ALIYU HAYDAR

Chapter 2

by @nieemartullah

Chapter two 2️⃣


A dan kishingide yake akan sofa din dake cikin office din shi kamar kullum Yau ma tunanin ta yake yi yana hango wannan kyawawan idanun nata da kuma murmushin ta mai mantar da shi dukkan wata damuwa da yake ciki kafadar shi da aka dafa ce ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya xamar mashi tamkar karatu,buddy wai tunanin me kake yi haka kullum kana cikin tunani amma Idan an tambaye ka kace babu komai ko kallon inda me maganar yake bai yi ba sai ma tashi da yayi ya dauki wayar shi da mukullin mota yayi gaba Idan da sabo zannur ya saba da halin abokin nasa bayan shi kawai ya bi suka fita tare,mota suka shiga babu wanda ya qara magana har suka dau hanyar komawa gida kaga bawan Allah gida na xaka kaini gurin iyali na tunda kai abinda ka xaba kenen parking yayi yace mallam fitar min daga mota kawai ka cika man kunne da surutu dariya sosai zannur yayi tuba nace angon safiyyah banza yayi da shi ya cigaba da driving har suka xo gidan shi da ke Victoria island dake garin Lagos unguwa ce ta manyan masu kudi da kuma qusoshin qasar,horn yayi a qofar wani tamfatsetsen gida daya gaji da haduwa duk irin yadda xan kwatanta maku ya shige haka,mai gadi ne ya bude masa gate ya shiga cikin gidan ashe bamu ga komai ba kallo yana ciki parking yayi ya bude mota ya fito hanyar da xata kai shi cikin gidan ya nufa qofar parlour ya bude Masha Allah wani hadadden parlour na gani tun daga kan curtains zuwa kujerun da ke parlour abin kallo ne fararen qafar sa ya dora akan Italian carpet din dake cikin parlour hanyar bedroom din shi ya nufa direct Kayan jikin shi ya rage ya shiga bathroom domin yin wanka zannur ne ya shigo cikin parlour ya zauna kan daya daga cikin kujerun dake parlour saboda yasan yana shiga cikin bedroom din xasu qara yin fada shiyasa ma ya zauna bai shiga ba saboda a yanxu baida lokacin qara yin wani hayaniya......

A hankali take bude idanun ta da suka yi mata nauyi ganin ta ne ya sauka akan jaiyana dake zaune gefen ta sannu mom kin tashi meke maki ciwo yanxu babu abinda ke man ciwo mom Toh me ya same ki haka kika suma babu komai jay kawai na gaji ne sosai shiyasa Toh shikenan ina son muyi magana amma sai kin samu Lpia sai muyi magana yanxu ki shiga kiyi wanka saboda ki samu qarfin jikin ki Tohm gudaliya sai yanxu na samu qwarin gwiwar yin breakfast kitchen na shiga ruwan zafi na dora a kettle sai kuma na dakko flour na fara hada pancakes ina gamawa na dauko plate na qara wankewa sannan na zuba komai na dakko na dawo dining area na zauna ina breakfast ayaanah ce ta fito daga daki riqe da waya ta da ake kira karba nayi sadiq ne ke kirana video call dagawa nayi sannan na xuba ma ayaanah pancakes ita ma ta fara ci,ta cikin wayar ne  sadiq yace hello pretty,sadiq ya kake bana Lpia Subhanallah me ya same ka sadiq nayi kewar ki ne sosai ni na dauka ma Baka da Lpia ne ya qatar din fatan komai yana tafiya yadda ya dace eh Alhamdulillah na ma kusa gama abinda ya kawo ni in shaaa Allah xuwa next week xan dawo Toh shikenan Allah ya kaimu badai sai yanxu kike breakfast ba Wlh sai yanxu nake yi haba jay Yau fa babu aiki me kike yi har yanxu baki yi breakfast ba na samu kiran gaggawa daga hospital sai yanxu nake dawowa eyyah that's why you looks dull sannu yawwa Wlh duk na gaji we will talk later bye ok take care of yourself dear sadiq loves you always and forever ending call din tayi ta qarasa yin breakfast din ayaanah ta kai dakin ta sannan ta wuce,dakin mom ta koma saboda su yi magana kaman yadda ta fada mata daxu sallama tayi sai da aka amsa sannan ta shiga cikin dakin xama tayi kusa da mom bayani ta fara yi ma mom akan ayaanah da kuma neman alfarmar riqe ayaanah xuwa wani dan lokaci haba jay da ai na kowa ne babu komai don kin riqe ta anan ai yawwa uwa ta gari thank you so much I love you side hug ta yi mata sannan ta koma dakin ta....

HAYDAR ne ya fito daga cikin bedroom din shi bayan ya  gama shiryawa zannur ya tarar a parlour yana kallo,buddy xaka sha coffee na hada maka eh wlh da ka kyauta kitchen ya shiga ya hada masu coffee ya fito da shi zannur ya miqawa na shi sannan ya xauna shima yana Shan nasa a hankali ya fara magana kaman wanda aka yi ma dole buddy yau ina ta kiran princess bata dagawa kuma bata Saba yi man haka ba hankali na yaqi kwanciya ina tunanin xan koma abuja naga ko Lpia eh gaskiya ya kamata ka koma kaga ko Lpia in shaaa Allah xuwa gobe nake tunanin tafiya tohm shikenan jirgin qarfe nawa xaka bi xuwa qarfe tara xan tafi Allah ya kaimu xanxo sai nayi dropping dinka a airport.....


Qawas ya ake ciki ne na ganki haka kedai bari ina cikin matsala Wlh Toh matsala tame kuma qawas ina wannan alhajin da nake baki labari wani abu yayi ne babba ma kuwa yanxu kwata kwata baya daga waya na kuma baya Idan na kira baya dauka Tabbbb dole kice kina cikin matsala sai da na fada maki wannan malamin ba wani aiki ya iya ba kixo na hada ki da nawa malamin aiki shi kamar yankan wuqa gaskiya ina Jin abinda xa'a yi kenan tashi yanxu ma ni mu tafi ke matsala ta da ke rashin haquri ki bari zuwa gobe da safe sai muje saboda gurin akwai nisa tohm shikenan gobe da asuba xan xo sai mu tafi tohm sai kin xo.....


Hira muke yi mai dadi cike da soyayya da kuma qauna labari muke yi mai cike da raha da kuma Farin ciki kirana akayi ana buqatar gani na a office yanxu sai kawai ta dauke man waya na wai baxan fita ba tashi nayi da niyyar na karbi waya na sai kawai na fado qasa auchhh na danyi qara saboda buguwar da nayi,ina son na manta da ita amma kullum cikin mafarkinta nake....................