Chapter 2
by @reza12
*YAN MATA*
*🥏Whasop Channel*
***
*Chapter 2️⃣*
Bayan sun gama cin abinci ne kowacce ta kama hanyar gidansu akan gobe da safe ne tafiyar. Koda Siyama ta shiga gida bata ga kowa a palo ba, hakan yasa ta kashe kayan kallon ta leƙa daƙin Mama ta ce "Na dawo" ta na faɗa ta wuce ɗakin su. A wannan daren dai barci rabi da rabi tayi, tana ta faman saƙe-saƙe. Misalin ƙarfe takwas bayan sun gama cin abinci, kasancewar yau asabar ne yasa Saddiƙa take gida babu school. Nana ta kalli Mama ta ce "Mama ƙarfe goma ne za'a tafi, gashi ma har motar tazo fa?" Mama ta kalleta tana godewa Allah da irin halin Siyama na naci idan tana son abu, ko maiyya iya kacin abun da zatayi kenan. Ta ce "Siyama ba zaki je ba" Siyama ta durƙushe a gurin ta kama ƙafafuwan Mama ta fara magiya. Saddiƙa ta ce "To Mama dan Allah kiyi hakuri ki barta tunda ai ba ita kadai ɓace kuma duk ƙawayenta ne zasu je fa". Mama ta ce "Ko kukan jini zatayi yau sai dai tayi, yarinyar da ko nan da unguwa uku bata taɓa zuwa ita kaɗai ba, sannan wannan yaran da suke da rawar kai sune za'a ce zasu raka amarya har wata duniya, ai gara a haɗa ta da masu hankali amma ba su ba". Da sauri ta ce "Wallahi Mama ba mu kaɗai bane harda yayanta gudu biyu, ga ƙanwar mamarta harda kuma wasu manya da zasu yi mata jere, mufa kawai zamu je ne a matsayin ƙawaye da zasu ɗebe mata kewa, kuma Allah angon ya ɗauki nauyin zuwa da dawowarmu kuma kwana ɗaya ne kawai zamuyi, haba Umma haba Umma ki tausaya min ki rufa min asiri dan Allah, dan yarasulullahi!. Nana ta faɗa ko haɗiyar yawu bata yi. Umma ta ce "Irin wannan shegen surutun naki da manyance su nake tsoro, ji yadda kike jero zance babu ko jan numfashi, a haka zan barki kije garin wasu har ki kwana ba tare dani ba?" "Na rantse miki da Allah bama zan dinga surutu ba, ni Umma idan muka je ma a ɗaki zan zauna har mu dawo na miki alƙawari". "Ke ɗin ko? Keda wannan ƙawayen naki ne zaku haɗu a guri kuyi shiru ko?" "Wallahi zamuyi Umma na miki alƙawari" "Ni dai har zuciyata bana jin wannan tafiyar da ke, kuma jikina na bani cewar tafiyar babu alkairi a cikinta sam wallahi" "In sha Allahu a kwai alkairi, kawai ki mamu fatan dawowa lafiya Umma". Umma tayi shiru. Siyama ta tashi da gudu ta rungume ta tana fadin "Na gode mamata, uwata wacce ta fi ta kowa, uwata abar alfahari na, uwata zinariya, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana, Allah ya bani miji mai kuɗin da zai ɗaukeki ya kaiki asibitin ƙasar waje a gyara miki wannan ƙafar taki da take hana ki sakewa". Umma ta murmusa tana jin har lokacin hankalinta bai kwanta da tafiyar ba. Ai nan take aka fara shiri na gasken-gaske. Mama ta ce "Kinga kira min su sauran ƙawayen naku baki ɗaya?" Ai kuwa nan take sai ga Abida Haura. Nan Mama ta haɗa su dukkan ta musu faɗa akan dan Allah banda rawar kai, kuma babu ruwansu da kula samari, abun da ya kaisu kawai zasuyi, kuma daga kwana ɗaya kar su ƙara.
Nan dai suka tafi akan zasu kiyaye komai. Misalin ƙarfe goma daidai Siyama ta shirya cikin shigar doguwar rigar da gaba dayansu zasu saka. Sosai ta ci uban kwalliya kamar itace amaryar, ga wata siririyar sarƙar wuya mai hoton zagi ya buɗe baki, ga agogo a hannu harda zobuna, bakin nan ya sha blue ɗin janbaki, fuskar nan fayau babu wata kwalliya mai hayaniya. Sai wata ƙaramar jaka a hannu wacce babu ko mai a ciki sai wayar ta mai maɓallai. Ta kalli Saddiƙa ta ce "Ɗauko min jakata" Saddiƙa ta tashi da sauri ta ɗauko jakar. Umma ta ce "Yanzu meye amfanin wannan kwalliyar ku da zaku shiga Mota?" tayi dariya mai sauti muryarta cike fall da kwantatcen farinci. ta ce "Mamata kenan, yanzu muna matsayin ƙawayen amarya idan bamu banbanta kanmu ba ta yaya za'a gane mu ɗin ne, kuma wannan ai ba wata kwalliya ba ce ban fa shafa komai ba". Ta faɗa tana nuna mata fuskarta harda dan juyawa. Umma ta ce "To Allah ya kiyaye hanya a dawo daku lafiya, kuma ban yarda ki ƙara ko kwana ɗaya ba, gobe-gobe ki juyo na faɗa miki" ta ce "Ai dama gobe zamu dawo Mamata". Umma ta zaro dubu biyar a fosa ta miƙa mata, ta ce "Ga wannan sai ki ajiye a gurinki, idan kika ga wani abu da kike so sai ki saya?" Siyama ta ce "Tom mama bari dai na ɗauki dubu biyu kawai domin babu abun ma da zamu saya, idan ma ta kama ai ga angon nan shi zai saya mana duk abinda muke so" Umma ta ce "Dalla karɓa na ce, da yake shi angon kun ajiye masa ne da zai baku duk abun da kuke so ko?" Siyama da take jin su da zasu je neman kuɗi ina zata wani buƙaci kudi, domin sosai suka ƙwallafa rai a kuɗin sayan bakin nan. Haka dai sai dubu biyun ta ƙarba ta tura ta a cikin jakan ta kama hanya. Har tazo ƙofar gida sai ga Yaya Salim ya dawo, kallonta yayi ya ce "Ƴan matan Mama sai ina haka irin wannan kwalliyar?" Ta ɗan yi farr da ido ta matso kusa da shi ta ce "Daga nan sai Kaduna yaya, zamu je raka Amera ɗakin miji!" Salim ya ce "Okay haka ne fa, ashe yau ne ko? Kuma Umma ta barki?" Ta ce "Sarai ma kuwa, ai kuka da magiya na dinga mata, tun jiya nake abu ɗaya har Allah yasa ta barni. Ya ce "To Allah ya kiyaye hanya, ya sa hannu a aljihu ya ɗauko dubu biyu ya mika mata. Ta ce "Yaya na gode amma ka ajiye min na bika bashi idan na dawo zan amsa" ya ce "Keda zakiyi tafiya ai ya dace ki riƙe kuɗi?" Ta ce "Yaya bafa motar haya ce zamu hau ba, zuwa da dawowa duk Ƙasim ya biya mana, kuma komai da zamu buƙata ai ya ce zai yi mana idan munje. Salim ya ce "Inji shi angon ko?" Ta ce "Eh amaryar ce ma ta faɗa mana" Salim ya mayar da kuɗin sa aljihu ya mata Allah ya tsare hanya.
Kujerar baya aka bar musu su huɗu. Abida ta fara shiga, sai amarya sai Siyama sai kuma haura. Tun a gurin shiga motar aka fara zage-zage, wannan na cewa ita ce zata je wannan na cewa ita ce zata je. Shi kansa dreban sai da abun ya bashi haushi. Ya ce "Idan fa ba'a zauna an natsu ba zan ja motata na barku anan?" Jin haka yasa aka ɗan natsu suka fara shiga a hankali. Sai dai duk da hakan wasu basu samu guri ba, motar kaya kuwa tun safe suka tafi yanzu ma sun isa Kaduna da ƴan jere. Ana tafiya ana hira, abokan tsokaanan amarya na yi, ƙawayenta na tare mata, sosai a kayi doguwar tafiya kafin suka iso cikin garin Kaduna. Ganin direba ya ɗauki hanyar da ba ita zasuyi ba wata daga cikin dangin angon ta ce "Kai direba ina zaka kaimu ne, ga hanyar da zaka bi damu nan fa?" Dreban ya ce "Amma ni angon ba wannan unguwar ya ce zan kawo ku ba, cewa yayi na kaiku NDC. Matar ta ce "To gidan iyayensa za'a fara Kaita, zuwa gobe sai a Kaita cen gidan nasa, ko ka taba ganin inda aka ɗauki amarya aka kaita gidan miji ba tare da an fara Kaita gurin iyayensa ba?" Jin haka yasa gaba ɗaya aka goyi bayan matar, ita dai amarya bata ce komai ba, ƙawayen amarya ma dai wannan fadan ba nasu bane. Dole direba ya faka ya shiga kiran number ango, bayan ya ɗaga ya faɗa masa halin da ake ciki. Ango ya ce "Kar ya sake ya sauke masa amarya anan gidan, kawai ya kawo ta inda ya faɗa masa idan ba haka ba zai bata masa rai. Bayan direba ya gama wayar ya faɗa musu abun da Angon yace masa. Amma sukayi cha a kansa kamar zasu cinye shi, kuma ya ce shi ba zai sauƙe a marya a ko ina ba sai gidan mijinta kamar yadda aka bashi umarni. Kafin kace me kowa ya fito daga cikin motar an fara zage-zage akan wani irin rashin ta ido ne yace ba za'a fara kaita gidan iyayensa ba. Wacce ta fara cewa a tsaya ɗin ta ce "Tsabar rashin kunya irin ta mazan yanzu, a kawo amaryar amma yace a wuce masa da ita saboda shi ɗan iska ne ba shi da Kunyar idanun mutane. Wata ta ce "To wai ke ina ruwan ki ina ce dai matarsa ce an riga da an ɗaura to meye a ciki?" Ta ce "To wallahi ba za'a kai masa ita yau ba duk jarabarsa sai ya jira anbi dokar al'ada. Wata ta ce "To a matsayin ki ta wa? Sai wani zaƙewa kikeyi kamar wata uwarsa" Ta ce "Matsayin yayarsa uba daya" Ta faɗa da fariya. Suka ja tsaki ɗaya ta ce "Ashe dai ƴar uba ce iyayen munafunci". Ta ce "Koma ƴar ƙani ce dai sai an fara kai ta gida wallahi kuma dole abi abun da nace". Haka dole aka kai amarya gidan iyayen ango saboda matar ta nuna cewar haka ake yi. Dreban ya juye su a ƙofar gidan ya kama hanyar sa bai ko tsaya bi ta kansu, tunda dai ya kawo su ai ya gama, kuma an biya sa kuɗin sa. Da guɗarsu suka shiga cikin gidan, amma sai me? gida babu kowa sai wata budurwa ita ɗaya. Yadda suka bita da kallo haka itama take binsu da kallon ƙarin bayani. Wannan yayar angon take tambayar ta ina masu gidan? Yarinyar tace ai itama matar gidan yau ta tafi Kano gidan bikin. Yayar ango mai suna Anty Walida ta ce "Amma ai tace ba zata je bikinba to mai yasa ta tafi?" Ganin an fara maganganu ne yasa ta musu iso izuwa ɗakuna ukun dake gidan. Amarya ɗaya ita da ƙawayenta, sai ɗaya na baƙi daya kuma ita da ƙanwar tasu da suka iso suka tarar da ita. Shiru-shiru har kusan magriba babu masu gidan gashi an kira ango tunda yaji cewar ga inda suke ya kashe wayarsa, sannan babu wanda yasan gidan nasa. Anty Walida ta kira number Mamarsu ta faɗa mata cewar suna gida fa tun ɗazu yaushe zata taso. Mamar ta ce "Gida kuma keda wa?" Ta ce "Amaryar Ƙasim ce fa aka kawo shine nace sai an fara kawo ta gida kafin a kai masa ita. Mamar ta ja dogon salati ta dire ta ce "Ke dai Walida anya wawiyyar yarinya, ina ruwanki, ko binkin ma kinji ya gaiyace mu, to ni yanzu haka ma ina Jigawa gidan biki, dan haka ki ɗauki amaryarsa ki kai masa kin dai san halin sa ba mutunci ne da shi ba. Idan ma bada hauka irin naki ni ina ruwana da sauran sa, ina ce dama na faɗa miki cewar ko bikin ba zan je ba, ai muda su har abada wanda ya haɗa ya taba". Anty Walida ta ce "To ai ban san gidan nasa ba ne bafa Mama". Mama ta ce "To sai kuwa ki ba zama nemo, ni dai yanzu sai anjima". Anty Walida taji wani lukutar tashin hankali na shigar ta. Gefe ɗaya kuma ga masu rakiya sun fara magana akan wai ina yan gidan ne. Wasa-wasa har a kayi magriba. Haka dole fa ta faɗa musu cewar ai masu gidan sunce kawai a kaita basa nan. Nan fa wani sabon tashin hankali ya fara domin kuwa kaf babu wanda ya san gidan nasa. Karshe dai dole number sa aka shiga kira amma bata shiga. Anty Walida ta kira ya kai sau goma, haka itama amarya. Hatta numbobin abokansa guda biyu suma basa shiga. Har bayan Isha ba'a samu wata number guda ɗaya da za'a samu ba. Izuwa lokacin hankali kowa ya tashi. Amarya kuwa har ta fara kuka. Ana haka aka samu number ɗaya daga cikin wanda suka yi jerin, saidai ta ce ai suna gama jere angon ya rufe gidan sa yace kowa ya tafi. Anty Walida ta ce To ta faɗa musu unguwar da gidan yake. Ta ce ita bata sani ba. Har karfe goma, gashi babu abun da suka ci, masifa kuwa har baka iya gane abun da ake cewa. Su kuwa ƙawayen amarya angon suke tsinewa akan mai zai sa ya kashe waya. Har karfe sha biyu kafin su kayi sa'a aka samu number wacce tayi musu kwatancen. Gashi kuma babu motar da zata kwashe su, dole sai keke Napep aka samu guda huɗu a kayi ciniki, suka ce sai anje za'a amsa a gurin ango. An sha bilayi kafin aka gano gidan wanda sai da mai keke Napep ɗin ya amshi wayar ya gane kwatancen. Sai dai kuma me, ƙofar gidan a garƙame da wani ƙaton kwaɗo. Har sun fara gardama akan ba gidan bane wata mata da tazo wucewa ta tabbatar musu da gidan ne. Masu keke Napep suka naimi da a basu kuɗin su amma suka ce sai fa ango yazo. Nan suka fara musu barazana, ai kuwa take aka haɗa kuɗin a gurin aka basu suka tafi. Har karfe ɗaya babu ango babu dalilinsa, kuma number sa ta ƙi shiga. Aikuwa faɗa ya kaure da Anty Walida da wata akan ai duk ita ce ta ja musu. Amarya kuwa tuni ta ɗora da kuka yayin da ƙawayen ta suka ƙullaci Angon...