IZAYA

1

by @pherty001

ﺑِﺴْـــــــﻢِﷲِﺍﻟﺮَّﺣْﻤَﻦِﺍلرَّﺣِﻴﻢ







Tun daga nesa da su ka hangi zuwan mota ƙirar Lexus RX 350 / RX 500h, suka hangame gate ɗin Mansion da sauri, kafin isowar motocin tuni duk securities dake gate ɗin suka bayyana cikin girmamawa kowane ya mayar da kansa ya sunkuyar cike da tsoro, yana ɗaya daga cikin tsarin gidan, duk wani bawa bai isa ya haɗa ido da ɗan gidan ba sai da izini, sai kuma kallo daga nesa. Motocin na gama shiga aka rufe gate ɗin da sauri, kafin securities da sauran guards su zagaye tsadaddiyar mota acikin motocin da suka shigo, ta jima acikin motar tana amsa call batare da ta damu da wadanda ke a tsaye waje suna jiran ta acikin rana ba, yanayin fuskarta bazaka tantance murmushi take ko akasarin sa ba saboda izza dake jinin ta, tana gama wayar aka buɗe motar da sauri, guards biyu da security detail duk suna tsaye suna jiran fitowarta, nan take wurin ya ɗauki qamshin turaren ta na Dior J’adore L’Or, ta fito da qafarta dake sanye da Muaddi Heels, farare tas masu ɗauke da zanen jan lalle da suka yi matuqar fito da kyawun ƙafar, ta fito cikin nutsuwa, tana sanye da white silk shirt, da wando Burberry high-waist trousers, mai launin beige, kayan dai dai jikinta, hannunta ɗaya ɗauke da Vertu Signature Cobra ɗinta, ƙirar custom made phone da aka yi da white gold da ƙaramin ruby a gefen logo, ɗayan hannunta kuma ɗauke da Saint Laurent black tote bag, Vintage scarf ɗinta mai launin cream da ƙaramin embroidery na silver, ya lulluɓe kanta zuwa wuyanta cikin kyan ado, jan bakinta mai launin deep crimson ba qaramin kyau yayi wa fuskarta ba, idanunta boye cikin oval Dior sunglasses masu smoky lens, duk suka sunkuyar da kansu cikin girmamawa suna gaida ta, ko kallo basu ishe ta ba, qaramin tsaki taja kafin ta soma tafiyarta mai ɗaukar hankali, yanda tsinin takalmin ke bugun marbles dole qarar tafiyar ke janyo hankalin mutane zuwa gare ta, tafiya take cikin kwarewa da takalmin da kuma izza, ta na kai gab da shiga babban falon mansion aka yi saurin buɗe mata ƙofa, security na wurin suka sunkuyar da kai cikin girmamawa, ta yatsina fuska kaɗan tana kallon su, “Next time, I want that door open before my shadow touches it, bana son jira” tayi mgnr cikin sanyi da izza da wata irin muryar ta mai daɗin sauraro, duk suka amsa kusan lokaci ɗaya cikin girmamawa, ta cigaba da tafiyar ta cikin taku na jan hankali, duk suka bi bayan ta da kallo, NIHAL BILAL, ƴa guda tak a gurin Comptroller General of customs (CG) Alhaji Bilal Usman, mutum ne mai tsananin zafin kai akan aikinsa, Yana da ikon da zai iya katse kasuwanci a minti 5, ko ya buɗe wa wani masarafi ƙofa zuwa biliyoyi a cikin kwana ɗaya. Shi ya ke karɓar daily briefing akan, tariff ɗin da ake collecting a borders, seizures na contraband, high profile clearances, security risk alerts. Ko kafin ya kai wannan matsayin, mutum ne mai arziki sosai shiyasa da sanin sa baya yarda haram ta shigo acikin dukiyar sa, yana da gaskiya da amana akan aikinsa, Albashin sa “legal” ya isa ya rayu kamar elite, amma network ɗinsa a cikin system, power, access, information, shine real currency. Duk wanda ya san “value of clearance” ya san cewa ko da babu cin hanci, in kana control gate keeper kana da control arzikin kasuwa. Shi mutum ne mai zafin kai sosai, babu wanda zai iya ƙalubalantar hukuncinsa face-to-face.
​Idan ya ce a riƙe container ana riƙe shi har sai ya bada go-ahead. Idan ya ce a buɗe ana buɗewa batare da bata lokaci ba, shiyasa sunan sa da zafin sa yayi fice a faɗin Nigeria. Yana da hannun jari a kamfanoni masu ruwa da tsaki (logistics, freight forwarding, warehouses). Wasu kamfanonin suna aiki a bayyane, wasu kuma a asirce suna rike contracts na clearance da warehousing, sai bangaren seized assets and resale kaya da ake kwacewa a gabar teku ko a filin jirgin ruwa irin su contraband, luxury cars, high-end electronics, ko drugs, kan ratsa hannunsa ta hanyoyi a ƙarshe wasu ana miqa su hannun gwamnatin, ko su sayar a kasuwa su kai kuɗin gidan marayu, ko su ajiye kayan a warehouse, Idan Kuma drugs ne qona su yake yi ba ruwan su da ko kayan billions ne, Sai kuma Informal revenue streams, akwai hanyoyin samun kuɗi na “service fees” da ba a rubuta ba, expedited clearances, waivers, preferential tariff rulings. Ba duk cin hanci bane mai suna, amma tsarin yana ba shi damar saka hannu cikin duk abinda ya shigo da fita. Sai kuma ta fannin Access to intelligence, yana samun daily briefings, manifests na containers, bayanan banki na masu clearance (ta hanyar haɗin gwiwa), da bayanan sirri daga hukumomin tsaro sannan yana da alaƙa da manyan 'yan siyasa, masu kamfanoni, 'yan sanda, da waɗanda ke aiki a tashoshin jiragen ruwa. Wannan network ne ke tabbatar masa babu mai yin masa gasa cikin sauƙi. A bangaren Patronage & appointments, zai iya tsara wanda zai samu contracts, wanda zai yi aiki a manyan mukamai, ko ya sauya wasu dokoki na ciki ta hanyar matsin lamba. Sai kuma Legal armor & impunity, ta hanyar ƙwarewa a tsarin, yana amfani da takardu, memos, da burodi na bureaucracy don kare kansa, yana da masaniyar yadda za a rufe bayanai idan hukuncin sa na rufe wani route ko dakatar da wani importer na iya haifar da hasara miliyoyin naira a cikin ƙasa ɗaya, wannan shi ne cikakken iko na tattalin arziki, bangaren tsaron kansa, yana da tsaro na musamman bodyguards, private security firms, da kuma sau da yawa da haɗin kai da hukumomin tsaro, kuma mutane suna girmama shi a ko ina saboda mutuncin sa, a gurguje ko Ince a taqaice dai CG Bilal Usman yana da mata ɗaya HAJIYA SALIMA da ƴarsa tilo NIHAL, duk zafin kansa, duk hardness nasa, duk wani iko nasa, Nihal ce week point ɗin sa, Nihal ita ce wani duniya daban a wajen sa ko Ince a zuciyarsa, harshen sa yana sauƙa idan yana cikin fushi ko faɗa saboda ita, muryar sa tana taushi idan yana tare da ita, haka yake komawa kamar yaro a gabanta sai ka rasa acikin su waye yake yiwa wani shagwaba acikin su idan suna zaune a guri ɗaya saboda ƙauna mai zafi dake tsakanin su, A duk duniya, babu wanda zai iya karya shi kamar yadda ta iya yi.
​Babu wani abu zai iya dakatar dashi daga yanke hukunci mai tsauri, sai dai idan ya shafi jin daɗin Nihal. Wannan shine crack ɗinsa. Idan za a rusa shi, ba a rusa shi ta office ko aikin sa ba, arusa shi ta zuciyar sa wato Nihal.

JIBRIL TAMBARI shine wanda mahaifinta ya zaba mata a matsayin wanda zata aura, yaron DCG ne, nutsuwar sa da hankalin sa ya saka sanda Jibril ya ga Nihal yana so kai tsaye CG Bilal ya aminta batare da dogon tunani ba sanin ko waye Mahaifinsa, kusan tsari da zafin kansu akan gaskiya guda ne, kuma Nihal ta amince da Auren Jibril saboda mahaifinta yana son shi, kuma Jibril irin mazan da take so ne, classic and rich, Yana nuna mata so da kashe mata kuɗi ko nawa ne, kuma duk abinda take so yana yi mata, yana biyewa duk wani hali nata batare da nuna damuwa ba, baya mata faɗa kamar mahaifinta, duk abinda take so ko tayi kuskure dai dai ne a gurin sa saboda baya son bata mata rai tace ta fasa auren.

Wannan kenan. 



#IZAYA
#Pherty
#Nihal
#Jibril