3
by @pherty001
Nnamdi Azikiwe Airport Abuja.
Shine mutum na biyu da ya fito acikin jerin mutanen dake fitowa a jirgi bayan saukar sa, fari Arab/fulani mix, glass milky complexion dogo mai ginannen jikin da babu rama acikinsa, physique ɗinsa neat, tall, built mai ƙarfi amma ba bodybuilding ba, heavy fit & elegant masculine frame, Gashin kansa black brown, yana da natural sheen, an gyara shi lightly. Idanunsa suna da wani depth mai ɗaukar hankali, sharp black eyes masu weight, hancinsa dogo ne, madaidaici, aristocratic angle, Sajen sa trimmed clean, short, neatly maintained. Bakin sa nicely shaped, little plush a lower lip, masculine lustre. Yana sanye da Tom Ford dark cocoa two-piece travel set (light silk cashmere blend), agogon hannunsa na Richard Mille RM, idonsa sun ɓoye a half under Cartier Santos-Dumont sunglasses, ƙafarsa sanye cikin Hermès Chukka Boots rich dark brown suede, Sai hannunsa rike da Goyard Boeing travel bag, a hankali yake taka steel stairs yana saukowa daga cikin jirgin, presence ɗin sa kamar old money prince, akwai AURA a tattare dashi ta ko ina, kai tsaye ya nufi motar sa ƙirar Maybach S680 V12 inda ya ga yaransa a tsaye suna jiran saukar sa, tun kafin ya qaraso suka buɗe masa motar tare da gaisuwa ta girmamawa, babu wanda ya kalla acikin su balle su saka ran zai amsa masu, fuskarsa a murtuqe like always Sai dai yau tafi ta kullum, yana shiga motar suka rufe da sauri kafin su qarasa tasu motar suka shiga da sauri suka morawa motar sa baya.
ESHRAQ QURAIM MANSUR, The young billionaire man, ɗan shekara 35 a duniya, wanda aka fi sani da Tycoon, sunan da yafi fice dashi a faɗin Nigeria fiye da asalin sunan sa Eshraq, yaro mai tashe a wannan ƙarnin, Alhaji Mansur Tycoon bafillatanin Adamawa, wani hamshaqin mai kuɗi a lokacin ganiyarsa, ɗan kasuwa mai hada hadar kasuwancinsa na gida da waje, ya haɗu da balarabiyar matarsa a Saudiyya, Hajiya Maryam, ƴar jinin sarautar Khobar, Soyayya Mai zafi ce a tsakanin su wacce ta kai Maryam ta yarda ta biyo sa gida Nigeria ta zauna dashi bayan duk faɗi tashi da tayi akan iyayen ta kafin amincewar su ta aure sa, sun haifi tilon ɗan su Eshraq, gata babu wanda basu nuna masa ba tun yana jinjirin sa, so da ƙaunar da suke masa kuma bai sa sun gurbata tarbiyar sa ta kowace hannya ba, yana shekara goma sha biyu a duniya mahaifinsa ya rasu, ya mutu ya bar masu tarin dukiya mai albarka, bayan yan uwa sa sun karbi abinda zasu karɓa ta tattara sauran dukiyar da komai suka koma masarautar Khobar a Saudiyya da zama, acan yayi karatun sa, ya taso cikin kulawa da soyayya irin ta UWA, ya taso cikin mulki da sarauta, bayan ya mallaki hankalin kansa ya dawo gida nigeria ya zauna, shekarar sa ɗaya ya sake tattarawa ya koma Saudiyya da zama, daga nan kuma ya soma zarya tsakanin ƙasashen duniya, zuwan yawon bude ido, kafin ya soma wata harkalla a boye wacce ko mahaifiyarsa bata san irin sana'ar da yake ba, na shigo da cocaine nigeria, tun yana yi kaɗan kaɗan har ta kai shi da shigo da container na cocaine yana siyarwa, babu abinda ya saka a gabansa kamar neman kuɗi, acewar sa yana son sunan sa yayi fice fiye dana mahaifinsa a nigeria, yana son yayi kuɗi masu yawan gaske kuma ya duba babu abinda zai bashi irin kuɗin da yake so kamar wannan sana'ar da yake a boye batare da sanin kowa nashi ba sai abokan sa guda biyu amintattu Rayhaan da Yusuf, mutum ne da bai damu da kowa da komai ba, idan nace komai ina nufin har da MATA aciki, mace bata taba burgesa ba, inshort, bai taba soyayya ko sanin yanda ake yin sa ba, bai taba kallon wata mace da sha'awa ba, mace biyu ce a zuciyarsa da duniyar sa MAHAIFIYAR Sa da kuma kakarsa, yanzu ma shigowar sa a wannan karon nigeria cike da tashin hankali ne matuqa amma bazaka taba ganin haka a fuskar sa ba, ya turo da container ta cocaine kusan billions of naira da zai samu a garesu ya sami labarin an kama containers ɗin, container ɗin da zata juya mafarkin sa daga small billionaire zuwa big billionaire, duk yanda ya so yayi magana da wanda ya kama containers ɗin abin yaci tura a waya shiyasa yayi tattaki da kansa zuwa nigeria domin haduwa da CG BILAL USMAN wanda ke kusa da rusa masa harƙallar sa, da sauri aka buɗe masa motar sanda ya iso, cikin girmamawa suke gaidashi, babu wanda ya amsa aciki, ya shiga motar driver ya tayar, security convoy 2 suka biyo bayan sa, ga hazard lights na luxury escorts suna haske kamar wani slow pulse mai jan hankali. Ya juyar da kansa gefen window yana kallon manyan tituna, da yanda motoci suke tafiya akan titin cikin rhythm ɗin su, streetlights suna haskaka steel rims da shiny paintwork na motoci kamar subtle glamour. Dukkan tafiyar ta kasance slow, deliberate, kamar scene na high-budget film, mai nuna wealth da power a kowane frame, basu yi doguwar tafiya ba suka iso Guzape Exclusive zone, unguwar da yawanci zaka sami duk wealthy people ne aciki, kai tsaye driver yayi left side ya shiga private inner street Mai security fencing two sided, sai a lokacin ya ɗauke kansa daga kallon window tare da sauke numfashi kaɗan ganin sun iso massive gate na private mansion ɗin sa.
Gate ɗin da kansa ya buɗe automatically da recognition, ya cira kai yana ƙara kallon ƙaton gidan mai ɗauke da compound mai yalwa, ga green lawns, palm trees, da long water channel a tsakiyar compound ɗin da ambient lighting masu laushi. landscape na compound ɗin shiru tamkar babu wata halitta dake rayuwa a gidan, dama babu kam, tunda babu mace ko ɗaya a gidan duk da tarin masu aiki dake gidan, shi fa duk wani abu da ya shafi mace baya so a rayuwar sa, ba wai kuma saboda wani dalili ba just haka ya taso babu mata a tsarin rayuwar sa may be sai dole idan ta haɗa wajen business ɗin sa, mace guda yake kallo a matsayin mace itace Umminsa sai kuma kakarsa, ko ƴan uwan sa babu ruwansa da su, daga gaisuwa shikenan, kai tsaye motar ta tsaya gaban parking space na gidan, Rayhaan da Yusuf dake bayan motar sa a qafa tun sanda suka shigo gate suke biye da motar har zuwa in da tayi parking, da sauri suka buɗe masa motar ya fito, Rayhaan yayi murmushi yana kallon sa, "Finally Eshraq is here", ya miqa masa hannu da sauri cikin girmamawa da ƙaunar dake tsakanin su da abokin su, Eshraq ya miqa hannunsa fuskarsa ba yabo ba fallasa saboda zuwan yayi sa ba'a cikin daɗin rai ba, Yusuf ma ya bashi hannu da sauri cikin murmushi, "welcome bro", Eshraq ya gyada kansa, har lokacin bai yi magana ba sai dai fuskar sa ta nuna pure calm composure a yanxu, ya soma takawa cikin izza zuwa foyer, har suka shiga cikin gida babu wanda ya sake mgn acikin su, sanin halin sa, suka isa qaton falon sa mai kyau da tsari, ya soma cire cufflinks ɗin sa yana ajiyewa a saman foyer console table, Rayhan da Yusuf suna tsaye a bayan sa, ya juya kaɗan yana kallon su, sai a lokacin ya buɗe baki yayi magana cikin izza, "let me settle in first", batare da ya saurare su ba kaai tsaye ya wuce su cikin nutsuwa, Rayhan da Yusuf suka je suka zauna a babban living area, wacce take facing inner courtyard glass, suna magana qasa qasa cikin tattaunawa akan matsalar da ta shigo masu yanzu, kai tsaye wing bedroom ɗinsa ya nufa, bayan ya cire komai na jikinsa yana daure da towel a qugunsa, kai tsaye ya haɗa ruwan wanka a jacuzzi tare da amfani da aromatherapy diffuser wacce ke fitar da Vanilla Oud mai daɗi sosai, ya lumshe idanunsa sanda ya shiga cikin bath ɗin Yana jin wani sanyi da daɗi a ransa, bai dauki wani dogon lokaci aciki ba ya fito sanin muhimmin abinda ke gaban sa, automatic wardrobe ɗin Sa ya buɗe kai tsaye bayan ya nufi gurin, ya ɗauki light custom Kaftan na gida marar nauyi ya saka very soft fabric, irin lounge wear na wealthy men, ya sanya slippers masu laushi ya fita, suka zuba mashi ido sanda ya fito, Eshraq miskili ne sosai sun sani, mutum ne daya tashi cikin kuɗi da gata, ga izza da iko, wanda prestige ba sabon abu bane a gareshi, yana da daɗin mu'amala ga wanda ya fahimci rayuwar sa, shiyasa duk acikin abokan sa su kaɗai ne suke iya zama dashi ba dan suma iyayen nasu basu da kuɗi ba, sai dan kaunar da suke masa shima yake son su, kuma sosai yake kyautata masu da duk abinda suke so idan bai fi qarfin shi ba, kuma kuɗin da suke samu a gurin sa ko a gurin iyayen su basa samun haka, kuma ko da ace suna samu still suna son zama da mutum irin sa, yana da kwarjini sosai a duk inda ya shiga, yana da mu'amala ta mutunci tsakanin sa da mutane, barshi kawai da miskilancin sa na rashin so hayaniya a duk inda yake, kallon su yayi yana faɗin "let's eat, haka na shigo jirgi ban ci komai ba", kusan a tare suka nufi dinning, an tanadar masu abinci mai rai da lafiya, suka zauna suka ci cikin nutsuwa, bayan sun gama suka koma main sitting room, Eshraq ya fara zama a single seat wanda yake a tsakiyar falon, hannun sa yana kam armrest na seater ɗin, ya kalle su a hankali da idanuwansa masu rikita wanda yake kallo, yace "am all ears", Rayhan da Yusuf suka dubi juna, kafin Yusuf ya gyara zaman sa kaɗan yace "container ɗin tana hannun CG BILAL, mun yi bincike a kansa mutum ne mai zafin kai sosai, da ƙyar ne ya iya bayar da container ɗin Eshraq cos an ce bai taba karba kaya ya mayar da shi a gun wanda ya karɓa ba", duk suka yi shiru suna kallon sa, shima kallon su yake, babu alamar bacin rai ko tsoro a tare dashi, abinda kawai ya sani he don't want to lose the billions Naira, Rayhan yayi sauri yace "Bilal bashi da sassauci akan komai idan kaya suka je hannunsa, musamman ma irin wanda muke shigo dashi which is not right, Ina jin tsoro kada ya hana kayan ko ya shigar da qara akan mu, and tunda container ɗin is a huge of money, and it will burn Idan ya cigaba da riqon ta a hannunsa kuma mu muke da asara, why not kaje ka same shi kai tsaye kuyi magana ko da wani abu yake so ka bashi sai a bashi ya sake mana kayan mu", sai a lokacin Eshraq ya ja wani dogon numfashi tare da lumshe idanunsa, kafin ya buɗe a hankali yana kallon su, "just give me real approach, I don't want to lose kun sani, ban taba samun kaya irin na wannan kuɗin ba, kuma with these billions of naira sunana zai yi fice a inda nake so wannan karon, and kuma kuna da babban kaso aciki kun sani, I don't want to be rude to him, kafin na ganshi ku fara ganin sa, idan yaqi ni sai naje da kaina". Yusuf yace "why not mu fara ganin DCG idan akwai wata hanya mai sauqi da zai ɗora mu akan sa wacce zai bamu kayan mu batare da wahala ba? Yusuf yace" Good idea, gobe da sassafe zamu je mu same sa", Eshraq yayi shiru bai yi magana ba, daga nan suka cigaba da tattaunawa akan sauran business ɗin sa, bayan wani lokaci suka tafi suka barshi ya huta, ya zauna ya kira mahaifiyarsa Vedio call wacce ita kaɗai take ɗebe masa kewar da duk ya tsinci kansa aciki koda yana cikin bacin rai kallon fuskarta da murmushi ta kawai kan gusar da komai, farinciki ta yana da matuqar tasiri a rayuwarsa.
#IZAYA
#Pherty
#Nihal
#Tycoon
#Jibril
#CG BILAL
#Yusuf
#Rayhaan