AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

PAGE 102

by @jikargarba001

Bayan foreplay na mintoci, Imam ya mayar da Zahra tashi, ya ƙula wani special bond a tsakaninsu, ya kuma mayar da ita cikakkiyar mace.

Despite how gentle Imam was, Zahra ta sha wuya sosai, duk yadda ta so ta daure it get to a point da saida ta fashe da kuka, she felt a sharp pain da ba ta taɓa tunanin haka abun ya ke ba, ta bashi haƙuri har ta gaji, but a lokacin Imam ya zama kurma, ba ya jin magiyarta.

Rungumeta Imam ya yi yana patting bayanta, tana silent kukan pains da kuma shagwaɓa.

Murya cike da shauƙi Imam yace; "I'm sorry wifey, ki yafe ni kin ji."

Zahra kuwa ta kasa ɗago kanta, sai ɓoɓɓoye fuskarta take yi a kirjinshi saboda kunya.

"Bari na haɗa miki ruwan wanka ki yi sit-bath za ki fi jin ƙarfin jikinki." Imam ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa, Zahra ta fashe da kuka tana ƙanƙame shi.

Bayanta Imam ya shiga shaidawa cikin lallashi, yace; Shikenan ba zan tashi ba, it's ok."

Ya gyara mata kwanciya a jikin shi, yana shafa mata kai a hankali, ita kuma tana ta ƙananun kukan shagwaɓa, a haka har ya ji ta fara sauke numfashi a hankali alamar ta yi bacci. Ciɓ ya ɗauketa ya kwantar akan cushion, ya duba wardrobe ɗin hotel ɗin, lucky enough ya gan extra bedsheet, ya cire wanda jini ya ɗan ɓata ya shimfiɗe sabon, cicciɓar Zahran ya ƙara yi, ya mai da ta gado. Bathroom ya shiga da bedsheet da ya cire, sai da ya wanke shi tsaf kafin ya yi wanka. Bayan ya gama wanka, ya tara ruwan ɗumi ya ɗan zuba dettol kaɗan a ciki, fita daga bathroom ɗin ya yi ɗaure da towel a ƙugunshi. Gaban gado ya tsaya yana kallon Zahra da ke bacci, idanunta sun kumbura, leɓanta ya yi pink sosai, ba tare da ya tasheta ba ya ɗauketa cib zuwa bathroom, cikin ruwan ɗumi da ya tara ya sauketa. Cikin bacci Zahra ta ji ta cikin ruwan ɗumi, ga wani zafi da ta ji tun daga private part ɗinta har ƙwaƙwalwata, kuka ta fashe dashi, ta rirrike hannun Imam tana son ta fito daga cikin ruwan, daneta ya ɗan yi, duk da kukan da Zahra ta rinƙa yi sai da Imam ya tabbatar da ta yi ten minutes a cikin ruwan ɗumin kafin ya cirota, ya zubar da ruwan, da kanshi ya yi mata wankan soso da sabulu, yana lallaɓata kamar jaririn yau, Zahra kuwa na zuba shagwaɓa son ranta.

Bayan ya gama wanketa tsada, ya ɗora haɓar shi a kafaɗarta, cikin husky voice ya ce; "Za ki yi wankan tsarki ko dai na yi miki da kaina."

Ture shi t ɗan yi, sai ta zumɓura baki, tace; "Ka fita mana to."

Hannu Imam ya ɗaga sama, yace; "As you wish my lady." Sai ya fita daga bathroom ɗin.

Simple night wear ya Ciro mata, ya feffesa masa turare, kafin shima ya shirya.

Yana zaune a bakin gado ta fito, tana tafiya da ƙyar, ƙafa a gwagwale kamar wacce aka yi wa kaciya, da sauri Imam ya miƙe da sauri ya ƙaraso wajenta, ɗaukarta ya yi zuwa kan gado, ya zaunar da ita, kwanciya ta yi tana mai da numfashi. Daga kwancen Imam ya shafa mata mai tsaf, kafin ya gama shafa mata man bacci ya ɗauke ta, murmushi ya yi ya rufeta da bargo kawai ba tare da ya saka mata kayan barcin ba.

Sallah raka'a biyu ya yi, ya godewa Allah da ya mallaka mishi Zahra, kuma a budurwa.

Folding darduman ya yi, ya ajiye sannan ya kwanta a gefen Zahra, ya ja ta cikin jikinshi ya rungumeta, A hakan bacci ya ɗauke shi.

Ƙarfe bakwai ɗin safe Imam ya farka daga bacci, cire Zahra ya yi daga jikinshi ya kwantar da ita a kan gadon.

Ya tashi daga kan gadon, alaula ya yi, yayi sallar Asuba.

Yana. Iddar da addu'o'insa ya koma bakin gadon, ya taɓa goshin Zahra da yayi zafi rau, sumbatar goshin nata yayi, ya miƙe ya fita daga ɗakin.

Ɗakin su Ammi ya fara shiga ya gaisheta, kafin ya fita daga hotel ɗin. Pharmacy ya tafi, ya siya wa Zahra maganin, sannan ya tafi eatery ya siyo musu abinci, kafin ya koma hotel.

Su Ammi ya fara kai wa abincinsu, kafin ya wuce ɗakinsu, har ya koma ɗakin, Zahra na bacci, shafa kanta ya yi a hankali ya ce; "I'm back my love."

A hankali Zahra ta fara buɗe idanunta da suka yi mata nauyi, ta ɗan gyara kwanciyarta tana sake lumshe ido.

"No please, ki tashi ki ci abinci ki sha magani sai ki koma baccin."

Shiru Zahra ta yi mishi.

"Please my love kin gan kina running temperature, Kin?"

Imam ya faɗa yana ƙoƙarin ɗagata.

"Ni ka bar ni, ai kaine ka janyo, sai da na ce maka ban shirya ba." Zahra ta faɗa tana kukan shagwaɓa.

Rungumeta Imam ya yi, yana bubbuga bayanta, yace; "I'm sorry, ki yafe mini, I promise ba zan sake ba sai da yardar ki, kawai yanzu ki ci abinci, ki sha magani, ba ki ma yi sallah ba and is pass eight already."

A hankali Zahra ta miƙe ba tare da ta cewa Imam komai ba ta fara takawa a hankali zuwa bathroom, alaula ta yi, ta fito, darduman da ta gani a shimfiɗe, ta zauna a kai ta kabbara sallah, bayan ta idar a kan darduman Imam ya kawo mata abinci, ɗebawa yayi a spoon, ya ce; "Haaaaa, open your mouth."

Kau da kai gefe ta yi, Imam yace; "Please wifey, ki ci ko kaɗan ne ki sha magani."

Da ƙyar Imam ya lallaɓata ta fara cin abincin, kaɗan ta ci tace ta ƙoshi, Inam ya rufe abincin don bai son ya takura mata, ya ɓalli magungunan da ya siya mata, ya bata da ruwa, da kƴar ta haɗiye maganin tana yamutsa fuska, Imam ya haɗa ruwan Allura, ya ja a sirinji, yace; "Let me give you this injection it will help."

Yamutsa fuska tayi, tace; "Ba na so."

Kwanciya ta yi akan darduman, duk yadda Imam ya yi da ita ta koma kan gado saboda sanyi, amma ta ƙi kulasa ta yi kwanciyarta a wajen. Tana fara bacci, Imam ya ɗauketa zai kaita kan gado, ta fashe da kuka, tana faɗin; "Ka bar ni, na fi son ƙasan."

"No Fatima, akwai sanyi a ƙasar, kar ciwo ya kama ki."

Kwantar da ita ya yi akan gadon, shima ya kwanta a gefenta ya janyota jikin shi.

Bacci suka yi har ƙarfe ɗayan rana.

lokacin kai Ammi asibiti Nana ta zo ta yi ta buga ƙofar ɗakinsu amma shiru, sai Ammi tace su tafi kawai tunda sun san Asibitin, har suka tafi asibitin suka dawo, su Zahra ba su farka ba, Ammi ta yi wa Zahra two missed call, sai kawai ta kira Imam, kiran ne ya tashe su daga baccin.

Imam ya ɗauki wayar, murya a ɗan shaƙe yace; "Hello Ammi."

Ammi tace; "Imam ina ka shiga ne?"

Sosa ƙeyarsa ya yi, yace; "Matatace ba ta ji daɗi ba."

"Subhanallah me ya sameta? Ga Ni nan zuwa ma."

Da sauri Imam ya fara kame-kame, yace; "A'a Ammi ba sai kin zo ba, jikin da sauƙi."

Katse kiran Ammi ta yi, tace; "Mu je ɗakin nasu Zahra ba ta ji daɗin jikinta ba."

Zahra kuwa kuka ta fara yi wa Imam tana karfe hannu, wai shikenan yanzu Ammi za ta fahimci komai da ya faru, Imam na cikin lallashinta suka ji ana knocking ƙofa. Imam ne ya tashi ya buɗewa su Ammi ƙofa suka shigo, Deen ne ya fara hawa gadon ya kalle Zahra yace; "Sorry momma, Ammi said you're sick."

Murmushi ta yi masa, ta shafa kansa, tace; "I'm feeling better now."

Ammi ta kalle Zahra da ta looking so pale, ga idanunta sun kumbura, ta matso kusa da gadon, tace; " Sannu Zahra, ya jikin?"

Ƙoƙarin miƙewa Zahra tayi don ta zauna, sai ta tuna babu kaya a jikinta, bargon ta ja ta rufe jikinta da kyau, kafin ta yi ƙoƙari ta zauna tana ɗan yamutsa fuska, murya a shaƙe na bacci da kukan da ta yi, tace; "Da sauƙi Ammi, daman Zazzaɓi ne."

Ammi dai ta rinƙa kallon Zahra tana observing ɗinta da ido, sai ta yi murmushi, tace; "Allah ya ƙara sauƙi to, kwana biyun nan sai zazzaɓi ake yi."

Imam dai ba gefe ya ƙi yarda ya haɗa ido da Amminsa, kuma ta lura da hakan, amma sai ta yi kamar ba ta gane ba.

Ta kalle Nana bayan sun gaisa da Zahra, tace; "Mu je Nana."

Imam ya ɗan daure yace; "Ammi ki shirya, yanzu zan zo mu tafi asibiti."

"Ni na tafi ko, sai dai ka kai matarka a duniya, don kamar zazzaɓin nan ya shigeta sosai." Ammi ta faɗa tana daɗa kallon Zahra da ta sunkuyar da kanta.

Imam yace; "Ta sha magani, idan ba ta ji sauƙi ba har yamma sai a yi mata allura kawai."

"Allah ya sauwaka." Ammi ta faɗa, ta fita daga dakin Farida na biye da ita a baya.

Tun daga ranar da Imam ya san Zahra a matsayin mace suka buɗe sabon shafin soyayya da kulawa, Zahra kuwa sai zuba shawaɓa take yi yadda take so, Imam ya mayar da ita kamar kwai. Dukkan su biyun sun yi kyau sunyi fresh saboda kulawar da suke ba wa juna, ko a gaban Ammi soyayyar su suke yi, wani lokaci sai dai Ammin ta ji kunya ta bar musu wajen.

Jiya da daddare a gaban Ammi, Imam yayi pecking ɗin Zahra a baki, don tace ya yi kyau, kunya Ammi ta ji kamar ta nitse, pillow ta ɗauka ta jefe shi dashi, tace; "Tashi ka tafi inda za ka mara kunya kawai."

Murmushi ya yi, yace; "Bye Wifey." Kafin ya fita daga ɗakin. Ammi ta bishi da kallo baki a buɗe, she never knew her son can be a lover boy like this.

A gida kuwa, zama tsakanin Abba da Anty babu daɗi, saboda yanzu Abba ya daina ba ta kudi a hannu, yace duk abinda take buƙata ta faɗa shi zai siya mata da kanshi, amma babu batun ba ta kuɗi, kuma ya kafa mata dokar rashin fita, yace duk ranar da ta fita daga gidan ba tare da sanin shi ba a bakin aurenta, wannan dokokin sun biyo baya ne sakamakon wasu layoyi da Abba ya tsinta a ƙasar gado. Wata rana ya dawo daga office yana neman wani file ɗinsa, bai gani ba kuma ba Anty a gida hakan ya sa ya fara neman file ɗin, yana leƙa ƙasar gadon ya gan ƙuliƙulin magunguna da tarkacen layoyi, tattara layoyin yayi ya ƙula a leda ya kaiwa malaminshi Malam Aliyu wanda ya kasance mahaifi ga Ammi.

Malam Aliyu ya karɓi layukan ya tabbatarwa Abba da cewa asiri ne a ciki, a gaban Abban ya sa aka hura wuta aka ƙona su, a take baƙin hayaki ya rinƙa tashi.

Abba bai yi saurin ɗaukar mataki ba har sai da Anty ta kuma yin na biyu, Abba ya dawo daga wajen aiki da daddare yana buƙatar shan shayi, sai ya shiga kitchen ya plugging ruwa a kettle, ya haura sama ya sauya kaya, yana sauka ya shiga kitchen ɗin daidai Anty na fitowa, bai ce mata uffan ba ya shiga kitchen ɗin ya ɗauki cup ya juye ruwan ba kamar yadda ya saba zuba su coffee da suga kafin ya zuba ruwa ba, to his greatest surprise ya gan ruwan baƙi a cup, fita falo yayi da kofin, ya ajiye shi a gaban Anty, yace; "Me kika saka min a ruwa?"

Anty ta wani yamutsa fuska, tace; "Me kuwa zan sa maka?"

Rai a ɓace Abba yace; Ni ba yaron cikinki bane Sakina so better mind the way you talk to me, ta yaya zan ɗebi clean ruwa na plugging yanzu kuma na zo juye ruwa na gan baƙin ruwa?"

"Nima ban sani ba." Anty ta faɗa tana kunna TV da remote.

Abba ya kalleta kamar ya kwaɗa mata mari, yace; "Da ke mu da wani ne a gidan dole kice min ba ki sani ba, da mai aiki ta zo gidan nan ne yau sai a zarge ta, but I want to tell you something? Ya pointing ɗinta da hannu, yace; "Be very careful."

Tun daga ranar ya fara dafa Anty da ruwan jikinta, duk hanyar da Anty ke tunanin zata samu mafita abin ya gagara, kuɗaɗen dake account ɗinta duk ta ƙarar dashi a tura wa ƙawayenta wai su nema mata taimako a wajen malamai tunda Abba ya hanata fita. Ta ɓarar da kuɗi sosai kuma buƙata bai biya ba.