Chapter 1
Chapter One 1️⃣
Kwance take akan makeken queen size bed din ta tana bacci cikin kwanciyar hankali,qarar wayar ta ne ya tashe ta daga baccin da take yi hannu ta saka ta janyo wayar saurin dagawa tayi ganin kiran daga asibiti ne,ok kawai ta ce ta miqe ta shiga bathroom wanka tayi cikin minti goma ta shirya cikin wata light blue din abaya,wayar ta da mukullin mota kawai ta dauka tayi waje,a bakin kofar dakin mom ta tsaya ta gaishe da ita ta amsa cikin Farin cikin ganin tilon yar tata JAY ina zuwa haka naga kina sauri na san dai Yau Sunday bakya fita aiki,Wlh mom yanxu aka kira ni wai emergency aka samu kuma Dr.sadiq yana Qatar,haka ne toh sai kin dawo,da sauri ta qarasa gurin motar ta yi mata key horn tayi ma mai gadi ya bude mata yana mata a dawo lpia cikin qwarewa take tukin har ta qarasa cikin asibitin emergency ta wuce direct ma'aikatan suna ta gaishe da ita har ta qarasa cikin emergency din gabanta taji ya fadi lokaci guda a hankali ta aro jarumta saboda bata son duk wani abu da xai tuna mata abinda ya faru a baya ta qarasa ciki duba tayi bayan ta ga halin da take ciki allura ta sa aka dakko mata tayi mata bayan kamar minti goma sha biyar ta gama yi mata allura saboda ba'a yin allurar lokaci daya saboda hatsarin ta ba ma kowa yake yi ba sai wanda ya iya bayan na gama yi mata alluran nace su kaita dakin hutu office na wuce mom na kira na ce mata ta bada breakfast a kawo man amma wanda mara Lpia xai iya ci,bayan minti ashirin aka kawo man daukan basket din dauka nayi na fita xuwa dakin aka canja mata sunan ta na tambaya tace man AYAANAH,tea na hada mata bayan ta sha na zuba mata soyayyen dankali da pepper soup shima ta ci sosai sannan na bata magani ta sha ina ke maki ciwo yanxu qafa ta tana ciwo sannu shima xuwa anjima zai daina kinji tohm amma zaki tafi dani gidan ku ai daddyn ki bazai bani ke ba kawai ki tafi dani daddy kullum baya xama a gida kuma aunty sai tayi saurin rufe bakin ta tayi shiru a hankali aka turo qofar dakin aka shigo har ya qaraso gurin gadon dr.sannu yawwa hajia qarama sannu ko yawwa baba tanimu daddy na bai dawo ba ko eh baba muje office dina muyi magana ko Toh likita office muka je bayan na xauna na nuna mashi gurin xama baba tambaya xan yi maka don Allah ka fada man gaskiya in shaa Allah likita don Allah ko kasan dalilin ayaanah na rashin son komawa gidan su likita ai dole hajia qarama taqi son komawa gidan su saboda abubuwan da ake yi mata a gidan mahaifin yana tsananin son ta amma kash mutum ne shi da baya zama saboda yana yin aikin shi sai kuma Allah ya hada shi da mata azzaluma kullum tana cikin dukan hajia qarama da saka ta aikin da ya fi qarfin shekarunta a wannan shekarun nata da baxa ta wuce shekera biyar xuwa shidda ba har wanki matar nan tana saka ta kuma akwai yan aiki gidan abubuwa babu dadin ji,ajiyar zuciya na yi sannan nace baba lokacin da xaka kawo ta asibiti da wanda yaga fitowar ka gaskiya a'a saboda me gadi ma ya xagaya lokacin da na saka ta mota yawwa Alhamdulillah yanxu ina son tafiya da ita gidan mu har xuwa lokacin dawowar babanta Wlh likita da kin taimaki marainiya Wlh yanxu Toh ka bani number wayan ka saboda Idan ya dawo ka sanar da ni Tohm shikenan sallama suka yi ya tafi ita kuma ta wuce xuwa dakin da ayaanah ke kwanace basket din abinci ta dauka sannan ta ce mata ta sakko su tafi dariya tayi har ana ganin haqorinta hannu ta na kama na riqe muka fita har xuwa bakin mota ta front seat na bude mata ta shiga na bude back seat na aje basket din breakfast sannan na koma driver seat na tada motar muka wuce gida a hanya na tsaya na siya mata fruit kafin na qarasa gida horn nayi aka bude man get na shiga cikin gidan parking nayi sannan na fito na zagaya side din ayaanah na bude mata muka shiga cikin gidan babu kowa a babban parlour har muka shiga qaramin parlour shima babu kowa direct dakin mom naje na tarar tana toilet miqewa tayi kawai ta wuce dakin ta wanka ta qara yi sannan ta yi ma ayaanah ma towel din ta ta daura mata suka fito ta shirya ta wani wandon ta three quarter ta saka mata da T shirt din ta amma duk da haka sunyi mata yawa kiran sallah ake tayi a lokacin sai kawai ta koma toilet tayi al'wala ta saka ayaanah ma tayi suka yi sallah sai a lokacin ta tuna ita ai ko breakfast bata yi ba miqewa tayi tare da kama hannun ayaanah suka fito adaidai lokacin kuma mom take fitowa daga dakin ta,bata lura da ayaanah ba Tace ma Jay ashe kin dawo na dawo mom kina toilet kuma banji shigowar motar ki ba tana juyowa idon ta ya shiga cikin na ayaanah da take ta murmushi wani irin bugu xuciyar ta tayi luuuuuuu ta fadi qasa sumammiya............