MASARAUTAR KAIZUR

MASARAUTAR KAIZUR 14

by @nusybee143

🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 





✍️Nusy bee 
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 




Page 14



Iya tsananin tashin hankali da firgici Sarki Iyaad ya shige shi lokacin da yake daf da ƙarasawa inda suke,don a bayyane yake cewa Kazuzi ya fara gazawa, murmushi sarki Al'as ya yi cikin ƙasaita yana kallon Kazuzi da shima yake kallonsa, cikin isa da gadara yake faɗin "gwara kawai ka saukar da kai yaro,don nasara kuwa mun gama yin ta a kanku,idan...."

Ba sarki Al'as ba,hatta sarki Iyaad da sauran dakarun shi da suka shiga tashin hankali sai da suka zabura ganin wani irin zafin nama da dabarar yaƙi irin ta Kazuzi, tuni ya saka takobin shi da babu wanda ya kula da lokacin da ya ɗago ta,ya daki ta sarki Al'as da ƙarfin tsiya,har sai da tartsatsin wuta ya tashi,sarki Al'as ya yi baya taga-taga kamar zai faɗi saboda tsananin ƙarfin dukan,kamar kuma wanda yake aiki da aljanu zumbur sai gashi a tsaye cikin tsananin zafin nama kamar ba shine wanda jikinsa ya fara gazawa ba

Da mahaukacin gudu sarki Al'as ya taho don ya É—auke masa kai da takobi,amma Kazuzi ya sare hannun,a wajen ya faÉ—i yana malelekuwar azaba yana kallon hannunsa da ya faÉ—i can gefe cikin tsananin mamakin wannan Sadauki,bai gama dawowa hayyacinsa ba Kazuzi ya sare masa kai a fusace,hatta da rundunar Tayaar sai da suka razana,ya É—auko kan sarki Al'as ya ya taho zuwa gaban sarki Iyaad ya rissina ya ajiye yana faÉ—in "fatan nasara da cigaba mara yankewa ya shugaba na!"

"Sannunka da ƙoƙari gwarzo kuma jajirtaccen mayaƙi sadaukin sadaukai!"a cewar sarki Iyaad cikin tsananin farin ciki da mamaki,bai yi magana ba, sai su Sarkin yaƙi Ra'uf ke ta maimaita kabbara

Babu jumawa suka gabatar da sallar asuba da ake cikin lokacinta,duk da kasancewar akwai waɗanda suka raunata nasarar yaƙi bata ba su damar jimami ba

Shugaban dakaru Amjad ne ya jagoranci sallar,kafin ya tayar da sallar sai da ya aikawa Kazuzi wani kallo,shi kam Kazuzi abin ma dariya ya so ba shi,ya matsa kusa da Ć™aton kogin da yake kusa da filin da suka yi yaĆ™in ya fara wanke duk inda jini ya É“ata a jikinshi 

Bayan an idar da sallar Liman ya miƙe ya yi jawabai sosai,na nuna tsantsar farin ciki da godiya ga Allah da wannan nasara da ta samu fiye da yadda suke tsammani a rayuwa,da godiya da yabo da jinjina ta musamman ga sadaukin sadaukai Kazuzi wanda ya bayar da kaso mai yawa don samun nasarar ta su,ba shi kaɗai ba,da yawan dakarun ma sun nuna jinjina da yabo ga Kazuzi da yake gefe kaɗan da su, kanshi a ƙasa ba tare da ya kalli kowa ba

A nan ne liman ya sanar da mutane Kamar yadda aka saba bayan É—agawar rana za'a nufi komawa cikin Tayaar,amma kafin nan za'a duba mayaĆ™an da suka ji ciwo a yi musu magani 

Hakan kuwa aka yi,a cikin mayaƙan da aka yi wa magani har da Kazuzi, wanda aka yanke shi a gefen kafaɗarshi,mai maganin ya tsorata sosai, saboda ya ga alamun akwai dafi a jikin takobin da ta yi wannan ɗanyen aikin,amma saboda jarumta da juriya ba lallai a gane hakan daga yanayin Kazuzi ba

Yana zaune yana Ć™arasa cin abincin da aka kawo masa, kamar wanda aka ce É—aga kai,ya hango dakare Amjad yana isowa inda yake,É—auke kai ya yi kamar bai ganshi ba,ya cigaba da cin abincinshi,dakare Amjad ya Ć™araso wajen ya zauna,amma kafin ya ce komai ya ji muryar Kazuzi yana magana 

"To yanzu yaya ka ji?wacce nasara kake samu idan ka kai min hari?

Menene ribarka idan ka yi makirci ka kashe Kazuzi?"

Duk da Amjad ya girgiza da yadda ya gane shine ya yanke shi,don ya canja kaya lokacin,kuma ya rufe fuskarshi,amma ya dake ya ce"har yanzu kana jin za ka cigaba da zama a cikin garin Tayaar tare da mu?

Har yanzu kana nufin shishshigin da kake yi kana samun mummunan sakamako bai ishe ka ba?

To ka cigaba,na yi maka alƙawarin watarana sai ka samu mutuwa muddin ina raye"

"Kasancewar ka a raye ra'ayin Kazuzi ne,ba na shakkar kashe ka a bainar jama'ar da ka saka fuskar mutanen kirki kana yaudarar su suna yi maka kallon na gari, saboda ni ba munafuki bane, irinka"

Amjad ya ce"kai ba munafuki bane,sai kafirci ko?

Kai yanzu don Allah ba ka ji kunya ba muna sallah kana gefe kana kallon mu?"

"Da me sallah ta zata ƙare ka dattijo?"ya faɗa yana kallonsa,don tun ɗazu maganar da yake yi ko sashen shi bai kalla ba

Irin yadda ya tsare Amjad da idanu ya sa hantar cikin Amjad É—in ta kaÉ—a,wani kwarjini da kamala ta musamman ya ga ya Ć™ara,hakan ya sa bai sake magana ba,shima dama Kazuzi tuni ya watsar da lamarin shi ya cigaba da abin da yake gabanshi 

Da É—agawar hantsi suka bar wajen,bayan sun kwashe shahidansu sama da ashirin da rundunar Haura ta Ć™arar musu 






*DAULAR KAIZUR*


Tunda aka rufe kuyanga Munaya tsawon kwanaki uku kenan ana yi mata sabon horo,don abu ɗaya ake buƙatar ta faɗa,amma hakan bai yiwu ba,shine inda Yarima Sahal yake,amma har yanzu babu amsa

A É“angaren yarima Jamal ma za mu iya cewa babu sauĆ™i, saboda duk yadda su sarki Mu'iz suka so jin wani abu daga gare shi hakan ya ci tura,sai nanata musu yake yi cewa da MASARAUTAR KAIZUR da duk abin da ya shafe ta baya gabansa,ba shi da lokacin É“atawa akan neman mulkin kaizur,wanda a bayyane yake,babu adalci da bin dokar addini yadda ya kamata a masarautar 

Yau ma Yarima Zaffar ya ziyarce shi,sai dai yau ziyarar a fusace yake ba kamar farko ba, cikin ɓacin rai ya dube shi ya ce"Jamal!

Baka da hanyar kuÉ“ucewa kamar yadda kake tunani 

Wacce mace ce wadda kuke haɗuwa lokaci zuwa lokaci kuna tattaunawa da wani zaurance wanda ba'a ganewa?ko kana tunani babu mai ganinka a ƙatuwar masarauta irin kaizur?

Faɗar gaskiya shine yiwa kanka da iyalanka adalci,akasin haka kuma kamar jefa kanka cikin masifa kake yi kawai,da ƙara bar wa ahalinka abin faɗa a kaizur, yanzu gaya min, menene shirin ka na gaba?me ka shirya a baya? wacece wadda kuke keɓewa da ita kuna magana?"

Kwarai da gaske yarima Jamal ya shiga tashin hankali fiye da tunani saboda bai taɓa tsammanin wani zai iya gano wani shirinsa har haka ba,amma hakan bai saka ya rissina ba,ya ce"kai ka san kana da wannan hujjar kuma ka zo nan ka turke ni?a maimakon a ganni a wajen rataya?"

Yarima Zaffar ya dube shi ya ce"ba zuwa na yi nan don ka yi min izgilanci ba,É—an yayana da ka saka aka sace,ina aka kai shi?"

Yarima Jamal ya girgiza kai ya ce"ba za ka samu amsa ba, saboda nima kaina ban san abin da ya samu yarimanku ba,a taƙaice ma dai ba ni na saka a sace shi ba,ku cigaba da bincike ko ku ɗauki mataki akaina,ba wannan ne karo na farko da kaizur ta yanke hukunci cikin fushi da son rai ba,kuma ba sai ka maimaita min ba,na san Sarkin ku ba ya nadama"

Kalmar ta yiwa yarima Zaffar zafi,amma bai iya yin magana ba sai kallo da ya bi da Jamal da shi, Yarima Jamal bai damu ba,ya sake duban Yarima Zaffar cikin tsananin tsana ya ce"amma tabbas akwai ranar ƙin dillanci Zaffar, musamman akan baiwar da kuka kulle tsawon shekaru ashirin kuna gana mata azaba,don matsayi da iko yana hannunku,idan ba ka da abin faɗa za ka iya tafiya "

Bai yi musu ba ya miƙe yana kallon Jamal da rinannun idanunsa, Jamal ma ƙyar yake kallonsa,a fusace ya ce"za mu haɗu nan gaba,zan dawo"daga haka ya juya ya fice daga ɗakin fuuuu, Yarima Jamal ya bi shi da mugun kallo cikin tsana







*DAULAR TAYAAR*


Kamar yadda aka saba na al'ada idan aka yi nasarar yaĆ™i kaÉ—e-kaÉ—e da masu tsaron Ć™ofa suke ji daga nesa ne yake alamta musu nasarar yaĆ™in da suka yi,hakan ya sa yau ma da zafi-zafinsu suka busa Ć™arar sarewa, cikin Ć™anĆ™anin lokaci gari ya hargitse da tsananin farin ciki,duk da cewa bai kai na nasara akan Baruda ba,mutane da yawa suka gabato don taryar mayaĆ™ansu gwaraza 

Da yawan mutane sai suka koma kallon Kazuzi da mamaki, musamman da wasu suka fara Ć™yanĆ™yaso shine Ć™arfin nasarar yaĆ™in ba tare da an wahala ba sosai,an yi masa magani a gefen kafaÉ—arshi an rufe ciwon,kanshi a Ć™asa kamar yadda ya saba,kusan shine a gaba-gaba bayan sarki Iyaad,Sarkin yaĆ™i Ra'uf,da badakare Amjad, shi kuma yana daga bayansu ,ya É—aure gashinsa ya sake shi bayanshi 

Da yawan mutane musamman yan matan da suka fito da kallo suka bi Kazuzi da ya wuce bai kalli sashen da kowa yake ba,sauran dakaru suka bi bayanshi, dama haka yake? kyakykyawa ne,ga cikar zati da kamala,kuma dama sun ji labarin ko da ya kasance bawa har yanzu bai yarda ya rissinawa wani an wulaĆ™anta shi ba,dama a bayyane yake Kazuzi baya tsoron mutuwa 

Ana sauka kai tsaye Kazuzi É—akinsa ya wuce ransa yana É“aci,ya yiwa gimbiya alĆ™awarin karÉ“ar musulunci kafin ya dawo daga yaĆ™in nan,amma sanadiyyar Amjad ya fasa,bai taÉ“a zama ya yi tunanin É—aukar wani mataki akan wani ba sai Amjad 

Bayan ya yi wanka ya sauya kaya yana jin ana ta nemanshi a fada amma ya yi banza,har zuwa lokacin da abokinsa khidr ya shigo yana nemansa,amma sai ya yi kamar barci yake yi,dole khidr ya juya ya koma, saboda masarautar Tayaar masarauta ce da take da tsananin bawa wanda yake Ć™arĆ™ashinta haƙƙinsa 

Yana nan kwance ya lumshe idanu Ć™amshin gimbiya Hayat ya ziyarce shi,da sauri ya buÉ—e idanu ya zauna,idan ya ce bai yi kewarta ba ya yi Ć™arya,kai tsaye zai iya cewa tana É—aya daga cikin waÉ—anda suka shiga rayuwarsa wadda ba zai taÉ“a mantawa da ita ba, tunaninsa ya yanke a lokacin da ta shigo É—akin da sallama 

Ɗaga kai ya yi yana kallonta, fuskarta ƙawace da murmushi, sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ciwo a jikinsa,ta ƙaraso ta zauna tana kallonsa, kafin ta ce"an ce kai ne gwarzon wannan yaƙin,kai ne ka jagoranci wannan tafiyar, saboda kai ne ƙarfin yaƙin,na yi farin ciki sosai,amma kuma na ji babu daɗi da na ganka da ciwo"

ĆŠan murmushi ya yi,ya ce"Barka da zuwa ya shugaba ta!

Ina fatan mun same ku lafiya 

A yi min aikin gafara ya shugaba ta, ban samu nasarar sauke alƙawarin da na ɗauka ba"

Shiru ta yi tana bin shi da kallo, kafin ta ce "ko dai wani abu ya sake faruwa tsakanin ka da dakare Amjad?"

Kanshi a Ć™asa ya jinjina kai a hankali 

Gimbiya Hayat ta harzuƙa,a fusace ta ce"menene dalilin da ya sa ba za ka ɗauki mataki akan shi bane?

Ko ƙarfinka ya fi ne?

To tunda kai ba za ka É—auki mataki akanshi ba zan sanar da Abby komai,idan ya so shi sai ya É—auki matakin da ya dace"

Ɗan murmushi Kazuzi ya yi,ya ɗago yana kallonta tana ƙoƙarin tashi tsaye,ya ce"

Ya shugaba ta yaushe kika shirya jin labarin soyayyar Kazuzi da Malli ne?

Ni kaina na ƙosa na ba ki tarihin"

Komawa ta yi ta zauna ta ce"ko a yanzu ma a shirye nake,amma na ga a gajiye kake,ga ciwo,zan bari sai gobe da safe,ya yi?"

Jinjina kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, gimbiya Hayat ta cigaba da magana "bari na saka a kawo maka abinci"Kazuzi ya rissina kai ya ce"godiya nake ya shugaba ta"

Har ta kai bakin Ć™ofa sai kuma ta juyo tana kallonsa ta ce"wai ka san suna na ma kuwa?"bai amsa ba ya yi murmushi kawai, ita ma murmushi ta yi ta fice daga É—akin,ya bi ta da kallo yana lumshe kyawawan idanunshi 

Washe gari da wuri ta tashi,bata san menene dalili ba amma ta Ć™agu ta ji labarin Kazuzi,ko da yake ta san dalilin ba zai wuce yadda ta fuskanci irin Ć™uncin da ya shiga a rayuwa ba,da kuma irin yadda ya rasa Malli É—inshi da yake ganinta a matsayin komai nashi 

Bayan ta kammala karyawa da Ć™afa ta taka har cikin lambunta, kuyangarta Huda tana biye da ita,bayan ta isa zuwa rumfar da take zama take hutawa Huda ta shimfiÉ—a mata kilishin da take zama,ta zauna sannan ta kalli Huda ta ce"ki yiwa dakare É—aya magana a cikin waÉ—anda suke gadin lambun nan ya kira min Kazuzi,ke kuma ki je na sallame ki"Huda ta rissina ta ce"an gama ya shugaba ta, Allah ya Ć™ara miki iymani d tausayi"daga haka ta miĆ™e ta fice daga lambun 

Jim kaɗan Kazuzi ya iso,a ɗan kallon da ta yi masa ta fuskanci ya ƙara jin sauƙi akan jiya,ya ƙaraso cikin lambun, Kamar yadda ya saba ya rissina ya gaisheta,bata amsa ba ta umurce shi ya zauna,sannan ta dube shi ta ce"na kasa haƙura akan batun labarin nan, saboda na ƙagu na ji me ya faru da Malli ɗinka har ta rasa ranta"

Ɗan murmushi ya yi,yana matuƙar girmama gimbiya Hayat,yana jin ta a ranshi saboda yadda ta damu da Malli,a hankali ya ce"na yi Miki alƙawari,kuma tabbas zan cika ranki ya daɗe,to ga labarin Kazuzi da Malli;






*Menene a cikin labarin Kazuzi da Malli haka ne?wanene Kazuzi ibn Murad? menene a ɓoye a rayuwar shi a Baruda wanda muke hasasowa?

Ku biyo alƙalamin Nusy bee don warware komai




#Nusy_bee