AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 44
Calmly ta furta, “Hello. Alhaji ina wuni.”
“Riƙe gaisuwar ki,” ya ce cikin muryar da ke nuna zallar ɓacin rai . “Ba don shi na kira ki ba. Ina kika shiga lokacin da nace ki koma gidanku har sai na neme ki?”
Mama ta ji jikinta ya yi sanyi tamkar ruwan sanyi aka zuba mata. Murya ta yi rauni, zuciyarta na tsalle kamar za ta fito ta ce;
“Ina Kaduna ne… a gidan Turai.”
“Turai?” Ya ɗaga murya, yana tsinkar kalmarta da ƙarfi. “Turai ce ke auren ki?!”
Kamar za ta shige ƙasa ta ce a sanyaye, “A’a.”
Shiru ya biyo kalmar nata, shiru mai nauyin gaske, kafin ya cije haƙoransa ya ce;
“Turai da bata da shaida a gari kika zauna da ita har watanni? Kin nuna min igiyar aurena bata da wata daraja kenan. Zawwarcin kema kike sha'awa? To shikenan, zawwarcin da kike nema kin samu; na sake ki. Saki ɗaya. Ba zan lamunci yawon banza da aurena ba!”
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Mama ta fashe da kuka, tana roƙo cikin rawar murya. “Alhaji ka yi haƙuri! Wallahi ba zan sake ba, ka rufa min asiri, ka…”
Sai kawai ta ji wayar ta yanke. Shi ya katse kiran.
Hannu biyu ta sa ta rufe fuskarta, kuka ya ƙwace mata mai ban tausayawa. Zuciyarta ta ɗauki nauyi da zafi, tunaninta ya fara rikicewa; Yanzu kenan na rasa komai? Amina tana gidan Alhaji a matsayin matar so, Zahra ta tsira daga hannun Kassim ta dawo gida a matsayin ƴar so, Musharraf yana riƙe da duk harkokin Alhaji… ni da ‘ya’yana fa? Za mu koma fagen talauci da wulakanci? Mu kenan wulaƙantattu?
Ta ɗora hannu a kai tana rawar jiki. Hawaye suka gama jiƙa mata fuskarta. Cikin jin tausayawa Inna ta ƙaraso ta zauna a gefenta. Da farko ta yi shiru tana kallon yarinyar tata da takaici da ta riga da ta samowa kanta mummunar shaida a gari. Daga baya ta jawo ta jikinta tana lallashinta cikin tausayi uwa ga ƴa.
“Sahura… ki yi shiru. Ki daina kuka. Zan kira Bashir da kaina. Zan roƙe shi ya dawo da ke. Amma wallahi ki gyara halayenki. Ki daina biyewa su Hajiya Turai. Wallahi abinda suke so shine su lalata ki, su baro ki ke kaɗai a lokacin da kika fi buƙatar wani a tare da ke.”
Mama ta share hawayenta, tana girgiza kai cikin tsoro. “Inna… kina ganin zai yarda?”
Inna ta dafa kafaɗarta, tana kallon ta cike da tausayawa. “Zai yarda. Amma ke ma ki tashi ki gyara kanki, Sahura. Wallahi ba wai Allah ba ya son ki ba, ke ɗin ce ba ki yin abinda ya dace.”
---
A wancan lokacin kuma, Mommy da ke shirya wa Daddy kaya ta tsaya cak lokacin da ta ji muryarsa mai ƙarfi ya furta kalmar saki. Jikinta ya yi sanyi, zuciyarta ta yi wani irin dokawa da bata taɓa jin irinsa ba. Ta juya a hankali tana kallonsa bayan ya katse wayar
“Haba Alhaji…” muryarta ta yi rawa. “Wane irin hukunci ne wannan? Ka yi tunanin ‘ya’yan da ke tsakanin ku. Ka yi tunanin cewa kai ma kana da ‘ya’ya mata, wanda basu wuce yin kuskure a gidan aurensu ba… me zaka ji idan wani ya ɗaura musu hukunci cikin fushi?”
Daddy ya ajiye shayin da ya ɗauka zai fara sha, ya ce da yanayin wanda zuciyarsa ta gama kafewa;
“Na gaji da matsalar Sahura. Kuma ban haifi ‘ya’ya mata don su yi irin halinta ba, saboda ba tarbiyyar da na basu kenan ba. Idan wata ta ɗebo halayyar ta, to zata ɗauki sakamakon ta. Hukuncin da na yanka shine daidai”
Mommy ta girgiza kai, muryarta ta yi rauni sosai;
“Abinda ka yi ba daidai bane, fushi ne kawai ya rinjaye ka. Zan jira ranar da hankalinka ya kwanta, ka gane illar wannan abu.”
Daddy ya juya, ya runtse ido, ya ce da sanyi amma da ƙarfin iko;
“Ki fita kawai. Ki bar ni in yi tunani.”
Mommy ta tsaya tana kallonsa da ƙwalla, amma ganin yanayinsa yasa ta juya ta fita. Da ta kai bakin ƙofa ta tsaya, ta juyo da muryar da ta cika da zuciya ta ce;
“Allah ya huci zuciyarka, na barka lafiya.”
Da ta shiga ɗakinta ta faɗa kan gado ta fashe da kuka. Duk jarumtar da ta ɗauka a zuciyarta ta rushe, hawaye suka zubo kamar ruwan sama. Tana jin sallamar Inna ta yi saurin share fuskarta tana yin kamar tana bacci.
---
Daddy na jin fitarta zuciyarsa ta buga. Bai ji daɗin yadda ya yi mata magana ba, bai kuma ji daɗin cewa ya koreta a ɗaki ba. Amma zuciyarsa na tafasa; yasan idan ya bari ta ci gaba da magana kan Sahura zai iya furta maganganun da duka za su yi nadama. Shi yasa kawai ya yi nemi da ta basa waje.
Wanka ya yi ya kwanta, tunani ya yi masa nauyi sosai. A zuciyarsa kalmar saki tana yawo kamar muryar ƙaho mai ƙarfi, ga kuma halin da ya gan Amina ta shiga.
---
Washe gari da sassafe, Musharraf ya zo da Zainab don kai Zahra da Inna airport. Duk gidan suka hallara a dining. Zaman ya cika da shiru. Mama Ladi tayi serving ɗinsu abinci, kowa ya fara ci cikin nutsuwa. Musharraf yana kallo Zahra da bata ci abincinta sosai ba, sai ya ce;
“Princess… ki ɗan yi sauri. Lokaci na tafiya.”
Ta tura abincin gefe, ta ce da rauni;
“Na ƙoshi.”
Daddy ya kalleta da damuwa. “Ko rabin ba ki ci ba, Zahra.”
“Wallahi Daddy na ƙoshi. Zan sha yoghurt kawai.”
Kowa ya yi shiru. Aka yi musu rakiya har mota. Iya ta riƙe hannun Zahra tana cewa;
“To Hajiya, Allah ya kiyaye hanya. Ke kuma Zahra, idan kin ga dama idan kina da damuwa kar ki buɗe baki ki tsaya wannan zurfin cikin naki har ki shiga matsalar banza.”
Zahra ta shiga mota, ta tura baki. Musharraf ya bi ta da kallo yana murmushi.
Bayan sun fita, Musharraf ya tsaya ya siyo mata waya da ice cream kafin ya kai su airport. A mota yana ta hira da Inna.
“Inna, kwana nawa zata yi ne?"
"Shekara.” Inna ta faɗa kai tsaye tana kallon waje.
Musharraf ya yi dariya sosai, “Haba uwargida! Ya da gatse?”
Inna ta juyo da dariya, “To na gan sai tambaya kake yi tun a gida, kamar baƙon waje zata tafi, ko kai ka fi mu sonta ne?”
“A’a fa… kawai dai ina so ta dawo da wuri ta yi registration, ta rubuta carry over ɗinta. Shi yasa.”
Zahra ta zauna a baya da Zainab, suna jin maganganun su ba tare da tsoma baki ba. Daga ƙarshe ma sabuwar wayarta ta fitar suka fara setting ɗin shi.
Suna isa airport kuwa da mintuna kaɗan aka fara kiran boarding. Zahra ta rungume wayarta ta kwanta a kujerar jirgin tamkar wacce aka zuba a kwando; bacci mai nauyi ya ɗauketa tun kafin jirgin ya daidaita a sama. Ita dai duk tafiya da ta saba yi a hanya da zarar iska ta ɗan buga fuskarta, sai ta nutse cikin duniyar bacci.
Suna sauka a filin jirgin hasken rana ya bugi fuskarsu, tafiyar taxi suka ɗauka zuwa gidan tsohon Senator Al-ameen. Suna ƙaraso ƙofar gidan mai girma, Zahra ta buga ƙaramar ƙofa da hannunta. Maigadi ya leƙo, sai idanunsa suka haska da annuri da ya ganta.
“Lalle, marhaba da amaryar seneta!” ya furta da murmushi mai faɗi, yana sosa kansa cikin fara’a.
Zahra ta yi masa dariya kaɗan, ta ce, “Yauwa, maigidan na ciki kuwa?”
“Eh mana. Tun ɗazun bai je ko ina ba, ina da tabbacin jiran zuwanku yake!”
Inna da ke gefe ta gyara gyalen kanta ta tsallake su ta ce, “Ke dai idan kin gama surutun nan sai ki shigo, Zahra.”
Wata ƴar dariya Zahra ta yi ta bi bayan Inna, maigadi kuma ya shigo musu da luggages.
Suna shiga babban falon gidan, suka tarar da Senator zaune yana karanta jarida, siririn gilashi a idonsa, yana daidaita sukar da yake yi wa shafukan labarai. Tsohon mutum ne mai tsantsar asalin Fulani, kyakkyawa irin wadda tsufa bai gusar ba; yana ɗauke dogon hanci, fata mai haske, da nutsuwa ta tsofaffi.
“Assalamu alaikum ,” Inna ta faɗa tana ɗan yin ƙasa da murya.
Senator ya ɗaga kai, murmushi ya bayyana a fuskarsa kafin ya maida hankalinsa kan Zahra, wacce ta shigo cikin sauri da farin ciki ya cika mata fuska.
“Grandpa!” ta yi ƙara cikin murna, ta yi gudu ta rungume shi kamar wacce ta yi kewar rai da rai.
Shima ya mike da kyar, ya jingina a sandarsa, yana dariya mai sauti. “Haba, amaryata! Na yi kewarki sosai. Ya kike? Jikin ya ɗan daidaita kuwa?”
“Alhamdulillah, Baba, na ji sauƙi sosai,” ta ce tana manne da shi.
“Alhamdulillah! Masha Allah! To zauna, bari in kawo miki ruwa da kaina.”
Ta zauna cikin murmushi, tana kallonsa yana tafiya cikin nutsuwar dattijo. Shi kansa sai zuciyarsa ta cika da farin cikin ganin ‘yar jikarsa lafiya.
Ya dawo da kofin fresh cucumber juice daga fridge, ya mika mata cikin kulawa. Zahra ta karɓa, ta yi sip ɗaya, nan take ta kwabe fuska.
“Grandpa, kai wannan juice ɗin sai kace magani! Wallahi babu daɗi,” ta yi maganar da dariya a murya.
Senator ya dafa mata kafaɗa. “Ku yara fa bakin ku ya saba da zaƙi kawai. Wannan ai lafiya ne.”
Ta miƙe da dariya, ta je fridge ta ɗauko exotic juice, ta dawo da cup ɗin. “Ɗandana wannan Baba, ka ji bambanci. Wannan ne juice, ba wancan ba.”
Senator ya girgiza kai yana dariya. “Ke dai sha zumami ce, yarinya.”
Suna cikin hira Inna ta fito daga ɗaki, ta sauya kaya zuwa simple wear. “Sannu da gida, Alhaji,” ta faɗa tana murmushi.
“Yauwa, Hajiya. Ya hanya?”
“Alhamdulillah."
"Sai dai me yasa ba ki sanar da ni za ku zo yau ba? Da sai na tura direba ya ɗauke ku.”
“Tunda mun iso lafiya, ai shikenan."
"To shikenan, bari na ɗsuko Miki ruwa." Ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa
"Ka huta, bari na dauko ruwan da kaina.”
“Kar ki damu,” Senator ya ce, amma Inna ta riga ta miƙe. Zahra ta tashi ta ce, “Bari na shiga ciki tunda uwargida ta fito, kar in zama yar kallo.” Dukansu suka yi dariya cikin farin ciki.
---
A gefe guda kuma Musharraf ya isa unguwar da Kassim ke zaune, bisa adireshin da Zahra ta ba shi. Cikin tambayar makwabta da bin bayan yara
, ya ƙaraso kofar gidan.
“Please,” ya ce wa wani yaro, “ka shiga, ka ce Kassim yana da baƙo.” ya faɗa yana naɗe hannun rigar sa kamar mai shirin dambe.
Yaron ya shiga gidan, ya tarar da Laure zaune a tsakar gida tana kula alalen siyarwa.
“Waye ke nemansa?” Laure ta tambaye shi, tana jujjuya kwanon alalen.
“Wani babba ne a mota. Big car ya zo.”
Tsoro ya bayyana a fuskarta. Ta ɗauki mayafi, ta fito. Musharraf wanda zuciyarsa ke cike da fushi, ya tsaya tsayin daka a gaban motarsa yana jiran fitowar Kassim ya fara kai masa naushi. Amma sai ya yi mamakin ganin mace ta fito.
“Assalamu alaikum,” Laure ta gaishe shi cikin tsoro.
Ya ɗaga mata hannu. “Ina Kassim?”
“Bai nan. Tafiya yayi, wallahi.”
“Ina ya tafi?”
“Ban sani ba,” ta ce tana rawar murya.
"Ke! Ba fa da wasa kazo ba, ina kassim?!"
"Wallahi yayi tafiya, bai kuma sanar dani inda zai tafi ba." Ta faɗa cikin matuƙar tsoro.
“Ke ce Laure?”
“Eh ni ce… Allah ya sa ban yi kuskure ba,” ta ce tana share zufa.
Musharraf ya buɗe motarsa, ya ɗauko wani envelope, ya miƙa mata. “Buɗe wannan.”
Tana karkarwa ta buɗe. Ta hangowa kudade ne – daloli! Idanunta suka zaro.
“Kin san Zahra?” Musharraf ya tambaya.
Kai ta gyada. “Kishiyata ce.”
“Madalla. Wannan saƙon ta ne. Idan Kassim kuma ya dawo daga duk inda yake ɓuya, ki ce masa ya aika min da takardar sakin ta kafin mu sake haɗuwa. Ki kuma sanar masa; idan ɓera na yawo, mage ma tana yawo. Zai iya gudu zuwa duk inda ya gan dama, amma ranar haɗuwa tana nan zuwa, sai ya ɗanɗana kuɗarsa. Zan iya yafe komai, amma ba zan yafe abin da ya shafi Zahra ba.”
Ya faɗi haka, ya shiga motarsa ya bar layin cikin speed. Laure ta tsaya, baki a buɗe, zuciyarta na bugawa. Sai da motar ta ɓace daga idonta, ta rungume envelope ɗin a kirjinta, hawaye suka zubo.
“Allah sarki Zahra,” ta ce a hankali, “kin cika yar halas. Allah ya saka miki. Ni kuwa yau na zama Hajiya Laure!”
Tana dariya ta koma gida da murna, ta kwashe alalen da tayi na siyarwa, ta kai ƙarƙashin gada ta raba wa mabukata.
---
A can gida kuma Mama ta fara narkewa a cikin tashin hankali. Tunanin saki da Alhaji Bashir ya mata ya yi nauyi sosai a ranta. Duk kiran da take masa baya ɗagawa. Kullum sai ta zauna tana jin zuciyarta na ƙuna.
A wannan daren, tashin hankali ya yi yawa har jikinta ya kasa ɗauka. Blood pressure ɗinta ya hau sama sosai. Inna Habi ta kira wata maƙociyar su ta taimaketa. Aka kwashe Mama cikin tashin hankali aka garzaya da ita asibiti. Likitoci suka fara mata treatment na gaggawa, zuciyarta tana bugawa da sauri tamkar zata faso ƙirji.