AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 47

by @jikargarba001

"Miss, if you don't mind, nayi dropping ɗinki a gida. Motarki tana buƙatar mechanic ya duba ta."

Zahra ta ɗan kalle shi, tana lura da yadda ruwan sama ke sauka a jikinsa da ƙarfi har ya jiƙa shi gaba ɗaya. A hankali ta miƙa masa umbrella tana cewa;

"I will just order a ride, just go."

Ba tare da ya krɓi lemar hanunta ba, ya ɗan girgiza kai sannan ya ce da cikin natsuwa;

"I insist to take you home."

Zahra ta ɗan runtse ido, tana jin sanyi sosai har cikin ƙashi, sai ta murmusa a cikin ranta tana mamakin yadda shi kuma ke tsaye a cikin wannan ruwan sama.

"Pls, ka tafi kawai. Baka jin sanyi ne?" Ta tambaya da raunin murya.

Yusuf ya ɗan yi shiru, sai kuma ya amsa da murmushi mai kyau

"Ina jin sanyi har cikin ƙashi na, but I'm going nowhere har sai Miss beauty ta yarda na rage mata hanya."

Zahra ta ɗan turo baki cikin rashin so, ta yi ƙaramar tsaki sannan ta kama umbrella ta fara tafiya zuwa karkashin wani shade domin ta yi ordering Uber. Sai dai a ruwan, Yusuf ya jingina a jikin motarta yana kallonta, idonsa na biye da ita tamkar wani abu ya riƙe shi a wajen.

Bayan ɗan lokaci, ya biyo ta har inda ta tsaya, murya cike da roƙo ya ce;

"ƴan mata, don girman Allah, na rage miki hanya."

"Mallam, wai an turo ka wajena ne?" Ta faɗa cikin fusace tana ƙoƙarin gujewa jin tausayi a kansa.

Yusuf ya murmusa, ba tare da ya ja da baya ba;

"Ni na turo kaina… saboda ganin dacewar hakan."

Dogon bayani ya ci gaba da yi mata har ta gaji, babu yadda ta iya. A ƙarshe dai ta bishi a baya zuwa inda yayi parking motarsa. Ya buɗe mata front seat da girmamawa, ta shiga ta zauna. Shi kuma ya zagaya ya shiga driver's seat, jikinsa duk ya jiƙe da ruwa, hakan yasa ya kashe AC ɗin motar.

Yana reversing, ya ɗan juyo ya kalli yaransa dake baya suna shan ice cream, cikin kuka ya ce;

"Sorry, sweethearts, daddy kept you waiting."

Yaran suka amsa da murna, suna fara hira da shi. Sai ya ɗan juyo ya kalli Zahra da ta dafe lemar a cinyarta, yana cewa cikin nutsuwa;

"Your address?"

Ta yi shiru na ɗan lokaci sannan ta kwatanta masa gidan su. Sai ta juya kai ta maida kallonta ga titin da ake wucewa.

"My name is Yusuf," ya ci gaba da cewa, murya mai sanyi da natsuwa. "I work with FIRS… and I’d like to know you."

Zahra ta yi kamar ba ta ji shi ba, shiru ta yi, zuciyarta na dokawa. Can dai ta ce a taƙaice;

"Zahra."

"Is that your name?" Ya tambaya, yana kallonta da murmushi.

Kai kawai ta gyada masa, ba tare da ta dube shi ba. Suka ci gaba da tafiya a shiru, sai surutun yaran a bayan mota ke ratsa zuciya.

Bayan wasu mintuna, Yusuf ya shiga area ɗinsu. "Your house number?" Ya tambaya.

"10." Ta faɗa a takaice.

Ya yi parking a gaban gidan. Zahra ta fara kiciniyar buɗe ƙofa, amma ta ji an kulle. Sai ta juya ta kalle shi tana cewa cikin ladabi:

"Zan sauka.

Ya ɗan juyo, idanunsa na cike da natsuwa amma murya ɗauke da daƙiƙar soyayya;

"Ki ɗan bani lokacin ki please. Ina son nayi magana dake."

Zahra ta kalli agogon hannunta, ta dubi waje inda ruwa ke sauka da ƙarfi, sannan ta ce;

"Ina ji."

"Dan Allah idan babu damuwa, ki bani lambar wayarki. Zan kira ki in na kai gida."

Zahra ta ɗan murtuƙe fuska tana tambaya cikin tsananin mamaki;

"For what? Me zai sa ka kirani?"

Yusuf ya ɗan lumshe ido ya ce cikin gaskiya;

"Saboda zuciyata na sonki. Ina son in bata mata abinda take so."

Zahra ta ɗan yi murmushi mai cike da takaici, sai ta ce;

"Da kayi haƙuri… babu wani space na soyayya a zuciyata."

Ya ɗan yi shiru sannan ya murmusa ya ce:

"To ai zan creating space ɗina da kaina… sai ki saka ni a ciki, ko da ƙarami ne."

Zahra ta yi jim, zuciyarta ta yi mata nauyi. Ta dube shi na ɗan lokaci sannan ta dubi yaran a bayan mota. Da sauri ta ce;

"Mu bar maganar nan. Akwai yara a nan."

"Yaran ba sa jin wannan, hankalinsu yana kan ice cream. Amma idan kina so mu dakata… sai ki bani lambar ki kawai."

"Mallam," ta ce da tsantsar takaici, "ba zan iya baka lambata ba… saboda ina cikin idda."

Yusuf ya yi mamaki, idanunsa sun faɗaɗa.

"Subhanallah…! Ashe akwai irin mace har haka? Wadda ta tsaya akan doka da darajar kanta? Ki yi haƙuri ban san kina da aure."

Sai ya ɗan yi shiru kafin ya ce da girmamawa;

"Ki yi haƙuri. Ban san kina da aure ba lokacin da na tsaya na tare ki. Amma ki yi min alfarma ɗaya…"

Zahra ta yi shiru, ta lumshe ido, tana fatan zai yi shiru ya buɗe mata mota ta fita. Amma sai ya ci gaba da cewa;

"Ki faɗa min, yaushe zaki fita idda? Don idan mijinki bai mayar dake ba, na zama mutum na farko da zai fara gwada miki soyayya."

Ɗan kallo ta yi masa, idonta cike da gajiya da rashin so. Ta matsu ta fita daga motar. Sai ta gyara murya ta ce da gajiyawa;

"Nan da sati biyu."

"Ok, idan—"

Ta dakatar da shi da hannu, cikin murya mai ƙarfi;

"Ka buɗe min ƙofa. Ba zan ƙara amsa ka ba."

Ya jinjina kai a hankali, ya buɗe mata ƙofa.

"Thanks for the ride," ta ce a taƙaice tana fita daga motar.

Idonsa ya bita har ta isa ƙofar gida. Ta ƙwanƙwasa, maigadi ya buɗe mata, da sauri ta shige ciki saboda ruwan da ke dukanta. Yusuf ya zauna yana murmushi, ya shafa sajensa, sannan ya tayar da motar ya wuce tare da iyalansa.

---

A gefe guda kuma, Daddy ya ƙara kula da Mommy, ya gane cewa kishin da yake damunta, ashe soyayyarsa ce kawai take cika mata zuciya. Ya rungume ta da ƙauna da fahimta.

Mama kuwa, bayan ta samu sauƙi daga rashin lafiya, sabon shiri ta fara. Tana neman yadda za ta tarwatsa Mommy da farin cikinta gaba ɗaya. Ginshiƙin farin cikin Mommy dai bai wuce Zahra ba. Wannan ya sa Mama ta ƙara tsanarta fiye da da.

Musamman ganin yadda Daddy ke ƙara nuna wa Mommy ƙauna a fili, da yadda Mommy ke samun ɗaukaka a wajen aiki, ya ƙara hura mata wutar kishi. Mama ta rantse sai ta daƙuhe Mommy, ta mayar da ita abin tausayi.

Tun bayan dawowar Mama gida, bata yi waya da Turai ba. Amma yau ta ɗauki shawarar sai ta kira ta, domin su haɗa kai wajen shirya mugun makircin da suka saba.

A gefe guda, Farida ta fara ja da baya daga muguwar hanyar da Mama ke turata tun ranar da Zahra ta roƙa ta dawo gida. Ta fara gane cewa yin sharri ga wanda bai cancanta ba, ba ya da amfani. Ta zauna tana nazari; me yasa suke ƙuntatawa Zahra alhalin bata taɓa yin musu laifi ba? Mutum ce mai sauƙin kai, mai ɗaukar kowa da mutunci. Tabbas, ta fi kowa sanin baƙin ciki fiye da farin ciki.

Farida ta yi faɗa da kanta, ta kuma kira Laura, ta nuna mata gaskiya. Laura dama ba ta cika shiga cikin batun cutar da Zahra ba, sai dai bin umarnin Mama kawai.

Sun yanke shawarar jiran dawowar Zahra domin su bata haƙuri, su haɗa kansu da ita a matsayin manyan ’yan uwa, su barta ta rike matsayin da ya dace da ita. A nan suka ce su koma gidan daidaito da soyayya. Amma duk wannan shirin ba tare da Mama ta sani ba

***

Laure tana tsakar gida tana tsintar wake kamar wacce take cikin mafarki, sai ta ji sallamar Kassim. Ta miƙe da sauri, tana kallonsa da mamaki.

"Wayyo, wa nake gani kamar Kassim? Hala ɓatar hanya ka yi ne?"

Ko kallonta bai yi ba, balle ya tanka. Ya shige ciki kai tsaye. Kai tsaye ya fara binciko ƙullin kayansa da ya bari lokacin da ya bar gida. Daga baya ya fito da wani file, ya buɗe ya dudduba. Credentials ɗinsa ne a ciki, sai takardar gidan da suke ciki. Ya rufe file ɗin ya ɗauka, sannan ya fito daga ɗakin.

Ya tarar da Laure tsaye a bakin ƙofa tana kallonsa, ta ɗaure fuska.

"Na faɗa miki ki koma ƙauye kin ƙi, ko? To, zan siyar da gida, sai ki nemi wajen zama."

Dariya ta yi mai cike da shu’umanci, hatta da tafa hannu.

"Ai Kassim, jiya ba yau ba. Yanzu da kake ganina, ni mai ƙarfin biyan kuɗin haya ce. Koda baka faɗa ba, ni ma na kusa barin maka wannan kongon da kake tutiya da shi. Mtsshew!"

Ta buga tsaki, ta juya ido.

Kassim ya tsaya yana kallonta da mamaki, zuciyarsa na cike da takaicin halin rashin tsoro irin na Laure . Sai kawai ya ce;

"Ya miki kyau, idan aka zo aka yi Miki watsi da kayan ki zaki sani"

Ya girgiza kai, yana shirin ficewa daga gidan.

Laure ta yi saurin cewa cikin yanayin raini;

"Ga saƙo daga yayar matar ka, Zahra. Ya ce duk lokacin da ka dawo ka aika masa da takardar sakin ƙanwarsa. Kuma yace in sanar da kai; idan ɓera yana yawo, to mage ma tana yawo."

Kassim ya tsaya cak. Zuciyarsa ta faɗi da ƙarfi. Wallahi yana jin tsoron dangin Zahra, musamman idan ya tuna halin da ya jefa Zahra a ciki. Ya juya ya koma ɗaki, ya ɗauki paper, ya zauna ya rubuta wa Zahra saki ɗaya. Yana fitowa ya mika wa Laure.

"Idan ya sake dawowa ki bashi wannan. Kuma ki faɗa masa cewa duk yawon mage, ba zai taɓa kama wannan ɓeran ba domin kuwa shegen wayo ne da ita."

Laure ta yi masa kallon raini, sannan ta karɓi takardar kamar wata muguwar nasara ta samu.

Yana shirin ficewa, ta ƙara masa magana cikin ƙin yarda;

"Yanzu haka zaka sake tafiya ba tare da ka sanar da ni inda zaka je ba? Ba ka kuma bayar da kuɗin abinci ba, balle na makarantar yara."

Kassim ya yi banza da ita ya fice daga gidan.

Laure ta ɗauki wayarta da take ajiye gefe, ta danna lambar Zahra.

---

A lokacin Zahra na kwance tana hira da Inna da Sen. Suna jiran Musharraf ya iso don su koma Kaduna. Sai kiran ya shigo. Zahra ta ɗauka ta kara a kunne, ta yi shiru.

Laure ce ta fara magana, cikin ƙasƙantar da murya amma cike da kissa;

"Hello Zahra. Yau sai ga Kassim ya zo gida."

Zuciyar Zahra ta buga da ƙarfi, ta dafa ƙirjinta saboda faduwar gaba.

"Hello, kina jina kuwa?" Laure ta ƙara faɗi.

"Eh, ina sauraren ki. Wai me ya zo yi?" Zahra ta furta cikin rauni da dauriya.

Inna da Sen suka dubeta da damuwa, suka lura da yadda yanayinta ya sauya nan da nan.

"Oho masa shi ya sani. Duk ba wannan ba, ga shi nan, ya bani takardarki."

"Wane irin takarda?" Zahra ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Takardar sakiana. Wai idan yayanki ya kuma zuwa na bashi."

"Takardar saki…?" Zahra ta maimaita cikin rawar murya. Hawaye masu zafi suka gangaro daga idonta. Da ƙyar ta iya murza zuciyarta ta ce;

"Nagode Laure… zan faɗa wa yayana."

Ta katse kiran, ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

Inna da Sen suka nufo ta da sauri, suna tambayarta me ke faruwa. Amma kuka kawai take iya yi. Sen ya miƙa mata ruwa don ta sha ko zuciyarta ta yi sanyi. Ta ƙi.

Sen ya ɗaga murya, cikin damuwa;

"Bani wayar ki na ga da wa kika yi waya. Kuma ki faɗa mana me ke faruwa."

Zahra ta ce cikin kuka mai cike da rauni;

"Kassim ne… ya sake ni."

Duka Inna da Sen suka tsaya cak, sun yi shiru na ɗan lokaci. Shin wannan ne dalilin kukan nata? Ba dai abinda suke jira kenan ba? Amma saboda kada su ƙara mata nauyin damuwa, suka fara lallashinta. Suka yi mata nasiha da faɗa game da amfanin imani da ƙaddara.

Cikin wannan yanayi Musharraf ya shigo. Zahra na ganin shi ta yi saurin faɗa jikinsa, ta sake sabon kuka mai tsuma zuciya.

Musharraf ya firgita da yadda take kuka. "Menene?" Ya tambaya, yana ɗaga habarta don ya kalli idanunta.

"Yaya…" ta kira shi da rawar murya, ta sake fashewa da kuka.

Ya girgiza kai alamar bai don kukan. Ya share mata hawayen da suka cika fuska, sannan ya ce;

"Faɗa min menene?"

Ta kwantar da kanta a kirjinsa, tana shesheƙa.

Inna ta taɓe baki ta ce cikin takaici tace;

"Wai tsinanen yaron nan ne fa ya sauwaƙa mata. Shine take wannan kukan."

"Wai Kassim?" Musharraf ya tambaya, yana kasa yarda.

"Shi fa," Sen ya amsa cikin takaici.

Musharraf ya ɗauki Zahra daga jikinsa ya dubeta da fushi.

"To me yasa kike kuka don ya sake ki? Ba abinda dukkanmu muke so kenan ba? Ko dai kina son sa ne?"

Zahra ta girgiza kai tana kuka.

"Mtsshew!" Musharraf ya yi tsaki.

"Je ki ɗauko jakarki mu tafi. Wannan kukan babu tushe, kuma ba zan ɓata lokacina ina lallashinki saboda tsinanen nan ya sake ki ba."

Zahra ta buɗe baki ta fashe da kuka sosai. Musharraf ya nufo ta cikin fushi.

"Zaki ɗauko jakarki mu tafi ne ko sai na tattaka ki a nan?"

Da gudu Zahra ta shige ɗaki tana kuka. Ta ɗauko jakar da ta riga ta haɗa da safiyar yau. Cikin sanyin jiki ta fito tana goge kwalla, ta nufi waje ba tare da ta amsa sallamar su Inna ba.

Sen ya yi murmushi, ya ce;

"Yaya Musharraf, ka kiyaye ni dai. Me yasa zaka yi wa amaryata tsawa haka, gashi ka ɓata mata rai."

Musharraf ya ɗan yi dariya.

"Amaryar nan, wani lokaci bata da hankali. Har yanzu ban gane dalilin kukan nata ba."

Dukkansu suka yi dariya suka raka su har motar.

Zahra ta zauna a baya, ta ƙi zama a gaba, ita a dole tayi fushi. Ko ɗago kai ta kallesu bata yi. Musharraf ya shiga mota ya ja suka bar gidan.

A baya Zahra ta ci gaba da shesheƙan kuka. Da farko Musharraf ya yi haƙuri, amma daga baya ya gaji. Ya daka mata tsawa cikin ƙarfi;

"Will you shut up and wipe those tears!"

Amma maimakon ta yi shiru, sai ta ƙara fashewa da kuka mai ƙarfi.

Musharraf ya yi parking a gefe, ya fito ya buɗe mata ƙofar baya.

"Fita min a mota!"

Zahra ta yi banza, ta ci gaba da kuka.

"Na ce fita ko!" Ya ɗaga murya.

Jiki na ɓari ta fito tana goge hawayenta.

Ya rufe ƙofar, ya ciro kuɗi daga aljihunsa, ya watsa mata a ƙasa.

"Idan kin gama kukan, sai ki tare motar haya ki zo gida."

Ya juya ya shiga mota, ya ja da speed ya bar wajen.

Zahra ta tsaya cak, jikinta na rawa, hawaye na zuba. Kamar wata da aka zubar a tsakiyar hanya. Ta share idonta, ta ɗaga kai tana kallon hanyar da motarsa ta bace. Mamaki ya cika zuciyarta. Ita ce yau Musharraf ya yi mata haka?