MASARAUTAR KAIZUR

MASARAUTAR KAIZUR 12

by @nusybee143

🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 




✍️Nusy bee 
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 





Page 12




Shiru ya sake yi yana jan numfashi a hankali,har yanzu idanunshi suna ƙasa,ita kuwa Hayat ƙamewa ta yi a inda take zaune tana kallonshi cike da tsananin mamaki da tausayin da suka daskarar da ita a inda take zaune, Malli ɗin da yake faɗa,yake bege a koda yaushe, wadda ta zama muradin ranshi bata raye dama?

Tunaninta ya yanke a lokacin da ta ji yana faɗin "da ace Ni mai yanke hukunci cikin fushi ne babu abin da zai saka Amjad ya kwana a duniya ranar da ya kalli idanuna da alfahari yana gaya min shi ya sa aka kashe min Malli,kashe ta bashi da bambanci da kashe dukkan farin ciki da burin rayuwa ta kamar yadda na gaya miki,kafin shigowar Malli rayuwa ta bata da wata ma'ana,zuwan Malli cikinta shine ya sa na fara yiwa kaina kallon mutum"

A hankali gimbiya Hayat ta ja numfashi mai nauyi ta ce"kenan kana nufin Malli bata raye?

Na kasa yarda da wannan maganar"

Kallonta ya yi, kamar a mafarki sai ta ga ya yi murmushi,duk da cewa murmushin mai ciwo ne sai ta ga ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarsa, musamman da ya kasance bata taɓa ganin murmushin shi ba,a hankali ya ce"Malli bata raye,a dalilin barinta duniya ne ya sa nake a wulaƙance a nan,don bana jin har abada zan iya yafewa kaina, saboda gani nake yi kawai nine na yi silar mutuwar ta "

Da sauri Hayat ta girgiza kai,ta ce"ko da ban taɓa soyayya ba na san ba ƙarya ba ce,na tabbatar a yadda kake sonta ba za ka taɓa bari ko tsinke ya soke ta ba ballantana har ta rasa ranta, ƙaddara ce kawai"

"Idan haka ne kuwa ƙaddara bata yi min adalci ba,a lokacin da nake tunanin zan zamo mutum mai daraja sai ta jefar da ni na zama abin ƙyama"

"Ƙaddara abu ce mai kyau,ba kamar yadda ka faɗa ba,wani lokacin ta kan takura zuciyar bawa har ya yi zufa,don ta sanya zuciyar a ganiyar farin ciki, saboda......"

"Ki gafarce ni ya shugaba ta,amma ni ban ga ta inda farin ciki zai ziyarce ni ba,ko na ce ni a tsawon rayuwata ma ni ban sanshi ba sai shigowar Malli cikinta 

Duniya cike take da abubuwa masu yawa,amma ababen ƙi sun fi yawa a cikinta "

Gyara zama Hayat ta yi tana kallonshi, a hankali ta ce"zan so na ji labarin Malli,ban taɓa ganinta ba,ban santa ba,amma na ji ina ƙaunarta "

Ɗaga kai ya yi da sauri ya kalle ta, murmushi sosai ya bayyana a fuskarsa,bata yi mamakin ganin hakan ba,a hankali ya ce"a tsawon rayuwa ta na ga mutane da yawa da suka tsani Malli saboda ta nuna Kazuzi a matsayin abin da take so,amma karo na farko kenan da na ga wadda ta so Malli saboda yadda ta so Kazuzi "

Murmushi ta yi ta ce"wataƙila ba su ga kirkinka da na gani ba, shiyasa suka tsane ka"

Kazuzi ya ce"halayena da ɗabi'u na ba su taɓa canjawa ba ranki ya daɗe, yadda nake mu'amalantar mutane a nan haka nake mu'amalantar mutane a ko'ina,sai dai mutane suna mu'amalanta ta da dabi'u dabam-dabam,ba na damuwa da hakan saboda ɗabi'ar ɗan adam ba ya zama ɗaya 

"Kai ba abin ƙyama bane, mutum ne mai daraja,babu wani a duniya da yake tsallake tarko da gwagwarmaya face ya kasance mai daraja,kamar kai

Musamman ma ya kasance ya zama macecin al'umma, darajar shi ta dabam ce"

Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba,a hankali ta ce "zan iya tambayar wani abu?"

Ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce "komai kike so ki tambaya kawai ya shugaba ta"

"Labarin MALLI nake so ka ba ni,ko na ce, labarin ku kai da Malli, rayuwarku da irin soyayyar da kuka yi a Baruda 

Da alamu soyayyar ku ta dabam ce"

Jinginar da kanshi ya yi a jikin bango yana sauke numfashi a hankali, cikin wata iriyar raunananniyar murya ya ce"Labarin soyayyar mu da Malli ba mai daɗi bane,ba labari bane da zai saka ki farin ciki kamar yadda kike tunani ya shugaba ta"

Gimbiya Hayat ta ce"na fahimci da wani zafi ko na ce tabo a rayuwarka,amma tabbas na san soyayyar Malli,ko na ce tarayyarku da Malli ya yi maka maganin ciwon,idan na canka daidai zan iya cewa tsawon zamanka da Malli babu wata damuwa da take yi maka tasiri,amma menene gaskiyar hasashe na?"

Shiru ya ɗan yi na yan daƙiƙu, kafin ya ce"zan iya ce miki eh,kuma zan iya ce miki A'a,a tsawon rayuwar Kazuzi bai san wani abu farin ciki ba,amma kasancewar Malli a rayuwa ta hakan ya bayar da ma'ana da a baya babu a rayuwata"

Hayat ta miƙe tsaye ta ce"shikenan, yanzu lokacin shiga ta na huta ya yi,amma zuwa gaba kaɗan zan sake nemanka,don tabbas na ɗokanta da jin labarin Malli "Kazuzi ya rissina ya ce"a sauka lafiya ya shugaba ta"Hayat ta fice daga ɗakin ba tare da ta sake magana ba,duk jikinta a sanyaye





*DAULAR KAIZUR*


A cikin ƙasa da kwana ɗaya da yini ɗaya kaizur ta hargitse gaba ɗaya,sarki Mu'iz ya dage babu ji babu gani sai ya yi bincike akan ɓatan ɗanshi Sahal,zuwa yanzu an kama yarima Jamal, kasancewar shine abin zargi na farko saboda ɗabi'ar da ya nuna jiya a gaban mutane,sarki Mu'iz ya bayar da umarnin a rufe shi don tuhuma

Sarauniya Amna kuwa rufe kanta ta yi a ɗaki,sai da ƙyar ta buɗe, saboda gaba ɗaya hankalinta ya kai ƙololuwar tashi, izuwa yanzu ta fara sarewa akan batun Yarima Sahal,ta fara cire rai da bayyanar shi, saboda akan binciken da ya fito wasu sababbin al'amura kawai ake tonowa,amma babu batun bayyanar shi

A killatacciyar kurkuku ta manyan mutane masu manyan laifuka aka kulle Yarima Jamal da ya firgice da tashin hankali,tsawon kwana uku ana hukunta shi cikin ruwan sanyi,duk wannan lokacin Sarki Mu'iz bai bi ta kanshi ba ko sau ɗaya, Yarima Zaffar ma hankalinshi yana kan ɗan'uwanshi wanda ya fi kowa zama abin tausayi, saboda cin amanar da yake zargin ɗan'uwanshi na jini ya yi masa

A hankali Yarima Zaffar yake taku zuwa ɗakin da aka rufe Yarima Jamal,dakarun da ke gadin ɗakin ya saka suka buɗe masa ɗakin, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga 

Yarima Jamal yana zaune,ya jingina kanshi da jikin bango,gaba ɗaya kanshi ya kulle,bai taɓa shiga ruɗani irin wannan ba,ya ɗago yana duban Yarima Zaffar da yake kallonsa shima,kafin ya yi wani ɗan murmushi ya samu waje ya zauna yana kallonsa 

"Yarima Jamal!

Barkanka da wannan lokaci ɗa ga sarki Ammar ibn SUHAIF BIN YASSAR!!!

Amma na yi mamakin abin da ka aikata, saboda sanannen abu ne wannan jini mai daraja basa cin amanar kowa,ko da ace maƙiyinsu ne a filin yaƙi kuwa,amma sai gashi kai ka ci amanar ɗan'uwanka da kuka fito daga tsatso ɗaya,me hakan yake nufi?

Babu yadda zan yi,dole na zargi mahaifiyarka, dama na ji ƙishi-ƙishin sarautar mahaifinta da cin amana ya same ta,to gashi kuwa an samu a tsatso

Duk da haka ina tantama,don in dai kai jinin SUHAIF BIN YASSAR ne babu kai babu cin amana,sai dai idan an samo ka a wani wajen ne don ka gaji abin da ba naka........"

"Zaffar!"Jamal ya daka masa tsawa, jikinshi har rawa yake yi saboda ɓacin rai"ina gargaɗinka da ka iya bakinka Zaffar, mahaifiya ta ta fi ƙarfin dattin tunaninka,ko da ace na yi faɗa akan kujerar kaizur na isa ne, saboda nima ina da haƙƙin gadarta "

Wata dariya Yarima Zaffar ya yi,ya ce"babu shakka!

Ashe har zuwa yanzu kana da ƙarfin hali kuma ba ka rissina ba,na jinjina maka,wannan ma ɗaya daga cikin ƙarfin hali ne irin na jinin SUHAIF BIN YASSAR 

Amma yanzu tambaya ɗaya ce zan yi maka zuwa biyu,ina ka kai Min ɗan ɗan'uwana? menene manufarka ta yin hakan?kuma me ka cimma zuwa yanzu?"

Kai tsaye yarima Jamal ya ce"baka da isar da za ka iya saka ni a gaba da tuhuma Zaffar!

Ka fara zuwa ka gayawa shi ɗan'uwan naka wanda mahaifiyar taku babu abin da ta iya sai haifar annoba irinku,cewa ya daina zaluntar waɗanda ba su ji ba ba su gani ba,kuma idan zai hakura da batun ɗan shi gwara ma tun wuri ya cire rai

Don ba zai taɓa dawowa ba"

Da kallo yarima Zaffar ya bi shi kanshi har yana juyawa,kafin Jamal ya ankara Zaffar ya sauke masa wani mari ya cakumi wuyan rigarshi,sam Jamal bai damu ba,sai da Zaffar ya cika masa wuya yana huci,sannan ya kalle shi yana wani murmushin ƙularwa ya ce

"Daga kai har sarki Mu'iz tunaninku ragagge ne,duk da cewa ina son Sarautar kaizur amma a halin yanzu babu dalilin da ya sa zan yi wani faɗa akanta,da zan yi faɗa akan sarauta da na yi tun lokacin da sarki Ammar ya bar duniya 

A yanzu na bar wa wawaye rigimammu sarautar da babu komai a ciki sai zalunci da son zuciya,dangin mahaifiyata ni kaɗai ne magajin sarautar su,don haka ku rabu da ni haka nan"

Wani mugun kallo Zaffar ya watsa masa kafin ya ce"kai ba ka isa akan wannan ƙasƙantacciyar masarautar ta su mahaifiyarka ka ciwa Sarautar kaizur mutunci ba, sanin kanka ne kaf nahiyar nan babu wata masarauta da ta kama ƙafar ta kaizur a girma da daraja, ballantana wata Sarautar su mahaifiyarku wadda bata wuce matsayin mai unguwa ba a kaizur 

Ban da wannan ma,ka san da hakan kenan amma ka shiga ka fita ka ɓatar da magajin garin nan ko?"

Murmushi sosai Jamal ya yi,sannan ya ce"za ka iya faɗar komai yadda kake so, lokaci ne Zaffar,amma ni bani da lokacin ɓatar muku da abin da nake da ninkin shi sau babu adadi,yara ne?maza ko mata?kaf MASARAUTAR KAIZUR na tabbatar babu mai yawan ƴaƴana,don haka ka tashi ka fita salin alin,kar allura ta tono harma"

Bin shi da kallo Zaffar ya yi na ɗan lokaci kafin ya ce"me kake nufi da maganarka jamal?"

Jamal ya kalli cikin idanunshi ya ce"ina nufin surutunka ya fara hawa min kai,bana buƙatar hayaniya,ka tashi ka fice daga nan"

Murmushi Zaffar ya yi yana kallon cikin idanunshi ya ce"kana so na miƙe na fice daga ɗakin nan?

To ka gaya min, menene alaƙarka da Nayyab da nake ganin ku wasu lokutan cikin dare kuna tattaunawa?

Me kuke cewa?kuma akan me kuke magana?"

A razane Jamal ya ɗago yana kallon Zaffar, Zaffar ya yi wani miskilin murmushi ya ce"kar nake kallonka Jamal,a kowanne lokaci ka gwada zalunci a shirye nake na ga bayanka,sai an jima"ya miƙe ba tare da ya sake magana ba ya fice daga ɗakin cikin zafin rai, Jamal ya bi shi da kallo yana tunanin yadda zai fitar da kanshi 







*DAULAR TAYAAR*


Yau an tashi da ɗimuwa da tashin hankali lokaci ɗaya, sakamakon buga gangar yaƙi da aka yi,hakan ya nuna an kawo wa daular hari kenan, tunda in dai su za su kai hari suna zaman tattaunawa a san yadda za'a yi,amma yanzu tunda aka ji bugawar gangar yaƙin hakan ya nuna an kawowa daular hari ne, kuma maharan suna kusa da garin 





💫

A yammacin ranar Alhamis,ranar da Kazuzi da gimbiya Hayat suka tattauna game da rayuwarshi ta baya da Malli ɗinshi,wanda a dalilin wannan tattaunawa gaba ɗaya jikin Hayat ya yi matuƙar sanyi,bata taɓa tunanin zata ji tausayin wata halitta ta damu da wani Kamar yadda take damuwa da Kazuzi ba,hakan ya sa ta ƙuduri aniyar dole sai ta ji labarin shi,kuma sai ta ribace shi ya karɓi Muslunci daga nan kuma ta lallaɓa mahaifinta ya ƴanta shi,ko babu komai sai ya samu rayuwa mai daɗi da farin ciki a cikin Tayaar 

Tana cikin wannan tunanin a sashenta su kuma su sarki Tayaar suka samu baƙin saƙo daga wani ɗan aike daga ƙasar Haura,ƙasar Haura mutane ne masu bautar gumaka,a wasu watanni baya Tayaar ta taɓa yaƙarsu,amma Sarkin da wasu daga jama'ar shi suka samu suka tsere,hakan ya sa suka ɗauka ko sun yi galaba akansu ne

Magatakarda aka kira don ya karanta wasiƙar da aka rubuta a jemammiyar fatar damisa, rubutun an yi shi da baƙar tawada,ya zauna ya fara karatun kamar haka

Zuwa ga sarkin ƙasar Tayaar, ƙasar da shugabansu yake jin kanshi kamar wani ne shi

Ya kai Sarki Iyaad, wancan karon ka zo har daula ta ka samu nasara akai na,ka kunyatar da Ni a idanun duniya,an gaya min kana yaƙi don ɗaukaka kalmar ku ta musulunci ne, to in dai ina raye,ni Al'as ibnu mugaar sai na durƙusar da wannan kalmar, yanzu haka tsakanin mu da garinku tafiyar yini ɗaya ce kacal,mun baka nan da gobe war haka ka fito,ko mu shigo har cikin garin naku, mu kashe ku,mu kwashi matanku a matsayin ribar yaƙin mu

Ka ɗauki hakan a matsayin gargaɗi na ƙarshe, sannan magana ta gaba kuma ko da a ce kun yi shiri ko ba kuyi ba maganar dai ɗaya ce,dole mu ci nasara a kanku, saboda kyakkyawan shirin da muka yi

Daga Sarkin garin Haura, Al'as ibnu Mugaar 





Nusy_bee