4
by @pherty001
Kallon shi tayi na ɗan wani lokaci kafin tace "wani abu yana damun ka? ya ƙanƙance idanunsa cikin ƙago murmushi yaqe yanda bazata gane damuwar sa ba, yace" damuwa kuma, am ok ", ta ja numfashi kaɗan tace", ya hanya, and ya Nigeria, am missing Nigeria insha Allah zan shigo duk ranar da ka sami matar aure, na san itama yar Nigeria ce", ta qarasa maganar cikin tsurawa kyakkyawar fuskarsa ido, nan take taga annuri dake fuskar sa ya kau, kamar bazai yi magana ba yace "bari na barki ki huta, Ina so zan fita yanzu", tace "tun da nayi ma magana akan abinda baka so ko, to shikenan na daina yi maka mgnr amma da gaske ina missing Nigeria", yace "kuma kinsan Anna baza ta barki ki zo ba, dan Allah umma me kike kewa a nigeria, ƙasar nan bata da daɗi", tayi murmushi, yana kallon fararen haqoranta da biyu su suke da ado da gold, tace "kai ma na fahimci baka son zuwa na Eshraq, idan har Nigeria bata da daɗi meyasa kullum kake hanyar zuwa? Yayi jim yana shafar sumar kansa, kafin yace" saboda friends ɗina mana", tace "meyasa baza su zo nan ba kullum kai kake zuwa", yace "muna yin business tare kin sani, and business ɗinnan anan yake, zuwan me zasu yi? Tace" shikenan, take your time Amma pls kada ka jima wannan karon baka dawo ba", ya kai bakinsa wayar dai dai goshinta ya sumabata, yace "I love you so much", murmushi tayi tana kallon sa kafin ta tsinke wayar, ya ajiye wayar tare da lumshe idanunsa a hankali cikin tunani iri iri duk akan container ɗinnan, bai taba shiga damuwa da tunani irin na wannan lokacin ba.
Washe garin ranar kusan 2pm sai gasu Rayhaan da Yusuf sun zo, sun sami ganin DCG kuma ya tabbatar masu babu mai iya karɓa kayan hannun CG kawai su hakura, kuma shi bazai iya basu kayan ba tunda CG babba ne a gurin sa, zabi biyu ne, is either yaje ya same shi ido da ido suyi magana or ya haqura da kayan. "impossible" Eshraq ya faɗa yana kallon su cikin bacin rai, "taya kuke tunani zamu iya bar masa mafarkin mu, kaya masu matuqar daraja irin wannan, billions Naira fa, bamu taba shigo da kaya masu nauyi har irin 500 billions Kuma ace mu bar kuɗin su je a banza saboda kuskuren mutum ɗaya, shi CG ɗin waye shi da baza kuje ku same shi ba? Yusuf yayi gyaran murya kaɗan yace "bafa yanda kake tunani bane Tycoon, CG Bilal yana da hatsari fiye da tunanin ka, wlhy zai iya saka a ɗaure mu da wannan babban laifi kuma kasan dauri ba qarami bane zamu bata shekaru da rayuwar mu a banza a prison k......Eshraq ya katse sa," ni zan ganshi, kuyi arranging tafiyar tamu a gobe, zan iya bashi 10% aciki idan har ya amince zai saki kayan, idan kuma yaqi I promise ko ta wacce hannya sai na ƙuntatawa rayuwarsa na ganin bani kaɗai zan yi asara ba ciki kuwa har dashi cos zai rasa aikin da yake taqama dashi", Rayhaan yace "calm down Tycoon, mu bi a sannu saboda mune muke so...." I can't do that", ya katse sa, kawai kuyi yanda nace", ya kishingida tare da lumshe idanunsa cikin ƙunar zuciya.
"Daga ina kika fito, na jima a gidan nan bakya nan, and Ina kira baki picking call ɗina ba why? Jibril yayi magana yana tsayar da idanunsa akan fuskarta wacce ke shigowa cike da gajiya, ta yatsina fuska kadan tana kallonsa, kafin ta juya tana kallon Hajiya Salima dake kallon ta, sai ta shagwabe fuska kamar zata yi kuka batare da tayi magana ba ta nufi part ɗin ta, Jibril ya tashi da sauri yabi bayan ta, gab da zata shiga bedroom ɗin ta ya riqo hannunta, ta juyo tana kallonsa cikin mamaki "are we married? ta tambayeshi ganin yanda ya bata rai yake questioning ɗin ta kamar wanda ya ajiye ta ko yake auren ta, ya girgiza kansa a hankali kamar wani soko, ta dubi hannunshi dake riqe da nata kafin ta dube shi, da sauri ya janye hannun gane nufin ta, tace "ka jirani ina zuwa" yace "for how many times will you keep me waiting, dan kin ga ina son ki, shin laifine soyayya ta gare ki da kike wahalar dani haka", tayi shiru tana kallon ƙwayar idon sa, tana jin babu daɗi a ranta ganin yanda ya marairaice mata har da kwallah a idanunsa, ta san yanda yake matuqar son ta da kaunarta, kafin tayi magana ya sake riqo hannunta karo na biyu cikin shigar rarrashi, yace "dan Allah ki gayamin me kike so daga gare ni, am ready for it, ni ko rayuwata ce wallahi zan baki Nihal, me kike so tell me? ta lumshe idanunta ta buɗe a hankali kafin tayi murmushi kaɗan tace" kana tambaya daga ina na dawo kasan bani da gurin zuwa kamar Millennium park muna tare da friends ɗina, and na san menene damuwar ka, aure ko, am ready for the marriage too, zan sanar da Dad idan ya dawo", bai san sanda ya rungume ta saboda tsabar farinciki, tayi wani murmushi tana qoqarin raba jikinta da nashi, bata ankara ba taji saukar lips ɗinsa a nata, "I love you so much, my happiest day today, yanxu xan je na sanar da Daddy too", ya juya batare da ya jira cewar ta ba ya fice da sauri saboda farin ciki, ta girgiza kanta kaɗan tana murmushi, waya ta soma yi da friends ɗin ta cewa she accepted Jibril. Da dare bayan dawowar Bilal ta sanar dashi, shima sosai yayi farinciki dama amincewar ta kawai yake jira, finally ta yarda da Jibril duk wahalar da yayi kafin ya shawo kanta, kai tsaye ya kira mahaifin Jibril suka tattauna akan bikin.
Washe gari
Rayhaan da Yusuf kusan a tare suka zo, duk suka shiga suka ajiye motocin su a parking space sanin tare da Eshraq zasu fita kuma a motar sa, dama duk zasu fita waje mai muhimmanci irin wannan mota ɗaya suke shiga, sai ta security a bayan su, babu bata lokaci Eshraq ya fito suka tafi, kai tsaye “Nigerian Customs High Command Apapa Headquarters” suka nufa, mota ƙirar Rolls-Royce Phantom Series II Arctic White ta tsaya a hankali a dai dai inda ake adana motoci, Rayhaan da Yusuf kusan lokaci ɗaya suka balle motar suka fito, Eshraq kuwa sai da guards ɗin sa yazo da sauri ya buɗe motar kafin ya fito da qafafun sa dake sanye cikin loafers ɗin Berluti patina, ƴa fito da azama cikin izza sanye da coal black Emirati designed suit, an yi masa stitching da champagne gold, idanunsa boye cikin Cartier Premiere Sunglasses. Kallo ɗaya zaka masa ka gane half cast ne saboda wata irin hasken fata dake jikinsa mai daukar hankali ta larabawan Khobar, ga kwarjini a ido ko ga maza yan uwansa balle mata, tun da ya fara takun sa na izza, su Yusuf na bayan sa securities na bayan su aka zuba ido ana kallon su a wurin, kallo daya zaka masu kasan ba qananun mutane bane, yadda ya murtuqe fuska babu walwala shows the silence around him was loud power without sound. Dama an San da zuwan su, shiyasa kai tsaye aka basu izini har zuwa office ɗin CG, da hannu ya yiwa securities alamar su tsaya daga nan batare da ya waiwaya ya dube su ba, suka shiga tare da Yusuf da Rayhaan, CG Bilal yana saka hannu a wasu takardu lokacin da suka shigo cikin izza, tsadadden qamshin turaren da ya doki hancin sa ya saka shi saurin dagowa da sauri yana kallon ƙofa, idanun su suka sarqe dana juna, a tare zukatan su suka buga lokaci ɗaya ba dan komai ba sai dan mamakin ganin juna, shock of recognition, shi Eshraq thinking zai ga wani olderly man irin masu kafuwar nan na mutanen da, sai yaga sabanin haka domin a wurin shi shawo kan CG qaramin abu ne yanzu, CG kuwa mamakin ganin Eshraq yake, Tycoon da ake faɗa a gidan radio da jaridu Wanda mutane da yawa basu taba ganin sa ba sai jin sunan sa a yanda yayi fice a faɗin Nigeria, Tycoon? This young? This refined? This composed?” wai shine wannan qaramin yaron dake gabansa yake da dukiya, business, influence, suna, duk shi ne?
Wannan saurayin da bai yi years of wrinkles ba dan ya tabbata ko aure bashi dashi? Tunanin sa ya katse lokacin da Yusuf ya miqa masa hannu suka gaisa, CG ya tashi daga inda yake zaune ya miqa masu hannu ɗaya bayan ɗaya har zuwa sanda hannun sa dana Eshraq ya haɗu, Handshake ɗin manya, ƙarfin Soja da definiteness, Firm, Warm, Silent and Respectful. “Welcome, Mr Tycoon.” CG ya faɗa cikin murmushi da ƙarsashi, Eshraq yayi wani irin murmushi yana kallonsa ƙasa ƙasa a ransa yana faɗin I see you, I respect you, but I’m not here to entertain you" a fili kuwa yace "Thank you CG Bilal". Ya basu izini su zauna, kusan a tare su huɗu suka zauna, har zuwa lokacin CG na cike da mamakin wai wannan yaron ne mai irin kuɗin da ake mgn a gari, shi wallahi ya ɗauka dattijo ne Tycoon koma mai irin shekarun sa haka, duk suka yi shiru na ɗan wani lokaci, kafin CG yace "Bari a kawo maku.... Rayhaan ya katse sa da sauri," no kada ka damu sir, we are not here for that, thanks we rilly appreciate", CG yayi murmushi kaɗan kafin yace “I received your request concerning the detained container. Before we proceed let me clarify something important, your container carries prohibited substances, Cocaine, high grade, Haram by law.” Eshraq ya zuba masa idanuwa bayan ya zare madubin idanunsa, Rayhaan ya buɗe baki zai yi magana, Eshraq ya ɗaga masa hannu alamar kada yayi, cikin muryar sa in calm and deep control yace da CG “Are you certain?” “Absolutely certain.” Bilal ya faɗa sounding serious, “And I know you are not the type to import such, But law is law, i cannot release that container, am sorry Mr Tycoon ", Cikin bacin rai Yusuf yayi caraf yace" saboda me, me kake so a baka? Kallonsa CG yayi yana bata rai kaɗan kafin yace "Even if you were the richest man in Africa, you can't buy me cos my seat is not bought.” Rayhaan da Yusuf sun nuna mamaki tsantsa da jin kalamansa, suka dube shi da sauri kafin su dubi Eshraq har lokacin ba alamar tsoro ko shock a tare dashi, sai jin suka yi yace "Good CG, I am not here to buy your seat, I’m here to clear my name TYCOON, kayana nake so". CG ya gyada kai kadan yace "abin da kaji a farko shi zan qara maimaita maka bazan iya bayar da wannan container dake tattare da kayan da aka haramta shigowar su a nigeria ba". Eshraq ya jingina da kujera yana kallon sa, “Alright, CG, since you’re insisting on the law, let’s talk percentages, kuɗi sun fi ƙarfin doka.” CG ya gyara zaman sa yana kallon Eshraq kamar bai fahimci me yake nufi ba, Eshraq ya gyada kansa kaɗan yace “Ten percent.” CG bai motsa ba ya zuba masa idanu cikin mamakin yaron, Eshraq ya yi wani murmushi da yake cin rai. “Too small? Fine.” Ya jingina gaba a kujerar. “Twenty percent.” Nan ma CG bai yi magana ba, Eshraq ya ɗaga hannunsa sama kamar wanda magana take masa dole, yace “Ok Thirty percent Final, Ka ɗauka ka rufe idon shari’a ko doka, Everybody walks away happy kuma kuɗi sune number 1, nan ne Bilal ya daka tsawa mai nauyi irin ta manyan uniformed officers,
“STOP right there!”
Ya miƙe tsaye da ƙarfi, kujera ta ja ƙasa kaɗan. Idanunsa sun yi jawur saboda bacin rai, “Do you think I’m desperate? Do you think I’m hungry for your money? Na fi ƙarfin karɓar kuɗi daga gare ka, Tycoon!”, Yusuf da Rayhaan suka firgita da bacin ran CG, Eshraq kuwa ko gezau, Rayhaan yace “Relax, CG It’s only money, and money solves problems, babu wanda zai san ka karbi kudinnan sai idan Kaine ka faɗa, and container yaran ka zaka iya sallamar su da su rufe case ɗin idan ma mu kake so mu sallame su duk zamu yi ka riqe percentage ɗin ka kai ɗaya". Bilal ya nuna shi da yatsa cikin bacin rai har zufa ke karyo masa cos bai taba tsintar kansa a tashin hankali irin wannan ba, cos ya sha kama kayan mutane kuma azo a ziyarce sa da makamancin magana irin wannan ta cin hanci da rashawa sai dai babu wanda ya taba zo masa a irin yanda Tycoon ya zo a yau, cikin izza da nuna rashin tsoro ko kaɗan a idanuwansa, and ga wani kwarjini nasa daya cika masa ido sosai, yace da Rayhaan “Ba zan karɓa ba! Kada ka sake gwada cin mutuncina da sunan offering bribe. I don’t work for boys like you!”
Eshraq ya yi ɗan murmushi mai zafi: “Boys?” Ya yi dariyar mugunta, the disrespectful wealthy laugh. Ya tashi a hankali, ya gyara suit ɗinsa, ya kalli Bilal kai tsaye cikin ido eye contact full of cold threat, yace “Listen very carefully CG, I’m giving you an option not begging for your help. Kuma ka ki, Fine... “But hear me well… Sai na karɓi container ɗina. Ko da me zai faru. I don’t care which law stands in my way. Ko kai ne kansa, ko doka ce kanta. One way or the other that container is mine And wallahi, CG Bilal… I will collect it, by force, or by system, or by whatever it takes ka daina min kallon yaro qarami cos naga hakan a idanunka, wannan container sai ta dawo hannuna very soon.” ya mayar da glass ɗin idanunsa yana qara faɗin “You just rejected money. Don’t make me offer something else.” kafin ya juya cikin nutsuwa ya fice su Yusuf na bayan sa, CG ya cika da mamakin sa, wannan yaron threatening ɗin sa yake ko me?yana tunanin zai ji tsoro ya bashi container ɗin ne kome? ya tuna yadda yake magana cikin ƙarfafa "I will collect it, whatever it takes.”
#IZAYA
#Pherty
#Nihal
#Tycoon
#Jibril
#CG BILAL
#Yusuf
#Rayhaan