AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 43

by @jikargarba001

Laure ta ƙare wa Kassim kallo daga sama har ƙasa. Ganin yadda ya tarwatse, jikinsa ke rawa, idanuwansa cike da damuwa ya sa ta furta da ɗan raini;

“Wai Kassim, Zahran nan azurfa ce ko zinariya ne da har ka tada hankalin ka haka?”

“Duka biyu!” ya amsa cikin fushi da tsantsar tashin hankali.

Laure ta yi ƙaramar tsaki, ta juya kai. “To, bansan yadda take ba. Saboda kai ba ka bani ajiyarta ba.” Ta faɗa cikin yanayin ko-in-kula.

Maganarta, ta ƙara ɓata masa rai. “Laure, kar ki ɗauki wannan magana da wasa. Wannan ba wasa ba ne. Ina Zahra? For the last time!”

Murmushi mai ɗaci ta saki. “Yau naga bala’i. Ranar da ka rufe yarinyar nan a ɗaki kamar akuya, ka bani maƙullin ɗakin ajiya ne? ashe dai ka san tana da daraja shine ka wulaƙanta ta haka?”

Kassim ya matse haƙora. “Bani da lokacin surutu. Ya zama dole in bar garin nan yau daren nan. Ki tattara yara ku koma ƙauye gobe da safe. Zan biyo bayan ku daga baya.”

Yana faɗin haka ya fice cikin sauri. Laure ta biyo shi da ido tana bin bayansa da kallon mamaki. “Ban gane wannan maganar komawa ƙauye ba, Kassim. Kai fa, ina za ka je?”

“Ban yarda da ke ba da har zan faɗa miki inda zan tafi. Idan kuma na dawo, tabbas sai na miki hukunci akan taimakon da kika yi mata har ta gudu. Yanzu dai bari na bar gari kafin iyayenta su shigo nemata don nasan tabbas za su biyo baya.”

Laure ta tsaya cak. Ba ƙarfin magana, ba ƙarfin motsi. Ta ji jikinta ya yi sanyi tamkar an tsiyaye mata ruwan sanyi. Ta kasa tanka masa, ta tsaya kawai tana kallon yadda ya ɗauki ƙaramin jakarsa, ya fita cikin duhun dare ba tare da ya bayyana inda zai tafi ba. Kafin ya fita, ya miƙa mata wayarta da ya riƙe tun ranar.

Zama ta yi dirshan a kan gado, tana ta nazari. “Kar dai wannan taimako ya saka ni a matsala. Ta yaya zan koma ƙauye da yara babu miji? Zan bar sana’a ta a nan? Wa zai ciyar damu? Makarantar yara fa? Wallahi ba zai yiwu ba. Ina nan. Amma wai ma wacece yarinyar nan da Kassim ya tsorata haka da lamarin ta?”

---

A bangaren Imam...

Direban ya sauke sa kai tsaye a gida. Babban gida ne, an shafe shi da fentin fari ƙal, alamar gidan masu kudi. Imam ya shiga da sallama, zuciyarta cike da nauyi.

A falo wata mata ce zaune tana latsa waya lokacin da Imam ya shigo. Ba tare da ya kula matar ba, Imam ya fara haura matakalai zuwa ɗakinta.

“Tirr! Wallahi an yi asarar haihuwa a nan,” matar ta faɗa cikin yanayin neman magana. Imam bai ko tanka ta ba, ya ƙarasa haura sama.

Ya buɗe ƙofarsa, ɗakin ya ɗan yi ƙura saboda kwanaki biyu rabonsa da shi. Ƙura ta dame shi sosai, ya tsani ƙura, musamman saboda cutar asma da yake fama da ita. Yana daƙunawa ya fita ya kira yaron mai gadi ya taimaka masa wajen tsabtace ɗakin da bathroom ɗinsa. Bayan ya gama ya ba shi kuɗi ya gode masa, ya koma ciki ya shiga wanka.

Bayan ya fito, ya ɗan goge jikinsa ya shafa mai. Ya buɗe wardrobe dake cike da kayayyaki birjik. Ya zaɓi Egyptian jallabiya fara ƙal da kayan ciki, ya shirya cikin tsabta. Imam dogon saurayi ne mai faffadar kirji, fatarsa baƙi amma tana sheƙi, idanuwansa manya ne masu ɗaukar hankali, gashin idonsa siriri kuma mai tsawo. A takaice, yana da kyan da yake jan ido.

Ya ɗauki wayarsa ya kira Sa’ud.

“Hello,” ya ce cikin kasalalliyar murya.

“Sai yanzu ka ga kiran da nayi maka?” Sa’ud ya tambaya cikin ɗan ɓacin rai.

“Eh. I was a bit busy ne. Sai yanzu na sami kaina.”

“Kun isa lafiya kuwa?”

“Alhamdulillah.”

“Ya ka sami mutanen gidan?”

“Komai dai yadda na barsu haka suke. Nothing changed.”

“Imam, kayi haƙuri da Anty. I know how she can be, amma ka yi ignoring ɗin ta.”

“Sa’ud, matar nan ba ta daga min hankali. Matsalata ta fi ƙarfin ta, kuma ka fi kowa sanin hakan.”

“Haka ne. Amma zuciya bata da ƙashi. Ka ci gaba da haƙuri.”

“In sha Allah. Ya Amal ɗina?”

“She's fine. Sun fita da mamarta.”

“Ok. Ka ƙara yiwa Aisha godiya don kulawa.”

“Ba damuwa. Have a rest. We’ll talk later.”

“Thank you.”

Ya kashe wayar. Ya ɗauki laptop ya ɗan yi dube-dube, sannan ya mayar. Wayarsa ya sake ɗauka ya shiga WhatsApp ya kira lambar da ya saka sunan Ammiey♥️ ta hanyar video call. Kamar daman jiran kiran take, domin da yana fara ringing ta ɗauka.

Fuskar wata mata kyakkyawa ce ta bayyana tana murmushi, hakoranta farare ƙal da golden tooth ɗinta ɗaya ya bayyana.

“My son, sai yanzu?” Ta faɗa cike da ƙauna.

Murmushi Imam ya yi wanda ya ƙara bayyana kyan sa, ya sunkuyar da kai kamar ƙaramin yaro. “Ammi, yau na dawo daga Ibadan. Wallahi I had a stressful day.”

“Allah sarki ɗana. Ya gajiyar hanya? Ya ka bar su Sa’ud ɗin?”

“Lafiya ƙalau, Alhamdulillah. Me zan samu a gurin ki?” Ya tambaya yana murmushi.

“Me kake buƙata?”

“Ina son na ganki, Ammi. Wallahi I missed you so much.” Ya furta cikin rauni. Shi mutum ne mai dauriya, amma idan yana tare da Ammi, wannan raunin nasa na bayyana.

Ammi ta yi dariya. “Kai, Baga shi kana ganina a video call ba.Ko dai wata rigimar ce?”

“Ammi ba ta waya nake son ganinki ba. Ina son ki rungume ni, mu fita mu sha iska kamar da. These years apart sun ishe ni, Ammi. Haƙurina yana ƙarewa da zamar gidan nan.”

“Imam, idan haƙurinka yana ƙarewa da zama a gidan nan, me zai hana ka yi aure ka bar musu gidan? Amma ka tuna, duk ƙin ka da gidan nan, gidan uban ka ne.”

“Ammi, mu bar wannan maganar. Ina Deen?”

“Dole kace a bar maganar tunda na kawo batun aure. Amma, Imam, do you think you are getting younger? Kayi wa kanka faɗa.”

Murmushi ya yi cikin jin nauyi, ya rasa abin cewa.

Ammi ta katse shirunsa cikin sanyin murya amma cike da damuwa.

“Na san aure lokaci ne, Imam… Amma kai ba ka ɗaukar wani mataki. Deen fa yana buƙatar uwa, ka gane mana.”

Imam ya jinjina kai, ya sauke numfashi mai nauyi.

“Hmmm… Ammi, ai ke kina nan da shi.”

“Kenan haka zaka ƙare rayuwarka ba tare da aure ba? Saboda ina nan don Deen?”

Ya ɗan murmusa cikin siririyar dariya, wacce ta fi kama da dariyar shu'umanci.

“Ammi, aure sunnah ne, ba farilla ba. Me ya sa kike ɗauka kamar babban al’amari ne haka?”

“Au, saboda ba farilla bane shikenan baza ka yi shi ba? To ai kayi abin da ya maka.”

Imam ya juya kai yana tambaya, “Ina Deen?”

“Sun fita shan ice cream da Nana.”

“Ok. Ya ƙafanki? Kin ce kina jin sauƙi?”

“Eh, da sauƙi sosai. Sai dai ɗan ciwon da ba za a rasa ba.”

“Allah ya ƙara sauƙi, Ammi. Zan samu lokaci inzo na ganki next month, In Sha Allah.”

“Allah ya kawo ka lafiya,” ta amsa da murmushi mai taɓa zuciya.

“Ameen, my Ammi,” ya ce yana kallon ta da kulawa.

Suka yi ɗan hira na soyayya tsakanin uwa da ɗa mai matuƙar shaƙuwa, kafin Imam ya yi mata sallama ya ce zai fice zuwa masallaci.

---

A falo Anty,uwar gida, mace mai zubin nutsuwa amma da kishi a zuciya, na zaune tana latsa waya, lokacin da Alhaji Muhammad ya dawo gida. Ya zauna a gefenta yana sauke nauyin gajiya, yana zama a kujera.

“Barka da dawowa, Alhaji,” ta ce tana ajiye wayar.

“Yawwa Sakina. Ya gidan?”

“Lafiya ƙalau, Alhamdulillah.” Ta tashi cikin ladabi, ta nufi fridge ta ɗauko masa ruwan sanyi. A wannan lokacin Imam ya fito daga sama.

“Welcome, Abba,” ya faɗa cikin ladabi da girmamawa.

Alhaji ya ɗan tsaya yana kallonsa na ƴan daƙiƙu, sai kuma ya ce da muryar uba mai iko;

“Ina ka ɓata kwanaki haka, Imam?”

“Ibadan na tafi, Abba. Kuma na faɗa maka kafin na tafi.”

“Ibadan dai da ka ce sati ɗaya zaka yi, amma yau makonni uku kenan kafin ka dawo?”

Imam ya ɗan kau da kai. “Things came up ne, Abba. Shiyasa ban dawo lokacin da na tsara ba.”

Alhaji ya ɗan girgiza kai cikin takaici. “Na ji. Amma ka sani, duk wani abu da zaka yi, kada ka sake ka jawo min abin zagi a gari. Allah ya bani kai ɗaya, amma hakan ba dalili bane da zai sa kake ja min magana a gari kullum.”

“Zan kiyaye, Abba.”

“Da kyau. Wannan ya fi.” Ya gyara zamansa yana kallon Imam da ido. “Yaushe rabonka da shiga asibiti?”

“Ina shiga, Abba. Tafiyar nan ce kawai ta hana ni naje kwana biyu. Amma yau da dare zan shiga, In Sha Allah.”

“Good. Allah ya taimaka.”

“Ameen,” Imam ya ce, sannan ya miƙe ya fice daga falon, ba tare da ya kula Anty da ke zaune tana kallo daga gefe ba.

Da zarar ya fita, Anty ta taɓe baki, muryarta cike da tsanar da bata iya boyewa ba.

“Alhaji, ina jin takaici idan na kalli Imam. Irin baiwar da Allah ya ba shi, amma duk ya watsar da ita ya zaɓi rayuwar banza. Tun da daɗewa nake gargaɗinka a kansa, amma ka ƙi sauraro. Gashi yanzu duk wata dama da ya samu, sai ya ja maka magana a gari.”

Alhaji ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi. “Sakina kenan… Nima wasu halayensa suna bani takaici. Amma kullum ina yi masa addu’a. Ina da tabbacin wata rana ɗana zai shiryu, ya zama abin alfahari ga duniya, ba ma ni kaɗai ba.”

Anty ta saki dariya mai ɗaci. “A yanda yake yanzu ne zai zama abin alfahari? Kai dai ka cigaba da addu’a. Allah yasa baƙin cikin shi ba shine maka ajalinka ba.”

“A’a Sakina, ki daina faɗar irin wannan magana. Daga ni har ke mun san abin da ya aikata tsautsayi ne, ba halinsa bane. Mu ci gaba da yi masa fatan alkhairi kawai.”

Ta juya kai gefe, ta taɓe baki. “Hmm, gaskiya dai da ɗaci yake, daga ƙinsa kuma sai ɓata. Ai gashi nan sakamakon ya fara bayyana.”

Alhaji bai ce komai ba, ya miƙe cikin kasala ya nufi ɗaki, ba tare da ya sha ruwan da ta kawo masa ba.

---

Mama kuwa bata jira dawowar Hajiya Turai daga yawon da ta fita ba. Ta tattara jikinta, ta kulle mata gidan, ta ɗauki hanya zuwa ƙauyensu. Adai-dai bakin ƙofar gidan su, adaidaita ya sauke ta. Ta biya shi kuɗinsa cikin sauri, ta tura ƙofar zinc ɗin da aka zagaye gidan, tana shigowa falon cike da sallama.

Inna Habi na zaune tana girgiza kai, ta ji sallamar Mama amma ta yi banza kamar bata ji ba. Kutsa kai tayi ta shiga fakon. Mama ta tsaya cak, tana kallonta da mamaki.

“Inna, daman kina ji ina sallama kika yi banza da ni?” Mama ta ce, muryarta na ɗan rawa.

Inna ta ɗaga ikai, ta zuba mata wani kallo mai zafi.

“Sahura, daga ina kike?”

Mama ta ɗan zumɓura baki. “Kaduna,” ta faɗa cikin rashin gaskiya.

“Kadunar uban ki!” Inna ta tsawata. “Mijin ki ya zo neman ki nan, amma sai kice min kin fito Kaduna?”

Mama ta durƙusa tana maida murya ƙasa. “Inna shi ne yace na bar masa gidan sa sai ya neme ni.”

Inna ta riƙe haɓa tana jinjina kai. “Hala wani mummunan halin kikayi. Wai ma tukun da yace ki bar gidan sai kika tafi ina?”

Mama ta ɗan kame fuska. “Babu abinda nayi masa, kawai sharri kishiyata suka haɗa baki suka yi min. Shi yasa na tafi gidan ƙawata.”

“Na faɗa miki tun farko kishiyar ki mace ce mai kirki, ki nutsu ki kwantar da hankalin ki kuyi zaman lafiya. Kin ƙi ji. Kin fi biyewa sheɗanun ƙawayen ki. Wallahi waɗannan kai ki zasu yi su baro ki . Yanzu gashi mijinki ya zo baki nan. Me zaki ce masa?”

Mama ta fara hawaye, ta durƙusa sosai. “Inna, ki taimake ni… Ki kira shi ki ce masa ina gidan ƙanwarki ne, baki sani ba.”

Inna ta girgiza kai. “A’a, wallahi ba zan yi ƙarya da girma ta ba.”

Mama ta share hawayenta. “To yanzu Inna, yaya kike son nayi?”

“Ga wayata nan,” Inna ta miƙa mata. “Kira min shi Bashir, muyi magana.”

Mama ta ɗauki wayar da hannunta na rawar jiki. “Me zaki ce masa, Inna?”

“Ke dai kira shi kawai.”

Ta kira Daddy da rawar jiki. Daddy na ɗaki yana shan shayi, Mommy na tsaye tana shirya masa kaya a wardrobe. Ganin kiran Inna Habi, Daddy ya aje shayin, ya gyara zama, ya ɗaga wayar cikin girmamawa.

“Assalamu alaikum, Inna,” ya furta da nutsuwa.

“Lafiya ƙalau, Bashir. Kun isa gida lafiya?”

“Eh, Alhamdulillah.”

“Masha Allah. Na kira ne don sanar da kai cewa bayan ka juya baya, Sahura ta shigo. Taƙi faɗa mini gaskiyar abin da ya faru har ka kore ta daga gidan ka. Ta kuma tabbatar min cewa tun daga lokacin da ka Koreta tana gidan wata ƙawarta a Kaduna.”

Daddy ya sauke numfashi. “Inna, al’amarin Sahura sai dai addu’a.”

“Ka ƙara haƙuri, Bashir. Lokaci zai koya mata darasi. Idan bata ji yau ba, wata rana zata yi nadama.”

“Babu komai, Inna. Na gode. Zan kira ta yanzu.”

“Allah ya yi maka albarka,” Inna ta ce da kulawa.

“Ameen, Inna.”

Bayan ta kashe wayar, Mama ta kifa kanta a gwiwarta tana kuka. “Inna kin kashe ni! Ya zaki faɗa masa haka?”

Kafin Inna ta ba ta amsa, wayar ta mama ta fara ringing. Sunan Daddy ya bayyana a fuskar wayar. Mama ta yi saurin share hawayen ta, ta shanye rawar jiki kafin ta ɗaga wayar.