AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Page 87

by @jikargarba001

Washegari jikin Imam ya ɗan yi sauƙi, Driver ya tuƙa shi zuwa Kano, Ya A'isha kuma ta koma ɗakinta.

Biki saura kwana uku aka yi wa Zahra jere a gidan da Abba ya siyawa Imam.

A ranar Imam ya dawo Kaduna, tare da su Ammi.

A gidansa da suka saba sauka, ya sauke su bayan sun duba sabon gidansa, da aka jera expensive furnitures ɗin Zahra.

Da yamma gidansu Zahra ya cika maƙil da mutane, kowa cikin shirin alfarma, masu anko sun fito cikin akonsu mai kyau. Shirye-shirye ake yi ta ko ina. A gefen girke-girke an sauke abinci ana packaging a takeaways.

A ɗakin Zahra kuwa, ita da ƴan uwanta ne da Sofia, su na ta koɗa kyau da ta yi. Sosai Zahra ta yi kyau kamar a sace ta a gudu, sanye take cikin dark purple gown ɗin material na material da aka yi mishi professional ɗinki mai kyau, an yi mata simple make-up wadda ya ƙara fito da kyaunta, tana sanye da silver jewelries masu danƙaran tsada, tsaf ta fita amarya abinta.

Farha ta miƙa mata clutch ɗinta silver color, aka ɗora mata net veil daga kanta ya sauko har ƙasa.

"Wow!" Dukka mutanen ɗakin suka faɗa lokaci ɗaya, a lokacin da Farha da Haj. Falmata mai make-up suka gama shirya Zahra. Hotuna suka fara yi a ɗakin cikin farin ciki.

Tunanin Zahra gabaki ɗaya baya hotunan da ake daukawa, tunanin Imam take yi, tunda garin Allah ya waye yau ba su yi magana ba, and this is so unusual, ta riga da ta saba kullum sai sun yi waya tun lokacin da ya yi rashin lafiya.

A kunne ta raɗawa Farha da ke riƙe da wayar ta; "Bai kira ba har yanzu?"

Farha ta girgiza mata kai alamar a'a. Karbar wayar ta yi, ta yi dialing lambar Imam.

Imam na bacci wayarsa ta fara ringing, lalubar wayar yayi, ba tare da ya duba me kiran ba ya picking, ya kai wayar kunensa.

"Hello Yaya..."

Buɗe idonsa yayi da kyau jin muryar Zahra, ya ce; "I'm sorry I haven't called through out today."

Murmushi ta yi, tace; "Babu komai, hope you're fine?"

"Yes I am, ya bikin?"

"Yanzu zan fita, shine na ce let me call you first na ji ko lafiya."

"Lafiya ƙalau, I'm just stressed."

"Ok, have a rest."

"Uhum, take care." Ya faɗa murya ƙasa-ƙasa.

Murmushi Zahra tayi ta katse kira.

Farida ta ɗan kalleta, cikin zolaya ta ce "Hmmm Iyayen ƙauna."

Zahra ba ta kula ta ba, ta gyara mayafinta, Farha ya riƙe hannunta na dama suka fita daga ɗakin, sauran ƴan uwansu na biye da su a baya zuwa filin gidan da aka ƙawata shi da decoration mai kyau don yin kamu. Zahra na fita MC ta fara yi mata kirari tana koda ta, mata kuwa sai guɗa ake yi, har ta zauna a wajen da aka tanada domin ta.

Cikin nutsuwa da maturity aka gabatar da Kamun Zahra, wadda Mama ko leƙa wajen ba ta yi ba, saboda baƙin ciki. Tunda Mama ta kyalara ido ta gan kayan lefen Zahra, ta san ta kwafsa da ba ta lalata auren nan tun farko ba. Kaya ne aka zubowa Zahra sosai na a zo a gani, masu tsada da ɗaukar hankali, lefe ne da babu ƴar da aka taɓa kawo mata ko rabin shi a gidan, lefe ne da bata taɓa tsammanin Zahra za ta samu irin shi ba, yanzun gabaki ɗaya tunanin Mama ya cunkushe, tunanin hanyar da za ta hana auren nan da gaggawa take yi. Gashi Hajiya Turai ba ta ƙasa balle ta taimaka mata, ga Farida da ta rage mata a gidan ta juya mata baya