1
*đź““KUNDINA*
BY
NAFISATU ALIYU SASAAL
BISMILLAH✍🏻
SHIMFIĆŠA
Karin maganar "matsoraci baya zama gwani" gazgatacce ne a gareni.
Dalili; duk kwanan duniya, sai na yi mafarkin na zama mace mai ƙwarin gwiwar da babu rauni a tattare da ita, amma da zarar na farka, tsoron da ya zamemin ɗabi'a yake rushe wannan mafarkin.
Sau dayawa ina tambayar kaina, menene yake mayar da ni baya, a duk lokacin da na yunƙura? "Tsoro" itace amsar da zuciyata take ba ni.
Fahimtar dagaske lokacina tafiya yake, tsoron maimatuwar tarihin cikin KUNDINA na riƙeni, yasa na yunƙura duk da irin bugun da na ke ji a cikin zuciya.
Ranar Alhamis da yamma, da ƙwarin gwiwa, na shirya cikin baƙar Abayar da ya yi matuƙar haskani, na nannaɗe kaina da baƙin mayafin daya taimaka wajen fitar da tsantsar kyan fuskata na hausa fulanin usul.
Zuciyata na tsananta bugu na nufi sashen Mahaifina.
Da sallama na buɗe ƙofar Parlon ba tare da jiran izini ba, na zura gangar jikina saboda yanda zuciyata take tsananta bugu.
A zaune na sameshi kan ɗaya daga cikin Kujerun da aka ƙawata Parlon nasa da su, ya zubawa ƙofar shigowa ido..
Irin kallon da yake min yasa na ji tsorona ya dawo sabo fil, ƙwarin gwiwar da na taho da shi a take ya bi iska, jikina ya fara rawa. Kasa tsayawa nayi don haka na durƙushe ƙasa na fashe da kuka.
Kamar ba zai tankamin ba sai kuma na jiyo muryarsa a sanyaye ya na cewa;
"Menene Fatima, ki daina kuka, ki faÉ—amin zan saurareki"
Muryata tana harÉ—ewa saboda tsoro da fargaba na ce;
"Baba Dan Allah ka yafemin, ka yi haƙuri ka ƙara bani dama a karo a biyu na koma Makaranta, ba na jin daɗin rayuwata a haka"
Na ƙarasa faɗa zuciyata na tsananta bugun amsar da zai ba ni.
Kamar saukar ruwa mai tsananin sanyi haka naji a cikin zuciyata da ya ce;
"Idan na baki dama a karo na biyu wani alƙawarin zakiyimin?"
Kaina na É—ago a hankali, kunyar abubuwan da suka faru a baya na mamaye ni, muryata a disashe na ce;
"Nayi alƙawarin riƙe martabar kaina da na kasa riƙewa a baya"
"Idan kika karya fa" ya ƙara jefomin tambayar ya na kallona.
Kaina na girgiza ina jin kamar na dawo da labarina na baya nasa abu na gogeshi, cikin kukan da yaƙi yankemin na ce;
"Baba dagaske nayi alƙawari"
Ido ya ƙuramin kamar yana so, ya gano da gaske zan iya cika alƙawarin da na ce na ɗaukar mai.
Ya jima yana kallona, kafin ya yi min alama da hannu na zo.
Da sauri na miƙe na isa gareshi. Hannuna ya kama na zauna a gefenshi. Cikin taushin murya ya ce;
"Fatima ko bayan ba na raye zaki tuna wannan maganar tawa, shi Mijin aure ba dabara ce take kawoshi ba, lokacine yake kawoshi, idan lokacinki ya yi har gida Mijin aurenki zai biyoki, ba sai kin wahalar da kanki ko kin zubar da darajar da Allah ya yi miki ba. Tashi ki je ki fara shirin komawar Makaranta, sannan ina ƙara jaddada miki wannan itace yardata a gareki na ƙarshe, Allah Ya yi miki albarka" ya ƙarasa faɗa yana zame hannunsa a cikin nawa.
"Ameen" na amsa a hankali ina miƙewa, kalmarsa ta;
"wannan itace yardata a gareki na ƙarshe" na kai kawo a cikin zuciyata, da haka na bar sashen zuwa Sashena...✍🏻