai na safe zasu bi. Farhana ta kai su airport tana addu’ar Allah ya sa suji alkhairi.
Da suka sauka Lagos, suka ɗauki motar haya zuwa gidan da Zahra da Kassim suka sauka. Amma suna zuwa suka tarar da gidan a buɗe, ana gyara.
Musharraf ya tambayi ma’aikatan wajen, suka ce maigidan bai dade da barin wurin ba. Ya roƙe su su bashi lambar wayarsa. Suka bashi, sai ya kira.
“Hello, Kassim?”
“Who be Kassim? Na Babatunde dey talk.”
“Babatunde kuma?” Musharraf ya yi mamaki.
Mutumin ya yi tsaki, ya kashe waya.
Anty Salima ta kalle shi: “Yaya, me yace?”
“Yace ba Kassim bane, wai Babatunde.”
“Babatunde kuma? To baka faɗa musu lambar Kassim zasu baka ba?”
“Na ce su bani lambar maigidan, shine suka bani wannan.”
“Eh, to gidan haya ne. Wannan Babatunde ƙilla shi ne mai gidan. Ka sake kiran shi, ƙilla zai ba mu bayani.”
Musharraf ya sake kira, da ƙyar ya samu mutumin ya saurare shi. Da Turanci suka yi magana. Babatunde ya ce;
“Wannan Kassim, ai hayar wata daya kawai ya kama. Bai ma kai wata ɗayan ba, kwana biyu kacal yayi ya bar gidan nan. Kayansu ma ni na kira dillaliya ta saye, na tura masa kuɗinsa.”
Musharraf ya ce cikin tashin hankali; "Please, zaka iya tura mini account lambar da ka aika masa kuɗin?”
“Wallahi wayata an sace jiya a beer palour.”
“Not a problem, zaka iya je bankinka ka ɗauko statement, account number zai fito.”
“Oga, why you dey find am like this? I no trust you. A POS ma na aika kudin.”
Duk yanda Musharraf ya yi, mutumin ya ƙi bada haɗin kai. Daga ƙarshe ma ya kashe waya.
Musharraf ya ce cikin damuwa; “Anty, mutumin nan baya son taimaka mana. Gaskiya abu mafi kyau mu koma Kaduna a tracking lambar su. Idan mun koma sai mu faɗa wa Mommy cewa mun ga Zahra, tana lafiya, kawai wayoyinsu ne aka sata wajen charging.
___
Bayan sun dawo Kaduna, suka faɗa wa Mommy daidai yadda suka tsara tun daga Lagos. Amma a daren ranar Musharraf ya tafi wajen Daddy ya ba shi cikakken bayani kan gaskiyar abin da ke faruwa. Hankalin Daddy ya tashi ƙwarai, ya fara tunanin ko lafiya suke kuwa.
Ya shiga ɗakin Iya ya same ta, ya sanar da ita abin da ke faruwa, sannan ya ce ma ta, sun ɓoye wa Mommy gaskiya.
Iya ta girgiza kai cikin alhini ta ce;
“Ai ɓoye mata shi ya fi alheri. Idan ba haka ba, wallahi zuciyarta za ta iya fashewa. Wannan lamari kuwa tashin hankali ne, ace yarinya daga tarewa sai shiru. Wallahi, Bashir, kar ka so ka ji yadda zuciyata ke min nauyi.”
Daddy ya ce;
“Ki kwantar da hankalinki Iya. In sha Allah gobe zamuje a tracking lambar wayar Kassim ko landlord ɗinsa, domin gaskiya nima na fara jin shakku a raina.”
“Don Allah Bashir, kar ku yi sanyin jiki. Ku tausayawa Amina ku yi duk abin da ya dace da wuri.”
“In sha Allah.” Daddy ya amsa.
---
Washegari, Daddy da Musharraf suka shiga yawon ofisoshin tracking a Kaduna. Amma duk inda suka je, labari ɗaya ne; ba za a iya tracking ɗin lambar ba saboda sim ɗin ba ya cikin waya.
Wannan ya sa hankalinsu ya tashi sosai. Zuciyar Daddy ta fara zargin ko dai an yi kidnapping ɗinsu ne. Amma idan haka ne, to me ya sa Inna Wuro ta tattara ta bar gidan? Kuma me ya sa Babatunde ya ƙi basu haɗin kai har ya cire sim ɗinsa daga waya?
Daddy ya share zufa ya furta cikin tashin hankali;
“Ya Allah, Ka kare min Zahra a duk inda take.”
Abin da suka ɗauka da wasa, ya fara zama gaskiya. Har sati ɗaya ta shige babu kira daga wurin su Zahra, ko an kira su lambar ba ta shiga. Tun suna ɓoye wa Mommy, har daga baya Daddy ya ga dacewar ya sanar da ita, saboda ta ƙara sa ɗiyarta cikin addu’a.
A ranar da suka cika kwanaki goma sha biyar ba tare da jin wani labari daga Zahra ba, Daddy ya faɗa wa Mommy duk abin da ke faruwa. Da farko Mommy ta fashe da kuka, ta shiga damuwa sosai. Amma daga baya sai ta miƙa lamarin hannun Allah. Wannan kuwa saboda Daddy da Musharraf kullum suna ta lallashinta, suna tuna mata da ayoyin Qur’ani kan tawakkali.
Anty Salima, wadda ta kasa komawa gida ta bar ‘yar uwarta cikin wannan hali, kullum tana tare da ita tana kwantar mata da hankali. Farhana ma ta shiga cikin damuwa. A kowane lokaci addu’a suke, suna roƙon Allah ya tsare Zahra a duk inda take.
---
Wasa-wasa, har wata ɗaya babu wani labari mai kyau. Wannan yasa wata safiya Iya ta yanke shawarar komawa ƙauyensu, ta nemi a yi addu’a, ko ma a faɗa mata inda Zahra take.
Da sassafe Musharraf ya shigo gidan don duba Mommy. A falo ya tarar da Daddy zai shiga ɗakin Iya. Suka shiga tare.
Iya na zaune tana haɗa kaya, suka shigo. Da mamaki Daddy ya ce;
“Iya, ina za ki ne kike haɗa kaya haka?”
Ta ɗan share hawaye ta ce;
“Bashir, ai ban ji daɗin zama ba. Wata guda kenan babu wani labari daga Zahra. Dukkanmu mun san babu lafiya, domin da lafiya ƙalau Zahra ba za ta yi mana shiru haka ba saboda tayi aure. Yanzu haka zan koma Kunya, in sa Mallam Hamisu ya yi mata addu’a, ko kuma ya faɗa mana inda take. Sai mu tafi mu same ta.”
Musharraf ya kalle ta cikin mamaki, ya ce;
“Haba Iya, yanzu saboda wannan jarabawar da Allah ya kawo mana ne za mu kasa ɗauka? kwata-kwata fa yau wata ɗaya ne kawai rabonmu da Zahra, ba shekara da shekaru ba. Wata ƙila ma tana nan lafiya, wani dalili ne yasa muka ji ta shiru. Amma fa ba wai sai mu faɗa shirka akan wannan ƙanƙanin gwaji ba.”
Iya ta yi tsaki, ta ce da masifan;
“Kai Musharraf, ka yi min shiru! Wallahi ko uban ka Bashir bai isa ya ce min me zan yi ba balle kai. Kai ma, da gaske kana son Zahra kuwa?”
Musharraf ya yi shiru, sannan ya ce a hankali;
“Iya, ina son ki gane cewa wannan lamari bai kai ga sai mun je wajen malamai ba.”
Iya ta banka mishi haramta, tace;
“Idan na tashi tafiya ka tare kofa, sai na san wuyanka ya isa yanka.”
Ta ci gaba da haɗa kayanta cikin jaka. Bayan ta gama ta kalli Daddy ta ce;
“Bashir, tashi ka kai ni tasha.”
Daddy ya miƙe yana cewa;
“Mu tafi.”
Musharraf ya ɗauki kayanta ya kai mota. Da ta fito sai ta tsaya a kan stair-case tana kiran Mommy;
“Amina! Amina! Ki sauko yau gardama ƙafan keyi bazan iya haurowa ba.”
Mommy ta sauko, ta tarar da Iya tayi shirin fita, har da mayafi.
“ Iya, fita za ki yi?” Mommy ta tambaya.
“Eh, gida zan koma.”
“Gida kuma?”
“Eh, can Kunya.”
Mommy ta ce cikin mamaki;
“Ina dai fatan ba wani laifi aka yi miki ba? Na ga kin ce sai nan da wata biyu za ki koma.”
Iya ta ce;
“A’a, babu wani laifi. Amma naga ya dace na tafi a nema mana mafita kan wannan shiru da muka samu daga Zahra.”
Mommy ta ɗan girgiza kai;
“Wacce irin mafita kenan?”
Iya tayi ƙasa da murya ta ce;
“Yau ɗin nan ina isa zan je wajen Mallam Hamisu. Ya faɗa min inda Zahra take, ko kuma ya yi mana addu’a Allah ya karkato da hankalinta ta dawo gida.”
Mommy ta ce a hankali;
“Iya, ni dai ina ganin addu’ar da muke yi ya isa. Kar mu je mu yi wa Allah shishigi.”
“Haba Amina, ke da nake tunanin kina da hankali! Wane irin shishigi kuma? Neman taimako a musulunci halal ne. Ke dai ki jira jin kyakkyawan labari.”
Mommy ta yi shiru, don tasan ko ta yi magana ba zata hana Iya yin abinda ta ƙudurta ba. Ta kalli Daddy da yake tsaye a falo, ta yi masa signal da ido akan ya yi ƙoƙarin hana Iya. Ya kaɗa kai kawai.
Iya ta ce;
“To Amina, dama na kira ki ne mu yi sallama. Don Allah ki cire damuwa a ranki, ki ci abinci, ki ci gaba da rayuwarki yadda kika saba. In sha Allahu zuwa gobe za ku ji kyakkyawan labari. Sannan kada ki yi wasa da addu’a.”
“In sha Allah. Bari na kira miki Salima ku yi sallama.”
Mommy ta haura sama ta kira Anty Salima da Farhana. Suka yi sallama da Iya, sannan ta ba su kwarin gwiwa cewa daga gobe komai zai zo ƙarshe.
Daddy ya kai ta har Kunya. Bai sauketa a tasha ba, ya kai ta har gida. Ya rinƙa roƙon Iya da ta bar maganar Mallam Jami'ai nan, da ta gan yadda yake ta roƙonta sai tace ta amince baza ta tafi kuma ba.
Amma da zarar Daddy ya juya, Iya ta ɗauki mayafinta ta nufi gidan Mallam Hamisu.