AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 37
This page is specially for you Hauwa Suleiman and your friend Zee Musa, Nagode da ƙarfafawar ku a gare ni.
Ƙarƙashin gadonta ta zare abin da ta boye, zuciyarta na bugawa kamar ta fito daga ƙirjinta. Da sauri ta leƙa, ta tabbatar babu wanda ya lura, sannan ta ƙarasa bakin ƙofar ɗakin waje. Hannunta na rawa, ta saka key ta buɗe ƙwandon ɗakin.
Zahra na kwance, jikinta ya yi sanyi, idanunta na ƙarewa saman rufin ɗakin, zuciyarta cike da firgici. Tunanin Kassim ke ratsa ta kamar wutar lantarki.
“Ke!” Muryar Laure ta katse mata tunani. Laure ta shigo cikin sauri, idonta na yawo cikin tashin hankali. “Tashi ki bar gidan nan kafin Kassim ya dawo! Wallahi idan ya same ki mun shiga uku!”
Zahra ta ɗago kai da sauri, zuciyarta ta buga. Laure ta ɗaga hannunta cikin zafin rai.
“Tashi! Kar ki tsaya kallona kin wani zuba min ido!” Ta kama hannun Zahra ta miƙar da ita da ƙarfi.
Ba tare da wata jinkiri ba Laure ta zaro ATM card ɗinta da wasu kuɗi guda biyu da ta kwaso daga aljihun wandon Kassim. Ta miƙa mata tana faɗin;
“Na rantse ban taɓa yi wa Kassim sata ba, amma yau dole nayi. Kuɗin nan ba zai ishe ki Kaduna ba, amma ki san yadda za ki yi. Ki fita daga wannan unguwar kafin wani tsautsayi ya dawo da shi gida.”
Zahra ta tsaya cak, zuciyarta cike da rikici da farin ciki lokaci guda.
Laure ta kama hannunta ta ja har bakin ƙofa. “Yi maza! Kar ki tsaya wani sokonci!”
Har Zahra ta fita sai ta dawo da gudu, ta rungume Laure tana kuka.
“Na gode, Laure! Ke ce ta ƙarshe a cikin mutane da zan taɓa tsammanin taimako daga gare ki. Allah ya saka miki da gidan Aljanna.”
Laure ta ja kanta da sauri, fuskarta a ɗaure.
“Lafiyarki kuwa? Ba za ki yi saurin barin gidan nan ba? Ko har yanzu ba ki gaji da wahala ba?”
Zahra ta share hawayenta da sauri.
“Yanzu zan tafi. Amma ki bani account number ɗinki, idan na isa gida za ki ji saƙo.”
Laure ta yi tsawa;
“Ke, Zahra! Ki rufa min asiri! Ki fita kafin Kassim ya dawo ya same ki nan.”
“To ga lambar wayata. Idan na samu na isa gida zanyi welcome back ɗon sim ɗina, ke dai ki kirani a duk lokacin da kika samu waya.” Zahra ta faɗa, tana karanta mata lambarta. Laure ta rubuta lambobin a ƙasa da gawayi, tana duba ƙofar shiga gidan zuciyarta na bugawa.
Zahra ta fita da sauri, tana daga wa Laure hannu, idonta cike da hawaye. Laure ta kwashe lambobin da biro, sannan ta wanke ƙasar da ruwa, zuciyarta na harbawa kamar ana buga ganga.
---
Da Zahra ta fita da lungu anguwar, ta tare taxi daga bakin hanya.
“Don Allah, ka kaini tasha,” ta ce cikin murya mai rauni.
Direban ya kaita, ta biya shi kuɗin ɗari biyar. A tashar, ta tambayi inda ake lodin motar Kaduna, aka nuna mata.
Ta roƙi direban ya ɗauke ta, za a biya shi idan sun isa Kaduna. Amma ya ƙi.
“Dan Allah ka yi haƙuri. Wallahi za a biya ka duk abin da ka faɗa idan ka sauke ni lafiya,” ta roƙa.
Direban ya kalleta da raini.
“Kin yi kama da wacce za ta iya biyan ko nawa na buƙata? Malama, matsa mini.”
Zahra ta juya zuciyarta na ƙara yin nauyi. Ta je motoci da dama, amma duk sun ƙi. Wani tunani ya faɗo mata; kira Musharraf!
Ta nufi wani direba ɗan Baba tsoho mai fuskar tausayi;
“Baba, don Allah ka ara mini wayarka. Zan kira gida su turo mini kuɗi, sai na cire nan in biya ka.”
Ya kalleta sosai, kamar yana nazarin gaskiyarta.
“Yarinya, ki yi haƙuri. Ban da kati a waya. Sai dai idan za ki sayo katin, sai ki kira su.”
“Eh zan sayo. A ina zan samu?”
Ya nuna mata wani shago a tsallaken titi. Zahra ta nufi wurin cikin gudu. Motar da take jira mutum ɗaya ta rage ya cika. Ta yi saurin tsallake titi…
GARRRBB!!!
Mota ta kwasheta da ƙarfi!
“INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!” Mutumin da ya bugeta ya fito da gudu, jikinsa na rawa.
Mutane suka taru. Zahra na kwance, jini ya rufe fuskarta, numfashinta na rauni. Wannan Baba da ya nuna mata shagon siyar da katin ya kawo tsumman zani, ya ɗaura a gurin da jinin ke zuba. Direban da ya buge ta ya tsaya cak kamar gunki, idanuwansa sun firfito.
“Oga! You don hit person, you just dey stand! Bring your car make una carry her go hospital!” wani daga ƴan tashan irin masu shaye_ahayen nan ya faɗa cikin tsawa.
Ɗayan wanda suke motar tare yayi sauri ya ƙara wajen, ya ɗauke ta da taimakon wasu, suka saka ta a bayan mota.
“Imam, shiga mota mu tafi asibiti!”
---
Suka isa wani babban private hospital a Ibadan. Likitoci suka karɓe ta cikin hanzari.
Sa’ud ya zauna a kujerar baranda, zuciyarsa na tafarfasa. Imam ya tsaya tsayin daka, hannuwansa a ƙugu, idanunsa na ƙasa cike da damuwa.
Bayan awa ɗaya, wani babban likita ya fito. Sa’ud ya ruga da sauri.
“Doctor, hope she’s alive?”
Likitan ya gyara gilashinsa, ya ce cikin nutsuwa;
“Tana da rai. Ku biyo ni zuwa office.”
Sa’ud ya dubi Imam. “Doctor wants to see us.”
Imam ya bi su cikin natsuwa. Rubutun DR. BOLAHUN ADEDIRAN ya yi ƙyalli a jikin ƙofar ofishin. Sa’ud ya zauna, Imam ya tsaya.
“You can sit, sir,” likitan ya ce.
“I’m fine here,” Imam ya amsa cikin muryar da ta yi ƙasa sosai amma cike da iko.
Likitan ya gyara zamansa.
“Mun yi nasarar ceton rayuwarta. Ta ji rauni mai zurfi a goshi, mun yi dressing ɗin raunin. Sai dai ta buga kanta sosai, ba mu san ko kwakwalwarta ta sami matsala ba, har sai ta farka.”
“Zan iya ganinta?” Imam ya tambaya kai tsaye.
“No, you can’t see her now,” likitan ya amsa.
“I have to,” Imam ya ce a hankali, ya zaro ID card ɗinsa ya nuna.
Likitan ya ɗan firgita, ya miƙe cikin girmamawa.
“Nice to meet you, sir.”
Bayan musabaha, ya raƙa su zuwa ɗakin da aka kwantar da Zahra.
---
Zahra na kwance cikin bacci mai nauyi, numfashinta na sauka a hankali. Kanta naɗe da bandeji, hannunta ɗaure da ƙarin jini. Imam ya matsa kusa, idanuwansa sun zurfafa kanta, zuciyarsa na bugawa da wani nauyi.
“She’s so beautiful… but so dirty,” zuciyarsa ta furta.
Ya taɓa wuyanta, yana jin zafin jikinta. Ya dubi likitan.
“Wane magani kuka bata na zafin jikin?”
“Allurar paracetamol muka yi mata, sir,” likitan ya amsa.
“Good. Ina so ku canza ta zuwa ɗaki mai kyau. Wannan ɗakin ƙarami ne, ba isasshen iska.”
“Ok sir.” Likitan ya fita don bada umarni.
Imam ya dubi Sa’ud, muryarsa na daɗa yin sanyi.
“Dole na sake jadawalin tafiyata saboda wannan.” ya faɗa pointing at Zahra
Sa’ud ya yi murmushi mai ɗaci.
“Tsautsayi ne, ba laifinta ba.”
“Da ta duba hanya, da ba haka ta faru ba.”
“Ko da ta duba, idan Allah ya ƙaddara, sai ya faru. Addu’a kawai muke yi Allah ya sa ta tashi cikin hayyacinta.”
“In sha Allah,” Imam ya ce cikin nutsuwa.
Ƴan mintoci kaɗan bayan haka, wasu nurses biyu suka shigo da gadon tura marasa lafiya. Suka ɗauke ta a hankali, suka fitar da ita zuwa wani ɗaki mafi kyau. Zuciyar kowa ta cika da fargaba da shiru.
A hankali aka turata zuwa wani sabon ɗaki—ɗaki mai girma da tsabta, wanda aka ware wa marasa lafiya masu matsayi. Wannan VIP room ɗin ya sha bamban da na farko; akwai cushion masu laushi, babban TV a bango, AC na busar da iska mai daɗi, da faffadar katifa. Ko bandaykin cikin ɗakin sheƙi yake cike da tsabta, yana ɗaukar ƙamshi mai sanyaya zuciya.
Imam ya zauna a kan ɗaya daga cikin cushion, hannunsa na riƙe da kansa wanda yake yi masa ɗan ciwo. Sa’ud ya zuba masa ido da damuwa.
“Lafiya?” ya tambaya.
Imam ya ɗan gyada kai, ya furta cikin kasala;
“Just a slight headache.”
“Allah ya sauwaƙa. Bari in kira matata ta zo ta zauna da ita, mu kuma mu tafi ka huta.”
Imam ya sake gyaɗa kai cikin gajiya.
---
Bai daɗe ba matar Sa’ud ta shigo asibitin, hannunta ɗauke da duk kayan da ake buƙata na jinya; abinci, ruwan zafi, toothpaste, sabulu, bargo, da sauran kayan amfani. Kyakkyawar mata ce mai shekaru kusan 26 zuwa 27, tana goye da yarinya ƙarama kyakkyawa wacce ta yi kama da ita sosai.
Ta nufi ɗakin kamar yadda mijinta ya kwatanta mata. Da sallama ta tura ƙofar ta shiga. Sa’ud yana zaune akan cushion, yana latsa waya, Imam kuma yana ƙoƙarin canza wa Zahra drip.
A’isha ta zauna kusa da mijinta, yarinyar ta miƙa hannu tana murmushi ga babanta. Sa’ud ya karɓe ta yana dariya;
“Yarinya ta riga ta saba da ni.”
A’isha ta murmusa.
“Sannu ku. Ashe tsautsayi ne ya fitar da ku haka.”
“Wallahi kuwa,” Sa’ud ya amsa. “Allah ya kiyaye tunda ba ta mutu ba.”
“Alhamdulillah. Amma kai fa? Baka ji ciwo ba?” ta tambaya tana duba shi da kulawa.
Sa’ud ya girgiza kai.
“No, ban ji ciwo ba. Ita ce kawai ta sami rauni.”
“Allah ya kiyaye gaba. Yaya Imam, sannu.”
Imam ya gama gyara drip ɗin Zahra, ya tsaya yana lura da numfashinta.
“Yauwa,” ya amsa cikin ƙanƙantar murya.
Ya ƙaraso ya karɓi Amal daga hannun babanta.
“Can we go?” ya tambaya kai tsaye.
“Of course, yes,” Sa’ud ya amsa. Imam ya fita ba tare da ya jira shi ba.
Sa’ud ya yi sallama da matarsa, ya ce za su dawo daga baya da daddare. Ta raƙashi har bakin mota. Imam na ciki, yana wasa da Amal, tana kyalkyala dariya. Sa’ud ya shiga, ya karɓi yarinyar ya mika wa A’isha, ya kunna mota suka bar asibitin.
---
Matsakaicin gida mai tsari ne da kyau suka tsaya, ya yi horn, maigadi ya buɗe masa ƙofa. Suka shiga, ya yi parking a filin ajiye motoci.
A farko Imam ya zauna a kan cushion yana lumshe ido da gajiya.
“Go and freshen up, guy, saboda muje mu ci lunc. Matata ta yi girki” Sa’ud ya ce, ya zama kusa da shi
Imam ya buɗe ido ya ce a taƙaice.
“Ka tafi gida kawai Sa’ud. Ni ba na jin yunwa.”
“Ban gane ba,” Sa’ud ya ce yana ɗaga gira. “Me ka ci tun safe bayan ruwan shayi?”
“I’m not hungry, I said.”
“To ka raƙani kawai na je na ci.”
Imam ya yi dariya mai ɗaci.
“For cry out loud, baka ganin kai na min ciwo bane? Ko gidanka ne sai na raƙa ka?”
Sa’ud ya ɗaga hannu alamar mika wuya.
“It’s ok, bari na tafi. Amma kar ka rufe ƙofa saboda zan dawo yanzu.”
“Kar ka dawo, please. I need rest.”
“Sai na dawo wallahi,” Sa’ud ya ce yana murmushi. Sau da yawa halin Imam dariya yake bashi.
---
Sa’ud na shiga gida ya nufi dining area, ya kwashe abincin da A’isha ta jera musu, ya zuba a basket, ya fita.
A falo ya tarar da Imam ya riga ya yi wanka, ya sa three-quarter wando kawai, riga babu. Ya kwanta kan three-sitter, kafafuwansa masu tsawo a miƙe, faffadan kirjinsa yana nuna ƙarfinsa, AC na busa masa iska. Ya ji lokacin da aka buɗe ƙofa, amma bai buɗe idonsa ba; ya san Sa'ud kaɗai ne zai iya shigo masa gida haka kai tsaye.
Sa’ud ya ajiye basket ɗin.
“I know you’re not sleeping,” ya ce. “Tashi mu ci abinci.”
Imam bai buɗe ido ba, ya ce!
“Kai maye ne, Sa’ud? An taɓa cin abincin dole?”
“Yau zaka ci na dole.”
“Eh sai ka tilasta min,” Imam ya ce yana gyara kwanciya.
“Imam,” Sa’ud ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce cikin taushin murya;
“Ban san me yasa kake hukunta kanka haka ba. Ni da kai mun san kai foodie ne. Me yasa baka son cin abinci yanzu? Ko har yanzu kaddarar ka ce ba ka iya karɓa?”
Imam ya mike tsaye;
“Serve us. Ban son dogon magana.”
Sa’ud ya yi murmushi. Ya buɗe basket ɗin, ya zuba abincin, yana cewa;
“Bismillah.”
“Ban gane ba,” Imam ya ce. “Wai tare za mu ci abinci?”
“Me laifin hakan?”
“Babu laifi, amma ni ba zan ci tare da kai ba.”
Ya janyo basket ɗin, ya ɗauki faranti, ya zuba abincinsa. Stir-fried spaghetti ne mai kayan lambu da pepper sauce ɗin kaza. Ya zuba isasshe.
Sa’ud ya tsaya yana kallonsa yana murmushi.
“Stop staring at me,” Imam ya ce, ya miƙe ya shiga ɗaki ya rufe ƙofa da key.
Sa’ud ya kwashe da dariya har da riƙe ciki. Imam ya ci abincin cikin shiru, sannan ya kwanta, bacci ya ɗauke shi.
---
Dab da magariba Imam ya tashi, ya yi wanka kafin ya fito falo. Sa’ud ya tarar yana kallon ball. Imam ya buɗe ido sosai.
“What are you still doing in my house?” ya tambaya.
“Abin da idonka ya gani,” Sa’ud ya amsa da murmushi.
Imam ya ɗauki mukullin mota.
“Ai sai ka tashi mu tafi masallaci.”
---
Suka yi sallah, sannan suka koma asibitin. A’isha, ganin dattin da Zahra tayi, yasa ta roƙi wata nurse ta haɗa mata ruwan wanka. Ta gogeta da Dettol, ta cire hular kanta. Gashinta bai yi datti sosai ba, sai cunkushewa kawai. A hankali A’isha ta gyara mata shi, ta yi parking tana yaba tsawon gashinta. Sabuwar doguwar riga ta saka mata, haskenta ya dan bayyana.
Sa’ud ne ya fara shigowa ɗakin, hannunsa ɗauke da leda cike da fruits, Imam na binsa a baya. Sa’ud ya karasa bakin gadon, ya zauna kusa da A’isha wacce ke kallon Zahra cikin bacci.
Imam ya ɗauki Amal daga kan cushion, ta kyalkyala dariya. Ya ɗan lakaci hancinta.
“How are you, darling?” ya ce cikin taushi.
Bayan Sa’ud ya umarci A’isha ta shirya, ya ce zai kaita gida ta huta kafin su dawo bayan Isha. Amal ya karɓa suka fita.
Imam ya miƙe ya karasa bakin gadon Zahra. Gashinta da A’isha ta gyara ya tsaya yana kallo, ya kai hannu a hankali kamar wanda zai taɓa wuta. Ya taɓa wuyanta, zafin jikinta ya koma dai-dai.
Ya zauna, ya ci gaba da kallonta, zuciyarsa cike da natsuwa da wani yanayi da bai bayyana ba. A ransa, ya yaba ƙoƙarin A’isha wajen tsaftace ta.