Kuncin zuci
by @bintuuu
Ranar da Bilal ya fita daga iyayensa sai ya rasa in ya dosa, komai na duniyar ji yake baya masa dadi, ga wani nauyi da yaji zuciyarsa ke masa kamar ta faso daga qirjinsa, yananan tsaye a kofar gidan nasu ya daga kafarsa ya fara taku a hankali har ya isa bakin street din unguwar tasu, napep ya tara sai ya rasa Ina zai ce akaisa sai ya kawai ya kwatanta masa gidansa da baida nisa dasu, a wannan halin ya isa gidan da babu ko megadi yanzu ya koma kamar kufayi, ko Ina shiru kamar babu dan adam dinda ya taba rayuwa a gidan, sauqinta sai da ya Hajiya ta sa shafa ta biyosa da key din gidan duk da bai taba kawowa aransa nan din zai zo ba koda yanada makullin gidan, dan shi kadai yasan me yake ji a zuciyarsa zuwa yanzu, ji yake ya tsani rayuwar sa da yayi wasa da ita a lokacin da Allah ya basa damammaki masu tarin yawa, yana shiga falon ya tsaya yana bin ko'ina da kallo memories suna ambaliyan zuwa cikin kansa, kayayyakin sunanan kamar yanda suke a baya babu abunda ya chanja, daya haura zuwa upstairs ma dakin da Na'ima ta rayu cikinsa ya wuce tareda tura kofan a hankali kamar wanda yake gudun ganin wani abun, Amma sai wani irin emptiness ya dakesa yayin da ya shiga dakin, zama yayi a bakin gadon yana jin zuciyar na shiga wani irin kuncin da bai taba zato ba, sai da ya kwashe mintuna fiye da sha biyar yana zaune a dakin sai ya kai yatsansa daya yana taba abunda yaji a fuskansa sannan ya dago hannun yana kallon ruwan hawayen dan baisan lokacin da hawayen yafara zuba masa ba, sai yakai tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa gaba daya yanajin kuka na zuwa masa mai zafi...Ranan Bilal yayi kukan da bai taba yi ba tun tasowarsa, gidan ya tado masa da kewarta matuka, kome ya kalla ita yake tunawa wanda yasan hakan ba daidai bane amma ya kasa hana kansa yin hakan, yayi dana sanin da bai taba yi ba, a ranan yayi tunani iya tunani akan inda hankalinsa ya tafi har yayi irin wannan rayuwar da Na'ima, yayi questioning tunaninsa sosai akan abunda ya shiga kansa ya musguna mata abaya, and yayi kukan rashinta, rashinta na har abada....
Daga karshe kasa zaman gidan yayi ya sake komawa gidan iyayensa, a wannan lokacin da Alhaji yaga yanda idanun dan nasa suka kada ga wata uwar rama da yayi shima saida yaji zuciyarsa ta karye amma ya dake yace masa ya fice masa daga gida dagaske yake ya yafesa yaje can yayi yanda yaso da rayuwarsa tunda be dauke su a bakin komai ba, sake durqushewa Bilal yayi a gaban maihaifin nasa yana kuka a wannan karon yace "Abba ji nake kamar zan mutu, wallahi mutuwa zanyi in kuma kuka ce ba ruwanku dani" sai Hajiya ta fashe da matsanancin kuka ta kasa magana, Bilal ya sake cewa "Dan girman Allah da manzonsa ku yafemin ko zan samu sauqi a rayuwata, wallahi inaji na tsani kaina, ji nake kamar in mutu" sai sannan Alhaji yace "Bazaka mutu ba Bilal, amma kasani kayi kuskuren da bazaka taba gyarawa ba sai dai ka nemi yafiyar ubangiji, kayi wasa da ni'imar da Allah ya maka a rayuwa, kasaka kafa ka ture duk wani alkhairinsa gareka, Bilal me Na'ima ta maka da tayi deserving abubuwan da ka mata, me yasa kayi choosing ka musguna mata ta mummunan hanya, meye laifinta dan tayi hakuri ta zauna cikin inuwar aurenka dake kanta a bayan" Bilal na kuka bilhaqqi yace "Wallahi bansani ba Abba, nima bansan dalili ba, inasonta Abba, wallahi Ina sonta, da inada halin dawo da lokaci da zan yi hakan dan in gyara kuskuren da na aikata gareta da ku ma Iyayena, Dan Allah ku yafemun ko zan samu sauqi a rayuwata" sai Hajiya ta share hawayenta sannan ta qarasa garesa ta dafasa tace "Na yafe maka babana, nima nayi kuskure da banyi iya kokarina gurin fahimtar dakai gaskiyar abunda kake aikatawa ba" Alhaji yace "Na yafe maka Bilal, Allah ya baka ikon gyara halayenka, Allah ya gani Ina matuqar son ka kasance da nagari da zanyi alfahari dashi a kullum, amma sai kayi choosing wani lane daban a rayuwarka, adalilin haka ko bacci bana iyayi wataran Bilal, Ina tsoron in mutu Allah ya tasheni akan hakan" Bilal yayi saurin cewa "Zan gyara Abba, in sha Allahu zan gyara, nayi alkawarin hakan" sai sannan Alhaji yayi murmushi tareda kamo hannunsa yace "Allah ya yafe mana gaba daya" Hajiya tana murmushi itama ta amsa da Amin suna kallon dan gudaliyan nasu da chanjin da ya samu a karo na farko cikin rayuwarsa.
Ranan wata alhamis wanda ta kasance kwana biyu da zuwan Na'ima gurin Nafisa, Ahmad ya mata wani alkhairi da bazata taba mantawa ba, yana zaune a falonsa misalin karfe daya da rabi na rana ta shigo hannunta riqe da quick lunch dinda ta masa kasancewar dawowa gidan da yayi da wuri kuma unexpected, sai da ta ajiye masa akan glass table din dake gabansa sannan ta zauna a kusa dashi yana kokarin unbuttoning hannun white sleeve din jikinsa takai hannunta tafara tayasa tace "Yau kun tashi da wuri ne?" ya dan girgiza kai alamun gajiya na bayyana a fuskarsa yace "Ba daga can office din nake bama, naje tank farms dinmu ne daganan na biya wani filling station da ya kammalu" sai Na'ima ta sake kai hannu tafara unbuttoning wuyar rigar jikinsa tace "Sannu, ko zaka fara wanka kafin kaci abincin toh" ta qarasa maganan tana tayasa cire sleeve din daga jikinsa ya rage white singlet ajikinsa da dogon wandon suit din nasa, sai yace "I'm so hungry Babe, let me dive into this food first then everything will fall into place" tana murmushi tayi serving dinsa ya fara ci a nutse tana kallonsa, ba su sake cewa komai ba suka zauna cikin shiru sai Tv ce ke aiki a falon, sai da Ahmad ya kai last spoon din abincinsa sannan ya ajiye akan plate din ya juya tareda jawo briefcase dinsa dake gefensa ya ciro wasu takardu ya miqa mata, yana kallonta yace "Here, this is for you" da dan confusion Na'ima ta karba tafara duban takardun, sai kuma ta dago ta kallesa da alamun mamaki a fuskarta tace "Nawa?" Ya gyada kai shima yana murmushi yace "Yes Babe, my gift to you" ai da sauri ta haye jikinsa sukayi baya dukansu akan kujerar yana dariyan reaction dinta, rungumesa tayi cikin farin ciki tace "Nagode, Allah ya biya maka buqatunka na alkhairy" sai ya fara shafa bayanta ya mata rada da "Anything for you Babe, you like it?" sai ta dagashi tana gyara zama tace "Are you kidding me? Of course I like it, I love it" sai ya danyi dariya ya kamo hannunta daya yace "Then am glad you like it" tana murmushi tace "Nagode sosai" sannan ta sake dago takardun tana ganin sunanta dake rubuce akan takardun gidan mai daya mallaka mata da sunanta, sai taji yace "Inata figuring sunan da zan saka, sorry ban tambayeki ba saboda Inason ya zamo surprise gift ne" tace "Wannan sunan ma is perfect, Dabo Energy..wow" ta juya tana kallonsa ganin yana kallonta da murmushi dauke a fuskarsa, ahankali tace "I love you so much" sai yakai hannunta bakinsa yayi mata kiss sannan yace "I love you more than words could tell Na'eemah" sai taji hawaye na zuwa mata tana kallonsa, He is really trying so hard for her, tun da tazo gidansa yake iya kokarinsa na ganin ya saka murmushi a fuskarta a kullum, kuma duk tana lura da dukkannin efforts dinsa, sai ta sunkuya tayi masa kiss a gefen kumatunsa tanajin sonsa na qara hauhawa acikin zuciyarta.
Washegari ya kasance Friday suna kwance a gado da safe bayan sunyi sallahn asuba tace masa tanason suje gida ta kaiwa su Abba takardun su gani, sai yace "Da Ina tunanin gobe Saturday sai muje, Inason in kaiki kiga gurin ne yau kinji" ta amsa da "Toh" sai yace "Inason muyi magana Na'eemah" nan ta maida dukkan hankalinta garesa tace "Meye faru?" gani tayi ya kamo hannunta, cikin kwantar da murya yace "Babe Inason ki fadamin duk abunda kikeso, I mean anything indai baifi karfi na ba zan miki" sai ta cigaba da kallonsa cikin neman qarin bayani, sai ya miqe zaune ya jingina da fuskar gadon, yace "Name anything Na'eemah, burina ki ajiye aikin bankin nan please" bai bar kallonta ba yasake kwantar da murya "We could plan something else kinji, I understand that you want to work and that's a good thing, amma banda banki Na'eemah, in kinaso ma sai in fara planning gina miki naki boutique din irin na Nafisa, kinga Fatima shi take running itama daga guda daya ta fara yanzu Ina tunanin tana da guda uku da take running here in Abuja" "And again Salma da Husna co-own a big Hotel together, kuma basu suke running da kansu ba, we could do that if you want, ba lallai sai da kanki zakiyi running business dinki ba, kinga filling station dinki, in kinga dama kije supervising sau daya a wata ma daidai ne" sai lokacin Na'ima tayi murmushi tace "Bari in kawo maka ruwa kasha, yau sai dogon magana kake" sai yayi dariya kadan yace "I'm nervous ne Babe, I want to convince you so badly" nan ma murmushin tayi tace "Then I'm convinced Baby" da mamaki yace "Dagaske kin yarda" sai ta gyada kai, yace "Kin tabbatar banyi forcing dinki ba" nan kuma ta fashe da dariya shima yana tayata, sai da tayi me isarta tace "Ko daya..amma zanyi shawaran dasu Abba tukunna sai inji mene zasuce akai" Ahmad yace "Thanks Babe" sai ta miqe zaune itama ta dan kwanta a jikinsa tace "Nice da godiya sosai, ko baka nemamun wani business din ba zan ajiye aikin indai haka kakeso" yace "Zakiyi business din ma kinji" ya qarasa maganan yana wrapping hannunsa a bayanta ta sake kwantowa jikinsa...
Da yammacin ranan bayan la'asar ya dauketa suka tafi ganin sabon gidan man da ya kasance nesa dasu, dan sai da suka fara daukan hanyar barin garin Abuja sannan suka isa, tunda suka isa take bin ko'ina da kallo da mamakin ganin girman gurin, bata taba tsammanin girman gidan mai din zai kai har haka ba, wani abun mamakin kuma sai ta samu har ma'aikata Ahmad ya diba already, kowannensu na kokarin gaisheta dan tayi noticing dinsa, a office din managern sukayi masauki itada Ahmad din aka kawo musu refreshment, nan ya hau briefing dinta a ladabce tana sauraran komai gameda yanda za'a tafiyar mata da ma'aikatar nata, basu suka bar wajen ba sai yamma lis suka dauki hanyar komawa gari, a hanyarsu na tafiyan Ahmad ya tsaya a wani babban eatery ya musu takeout suka qarasa gidan, isarsu gidan aka kira sallahn maghrib sai Ahmad yayi saurin ajiye ledojin hannun nasa a nan falon qasan yace mata "Bari naje sallah Babe" tana kokarin cire gyalenta ta amsa masa da "Toh, sai ka dawo" da haka ya shige extra toilet din cikin falon yayi alwala sannan ya fice, itama miqewa tayi ta tattare kayan ta nufi kitchen ta killacesu sai ta fito ta fara neman Simba jin shiru bai fito ba tun shigowarsu, cikin seconds biyar ta hangosa da gudunsa yana sauqowa daga stairs sai tayi murmushi ta juya ta koma kitchen din yana biye da ita a baya, saida ta zuba masa abinci sannan ta fito ta wuce part dinta domin tayi sallah, bayan ta idar sai tayi deciding tayi wanka kafin Ahmad ya dawo daga massallacin, shiganta toilet din sai ta debi towels dinta na hanger ta saka su cikin washing machine domin sake wankesu, da haka ta bude glass din gurin shower section na toilet din ta shige cikin cubicle din tareda kunna ruwan showern yana zuba akanta, tana cikin wanke gashin nata taji kamar alamun mutum a toilet din sai ta juya da sauri tuna bata rufe kofan ba, aikuwa nan ta gansa tsaye yana kallonta tun daga sama har qasa, a yanda yake kallonta dinne yasa tayi saurin juyawa zata jawo towel sai taga wayam babu ko daya a hanger, da sauri ta juya masa baya tana rufe fuskanta da tafin hannunta tace "Oh God..Ahmad wanka nake fa" ta qarasa maganan tana dana sanin rashin rufe glass din da bata yi ba gashi har sannan tanajin sauqan ruwan showern a kanta amma ta kasa kashewa.
Ga wa'inda basuyi following account dina ba, Ina qara muku tuni please.
Bintu Musa✍️😍