KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Har parking space Husna ta raka Na'iman suka samu har sannan Ahmad na zaune a driver's seat while cab din motan a bude yana magana da Adam dake tsaye a gefensa, har suka qarasa Na'ima ta shiga seat din gaban motan bata kalli Ahmad ba kuma duk yana lura da hakan, bayan tayi sallama da Husna sai shima yayi sallama da Adam din sannan ya rufe motan ya tayar suka bar gidan, saida suka hau titi sannan ya juyo ya kalleta ganin kanta a juye tana kallon window, a nutse yace "Babe" sai ta dan juyo amma bata amsa ba, ganin yanda yanayin ta yayi sanyi yasashi miqa hannusa ya riqo nata amma ga mamakinsa sai yaga ta janye nata hannun ta cigaba da kallon window din, Har suka isa bata kallesa ba, bayan yayi parking tayi saurin fita amma sai ta jira ya fito, sai kuma ya nufota yace "Babe what's wrong?" fuska a dinke tace "Mu shiga ciki" sai ta gyada kai tareda riqo hannunta suka nufi entrance din a jere, sai da suka shiga falon sannan ya jawo hannunta zuwa garesa yace "ki fadamin meya faru?" ahankali tace "You beat her Ahmad, banason duka a rayuwata kuma ka sani, meyasa kayi please?" sai ya sake hannunta yanajin bacin rai na taso masa tuna abunda Lailan tayi, sai yace "Na'eemah na dake ta a matsayina na Yayanta, kuma ko ba ita ba, indai cikin qannena wani zai kwatanta abunda tayi sai na sake repeating dukan nan da nayi" kallonsa ta tsaya yi sannan kuma ahankali tace "Banaso, banason kayi duka Ahmad, dame ka daketa?" shiru yayi da farko sai yace "Belt" aikuwa da sauri Na'ima takai hannu baki tuna wasu memories da suka dawo mata, tace "Tayaya zaka daketa da belt, why are you like this?" nan kuma ransa yaji ya baci sai ya fara kokari barin kusa da ita yace "Ko gobe in ta sake, billahi sai na daketa" yana kallon idanunta yace "I'll beat her blue black, No one messes with you and go scot free by me" shiru Na'ima tayi har ya nufi stairs ya haye bai juyo ba ya barta nan tsaye tana binsa da kallo, ahankali ta qarasa kan kujera ta zauna at the same time tanajin kuka na zuwa mata amma ta danne, ta dauki kusan minti biyar kafin ta miqe a sannu ta nufi saman itama, amma hawan ta keda wuya ta gansa tsaye anan corridor'n yana kallonta sai ta tsaya a inda take bata qarasa garesa ba ta duqar da kanta tana jin hawayen na zuwa mata, bataji zuwansa gareta ba sai jinta tayi a qirjinsa yayi wrapping hannayensa a bayanta yana qara hadeta da jikinsa sai kuma yayi burying fuskarsa a wuyanta sukayi shiru ahakan, sai can yayi mata rada a kunnenta yace "Bazan sake ba, I promise you kinji" jin hakan sai itama tayi wrapping hannuwanta a bayansa ta gyada kai tana shaqan kamshinsa mai kwantar mata da hankali, sai Ahmad ya dago kansa yayi mata peck a goshi sannan ya sake cewa "Nakasa controlling bacin raina akan abunda tayi ne, they took you away from me Na'eemah, Allah ne kadai yasan me nayi going through a wunin ranan da kika bata, Ina addu'an kar Allah ya sake nunamin tashin hankali irin wannan lokacin dan I'll loose my sanity" sai ta dago kanta tana kallonsa, da hannu ya tallabo kumatunta yana kallontan shima yace "Ina miki son da bazan iya barin duk wanda ya musguna miki ba Na'eemah, I can't bear it, but I promise you bazan sake yin duka da hannuna ba" bata bar kallonsa ba tadanyi murmushi tace "Nima Ina sonka Ahmad, it's just that banason inga wasu sunyi experiencing abunda nayi going through a baya, did you know that in akayi duka da belt toh wannan dukan farkon yafi kowanne zafi" sai yayi saurin maida ita jikinsa yace "Let's not talk about this Babe, please don't" tace "Banaso ne, Ina tsoron wataran ka yimin ko ba'a saninka ba" sai ya danyi stiff sannan ya sake ta a hankali yana kallonta, ganin haka sai taqi kallonsa ta fara kokarin barin jikinsa sai yace "Na'eemah meyasa zaki kawo irin wannan tunanin a kanki?" sai ta kallesa batace komai, ahankali ya sake cewa "How can i beat you when all I wanted to do in this life is to love you endlessly" nan kuma hawaye suka kawo a idonta sai yayi saurin kama hannunta suka nufi falonsa, akan kujera ya musu masauqi sannan ya riqo hannayenta duka biyu yace "Na'eemah ko da wasa karki sake fadin irin wannan maganan, Billahi ko cikin hauka nake bazan taba laying hannuna akanki da sunan duka ba, not in this life Baby, not everr" sai ta gyada kai tareda fadin "Bazan sake ba".
Bayan wannan zaman nasu a falonsa sai ta nemi zuwa dakinta akan zata cire kayan jikinta sun dameta, da haka ta barsa a nasa part din ta nufi nata sannan ta shiga wanka, da ta gama ta fito sai ta samesa a tsaye yana riqe da plate me dauke da berries da slices na pineapple yana jiran fitowanta, murmushi ya mata yace "Here, this is for you" ya ajiye akan bedside drawer sai tayi murmushi tace "Nagode, kaifa" ya gyada kafada kawai sannan ya nufi cikin closet dinta bai dade ba ya fito hannusa dauke da wasu fararen kayan bacci, qarasowa yayi gareta tana zauna a gaban mirror, yana qoqarin tayata saka rigan yace "Do you feel hungry, mu fita eatry" ta girgiza kai tace "No, thank you" . Anan dakinta Ahmad ya kwanta ranan, abubuwan da suka biyo ba ne yasa kayan baccin Na'ima suka qare a tsakar dakin, amma har sannan be dauki hanyarsa ba ya qyaleta, duk irin yanda yakeji akanta haka ya hakura ganin yanda har sannan take tsoron kusantuwansu sai ya rungumota garesa yana shafa kanta har ya samu nutsuwa ta fara shigarsa.

Wayewar washegari da safe Bilal ya dira gidan iyayensa, da wani irin sanyin jiki ya shiga cikin gidan sannan ya qarasa falon da yasan zai samesu, Alhajin ya samu zaune shi kadai a falon saman yana kallon news hannunsa riqe da cup of tea yana sipping, sai ya juyo dan ganin wanda ya shigo duk a tsammaninsa Hajiya ce data je kitchen, miqewa yayi da dan hanzari sai Bilal ya duqar da kansa yanajin guiltiness na qulle dukkan jikinsa, Anutse Alhaji yace "Ka fita min daga gida, ka koma in da ka fito" jin haka yasa Bilal din zube gwiwowinsa a qasa yana hawaye yace "Abba kayi hakuri" a tsawace Alhaji ya sake cewa "Banason jin komai daga gareka ka tashi ka bar min gidana" sai sukaji muryan Hajiya ta shigo hankali a tashe ta duqa kusa da Bilal din tana kokarin miqar dashi amma yaqi tashi yana kuka, sai ta juya ga Alhajin tace "Alhaji dan Allah karka koresa, kayi hakuri ka sauraresa" Yace "Banason jin komai, abubuwan da yayi kadai sun isheni, bazan rayu da mugu wanda bai san ciwon kansa a gidana ba, ya je can ya cigaba da shaye shayensa" sai Bilal yace "Abba kayi hakuri, wallahi na daina shan komai, nasan abubuwan da nayi bazasu gogu ba amma dan Allah kuyi hakuri ku yafemin" Hajiya tayi saurin cewa "Mun yafe maka Bilal, wallahi mun yafe" Alhaji yace "Ka tashi ka fita nace, sannan ke kuma in kika cigaba da bin bayansa zaku tafi tare kinji na gaya miki" da haka ya juya ya nufi dakinsa rai abace, jin haka yasa Bilal miqewa ya juya zai bar falon Hajiya na kallonsa tana kuka amma ba halin binsa.


Two weeks Later.
Na'ima na kitchen tana hada musu breakfast while Ahmad yana zaune kan kujera ajikin kitchen island din yana riqe da cup of tea, wayarsa ce a hannunsa yana scrolling while sipping tea, Na'ima na tsaye jikin gas cooker tana kwashe plantain daga cikin frying pan tace masa "Nafisa ta kirani akan zata fara stocking kaya a store dinta" sai Ahmad ya dago kai yace "Har an gama komai ne" ta juyo tace "Saura dan kadan, and she wants me to be there for her office arrangements" ya gyada kai "Nima inada NOG conference da zanyi attending anjima, I'll drop you by her place sai na dawo in dauke ki" sai da ta dauko full breafast plate din ta qaraso tareda ajiyewa a gabansa sannan ya ja mata kujeran gefensa ta zauna, a sanyaye tace "A Lagos ne?" ya amsa da "No Babe, nan cikin Abuja ne fa, kuma ba'a daukan lokaci sosai, zan fara zuwa office ne in dauki wasu takardu" tace "Ba damuwa, I can drive myself there kar in bata maka lokaci" ya girgiza yace "No zan kaiki first" sai ta gyada kai tana murmushi ganin ya miqo mata fork me dauke da plantain daya daidai bakinta, ahankali ta bude bakinta ya saka mata yana kallonta, sai ta sake cewa "Menene shi NOG conference din?" yayi murmushi yace "Nigerian oil and gas conference and exhibition, yawancin mutanen dake cikin industry din muna attending kusan every year anan Abuja" sai Na'ima ta gyada kai cikin fahimta tace "Allah ya taimaka" ya amsa da Amin suka cigaba da cin abincin cikin plate daya.
A hanyarsu na tafiya Na'ima tayi insisting Ahmad ya tsaya su siya wa Nafisan snacks, a wani supermarket suka tsaya ya jido mata kayan ciye ciye masu yawa sannan suka qarasa. Da motar Lamin suka cin karo a cikin premises din bayan sun shiga, Ahmad ne ya fara fitowa yana  kallon motan sai yayi murmushi suka jera atare suka shiga, tunda suka shiga Na'ima ke bin ko Ina da kallo ganin yanda komai ya tsaru gwanin sha'awa, tana murmushi suka isa har office din Nafisan dake upstairs, sai suka sameta tareda Lamin din har Abu suna tayata unveiling lounge sofas dinta, tana murmushi ta taho garesu tace "Bobo na Oyoyo" sai Na'ima ta qarasa sukayi side hug sannan tace "Nafee komai yayi kyau sosai, ma sha Allah" tace "Thank you, ki huta sai muje kiga glasses din" ta gyada kai tana gaishe da Lamin, da haka Nafisa ta juya gurin Ahmad da ya qarasa gurin Lamin suna magana tace "Yaya Ina kwana" yace "Lafiya Nafisa, guri yayi kyau, Allah ya sanya alkhairi" tana murmushi ta amsa da Amin, sai da Abu ya gaisa da Yayan nasu sannan ya gaisheda Na'ima, ta amsa sannan ta miqawa Nafisa ledan hannunta tace "For you" Nafisa ta ware Idanu tana leqan cikin ledan tace "Awwn, Thank you Bobo, Aikuwa zan boye a mota kar Mami ta gani" Abu yace "Ki fara bribing dina in kinason plan dinki ya tafi daidai" sai ta ranqwasheshi akai sukayi dariya dukansu, anan Ahmad ya barta tareda da Nafisan ya tafi gurin meeting din nasu tareda Lamin, basu wani bata lokaci ba sukayi shawaran inda za'a saka glasses din acikin office din sannan Nafisa ta kira masu aikin suka fara suna gani.
Sai bayan azahar sannan Ahmad ya dawo daukanta shi kadai ba tare da Lamin ba, tana zaune bisa cushion a space din downstairs ita kadai ya shigo, sai ya qaraso gurinta, yace "Sannu da aiki Babe" tana kallonsa tace "Sannu kaima, kun gama" ya gyada kai, kawai sai gani tayi ya duqo yayi hugging dinta a jikinsa sai ta fara kokarin barin jikinsa tana fadin "Nafisa da Abu sunanan fa" yana murmushi yace "So?..I missed you" tace "Nidai ka sakeni kar su fito please" bai bar murmushin ba ya saketa ya miqe sannan yace "Kinci abinci" tace "Eh munyi ordering dazu" yana kallon fuskanta yace "Mu tafi gida ki huta, aikin ya isa haka, zanci taron Nafisa gaskiya" tana murmushi tace "Workers sunzo ai, suna sama har yanzu ma" kafin yayi magana Nafisan ta sauqo,  tana ganinsa tace "Yaya sannu da dawowa" yace "Sannu Nafisa, ya ayyukan?" tace "It is almost done, gida zamu tafi sai gobe kuma" yace "Zamu tafi yanzu muma" da haka ya fara tattare kayan Na'ima dake gefenta yana saka mata a jakanta ko a jikinsa, sai ta miqe tana gyara gyalenta ya miqa hannu yana tayata duk akan idon Nafisan dake kallonsu admiringly.


Don't forget to follow my account and like this story please.