IZAYA

2

by @pherty001

Yanayin tafiyar nata ya saka Hajiya Salima cira kai daga danna wayar da take tana kallon ta, ko ba'a faɗa ba tasan mutum ɗaya ne mai wannan izzar, ita kaɗai zata shigo gida da irin wannan tafiyar ta ɗaukar hankali, ta jefar da bag ɗin ta akan seater da duk abinda ke hannunta, vintage scarf ɗin ma fisge sa tayi nan take gashin ta dake ɗaure ta ribbon ya biyo gashin ya warware, madubi idanunta da takalmin ta kusan a tare ta cire su, ta dubi mahaifiyarta a shagwabe kamar zatayi kuka tace "mamee, the birthday party wasn’t fun, da na sani ma banje ba.” Hajiya Salima ta tabe bakin ta cikin jinjinawa kafin tace" yayi maki kyau ai, tun da baki da aiki kullum sai yawon club da party, kullum ina addu'a Allah ya shirya ki keda mahaifin ki dake ɗaure maki", Nihal tayi mata wani kallo, har ta buɗe baki zata yi magana sai kuma ta juya da sauri ta bar falon cikin bacin rai, tana ƙwalawa Lawee kira, da hanzari ta fito tana russunawa cikin girmamawa, kallonta Nihal tayi tana yatsina fuska, 'ki ɗauko kayana a falon umma", da sauri Lawee ta raba ta gefen ta, tana shiga part ɗin ta, lumshe idanunta tayi cikin wani yanayi na jin daɗi saboda qamshin da ya bigi hancin ta, hannu ta saka ta balle maballin gaban rigar ta, Lawee ta shigo bayan ta bata izini, ta ajiye komai a muhalli sa kafin ta bar ɗakin da sauri ganin Nihal na cire kayan jikinta, towel ta daura tana ƙoƙarin shiga wanka wayar ta, ta ɗauki qara, ta juya tana kallon wayar, daga yanayin tone ɗin ta gane Jibril ne, bata tsaya bi kan wayar ba ta shiga bayi, ta jima sosai kafin ta fito kamar wacce zata canza fatar jikinta, shiru tayi tana kallon Haleema dake fito mata da kayan da zata saka a wannan lokaci, duk wanda ke aiki qarqashin Nihal yasan halin ta na rashin son surutu da hayaniya akan masu aiki, kuma kowacce mai aiki dake sashen ta tasan aikin ta akan uwargidan ta, basa son bacin ranta ko kuskuren abinda zai bata mata rai har su rasa aikin su, ba qaramin kuɗi ake biyan su ba a duk wata saboda kula da komai nata, kuma kowacce acikin su da aikin da take yi a qarqashin Nihal, sun sani Nihal tana da faɗa da tsiwa sosai shiyasa suke ɗari ɗari da ita, Haleema itace mai kula da kayan sakawar ta, a kowane rana, kowane lokaci tana sane da irin kayan da Nihal take sakawa a kowane yanayi sai idan itace ta nemi sauya wa, Lady Norah itace jewels keeper na Nihal mai kula da jewel chamber, duka kayan da Nihal ta saka tana bata jewels na dai dai da shigar jikinta wanda zasu fito da ita sosai, laweeza itace Head of the house maintenance na Nihal, kowa a qarqashin ta yake, itace mafi kusa da Nihal acikin masu aiki, ta fi shaquwa da ita sosai shiyasa komai lawee, lawee, Sai Hadiya room fragrance, da ma turaren sakawar ta duk itace, komai da ya shafi qamshi na part ɗin Nihal to Hadiya ce, Aysha hairstylist mai gyara gashin Nihal, and her makeup & skincare specialist, tana da certificate na karatu a Paris academy of beauty, Dr. Elenora itace family Doctor ɗin su, wacce ke kula da Nihal da mahaifiyarta idan buqatar hakan ya tashi, ko da bata qasar CG Bilal da kansa yake kiran ta akan tazo ta duba Nihal ko matar sa, sun saba da ita sosai kuma tana jin daɗin aiki dasu saboda yanda yake girmama ta, masu tsaron Nihal a duk inda zata je guda shidda ne, suna amfani da earpiece na communication a tsakanin su ko da yaushe, basa magana da kowa sai da Nihal ita kaɗai, ko party ko club duk inda zata je suna tare da ita suna tsaron lafiyar ta, suna da training daga Switzerland kuma suna canza shift kamar yanda CG Bilal ya basu umarni, bai yarda da kowa ba shiyasa yake da tsaro akan Nihal, kada maqiyansa suyi amfani da ita, shiyasa ko guards ɗin dake tsaron lfyrta yake canza su akai akai gudun kada a haɗa baki da wani acikin su a cutar da ita, Mota uku ce take amfani dasu, sune ababen hawanta Idan tana qasar, Lexus RX 350 / RX 500h, Range Rover Serenity da kuma Rolls Royce Dawn, kowacce da tambarin N.B a plate number ɗin ta.

Tana gama shiryawa ta dauki wayar da har zuwa lokacin ringing take ta ƙara a kunnen ta batare da tayi magana ba, ya ja numfashi kaɗan acan bangaren yana faɗin "Hey Beauty, where have you been Ina ta Kiran wayar? ta soma taka stairs kamar bazata yi magana ba tace" ina wanka, and you keep on calling, why? Yace "ina jin tsoro ko nayi wani laifin ne ake fushi dani", tayi shiru bata yi magana ba, ya cigaba da faɗin "and shine kika je kika yi wanka baki jira nazo mun yi tare ba", tayi far da ido kamar yana ganin ta a lokacin tace "don't expect that ko bayan auren mu", "why? ya tambaya sounding worried, we are married, meyasa baza muyi tare ba, akwai lada mai tarin yawa My Beauty", ya qarasa mgnr cikin shigar rarrashi", ta zauna a balcony tana kallon gate ɗin gidan, cikin muryar ta mai daɗin gaske tace "is like kana son saba alƙawarin mu, ka manta yarjejeniyar da muka yi kafin na amince da auren ka", yace "am not requesting for sex, wanka kawai nace mu riqa yi tare when ever am at home", tayi shiru batare da tayi magana ba, ya sassauta muryar sa kaɗan kamar mai jin tsoro yace, "ai nasan kin ce bazaki haihu da wuri ba, bakya son ki tsufa ki rasa shape ɗin jikin ki, I accepted bazamu haihu da wuri ba, and kin ce ko kin haihu bazaki shayar da babyn ba cos bakya son boobs naki suyi sagging, I accept cos nima is what I like most a tare dake, let it be mine, ni kaɗai ko ɗan cikina ina mai jin kishin nayi sharing dashi", ta lumshe idanunta ta buɗe batare da tayi magana ba, yace "kin yi shiru my beauty", tace "baka gama faɗin alqawarin ba, you only says two? yayi jim cikin tunani, yace" na manta am so sorry, ki tuna min", ta bata rai kafin tace "saboda baka dauke su da muhimmanci ba har kake manta wa..... yayi saurin katse ta, Every single thing you say matters to me, yanayin ayyuka ke sa nake da saurin mantuwa amma ba'a kanki ba, kiyi hak'uri", tace "I will not be your sex machine, zamu kasance da juna once in a month, if you accept am ready to get married to you", ya sauke nauyayyen numfashi yana jin tsikar jikinsa na tashi, a ransa yace "kizo hannu tukunna", a fili kuwa yace "accepted", ta saki wani lallausan murmushi, kafin tace "idan ka saba alqawari ko ɗaya aciki, Daddy zai raba auren", yace "matsalar ina son ki da yawa, if not I will not accept, I want to be with you Ko sau ɗaya ne, idan zamu yi barci tare and cuddle I promise bazamu kasance da juna ba sai da amincewar ki", tayi shiru batare da tayi magana ba, ya qara qasa qasa da muryar sa cikin rarrashi, "dan Allah kada kice a'a, na yarda da dukkan alqawarin ki kuma bazan saba ba, amma wannan alfarma ina son, please Nihal l.... ta katse shi da sauri," shikenan na amince", taji ajiyar zuciyarsa da qarfi, har cikin ransa ya amince kuma yaji daɗin da ta yarda da hakan, in dai har zasu riqa barci a gado ɗaya kuma yana taba jikinta, zai iya haqura da wancan dan farinciki ta da kuma son kasancewar sa tare da ita, yanda yake son ta da jinta a zuciyarsa babu abinda bazai iya mata ba, and he keep his promises insha Allah, yace "zan shigo anjima", kai tsaye tace "ok" tare da katse kiran, bata jima a gurin ba ta tashi da sauri ta nufi cikin gida. Da dare bayan yazo ya jima zaune a falon ta yana jiran ta, cos kai tsaye ake bashi damar shiga har part ɗin ta ya jira ta batare da damuwa ba tunda shine zai aure ta, yana zaune kan single-seater couch, he is so charming and classic, irin kalar fatar jikinsa caramel chocolate, kyakkyawan gaske, wanda ke ji da kuɗi da ilimi, da ka ganshi Kaga yaron Daddy, Yana sanye cikin black cashmere polo top da dark tailored pants, kamilallen gentleman look, ya duba time yafi awa ɗaya da zuwa amma shiru ba alamar ta, fuskarsa ta canza zuwa fushi da takaici kansa yanda yarinya qarama take walagigi dashi, ya dubi tarin abinci da aka jera a gabansa sai kace wanda cin abinci ne ya kawo shi gidan, yaja qaramin tsaki dai dai lokacin da qamshin turaren Louis Vuitton Pur Oud ya ziyarci hancin sa, ko ba'a faɗa ba yasan itace mai zuwa daka yanayin takun tafiyar ta na izza, ya cira kansa daga wayar sa yana kallonta sanda ta shigo falo, Tana sanye da Zimmermann dusty rose lace two-piece, Top ɗin nata long sleeve modest, lace ɗin high-end mai matuƙar tsada, lace ɗin ba aikin ƙananan brands bane wannan special edition ne irin na wealthy elites. Skirt ɗinta long, soft flare, ankle length shape ɗinta ya bayyana lightly, ba bold, ba loud perfect feminine modest silhouette. Skin nata fari porcelain, milky clear, no blemish, fuskarta tafi kyau a natural ɗin ta, tana da deep dark brown eyes manya masu matuqar haske da daukar hankali, musamman idan ta zuba maka su, hancinta dogo siriri dai dai fuskarta, lips nata baby-soft natural pink, little full masu matuqar taushi, gashin kanta a gyare neatly anyi parking ɗin shi at her back, ƙaramin mayafi ne akan ta hakan ya bashi damar ganin yalwar gashin dake kanta sosai, yanda take tafiya cikin ɗaukar hankali yaji ya qara narkewa a inda yake zaune duk wani fushi da bacin rai lokaci ɗaya ya neme su ya rasa musamman daya ɗora idanunsa akan kissable lips ɗin ta, every step of her is a confidence in quite, ta zauna tana fuskantar sa, "ya ilahi ya furta a zuciyarsa, ya Allah kasan yanda nake son wannan baiwa taka ka mallaka min ita", yayi maganar a zucci, yaji tace "sorry I keep you waiting", cikin muryarta mai sanyi da daɗi, yace "kome kika yi you're right, bazan Iya fushi dake ba, I so much love you Nihal", ta lumshe idanunta a hankali kafin ta buɗe tana kallon sa, "same with me", yaji wani sanyi a ransa, yace "kin yarda Abba ya yiwa mahaifin ki magana, I want us to get married as soon as possible, wallahi bazan jure kallon ki haka kullum ba without touching you", ta bata fuska kaɗan kafin tace "it seems kana manta alqawarin mu yanda kake nuna zaquwa akaina kullum, Ina jin tsoro..... bai bari ta qarasa ba yayi saurin taryar numfashi ta, yace"  Aure sunnah ne kuma Allah ya halatta shi akan kowanne musulmi mai lafiyar da zai iya aure Nihal, Wallahi kin ji na rantse a kowane yanayi kika tsinci kanki zan so ki har bayan raina, bazan taba juya maki baya ba dan kawai shape na jikin ki ya canza ko da kin haifa min yara goma ne", nan take ta bata fuska, taji wani bacin rai, ta sauke qafar ta ɗaya dake kan ɗaya ta soma qoqari tashi ta bar masa falo, kamar yasan abinda take shirin yi, yayi saurin taryar gabanta tare da riqo hannunta, nan take ya langabar da kai cikin shigar rarrashi kamar wanda zai mata kuka, "shikenan na haqura, abinda kike so shi zaa yi, am so sorry my beauty", tace "abu ɗaya zan lamunce maka aciki only romances na haqura da wannan", ya gyada kansa alamar amincewa yana kallon lips ɗin ta kamar ya tsotsa yake ji, duk jikinsa ya gama yin weak saboda wani qamshi mai daɗi da sanyi dake tashi a jikinta, ta koma ta zauna, suka cigaba da hira cikin kulawa, bayan ta amince da ya yiwa mahaifinta maganar auren ta shirya a yanxu.

#IZAYA

#Pherty

#Nihal

#Jibril