Na Shiga Ban Dauka Ba

page 9&10

by @hammaabdul

🙆‍♂️🙆‍♂️ *NA SHIGA BAN ƊAUKA BA* 🙆‍♂️🙆‍♂️
               _(Bata fidda barawo)_ 








 *Writing By Hamma Abdul (Dan Salma)* 





 *MARUBUCIN.....🖊️
 _YAREEMA_ 
 _INUWAR KAKA_ 
 _BIYU BABU_ 
 _AZUMIN LADO_ 
   




📚JARUMAI WRITTERS ASSOCIATION TAKEN MU ALKALAMI YAFI TAKOBI📚





_____________9&10



Ranar Litinin: Babban Kotun Tarayya

Gari ya waye da wani irin yanayi na cunkoso da hayaniya a harabar Babban Kotun Tarayya. 'Ćłan jarida daga gidajen talabijin da jaridu daban-daban sun cika wurin da kyamarorinsu, kowa yana son ya É—auki hoton matashin da ake zargi da sace Naira Biliyan Biyu da Miliyan ĆŠari Biyar na kuÉ—aÉ—en gwamnati. Wannan ita ce shari'ar da ta fi É—aukar hankalin jama'a a wannan shekarar, domin kuÉ—aÉ—en da suka bace na aikin gina asibitoci ne a yankunan karkara.

Wata katuwar motar jami'an tsaro (Black Maria) ta iso harabar kotun tana wani irin kukan jiniya. Da zarar ta tsaya, jami'an tsaro masu É—auke da bindigogi suka fito, suka bude kofar baya.

Kamal ya fito daga cikin motar. Yana sanye da kayan gidan yari masu launin ruwan kasa, hannayensa da kafafunsa a ɗaure da sarƙoƙi masu nauyi waɗanda suke bayar da sauti Kyal-kyal a duk lokacin da ya taka kasa. Fuskarsa ta rame sosai a cikin kwanaki biyu kacal da ya yi a tsare, idanuwansa sun faɗa ciki, sannan gashin kansa ya fara hargitsewa.

'Yan jarida suka fara haska masa kyamarori suna yi masa tambayoyi a lokaci guda:
"Kamal, ina ka boye kuÉ—aÉ—en?"
"Shin da gaske ne ka yi wa budurwarka barazana da wuka?"
"Me za ka ce ga talakawan da ka sace kuÉ—aÉ—en asibitocinsu?"

Kamal bai amsa ko É—aya ba. Ya sunkuyar da kansa kasa, hawaye yana taruwa a idonsa. Ya ji wani irin tsananin wulakanci wanda ya fi kowane irin duka ciwo. An mayar da shi abin kyama a idon duniya, alhali shi ne wanda aka zalunta. Jami'an tsaro suka tura shi cikin kotun da karfin tsiya.

A cikin kotun, É—akin ya cika makil da mutane. A gaban kotun, a bangaren masu kara, akwai wasu manyan lauyoyi guda uku masu sanye da bakaken kaya da fararen hula (wigs), waÉ—anda Sanata Buba Gwamna ya É—auki nauyinsu don su tabbatar da cewa Kamal bai tsira ba. A bangaren wanda ake kara kuwa... babu kowa. Kamal ba shi da lauya. Ba shi da kuÉ—in da zai É—auki lauya, sannan babu wani lauyan gwamnati da ya yarda ya tsaya masa saboda girman laifin da ake zarginsa da shi da kuma tsoron karfin Sanata Buba.

Alkalin kotun, Mai Shari'a Mahmud, wani tsoho ne mai tsananin kwarjini da kuma fuskar da ba ta nuna alamar wasa, ya shigo É—akin. Kowa ya mike tsaye har sai da ya zauna.

"A kawo wanda ake kara gaba," Alkali Mahmud ya bayar da umarni.

An tura Kamal zuwa cikin akwatin wanda ake zargi (Dock). Ya tsaya yana karkarwa, ya kalli É—akin kotun yana neman ko zai ga wata fuska ta sani wacce za ta nuna masa tausayi. Idonsa ya sauka a kan layin baya... inda ya ga Nafisa a zaune! Tana sanye da wani tsadadden leshi, fuskarta a rufe da wani babban tabarau na rana (sunglasses), tana zaune kusa da wani hadimin Sanata Buba.

Zuciyar Kamal ta yi wani irin bugu. Macen da ya so da dukkanin ransa, wacce ya yi mafarkin gina rayuwa da ita, tana zaune a kotu don ta bayar da shaidar karya a kansa!

"Kamaluddeen Abubakar," Babban Lauyan masu kara ya tashi tsaye, ya fara karanta tuhume-tuhumen da ake yi masa. "Ana tuhumarka da laifuka guda uku masu girman gaske. Na farko, karkatar da kuÉ—aÉ—en gwamnati har Naira Biliyan 2.5 zuwa asusunka na kashin kanka. Na biyu, yunkurin sace takardun shaidar kamfani a ofishin Sanata Buba Gwamna. Na uku, yin barazana da makami ga rayuwar Malama Nafisa domin karbar makullin ofishi. Shin ka amsa laifinka ko baka amsa ba?"

Kamal ya rike karfen akwatin da karfi, ya É—aga muryarsa wacce take rawa saboda kuka. "Ban amsa ba! Ya Mai Shari'a, wallahi ban saci kowane kuÉ—i ba! Sanata Buba ne ya sa ni in sa hannu a kan takardun asusun ba tare da na san kuÉ—aÉ—en gwamnati ba ne! Kuma Nafisa ita ce ta ba ni makullin ofishin da hannunta ba tare da na yi mata wata barazana ba! Tarko suka kulla min!"

Lauyan masu kara ya saki wata 'yar dariya ta isganci, ya kalli Alkali. "Ya Mai Shari'a, wanda ake kara yana kokarin ɓata sunan wani babban ɗan kasa mai mutunci ne don ya rufe laifinsa. Muna da shaidu guda biyu waɗanda za su tabbatar da wannan laifin a yau ɗinnan."

"A kira shaidu," Alkali Mahmud ya faÉ—a.

Shaida na farko da aka kira shi ne Manajan Bankin da aka buÉ—e asusun kuÉ—aÉ—en. Ya shiga akwatin shaidu, ya rantse da Alkur'ani, sannan ya fara bayani.

"Ya Mai Shari'a," Manajan bankin ya faÉ—a. "Wannan matashin, Kamaluddeen, shi ne ya zo bankinmu da kansa ya buÉ—e asusu guda uku. Ya kawo hotunansa, katin shaidarsa, sannan ya sa hannu a gabanmu. Dukkanin kuÉ—aÉ—en da suka shiga asusun, shi ne yake bayar da umarnin a fitar da su zuwa wasu asusun na kasashen waje. Muna da dukkanin takardun da ke É—auke da sa hannunsa a matsayin shaida."

An mika takardun ga Alkali. Alkali ya duba su, ya kalli Kamal. "Wannan sa hannunka ne Kamaluddeen?"

Kamal ya zubar da hawaye. "Eh sa hannuna ne... amma Sanata ne ya ce in sa..."

"Wannan ya isa," Alkali ya katse shi. "A kira shaida na biyu."

Nafisa ta tashi daga inda take zaune, ta cire tabaranta na rana, ta nufi akwatin shaidu. Tana tafiya da wani irin taku na kasaita, ba tare da ta kalli inda Kamal yake ba. Ta shiga akwatin, ta rantse.

"Malama Nafisa," Lauyan ya tambayeta. "Kina iya gaya wa kotu abin da ya faru a ranar Juma'ar da ta gabata?"

Nafisa ta yi wani irin kukan karya, ta sa kyalle ta goge idonta. "Ya Mai Shari'a... a ranar Juma'a da yamma, ina zaune a ofishina ina aiki, sai Kamal ya shigo a fusace. Ya zaro wata wuka ya sa a wuyana, ya ce idan ban ba shi makullin ofishin Sanata ba zai yanke ni. Na ba shi makullin saboda tsoron rayuwata, sannan na gudu na kira jami'an tsaro. Ban taɓa sanin cewa mutumin da muke aiki tare zai zama kasurgumin barawo ba."

"Karya kike yi Nafisa!" Kamal ya kwalla ihu daga cikin akwatinsa, ya kamo sarƙoƙin hannunsa yana girgiza su. "Meyasa kika yi min haka?! Na ba ki dukkanin soyayyata! Na amince da ke! Me ya sa kika sayar da rayuwata ga Sanata?!"

"Order! Order in court!" Alkali Mahmud ya daka tsawa, yana dukan teburinsa da gudumar katako. "Idan wanda ake kara bai yi shiru ba, zan sa a fita da shi a yanke hukunci ba tare da shi ba!"

Kamal ya zube a gwiwowinsa a cikin akwatin, ya sa kansa a tsakanin hannayensa yana wani irin matsanancin kuka wanda ya sa wasu daga cikin mutanen kotun jin tausayinsa, amma doka ba ta aiki da tausayi, tana aiki ne da shaidu. Kuma dukkanin shaidun suna nuna cewa shi ne mai laifi.

Bayan an gama sauraron shaidun, Lauyan masu kara ya nemi a yanke hukunci mafi tsauri don ya zama darasi ga sauran matasa. Kamal ba shi da lauyan da zai yi masa magana, sannan bai da wata shaida da zai kare kansa da ita.

Alkali Mahmud ya yi shiru na wasu mintuna yana rubutu a kan takardarsa. Sannan ya É—ago kansa, ya kalli Kamal wanda ke durkushe.

"Bisa ga shaidun da aka gabatar a gaban wannan kotu," Alkali ya fara karanta hukuncin, muryarsa tana amsa kuwwa a dakin. "WaÉ—anda suka haÉ—a da takardun banki masu É—auke da sa hannun wanda ake kara, da kuma shaidar gani da ido ta Malama Nafisa... wannan kotu ta gamsu cewa Kamaluddeen Abubakar yana da laifi dumu-dumu a kan dukkanin tuhume-tuhumen da ake yi masa."

Zuciyar Kamal ta tsaya cak.

"Saboda haka," Alkali ya ci gaba, "Wannan kotu ta yanke wa Kamaluddeen Abubakar hukuncin daurin shekaru ashirin (20 years) a gidan yari mai tsanani (Maximum Security Prison) ba tare da zabin biyan tara ba. Sannan za a kwace dukkanin kadarorin da ya mallaka a tsawon wannan lokacin don mayar da su ga asusun gwamnati."

Kyam! Alkali ya daki teburinsa da gudumar katako.

Wannan karar ta kasance tamkar karar rufe kofar kabarin Kamal ne. Shekaru ashirin? Zai shafe mafi kyawun lokacin kuruciyarsa a cikin gidan yari a kan laifin da bai aikata ba?

Jami'an tsaro suka kamo shi da karfin tsiya, suka fara jan sa zuwa waje. Kamal ya É—aga kansa, ya kalli Nafisa wacce ke tsaye tana murmushin cin nasara tana gaisawa da lauyoyin Sanata.

"Nafisa!" Kamal ya kwalla ihu, muryarsa tana ɗauke da wani irin zafi wanda ba zai taɓa warkewa ba. "Zan dawo! Koda bayan shekaru ashirin ne, zan dawo in nemi hakkina! Ke da Sanata Buba ba za ku taɓa samun salama ba!"

An tura shi cikin motar Black Maria, kofofin karfen suka rufe a kansa. Duhu ya lullube shi gaba daya. Wannan shi ne karshen rayuwar Kamal a matsayin matashi mai mafarki, kuma farkon rayuwarsa a matsayin fursuna mai lamba 404 a gidan yari mafi muni a kasar.

Alkalamin Hamma Abdul (Dan Salma)................🖊️