AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

PAGE 104/105

by @jikargarba001

Zahra na kwance akan darduman har ta fara gyangaɗi ta ji ƙarar ƙofa, ɗago idanunta ta yi tana kallon Imam da ya shigo ya tsaya a kanta yana doka murmushi.

"Lafiya?" Ta tambaye shi.

Tsugunawa ya yi, ya kawo fuskar shi saitin na ta, hancin shi na gogan nata, lips ɗinsu na brushing na juna, murya ƙasa-ƙasa cike da farinciki, yace; "In eight months and some weeks we're going to be parents wifey."

Zaro ido Zahra ta yi, ya gyaɗa mata kai alamar tabbatarwa. Zahra ba ta san lokacin da ta tallaɓo ƙeyarsa ta fara ba shi hot french kiss ba, Imam kuwa kamar mai zaman jira, ya fara mayar mata da martani, ganin abin na su ya fi ƙarfin darduma ya sa ya ɗauke ta cib sai kan gado. Daren ranar dare ne da ba za su taɓa manta da shi a rayuwar su ba, saboda sun ba wa juna extreme satisfaction, wasu abubuwan da Zahra ta yi wa Imam bai taɓa expecting zata taɓa yi ba saboda yadda a kowane lokaci take nuna kunya. Bayan all the lovey-dovey sai suka yi alaula, suka yi sallah raka'a biyu don nuna wa Allah godiya ga kyautar da ya yi musu, da kuma fatan Allah ya kawo mata nata laulayin cikin da sauki sannan ya raba lafiya.

Tun daga ranar da su Zahra suka tabbatar tana ɗauke da juna biyu Imam ya fara sabon taraiyar ta, daidai da aikin gida ya ɗauke mata yin komai, shi da kansa ke gyara gidan tsaf, girki kuma sai dai ta zauna daga gefe a kitchen ɗin ta rinƙa ba shi instructions, a office kuma ba ya yarda ta duba patients fin biyu a rana. Sosai dukkan su suke kula da unborn baby ɗinsu, Iyayyen Zahra ma ba a bar su a baya ba, don kullum cikin turo mata da kayan ƙwaɗayi da suka san mai ciki za ta buƙata su ke, Abba da Musharraf ba su taɓa tsallake kwana ɗaya ba tare da sun kira Zahra sun ji lafiyar jikinta ba tun daga ranar da suka san tana ɗauke da juna biyu. Ammi ma ta ba da gudunmawa wajen kula da Zahra for few days da ta yi bayan dawowarsu kafin ta koma Kano, ko da ta koma Kanon ma ba ta daina kirarta ta ji lafiyarta ba, ko ba ta kira bama Deen zai ɗauki wayar ya kira yace yana son ya ji ko Mommynsa ta riga da ta haifa masa little baby.

A haka kwanaki suka shuɗe zuwa satuttuka, satuttuka zuwa watanni, har cikin Zahra ya kai wata tara da kwanaki biyar, saboda yadda cikinta ya yi girma sosai, zama da ƙyar tashi da ƙyar ta daina zuwa wajen aiki, kafin Imam ya tafi wajen aiki yana fara dropping ɗinta a gidan Ya A'i, wasu lokutan kuma gidansu, don ba ya son zamanta ita kaɗai a gida, ta anytime za ta iya fara naƙuda.

Zahra na kwance a shagon Ya A'i su Akram na yi mata tausa a ƙafarta da ya kukkumbura sosai, Ikram tace; "Favorite Aunty your leg is like balloon."

Dariya sosai Ya A'i da Zahra suka yi, Zahra na murmushi tace; "Haka naki ma zai zama wata rana."

Girgiza kai Ikram ta yi, tace; "No, my leg is small." Tana nuna wa Zahra cute fararen ƙafarta da ke nan ɗan ƙarmi irin ta yara, murmushi kawai Zahra ta yi tashafa ƙafar.

Ya A'i na lura da yadda Zahra ke ta juye-juye, ta juya dama bayan few minutes ta juya hagu, sai tace; "Ya dai Zahra? Ko dai abun ya zo ne?"

Girgiza kai Zahra ta yi tana murmushin ƙarfin hali, tace;"Gaɓɓai nane duk ke ciwo."

"Sannu, ai daman da zarar ka ɗauki ciki to fa ciwo ne upon ciwo har sai kin sauke, Allah ya raba lafiya."

"Aameen." Zahra ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa, Ya A'i ta miƙa mata hannu, ta taimaketa ta miƙe tana tambayarta ko fitsari za ta yi, kai Zahra ta girgiza tace; "A'a, I just want to stroll ko zan ji dama-dama.

Ya A'i tace; "Yana da kyau hakan"

Tunda Zahra ta yi step ɗaya ba ta kuma yin na biyu ba, saboda yadda bayarta da mararta suka riƙe lokaci guda, tsugunawa ta yi tana riƙe da bayanta tace; "Inalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un."

Da sauri Ya A'i da su Akram su ka yo kanta, Ya A'i tace; "Zahra ko dai naƙudar ne?"

Dafe cikinta Zahra ta yi tana kuka, Ya A'i ta taimaka ta ɗauketa za ta kaita gado, tana miƙewa kawai ruwa ta fashe mata, Ya A'i na riƙe da ita, yace; "Akram help me with my phone."

Da gudu Akram ya kawo wa Ya A'i wayarta, tace; "Call Uncle Imam for me."

Imam na zaune a office ya gan kiran Ya A'i, yana picking ya ji muryarta tana faɗin; "Imam ka zo gida yanzu Zahra ta fara naƙuda.

A rikice Imam ya fita daga office ɗinsa, bai tsaya rufe office ɗin ba ya yi tafiyarsa zuwa parking lot, mota ya shiga. Cikin ƙanƙanin lokaci ya isa gidan Ya A'i saboda irin speeding da ya yi, tun daga tsakar gida da ya yi parking ya ke jiyo muryar Zahra tana salaati, da gudu ya nufa shagon Ya A'i, Zahra ya gani kwance tana mutsu-mutsu, zufa na bin ko ta ina a jikinta, salaati kawai take iya furtawa a bakinta.

Ya A'i ta taimaka masa suka kai ta mota, a backseat ya zauna da ita, Ya A'i kuma ta yi driving motar zuwa asibiti, suna shiga asibiti nurses suka kawo gadon mara lafiya, aka ɗora Zahra akai, ɗakin dake office ɗin Imam aka kaita, daman a nan suka ajiye kayan haihuwa.

Imam da kanshi da wata midwife suka karɓi haihuwar Zahra. Ba ta daɗe tana naƙuda ba, ta sumɓulo ƙaton ɗanta kyakyawa fari tas dashi.

A lokacin da midwife ta tsaftace yaron tsaf ta kawowa Imam, ya kasa iya ɓoye farin cikinsa, murmushi kawai yake tayi yana kallon yaron yana hamdala, gefen Zahra ya zauna yana shafa kanta ya ce; "My love kin gan kyautar da Allah ya yi mana ko? Allah ya raya mana shi, ya ƙaro mana masu albarka."

Lumshe ido kawai Zahra ta yi ta buɗe a hankali don ba za ta ma iya magana ba saboda gajiyar da take ji gabaki ɗayar jikinta, bakinta ma nauyi ya yi mata, gyara kwanciyarta ta yi tana maida numfashi, yaron Imam ya kwantar a gefenta, yace; "Look at what God bless us with."

Zahra ta shafa fuskar yaron, ta ɗan saki murmushi tana jin son yaron a can cikin zuciyarta, janyo yaron ta yi, ta rungume shi, ta sumbaci kansa, "Allah ya raya min kai, ya yi maka albarka." Ta faɗa da muryarta da bai fita sosai.

Imam na murmushi, yace; "Aameen Maman baby."

Ɗago Ido Zahra ta yi ta kalle Imam tace; "Ina neman alfarma..."

Imam ya ce; "Faɗi ko menene masoyiyata."

"Ina son ka yi wa yarona huɗuba da sunan Ya Musharraf."

Ido Imam ya zaro, yace; "Wato yaron ki, ba ma yaron mu ba."

Murmushi Zahra tayi tace; "Ni kaɗai na sha wahalar fitar da abuna.'

"Abun babu ma kara kenan, miƙa min shi to."

Ɗaukar yaron Imam ya yi, ya yi masa huɗuba da sunan Musharraf. Bacci sosai Zahra ta yi har bayan La'asar kafin ta farka, babu laifi ta ɗan ji ƙarfin jikinta, kallon ɗakin ta fara yi, idonta ya sauka akan Imam dake zaune yana duba wani folder, gyaran muryata yi, yana juyowa tace; "Ina yarona?"

Imam ya kalleta, yace; "Lallai kam, yanzu ke ko kunyar ɗan fari ba ki yi? To yana wajen Ya A'i a office, ko dai na je na ɗauko shine?"

Girgiza kai Zahra ta yi tana ƙoƙarin sauka daga kan gadon, tace; "Ina jin fitsari."

Imam ya zo ya taimaketa ta shiga bathroom tayi fitsari, tana fitowa yace; "Mu tafi gida."

Kallonsa ta yi, tace; "Ka faɗawa ƴan gidan mu na haihu?"

Girgiza kai yayi, yace; "Sai mun tafi gida tukuna, babu wanda na sanar yanzu."

"Please daga nan ka kaini gidanmu, I want to be with my Mom."

Kai ya gyaɗa mata, yace; "Yadda kike so haka za a yi ranki shi daɗe."

A office suka tarar da Ya A'i, sannu ta rinƙa yi wa Zahra har suka isa gun mota, Imam ya buɗewa Ya A'i ƙofa ta shige backseat ɗauke da jaririn da ta naɗe cikin lallausar towel, sannan ya buɗewa Zahra front seat ta zauna.

Imam na horn a gate ɗinsu Zahran aka buɗe musu gate, a parking lot ya parking motar, ya fito ya buɗe musu ƙofa suka fito. A falo Zahra da suka shigo da Ya A'i suka tarar da Farida da Khalil suna buga game a TV,  Farida na ganin yadda Zahra ta shigo tana takowa a hankali, ga jinjiri ɗauke a hannun Ya A'i da ta san ba ciki gareta ba, batare da ta amsa sallamar su ba, cikin mamaki tace; "Ba dai kin haihu ba Sis?"

Kai Zahra ta gyaɗa mata tana zama a kan kujera, Ihun murna Farida da Khalil suka yi, wadda ya saka mutanen gidan rige-rigen fitowa, Iya har zaninta na faɗuwa, Mommy da Iyar duka tsayawa suka yi suna zazzare idanun, Zahra ta kallesu, ta saki murmushi tace; "Iya, Mommy...na haihu." Ya A'isha wata kunyace ta rufeta, har sai da ta kau da kai gefe. Iya ta ƙaraso gefen Ya A'i, ta leƙa fuskar yaron, ɗago ido ta yi tace; "Tabbas wannan ɗan Zahra ne, kammani ɓaro-ɓaro sai dai hasken da ya fita dashi."

Ta maida kallonta ga Zahra tace; "Sannu Zahra, sannu da ƙoƙari, amma dai ai sai ki yi karar ɗan fari mara kunya kawai." Ta ƙarasa faɗi tana dungurar kan Zahra. Zahra ta zumɓura baki tace; "wai me haka Iya, ba za ki ma bari na ji da zafin da nake fama dashi ba."

Iya ta riƙe baki, tace; "Lallai kam Zahra, ai idan ni baki ji kunya ba za ki ji ta uwarki Amina."

Mommy kam ƙarasowa ta yi, ta karɓi ɗan daga hannun Ya A'i tana mamakin wai yau Zahra ce ta haihu, tabbaas Allah baya bacci, kuma ma ji kukan bawa ne, murmushi ta yi ta sumbaci kan yaron dake cike da gashi, Iya ta miƙa hannu, tace; "Bani yaron, ko kema kalar rashin kunyar taki zaki gwada min?"

Miƙa mata ɗan Mommy ta yi, ta kalle Zahra tace; Let's go up."

Zahra ta miƙe za ta bi bayan Mommy, Iya tace; "Ina kuma zaki bi ta, dalla wuce ɗakina ki zauna, ko dai uwar taki ce za ta yi miki wanka?"

Juyowa Zahra ta yi ta shige ɗakin Iya, Mommy kuwa ta tafi fridge ta ɗauki ruwa da lemu a fridge ta kawowa Ya A'i dake zaune a falo tana dariyar masifar Iya. Bayan ta sha ruwar kaɗan, Iya ta yi mata jagora zuwa ɗakinta wajen Zahra, ta miƙa musu ɗan ta fita. Bayan gida ta tafi, ta hura wuta da wasu katakai dake bayan gidan, babban tukunya ta ɗora a wutar, ta cika shi da ruwa.

Zahra na kwance suna ɗan hirarsu da Ya A'i Iya ta shigo, daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Ya A'i,tace; "Ke zo ki taya ni da ɗaukar wani abu."

Ya A'i ta bi bayanta zuwa backyard ɗin gidan, ruwan zafin da ta zuba cikin bokati ta nuna mata, tace; "wannan zaki ɗauka min zuwa banɗakin ɗakina."

Murmushi Ya A'i ta yi ta ɗauki ruwan zuwa banɗakin Iya, Iya na shiga ta kalle Zahra dake kwance tace; "Tashi za ki yi na miki wanka ba wannan kwanciyar ba, don ba taimakon ki kwanciyar nan zai yi ba."

Zumɓura baki Zahra ta yi tace; "wankar ne sai an yi min kamar wata ƙaramar yarinya."

Banɗakin Iya ta shiga, tace; "Ni dai ina jiran ki."

Ya A'i ta ce; "Zahra ki je ta yi miki wankar, za ki fi jin daɗin jikinki."

Kamar za ta yi kuka ta tashi ta shiga bathroom ɗin tana zumɓure-zumɓuren baki."

A ɓangaren su Abba kuwa, ya kama Anty red handed tana barbaɗa masa garin magani a abincin da ya siyo, yana fara mata magana, ta riƙe ƙugu tana tsiwa, ta yadda take shiga ba ta nan take fita ba, tana faɗin; "Daga taimako sai cibi ya zama ƙari, da rsada fa na siya maka wannan maganin tsarin, amma ka zo kana wani tsitsiye Ni kamr wacce za ta cutar da kai."

Abba da saboda tsabar takaici ma ya rasa abin faɗa har ta gama masifarta, sai yace; "Sakina, ki tafi gidanku na sake ki saki biyu."

Lokaci ɗaya Anty ta fara ganin hajjijiya, dage kanta ta yi, ta zauna a ƙasa ta tsandara ihu, ta fara faɗin; "Wallahi ba ka isa ba, idan ka isa Allah ya tsine min."

Maganganu ta fara yi tana ihu kamar mahaukaciya, Abba ya tsallaketa ya wuce ɗak+1insa, yana shiga ɗakinsa kiran Ya A'i ya shigo, take sanar masa da haihuwar matar Imam, lokaci ɗaya farinciki ya mamaye baƙin cikin da yake ji, ya miƙe tsaye cikin farinciki yace; "Ina ta ke yanzu?"

Ya A'i tace; "Mu na gidan su yanzu."

Two million Abba ya tura nan take, yace a yi wa yaro siyayya.

Ammi ma da aka sanarwa  haihuwar, kawai ta fara shirin zuwa Kaduna.

Ranar suna aka raɗawa yaro suna Musharraf, inkiya da Adyan. Akwati biyu na kayan yara, da akwati ɗaya na kuma cike da atamfofi da lace, Zahra ta sha kyau kamar a saceta a gudu, Imam uban gayyar kuwa shima ya haɗe iya haɗuwa cikin farin shadda ƙal. Raguna biyu aka yanka, aka yi shagali iya shagali.

A ranar da Zahra ta cika kwanaki arba'in da haihuwa, Ya A'i ta zo ta ɗauki Zahra, saloon ta fara kaita aka yi mata gyaran jiki sossai, aka wanke mata kai aka tsantsara mata kitso ƙananu masu kyau, sannan aka yi mata lalle mai danƙaran kyau, daga nan sai ta wuce da ita ɗakinta. Imam da ya kasa fita aiki yau tunda akace yau Zahra za ta dawo, yana jin horn a bakin gate ya fito da sauri, shi da kansa ya yi buɗe musu gate suka shigo, ya buɗe ƙofa wa Zahra dake zaune a gefen Ya A'i, ya ɗauki Adyan da ke kwana cinyarta, ya sumbace shi, yace; "Welcome home my son."

Side hug ya ba wa Zahra da ta fito, ya ba ta light kiss a baki, yace; "I miss you sweetheart."

Horn Ya A'i ta danna musu, tace; "Na tafi marasa kunya."

Murmushi Imam ya yi ya sosa ƙeyarsa, Zahra kuwa rufe fuskarta ta yi da tafin hannunta.

Imam ya buɗe mata gate ta fita, sannan ya bi bayan su Zahra zuwa ciki.

A daren ranar Zahra ta tabbatar da kewar da Imam ke ikirarin ya yi mata, sosai suka zuba love ɗin su kamar babu gobe.

The End

_____________

Tabbas rayuwar Zahra akasin tsammani ne, babu wanda ya taɓa tsammanin Zahra za ta yi farinciki a rayuwarta saboda irin ƙalubalen da ta rinƙa fuskanta, amma da ta yi haƙuri ta miƙa wa Allah lamuranta, sai ya saka mata da mafificin alkhairi.

Cikin daɗi da rashinsa mu miƙawa Allah lamurar mu, sai mu zuba ido mu gan yadda zai yi, a lokacin da maƙiya suka zuba ido don ganin abinda zai faru a rayuwarka, sai su gan alkhairi akasin abinda suke son gani.

Mu kasance masu Imani da ƙaddara alkhairi ko sharri.

JIKARGARBA✍️