AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 42
"Hello Mama..." Farida ta kira cikin wayar, muryarta tana rawa kamar wacce ta sha kuka.
"Farida, yaya ne? Me ya faru na ji muryarki haka?" Mama ta tambaya, tana jan numfashi a hankali. Zuciyarta ta fara bugawa da sauri, ba a yawan samun Farida da wannan muryar.
"Ina kike, Mama?" Farida ta sake tambaya, muryarta na cike da damuwa.
"Wane irin tambaya ne wannan? A gidan Turai nake mana," Mama ta amsa, tana ɗan jin tsoro saboda yanayin da take ji a muryar ɗiyarta.
Farida ta sauke wata doguwar ajiyar zuciya, ta tattaro ƙarfin hali. "Mama, me yasa ba ki gajiya da jawo wa kanki matsala? Jiya na kira ki, na faɗa miki Zahra ta roƙi Daddy ya dawo da ke gida, kuma ya amince. Amma har yanzu kina gidan Hajiya Turai! Kin san me ke faruwa yanzu? Daddy ya tafi ƙauye wajen Inna. Ita kuma ta shaida masa baki je can ba! Bata ma san yaushe rabon da ya ganki ba."
Mama ta firgita tamkar an zuba mata ruwan sanyi. Ta ɗago da sauri, zuciyarta ta yi wani irin mummunan bugawa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Na shiga uku, ni Sahura!" Ta yi magana tana miƙewa tsaye, jikinta na rawa. "Farida, me ya hana ki gaya min yau zai tafi? Na rantse ban yi tsammanin daga magana jiya zai ɗauki hanya yau ba!"
Farida ta girgiza kai, duk da Mama ba ta ganinta ba. "Babu wanda ya faɗa wa Mama. Musharraf kawai ya raƙa shi. Sai da ya dawo ne ya sanar wa Iya yadda aka yi. Daga nan ne muka san ya tafi."
"Oh ni Sahura! Yanzu wanne mataki zai ɗauka a kai na kuma? Na shiga uku, na shiga uku! Ashe haka zan ci gaba da cin karo da fushinsa?" Mama ta yi magana da rawar murya, idanunta sun kaɗa da hawaye.
Farida ta saki gajeriyar ajiyar zuciya. Ta fahimci cewa Mama tana dab da rikicewa. "Mama, ki natsu. Babu amfani da rikicewa yanzu. Abin da za ki yi kawai shi ne ki tabbata kin tafi gida yau ɗin nan. Ki sami Inna, ki sanar da ita komai. Kin san Daddy na jin maganarta, killa idan tayi masa magana yayi haƙuri, ki daina bin na Hajiya Turai wlh kaiki zata yi ta baro ki."
Shiru ya cika ɗakin Mama na ƴan daƙiƙu. Ta tsaya tana kallon waje ɗaya, zuciyarta na shawagi tsakanin tsoro da nadama. Sai ta furta cikin muryar da ke rawa, "Eh, gaskiya ne. Bari na koma gida yanzu."
Ta shige ɗaki da sauri kamar wacce ke gudun wani bala’i, ta soma haɗa kayanta, zuciyarta na dukan tara-tara.
* * *
Kassim na dawo gida, bai ma lura Zahra ta fita ba. Laure ta yi dabara, ta mayar da ƙwado ta rufe ɗakin kamar babu wanda ya fita.
Shi kuwa Kassim, banɗaki ya shige, ya yi wanka, ya fito yana shafa mai a jikinsa. Ya zauna bakin gado, yana kallon Laure da ta rufe ido kamar tana bacci, alhalin ba bacci take yi ba, tana jin shigar Kassim banɗaki ta mayar da maƙullin da ta ɗauka a yanda ta Ciro, shine ta kwanta ta rufe ido. Muryarsa ta cika da masifan da ƙarewar haƙuri.
"Ke Laure," ya ce, muryarsa na daɗa yin zafi ɗauke da gargaɗi, "wallahi ki je asibiti a duba ki. Idan ciki ne dake, a san abin yi tun yanzu. Ni ban shirya ƙarɓar wani ɗa kuma ba."
Laure ta motsa a hankali, ta ɗago kai kamar wacce aka taso daga barci. Fuskar ta cika da fushi da baƙin ciki. " Da wane zanji Kassim? Jikin da ya matsa mini, ko fitinar ka?" ta faɗa a hankali, tana matse numfashi. "Idan ma ciki ne, ina ruwanka? Ni dai ba ruwanka."
Kassim ya yi tsaki mai sauti. "Na faɗa miki gaskiya ne. Ba zai yiwu ki ƙara mini wani ɗawainiya yanzu ba."
Laure ta yi masa wani kallo mai cike da raɗaɗi da ƙiyayya, zuciyarta na ɓaci. "Ɗawainiya? Wace ɗawainiyar ka ke yi min? Ka san cin mu ko shan mu? Ai kai maza kawai ka raƙo duniya! Ni a hannunka ƙaddara ta jefa ni. Wallahi, kaine hukuncin rayuwata."
Hannu ya ɗaga yana shirin mareta. Laure ta yi saurin kaucewa, idanunta sun cika da zafi da ƙiyayya. Ta tsaya tsayin daka, ta ɗaga hannu tana nuna shi.
"Kada ka sake wannan ƙazamin hannun taka ya taɓani Kassim!" Ta ce da murya mai kaifi. "Wallahi, idan ka kuskura ka taɓa ni, zan tabbatar maka cewa noma ƴar bariki ce, kafin kowa sani wacece Ni ba sai an baka labari ba!"
Ta buga tsaki mai ƙarfi, sannan ta fice daga ɗakin cikin huci.
Kassim ya zauna a bakin gadon ya saki wata irin gajiyar ajiyar zuciya. "Laure kenan," ya ce cikin raɗaɗin zuciya. "Nan kaɗan ba da jimawa ba sakamakon kuskurenki zai same ki."
Ya saka rigarsa, ya fito falo ya zauna, zuciyarsa cike da tashin hankali da tunani.
Da dare Laure ta kulle kanta a ɗakin Zahra ta zauna, kuka mai cin rai na fita daga zuciyar ta
Kukan nan ba na yau ba ne; ya tattaro duk shekaru na zafi, kunya, da baƙin cikin rayuwa.
A ƙwaƙwalwarta, ta ga rayuwarta ta baya kamar fim. Ta tuna lokacin da take sarauniya a idon duniya. Mahaifinta ya rasu tun tana ƙarama, mahaifiyarta ta sake aure, aka dawo da ita gidan ƙanin mahaifinta, Kawu Bala, manomi mai ɗan hali wanda ya riƙe ta tsakani da Allah. Amma daga baya, ta butulce masa, abin da ya kawo tsananin hukuncin da ya yi mata.
A lokacin, matar Kawu, Tani, mace ce mai zuciya mai taushi, wacce ba ta da ido sosai. Ita ce kan bata abinci ta kai wa Kawu idan yana gona. A wannan kai abinci ne Laure ta haɗu da Kassim.
Kassim, wanda ke aiki a Coca-Cola Company a Ibadan, yana cikin masu sauke kaya. A wani lokaci, ogansa ya nemi ya taimaka masa noma da damina saboda ganin ƙoƙari da ƙarfinsa. Kassim ya yarda saboda alawus ɗin da zai samu ya fi albashinsa.
Gonar ogan nasa babba ce, wadda ba a iya ganin ƙarshenta. Gonar Kawu Bala kuma tana gabanta kaɗan. Laure, duk lokacin da ta kawo abinci, idan ta wuce gonar Kassim sai ta lura yana kallonta sosai. Har sauran ma’aikata suka lura, suka ce masa ya yi mata magana mana idan sonta yake.
Da farko, Laure ta ƙi saboda tsoron Kawu Bala. Amma a hankali, Kassim ya rinƙa shawo kanta da kyawawan kalamai da ƙananan kyaututtuka. Kasancewarta mai son abin duniya, hakan ya sa ta amince da soyayyarsa.
Soyayya mai ƙarfi ta kullu tsakaninsu. Idan ta kawo abinci, sai ta tsaya a gonar Kassim su yi hira yayin da yake aiki.
Lokacin da ya kammala aikin gonar ya koma Ibadan, ya ba ta ƙaramin waya. A farko ta ƙi karɓa saboda tsoro. Amma daga baya ta amince, ta rinƙa boyewa. Duk dare sai su yi waya.
Har Kassim ya saba da kiranta sosai, ya zama babu ranar da ba su yin magana ba. Laure, ita kaɗai ce a ɗakinta, hakan ya ba ta dama sosai.
Da daddare, kamar yadda Kassim saba, sai ga kira ya shigo wayar Laure. A hankali wayar ta yi vibrating a ƙarƙashin pillow ɗinta, vibration ɗin ya tashe ta daga barcin da ta fara. Da sauri ta buɗe idanu, ta kamo wayar da hannayenta masu ɗan sanyi, zuciyarta na harbawa. Ta leƙa tsakar gida ta tabbatar babu kowa kafin ta ɗaga kiran da ya kusa katsewa.
“Hello, baby na,” muryar Kassim ta ji, siririyar murya mai shu’umi da birkita zuciya.
Laure ta yi shiru na ƴan daƙiƙoki, sannan ta ce da ƙanƙanin muryarta, “Sai yanzu kake kira?”
“Sorry, my love,” ya amsa cikin tausasa murya, “Wallahi aiki ne ya yi min yawa. Yanzu me kike yi?”
Laure ta rufe idonta, ta ja numfashi mai zafi, ta gyara kwanciyarta. “Babu komai. Daman bacci na fara.”
“Ayya… sorry na tashe ki, ko? Amma wani mafarki na yi jiya… na ga ya dace na baki labari.”
Laure ta ɗan murmusa kaɗan, tana daɗa lumshe ido. “To wani mafarki ne wannan mai muhimmanci haka da har kake ganin ya dace ka sanar dani?”
“My love,” Kassim ya ce, muryarsa ta ƙara sanyi, ta koma kamar yana raɗa mata, “Ina ganin lokaci yayi da zan zo na sami Kawu da maganar aure… saboda kullum idan na kwanta sai na yi mafarkin ki… mafarkin ina…”
Ya yi shiru, yana neman kalma. Sai kuma ya furta cikin rawar murya: “…ina shan nononki ko wani mu’amala na aure. Laure… ba zaki gane yadda nake ji ba.”
Kalmar ta daki zuciyar Laure kamar wuta. Da sauri ta cire wayar daga kunnenta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi, ta katse kiran tana jin wani irin nauyin kunya da tashin hankali. Bata taɓa tunanin Kassim zai iya furta mata irin wannan magana ba.
---
Kwanaki sun shuɗe. Abubuwa da dama sun faru daga cikin su, ciki har da koyon kalamai na batsa daga bakin Kassim, wanda a farko ya ba ta kunya, amma yanzu ta saba. A kowane dare, suna raba lokacinsu suna tattaunawa da kalaman da ke kunna sha’awa.
Lokacin girbi ya yi, Kassim ya dawo ƙauyen su Laure. Wannan dawowa ce da ta canza komai, a duk lokacin da suka haɗu, ya kan rungume ta, ya taɓa jikinta ba tare da tsoro ba. Da farko tana tururuwa, tana jin kunya, amma daga baya ta fara amincewa da abin, har ta kai ma ta kan fara taɓa shi ma kafin shi ya taɓata.
Wata rana, Laure ta kai wa Kawu Bala abinci a gona, sai ta bi ta gonar Kassim. Ta same shi shi kaɗai, yana zaune yana jiran ta. Yana ganinta, ya miƙe ya rungume ta ƙyam, hannayensa sun kulle ta cikin jikinta. Laure ta sakar masa murmushi na sirri.
“My love,” ya ce cikin ɗan dariya, “mu ɗan ƙarasa bakin rafi. Na wuce can ɗazu, wajen shiru yake.”
Ya kama hannunta, suka nufi bakin rafin. A kan wani gungumin itace suka zauna. Yana rungume da ita, yana lallabarta a hankali. Hannunsa ya zura ta cikin rigarta, ya damƙi nononta. Numfashin su ya fara sauyawa, yana fita da sauri da sauri.
A wannan bakin rafin, Kassim ya rabauta da budurcinta.
Laure ta dawo gida da jiki mai ciwo, idanunta sun yi ja sun kumbura, tafiyarta ta zama a hankali, ƙafa a wawware kamar mai rauni. Tani ta lura da canjin nan take ta miƙe da sauri ta biyo ta har ɗaki.
“Ke Laure!” Tani ta tsawata tana tsaye bakin ƙofa, idanunta cike da shakku. “Wai me ya same ki haka? Wace irin tafiya kike yi haka?”
Laure ta fara kame-kame, “Errmm… Baaba… Dama—”
“Ke Laure! Saka idanunki cikin tawa. Me kika aikata? Ko dai abin da nake zargi ne?”
Kuka ya kubce wa Laure, hawaye na zuba ba tare da ta iya magana ba. Tani ta ƙaraso kusa da ita da sauri, ta buɗe ƙafafunta.
Wani ihu mai raɗaɗi ya fito daga bakin Laure yayin da Tani ta tabbatar da abinda take tsoro. “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Tani ta fasa kuka. “Laure! Wannan shi ne abin da kika yanke wa kanki? Kin cuce ni! Me kika nema kika rasa? Yanzu me zan ce wa Malam?!”
Sun yi kuka sosai tare. Daga baya, Tani ta je ta hura wuta, ta dafa ruwa da bagaruwa da ganyen magarya. Ta yi mata wanka mai zafi da kuma sit bath don rage mata ciwo.
Laure ta kwanta tana kuka, jikinta duk ciwo. Tani ta shigo ɗakin ta tsareta da ido. “Ke! Ki saurare ni da kyau. Wannan magana ta mutu a nan. Karki kuskura Malam ya ji komai! Idan kika tona, ni za ki jawo wa bala’i. Ki kiyaye gaba, Laure! Bana son na ma san waye ya aikata hakan a gareki, amma ki kiyaye!"
Laure ta gyada kai cikin kuka, ba ta iya cewa uffan ba.
Bayan wata ɗaya, Laure ta fara fama da zazzabi da amai. Tani ta je bikin ƙanwarta a lokacin abin ya fara, sai Kawu Bala ya ɗauketa zuwa asibiti. Likita ya tabbatar da cewa tana da ciki.
“Kin cuce ni, Laure,” Kawu ya furta yana kuka. “Me kike son mutane su ce a kaina? Na kasa riƙe marainiya? Me na gaza miki?”
“Kawu… don Allah ka yi haƙuri… sharrin shaiɗan ne…”
“Ki min shiru da wannan maganar shaiɗan! Wane ne uban ɗan?”
“...Kassim ne.”
Wani irin baƙin ciki ya bayyana a fuskar Kawu Bala. Ya je ya kai ƙara wajen mai gari. Kassim ya ƙaryata komai, ya ce bai taɓa hulɗa da Laure ba, har ma ya yi iƙirarin cewa shi yace zai nemi auren ta, amma ta ƙi, shine ta fita harkata.
Ranar da Laure ta ji wannan zargi, ta yi kuka kamar ranta zai fita. Duk ƙaunar da Kassim ya yi mata ikirari a wayoyi ta zama ƙarya.
Amma bayan wata takwas, Laure ta haifi ɗa, Musa wanda kamarsa ta Kassim ce ɗari bisa ɗari. Babu ko inda Kassim zai ƙaryata haka.
Mai gari ya kira Ogan Kassim. A nan Kassim ya kasa ƙaryata maganar, saboda ga gaskiya ta bayyana, ya amsa laifinsa. Haka aka ɗaura aure tsakaninsa da Laure, ba don son zuciyarsa ba, sai don matsin lamba daga manya.
Washegari Laure ta tattara kayanta ta bishi Ibadan. Kawu Bala ya jaddada mata; “Ko me kika tarar, Laure, ki daure. Kada ki kuskura ki dawo min gida, duk rintsi duk wuya na yafe ki.”
Zaman da ta yi tare da Kassim a Ibadan ya zame mata masifa. Rashin kulawa, zagi, duka, yunwa… Duk ta sha. Amma a hankali ta miƙe tsaye, ta koyon jarumtar rayuwa, ta koma yin sana’o’i, ta fara da sayar da lemun kwalba, sai gashi ta koma dafa abinci da kitso, ta fara samun kuɗi, ta gyara kanta. Ibadan ta ba ta ido da ƙwarin gwiwa.
A hankali Laure ta share hawaye, ta miƙe tsaye daga kwanciyar tunanin da take ta ce a fili “Wallahi, Kassim… baƙin cikin ka ba zai kashe ni ba, sai dai dukkan mu mutu.”
Sai kawai aka hankaɗo ƙofar ɗakin! Laure ta juyo da mamaki, zuciyarta ta buga. Kassim ne ya shigo, fuskarsa a ɗaure, kamar ruwan sama zai sauka.
“Ke! ina yarinyar nan?” ya tambaya cikin tashin hankali.
Laure ta kalle shi da tsantsar raini. “Wace yarinya ka bani ajiya?
“Zahra mana! Ina take?!”🔥