Kuncin zuci
by @bintuuu
Mamma na kallonta ta qaraso cikin falon tace "Habibti na barki da aiki ko" nan ma Na'ima tayi murmushi a kunyace tace "A'a" sai Mamma tace "Barsu hakanan zan qarasa, Muje falon qasa yanzu tukunna" ta amsa da "Toh" ta fara gyara gyalenta sannan ta miqe ta bi bayan Mamma da ta juya ta fice.
Fitowan su Babban falon gidan sai da Na'ima taji zuciyarta ta buga na ganin yawancin Familyn duk sun hallara a zazzaune wasu bisa kujera wasu a qasa, ga mamakinta sai taga har dasu Abba, Mami da Faruk suma, jiki a sanyaye ta qarasa falon biye da Mamma ta samu guri a qasa kusada Anty Fatima ta zauna kanta a duqe, shiru babban falon ya dauka sai kuma su Ahmad suka shigo, qamshin turarensa kawai Na'ima taji ta shaida shine amma bata dago kanta ba har suka zauna shima kansa a sunne bai dago ya kalli iyayen nasa dake binsa da kallo ba, sai kawai Baba ya dan jijjiga kai ya gyara zama sannan ya kalli Abba yace "Bari in sake kiransu" da haka ya ciro wayansa daga aljihu ya sake danna kira a line din Daddy har ta katse ba'a dauka ba, rai a bace Anty Amnah ta danyi qwafan da ba kowa bane ya jita a falon, Sunanan zaune ba wanda ya sake magana suka jiyo qaran shigowan motan a compound, jim kadan Daddy ya shigo su Mummy da Laila har da Murja biye dashi a baya sai duk mutanen falon suka juya kai suna kallonsu more especially Laila da tayi wani laushi da ita a jikin Mummy, fuska a dinke Abba yace da Daddy "Yanzu Baba ya kira wayarka" sai yayi saurin cewa "Wayar tana gida ne kuyi hakuri" Mummy dake bayansa tace "Zuwa ai dole muyi tunda bashi ya haifa min 'ya ba da zai je har gida ya dukarmun Ita babu dalili, kuma wallah tallahi..." kafin ta qarasa Anty Amnah ta miqe ta tareta da "Ke har kinada bakin magana uwani" rai a dan bace Baba yace "Ya isa haka" Mummy tace "Dan Allah tayaya zanyi shiru an yi wannan dukan wa 'yata, yau ko menene tayi ai beci Ahmad yaje har dakinta ya mata wannan dukan ba" Abba yace "Ku zauna tukunna" Mami dake zaune kusa da Mamma sai raba Idanu take in confusion, inta kalli wannan sai ta juya ta kalli wannan cikin rashin sanin abunda ke faruwa dan babu wanda ya sanar da su dalilin kiran da Baba ya musu, Abba ne kadai ya sani kuma ya boye mata hakan ne saboda sanin hawan bacin ranta kafin su iso. Bayan kowa ya zauna sai Daddy ya daga kai ya kalli Baba yace "Yaya raina yayi matuqar baci da abunda yaron nan ya aikata akan Laila, ace yana Yayanta shi da zai bata kariya a rayuwa kuma shine zai zamo na farko gurin illatata" Baba yace "Osagie bai kiraka ba kenan?" sai Daddy yayi shiru yana kallon Baban dan neman qarin bayani, nan Baba ya cigaba "A yanzu haka sunada warrant din kama iyalinka su kullesu muka hana faruwan hakan gudun kare mutuncin gidan ka Sani, abunda me dakinka da yarinyar nan sukayi ya wuce tunaninka, dan haka ka tsaya ka saurari abunda suka aikata kafin ka fara fadin nonsense a gurin nan" saida kowa na falon suka kalli Baba jin kalman data fito daga cikin furucinsa, rai a bace ya cigaba "Ya kana da iyali, da girmanka ace ka kasa maida hankali ka zamto jagora a gidanka kayi saken da har wai yau ace ba mai dakinka ba har da yarinya qarama kamar Laila tana iya tayi alaqa da kidnapper" ga mamakin kowa sai Laila tace "Baba wannan karon ne na farko wallahi ban.." tass Anty Amnah ta dauketa da mari sannan ta nuna ta da yatsa tace "Ko mu ba mu isa muyi magana Idan yana magana ba balle ke, kina jina" da sauri ta gyada kai kuka na zuwa mata, Mummy dake zaune gefenta ta kasa magana jin inda Baban ya dosa nan ta fara gumi kuma ta sunkuyar da kai zuciyarta na kadawa, sauqe numfashi Baban yayi sannan ya sake maida kallonsa ga Daddy yace "Osagie ya kiramu kuma ya sanar damu maidakinka da 'yarka suna da hannu gurin dauke iyalin Ahmad kwanaki" tsit falon yayi na wasu 'yan daqiqu, Daddy ya ware idanu cikin tashin hankali da mamaki batareda sanin me zeyi ba, Mami da Faruk are more than shock a wannan lokacin, Mamma da Anty kuwa shiru sukayi dan maigidan nasu ya sanar dasu daman, shiru falo yayi na wa'ensu daqiqai bayan Baba ya gama musu bayanin da tiyaga ya bayar a police station, kan Mummy a sunkuye taji an fusgo dankwalinta tareda gyalen kafin ta dago kanta kawai ta fara jin sauqan dukan da Mami ke kai mata wanda duk rukunin mutanen falon baza suce ga lokacin da Mami ta isa ga Mummyn ba, da sauri kowa ya miqe su Mamma da Anty suka nufesu, Baba na tsayen yace "Ku rabasu, menene hakan kuma?" ganin yanda Mami ta danne Mummy akan kujera tana dukanta yasa Abba da Faruk sukayi kanta suna qoqarin daukanta ma gaba daya, rai a bace Mami take cewa "Ai nayi alqawari, ku barni in sauqe alqawarina" rai abace Abba ya riqeta yace "Haba Fatima, Haba mana, menene hakan a gaba yara fisabilillah" Na'ima daman tun farkon faruwan abun ta miqe nan kuma ta hau kuka, Ahmad dake tsaye shima beyi gigin isa gurin badakalin ba yana kallonsu cike da satisfaction, dan abune da shima in yanada halin yin haka to zeyi, ganin Na'ima na kuka ya matsa gareta sai baice mata komai ba ya riqo hannunta daya kawai, da kyar akan raba Mami da Mummy a falon nan, Anty Amnah na gyara wa Mamin gyalenta tace "Kiyi hakuri Anty Fatima, abun babu dadi sam ace naka na jikinka zai maka haka amma hakuri zakiyi kamar yanda mukayi" a fusace Mami tace "Wallahi uwani ba ta jikina bace, bazata taba zama ba kuma, tunda har ta iya aika mana mugu har gida ta aikata haka akan 'yata to bansan me zata iya yi akan Baby ba kuma" tana nuna Mummyn da yatsa tace "Ki cire idonki akan 'ya'yana uwani, ki yi nesa da duk abunda ya shafeni da gidana dan wallahi yanzu zan saka kafar wando daya dake muguwa makira kawai" sai da Baba ya musu jan ido sannan kowaccensu tayi shiru suka zazzauna, Mummy har sannan babu bakin magana sai kuka itada Laila da Murja, Na'ima daman tuni ta zare hannunta daga cikin na Ahmad ta koma gurin Mamin ta zauna a qasa, sai Mamin takai hannu tana shafa kanta, sai da aka sake nutsuwa Baba yace "Banason tashin hankali, na tara kowa anan ne gudun faruwan haka, mai faruwa ta faru kuma laifi dai Amina kinyi sa wanda babu abunda zai goge hakan, abunnan da kukayi was a disgrace to this family and nothing will change that, a matsayinki na uwa kuma wadda tasan ciwon kanta bamu taba tsammanin haka daga gareki ba, haqiqa Fatima tanada gaskiya ke abun tsoro ce yanzu" Daddy ya tari maganan Baban da cewa "Nima bazan iya cigaba da zama dake ba Amina" da sauri Baban yace "Babu wannan maganan, kai zaka gyara saken da kayi da iyalinka dakanka, dan haka babu maganar saki a zaman nan namu" Mummy ta sake fashewa da kuka tace "Dan Allah ku yafeni, wallahi sharrin shaidan ne" sai lokacin Mamma tace "Da son zuciya kuma uwani, 'ya'yan nan kowa yana dashi kuma munason su amma hakan bawai shi zai rufe mana ido mu kasa dorasu a hanya madaidaiciya ba" Anty tace "Wannan hakane gaskiya" sai Mami tace "Kinji kunya Uwani, Wallahi tirr da halinki" Abba ya kalleta yace "Fatima kiyi hakuri haka dan Allah" sai ta sunkuyar da kai bata sake cewa komai ba, Daddy dai har sannan kansa a duqe kamar ruwa ya cinye sa gasu Ahmad, Adam da Faruk ma nan zaune a qasa kowan nensu na sauraron tattaunawan iyayen nasu, Baba ne ya sake cewa "Ba a gurinmu zaku nemi yafiya ba Amina, ga yarinyar da kuka cuta nan zaune Ita zaku nemi ta yafe muku dan in har ba kuyi hakan ba, kisani sakayyar da Allah zai mata sai ta taba rayuwarku sosai" da hanzari Mummy ta share hawayenta tace "Dan Allah Na'ima ki yafe mana, nasan ba muyi daidai ba, kiyiwa Allah ki yi hakuri" sai lokacin Laila ta sake fashewa da wani kukan tace "Baba wallahi Inason Yaya Ahmad, wallahi ko me nayi, nayishi ne dan Ina sonsa" Anty Amnah ce ta saka kafarta daya ta haureta, rai abace tace "Ke wace irin mahaukaciya ce, banza shashasha haka ake son, banda dabbancin a Ina kikaga ana son namiji dole" Daddy ma yana huci yace "Idan na gaura miki mari sai kin daina jin magana har abada, stupid girl" nan ma Laila ta sake fashewa da wani kukan ta fara kururuwa tana fadin "Wallahi sai na kashe kaina, kashe kaina zanyi in huta tunda babu wanda yake so na anfi sonta" Daddy yayi kanta da hanzari Abba na qoqarin riqosa sai Adam ya rigasu isa gareta ya dauketa da marin da saida qaran ya karade falon, Anty Amnah tace "Qarawa 'yar banza Adam" sai Daddy ma ya qarasa gareta zai daketan Baba ya miqe yace "Ka barta haka Sani, karka sake tabata yarinyar nan duk mun sani zuwa yanzu alamu sun nuna ba cikakken lafiyan kwakwalwa gareta ba" Daddy yace "Wallahi Yaya lafiyanta qalau kawai iskanci ne" Abba yace da Daddy "Yaya ka barta Dan Allah" da kyar suka bawa Daddy baki ya zauna yana nuna Mummy dake kuka haniqan yace "Duk kece, duk ke kike dorata akan wa'ennan baudaddadun hanyoyin, wallahi halinki be yi ba Amina" sai ta duqar da kanta tana kukan tace "Kayi hakuri Dan Allah ka rufamin asiri karka rabu dani" ta juya gurinsu Baba tace "Dan Allah Yaya kuyi hakuri ku saka baki" sai ta sauqo daga kujeran ta tsugunna tana fadin "Ku rufamin asiri Dan Allah, wallahi nasan munyi laifi kuma nayi alkawari hakan bazai sake faruwa ba" nan ma ta juya gurin Na'ima tace "Dan ya rasulullah kiyi hakuri Na'ima, Kiyi hakuri ki yafe mana" sai Lokacin Na'ima ta dago kanta idanunta na kawo hawaye tace "Ya wuce Mummy, Allah ya yafe mana" sai Mummy ta kamo hannunta tace "Nagode Na'ima, Nagode Kinji" daganan kuma ta juya gurin Ahmad yace "Ahmad kayi hakuri kaima mun
shiga hakkinka" Anty Amnah tace "Kowa da kika gani a falon nan kin shiga hakkinsa, dan babu wanda ya sha ruwa ranan balle abinci tsabar tashin hankali kuma duk kina gani" ta nuna Ahmad ta cigaba "Bawan Allah'n nan har faduwa yayi ranan sai da likita yazo kansa, amma ace tsabar zuciyar kafirai gareki kina gani muna cikin wannan tashin hankalin kika saje a cikinmu tsabar rashin imani, wallahi tallahi ke abar tsoro ce Uwani, innalillahi" ta qarasa maganan tana tafa hannu cikin takaici da al'ajabi, sannan ta juya gurin Laila tace "Ke kuma makira, karamar yar iska ki kalli idona dakyau" Laila ta sunkuyar da kai tana cigaba da kukan sai Anty Amnahn ta cigaba da fadin "Sai na koya miki hankali, ko da kowa ya daga miki qafa wallahi sai naci uwarki" Abba yayi saurin cewa "Ayi hakuri Amnah" tace "Yaya you can't be saying ayi hakuri ayi hakuri, abunnan da sukayi fa is beyond hakuri, in kun yafe su Ahmad da Na'ima fa abunnan da aka musu will forever be their agonizing memory, haba mana" Mami tayi saurin cewa "Ahtoh" dan bazata sake dogon magana ba kuma tunda Abba ya nemi ta yi shirun, Anty ma dake gefen Mamma ta gyada kai cikin gamsuwa da maganan Amnahn sai Daddy yace "Wannan hakane Amnah kinada gaskiya, abari hukuma tayi aiki akansu shine daidai" Baba yace "Babu abunda hakuri ya bari a rayuwar nan, kuma duk wanda yayisa bai fadi ba shi keda riba, wannan abu ya riga ya faru ba abunda zamuce sai dai mu bawa yaran nan hakuri more especially Na'ima, an zalunceta hakika mun shaida amma hakurin shine zamu bata" ya juya ga Na'ima yace "Kiyi hakuri Na'ima, in sha Allah kece da riba a rayuwar nan kuma bazaki taba faduwa qasa ba" sai ta sunkuyar da kai tace "Na yafe ya wuce a gurina. Allah ya yafe mana gaba daya" sai duk aka amsa da Amin, nan kuma Baba yace da Daddy "Ka dauki yarinyar nan ka kaita kuga likita, in ta kama har rehab center ne ma akaita, nayi bincike sosai daga ranan da tasha pills dinnan na samu cewa ba su kadai take sha ba, kayi hanzarin kaita rehab" nan kuma Laila ta sake bare baki ta fara magana kamar me tabin kwakwalwa wanda saida mutanen falon suka rinqa kallonta cike da mamaki, kuka take tsakaninta da Allah tana fadin sai an aura mata Ahmad ko ta kashe kanta, Ahmad na kallonta yanajin ransa na tururin bacin rai, a lokacin yayi deciding yayi magana sai ya gyara zama yace "Baba Ita ta aiko maka da takardun can a boye kwanaki" da haka kuma yayi shiru bai sake magana ba yana bin mutan falon da kallo ganin yanda suka bude baki tsabar mamaki a yayinda Baba yake musu qarin bayani akan takardun da Lailan ta aiko akan Na'iman zuwa wajensa kwanakin baya, Daddy dai was mortified a wannan lokacin, wani irin kunya ce da takaici suka rufesa a lokaci daya yanajin baqin cikin abunda iyalinsa suka dade suna aikatawa.
A iya nan Baba ya tsayar da taron ganin zuciyar kowa a kusa take kar asamu sabani kuma, sai da Na'ima ta jira su Anty Amnah suka miqe itada Fatima sannan ta miqe itama sai kuma Anty Fatiman ta riqo ta suka nufi stairs zasu koma part din Mamma tare aka bar Mazan zazzaune a falon Baba na bayani a Daddy ta yanda zasu rufe case din a gurin su Osagie, ko da wasa su Mummy basuyi gigin bin su Mamma ba sai ta nufi hanyar fita daga falon jiki a sanyaye Murja na biye da ita riqe da Laila, da su Na'ima suka isa corridor sai suka samu su Husna, Ummi, Salma da twins a tsattsaye suna jiran hawowarsu, da sauri Husan ta iso garesu tace "Anty Fati meyake faruwa ne, muna ta jiyo kuka" muryan Mamma taji a bayan su Na'iman tace "Sannu zabeerah" sai duk akayi murmushi da haka kowa ya nufi nasa guri. Anan falon Mamma duk suka zauna suna maida zancen, Mami tace da Mamma "Mamma na fada miki daman tun farko ban yarda dasu ba ganin abunda sukayi ranan babu tausayi ko jimami a lamuransu" Anty tace "Har yanzu na kasa digesting wannan al'amrin wallahi, wannan wace irin masifa ce" Mamma tace "Wannan shine makashinka yana tare da kai, ace mutane babu tsoron Allah a lamarinsu ni Aisha" Anty Amnah ta gyara zama tace "Wallahi basuci bulus ba, Mamma dan Allah kar ku bari su Baba su kashe maganar nan" sai Mamma tace "Amnah hakurin dai daya ce ayin shi za'a yi, ko dan dan'uwansu" nan kuma Mami tace "Aikuwa ni da Uwani sai a qiyama Mamma, wallahi bani ba ita" itadai Na'ima na zaune a gefen Fatima tayi shiru tana jin duk yanayinta babu dadi, Bayan Maghrib Abba ya aiko acewa Mami taje su tafi, haka ta dafa Na'ima tayi ta bata hakuri sai Na'iman tace "Mami zan biki mu tafi tare" tace "A'a Habibti, yayi wuri fitan naki kinji, ki bari ko nan da two weeks sai kizo din" Mamma na kallonsu tace "A'a in tanason zuwa sai taje ai" sai Mami tayi dariya tace "Kiji Mamma da wani zance, mijin ta ma bazai bari ba kinsan hali" Anty Amnah tace "Uhm, Na'ima ki bi yanda Mamin tace kinji" sai Na'ima ta gyada kai batace komai ba ta sunkuyar da kanta tanajin babu abunda takeso irin ta zauna a kusa da Mamin nata, ahaka tana gani Mamin ta musu sallama ta tafin.
Sai bayan Isha Ahmad ya shigo Falon tareda Adam suka samu har sannan Anty Fatima da Anty Amnah sunanan zaune tareda Mamma dasu Husna a falon, Na'ima na zaune kusada Fatiman suna cin Abinci wanda sama sama take tabawa bisa tilastawan su Mamman, dan cewa tayi ta qoshi sai da suka sakata a gaba sannan ta dauki spoon ta fara ci kadan kadan, a bisa carpet din suka zauna Ahmad ya da tankwashe kafa yana facing Mamma sai ta turo masa plate din abincin gabanta da bata fara ci ba tace "Ga abinci ko kunci acan gurin Baban naku?" Adam yace "Munci fah" Anty Amnah ta kalli Ahmad tace "Son a nan zaku kwana ne?" sai ya girgiza kai yace "Yanzu da nake tunanin zamu wuce" Mamma batace komai ta jawo abincinta ta fara ci, Hira suka fara yi anan falon babu wanda ya sake maimaita abunda ya faru har sai daga qarshe su Ahmad suka miqe zasu fita ya kalli Na'iman yace "In kin gama Ina waje" ahankali ta amsa da Toh sannan suka fice, sai lokacin Mamma tace "Na'ima kiyi hakuri da abunda ya faru dan Allah" kafin Na'iman ta amsa Anty Amnah ma tace "Daughter muma munji zafin abunnan amma bazai kai naki ba munsani, Kiyi hakuri" sai Na'ima ta sunkuyar da kai tace "Babu komai, wallahi ya wuce" Anty Fatima ma ta bata hakuri while Husna sai raba ido take cikin rashin sani, can kuma Mamma tace "Tashi ki bi mijinki yana jira, Allah yayi albarka" sai Na'ima ta miqe a hankali tana gyara mayafinta Husna ta miqe itama ta nemi rakata, sai da ta musu sallama sannan ta bi bayan Husna da ta rigata fita daga falon.