42
by @zahrabmrs02
page 42 💬⌨️
Bayan kwanaki biyu da faruwar abin Zaria, AK ya fara saukowa da kansa. Ganin yadda Farhana ta koma shiru, shiru ta fara rama ,tana cin abinci kadan kuma tana guje masa, sai yaji jikinsa ya yi sanyi. Shi kansa yasan cewa yana son Farhana, kuma kishin da yake mata ne yake sa shi fita hayyaccinsa.
A daren ranar Litinin, ya shigo dakin Farhana da wasu kyaututtuka na alfarma. Ya zauna kusa da ita, ya kamo hannunta cikin sanyi.
"Wifey... kiyi hakuri da abinda ya faru. I was just angry because I care about you too much. Bana son ganin wani namiji kusa da ke. Let's put everything behind us, saura 2 weeks mu tafi USA, bana son mu tafi muna fushi da juna."
Farhana ta kalle shi, hawaye ya cika idonta. Duk da radadin dake zuciyarta, amma kalamansa sun sanyaya mata rai. Ta gyada kai, "Nagode AK. Nima bana son fushinka."dan Allah kuma ka dena min hukunchi a shimfida bana jin dadin hakan ,shiru Ak yayi yanzu so yake so shirya amma da fada mata shifa haka salon sa yake,amma time will tell
Daga nan, AK ya koma Lovely and Caring Husband. Ya fara mata lallashi na musamman, har yana koya mata tuki da kansa da yamma. Komai ya fara dawowa daidai, soyayya ta dawo sabuwa.
hanadi
nayi mamakin yadda Ak ya sauko easily har yana mata driving lesson da kansa ,dan nasan Ak yana da wuyar shaani ,amma love won ,tinda gashi farhana tasa ya zama soft ,a yau zan sakar mata da next boom din,and she will not see this coming
text na turawa partner dina
plan B actived
na dade zargin furnitures din farhana ba iyayenta bane suka mata amma Alhamduillah na sami evidence din da nake da bukata
nice Hanadi, wadda take da idon sani, cikin saa Wata rana AK yana wanka, ta shiga dakinsa ta duba cikin wasu takardu, nan ne ta ci karo da Receipt din kayan dakin na Farhana wanda AK ya biya da kansa.murmshi hanadi tayi already ta yi snapping din receipts din a wayar ta
Cikin hanzari, Hanadi ta kira Yaya Ramla.
"Yaya Ramla, ai asirin amaryar Ak ya fito. Wai ashe duk takamar kayan dakin da take yi, AK ne ya saya mata su! Kayan da danginta suka kawo duk yana can wani daki a matsayin na baki. Karya suke yi wa mutane!"
ina shaidar ki?dan bazaki sa naji kunya irin na last time ba
na tura miki yanzu ta WhatsApp yaya ramla hau ki gani .
washegari
Farhana tana kitchen dinta na main falo tana shirin breakfast, sai ga Yaya Ramla ta shigo gidan tare da yaya safiyya Fuskarsu babu fara'a.
"Farhana, baki da kunya ko?" Yaya Ramla ta fara magana tun kafin ta zauna. "Ashe duk karyar da kuke yi mana, AK ne ya saya muku kayan daki? Muna ta murna 'yar mutunci aka kawo mana, ashe 'yar kishin talala ce?"
Farhana ta zaro ido, "Yaya Ramla me kike fada haka?"
"Karki yi mana hauka! Mun riga mun sani. Kayan da iyayenki suka kawo ba su kai matsayin gidan AK ba, shine ya rufa muku asiri ya saya muku wasu. sabida baki da sirri, kika je kika fada wa kawayenki har maganar ta zo kunnenmu!"
Farhana ta ji duniyar tana juya mata. Maganar nan sirri ce tsakaninta da AK kadai. Babu wanda ya sani sai shi.
alhakin mummy ne ya kama Ak shiyasa ya auro yar matsiyata cewar yaya Safiyya tana banka wa farhana harara.
kasa magana farhana tayi dan bata da abin cewa
suka cigaba da ranting suna zage zage har hanadi ta fito tana basu hakuri
Lokacin da AK ya shigo, ya tarar da falon ya rude. Yaya Ramla ta zazzage shi akan me yasa zai saya wa mace kaya bayan danginta sun kawo, ta nuna masa cewa ya yi asara.
fada ne sosai ya kaure tsakanin yaya ramla da Ak dan har duka ya so kai mata farhana ta shiga tsakani
da kyar yaya safiyya taja ramla wanda take ta zage zage tana cewa sai ta ga bayan farhana kuma ba ita ba AK
Bayan sun tafi, Farhana ta kalli AK da idanu jajir.
"AK... me yasa kika fada musu? Ka ce min sirri ne, ka ce ba za ka taba kunyata ni ba. Me yasa ka tafi ka fada wa danginka suka zo har gida suna min gori ?"
AK ya shiga cikin rudani, ya zare ido. "Farhana wallahi ban fada wa kowa ba! Ni kaina mamaki nake yi yadda suka sani. I protected you, me yasa zan fada?"
"Karya kake yi! Babu wanda ya san wannan maganar sai kai da ni. Idan ba kaine ka fada ba, ta yaya suka sani?"
Farhana ta juya ta wuce daki tana kuka, tana jin cewa AK ya ci amanarta ya siyar da mutuncin danginta. Shi kuma AK ya tsaya a tsakiyar falo, yana tunanin ta yaya sirrin nan ya fita.
A dayan bangaren, Hanadi tana zaune a balcony dinta, tana shan apple dinta tana murmushi. Ta san cewa yanzu Farhana ba za ta sake yarda da AK ba, kuma soyayyar da suka fara kullawa ta sake rugujewa kafin su tafi USA
gaban Ak ne ya fadi daya ga call din mommy,ko gaisuwar sa bata tsaya amsawa ba cikin dakakiyar murya ta fara
Abdulkadir yaushe ka zama haka?ramla ka kaiwa duka a gaban matan ka?
wani irin salon raini kake so ka janyo mata ,tun da kayi auren nan ka tsani ramla ,dole ne sai taso matar ka,dayake bani da hakkin ka Allah ya tona maka asiri ashee kai kayi furniture’s wallahi dangin farhana sunji kunya shame on them
numfasawa Ak yayi ransa ya kai kolulowar baci ,veins dinsa sun fito rada rada
mommy can you support me once in your life ?duk abinda sisters dina suka kira suka fadi miki kawai zaki hau ni da fada?anya ke kika haife ni?
akan me ramla take zuwa gidana a gaban matana tana zagi na … ya fada da tsananin fushi sai da gaban mummy ya fadi
ki bata last warning maman ramla ,tell your daughter duk ranar data kara tako kafarta gidana sai na ballata I don’t fucking give a shit ,kit ya kashe wayar be jira abinda mummy zata ce ba
sararo mummy tayi da waya a hannu ,anya Ak bashi da mental issue?ko dai yana shaye shaye ?yadda yake bata warning maybe da a gabansa take sai ya make ta .
hanadi ki fada min gaskiya Abdulkadir yana shaye shaye?mummy ta tambaya hanadi muryar ta a sanyaye
wallahi billahi mummy baya shan komai,meya faru ne?hanadi ta tambaya da mamaki,
ba komai ,ki gaishe dasu kausar dif mummy ta kashe wayar .dan tana bukatar bincike akan Ak ,tunda baya shaye shaye to tabbas yana da psychological problem
farhana ta fito main falo daukar brekafast din da take hadawa kafin zuwan su yaya ramla ,bayan ta gama kuka wani irin zafi kirjinta ya fara alamun ulcer,da mamaki take kallon Ak yana waya da mummy tare da kankara mata warning take jikinta ya fara tsuma ,fuskar Ak ba kyan kallo gaba daya idonsa ya jajir ,ido suka hada ba rahama ba wasa ,a guje farhana ta fada part dinta tare da danna sakata ,Innallahi wa innaillahi rajjiun ,ni maryama wa nake aure ?waye Ak?