IZAYA

5

by @pherty001

Tun bayan dawowar su gida suka zauna shiru cikin tunanin mafita,

​Eshraq ya zare wristwatch ɗinsa ya ajiye saman coffee table, yana ta kallo sama, ya tsurawa chandelier ido, zuciyarsa cike da tunani iri iri,

​Rayhaan ya dube su yace “Guys! this thing can’t continue like this,wallahi this container matter is getting out of hand."

​Yusuf yaja numfashi kaɗan yana faɗin “Let’s think straight first. Me za’a iya yi? Shi wannan DCG babu abinda zai iya tun da shi muka fara gani kafin CG gabaki ɗaya yafi bata min rai akan yanda yake tsoron CG ɗin ma",

​Rayhaan yaja tsaki yana kallon su, “But guys, if we don’t trace this CG guy properly, we’re just wasting time, the guy is too smart he’s not a random hustler on the street i think he has roots, influence, and serious connections.”

​Har zuwa lokacin Eshraq bai yi magana ba sai kallon su yake daya bayan ɗaya with deep thinking, bai taba shiga matsalar da ya kasa warware ta irin wannan ba,

​matsalar da take gab da rusa mafarkin sa a duniya, Eshraq ya jingina baya sosai, ya furzar da iska a hankali.

​His tone was calm but deep,  yace "Right now ba maganar container kawai nake tunani ba, if a man can hold my goods this long, without trace, without pressure affecting him… then that man is not small,

​kowa ya san TYCOON a faɗin ƙasar nan, amma ƙalilan mutane ne suka san waye TYCOON a zahiri, ​duk da bayyana ta garesa a yau hakan bai sa ya girmama buqata ta ba, bai ji tsoro na ba, bai kuma duba girman shahara ta ba yake gayamin bazai saki container ɗin ba",

​ya runtse idanunsa kaɗan yana jin wani bacin rai a wannan karon, kafin ya buɗe yana kallon su,

​“I don't want to lose that container. Not even one item inside. You all know how important this shipment is, kafin naje next step a move Ina, I want EVERYTHING about him, his business, his office, his partners, his suppliers, his house, his routines, his weakness, and every single person connected to his network.” Rayhaan da Yusuf suka tsura masa ido ganin a wannan lokacin ya soma nuna damuwa a fuskarsa, batare da ya saurare su ba yace "in just 2 days nake son jin komai, Ina jiran ku",

​ya tashi da azama ya bar falon cikin takun sa na izza, Yusuf ya sauke numfashi kaɗan yana kallon Rayhaan, yace "let's start tomorrow". Rayhaan ya gyada kai cikin amincewa.

​CG BILAL MANSION

​A gajiye friends ɗin ta suka shigo gidan dawowar su daga bikin wata friend ɗin su kafin su biya boutique suka yiwa NIHAL siyayyar Engagement ɗin ta as surprise gift,

​kowanen su ɗauke da shopping bag a hannunsa Cike da kayan designers, beauty products, da sauran su,

​kai tsaye bedroom dinta suka nufa tana kwance da waya a hannunta tana game, kallo ɗaya tayi masu ta dauke kanta da murmushi a fuskarta,

​a tsakiyar gado duk suka zauna kusa da ita, itama ta tashi tana kallon su, ''ya bikin? ta tambaya da muryar ta mai sanyi kamar ko yaushe,

​"bikin yayi daɗi, wai meyasa baki je ba, and she asked of you", cewar Rumah tana kallon ta,

​ta lumshe manyan idanuwanta, kafin tace "just not interested in going" sukai yi shiru sanin halin ta musamman akan abinda bata da niyar yin sa babu wanda ya isa ya saka ta ko hanata,

​suka soma duba kayan da suka siyo mata, Rumah ta ɗauko wata babban box mai cover mai launin champagne ta miqawa NIHAL tana faɗin 'just look NIHAL wannan yayi kyau sosai set of Dior".

​NIHAL ta karɓa da sauri tare da kai hancin ta, ta lumshe ido cikin murmushi kaɗan tace "it smells so good, and I like the packaging",

​ta soma duba perfumes da cream, kafin ta soma duba kayan da suka shigo dasu tana kallon su fuskarta dauke da surprise look, tace "daga biki kuke kuwa?

​Hafsat ta gyada kai kadan tace" yh but mun tsaya boutiques to get you something",

​ta jinjina kanta cikin murmushi da farinciki, ta sani duk abinda zasu siyo mata tana da wanda ya fishi a tare da ita,

​babu abinda mahaifinta ba ya yi mata na more rayuwa sai abinda ya sabawa addini, but wannan small gifts nasu makes her feel extremely happy and ko yaya ne sun nuna suna son ta da son farinciki ta,

​haka take tana da son kyauta komai qanqantar ta, bata duba tafi qarfin abu, ta dauki kyauta wata babbar aba a rayuwa,

​shiyasa bata raina kome mutum zai bata ko da kuɗin sa bai kai darajar naira dubu ba, tana appreciating,

​Serdia ta bude wani bag mai leather mai laushi, ta ɗaga wani pair of silk pajamas (kayan barci masu matuqar kyau da laushi) daga Fendi,

​“Oh my God, NIHAL! Kin ga wannan set, and the color will suit you, it will be special Idan kika sa gobe at night after your engagement",

​cikin murmushi ta karbi kayan ta ɗaga tana duba su da kyau, daga yanayin murmushi da take suka san tana farinciki da small gifts ɗin su,

​cos bata da yawan murmushi ko dariya kamar su, shiyasa da yawa qawayen su suke mata kallon mai girman kai har basa son friendship da ita,

​a ganin su tana da zafin kai da wulaqanci bayan ba haka bane, sai wanda ya zauna da ita kawai zai fahimci hakan,

​cikin murmushi ta dube su tana faɗin "I like it too, the soft slippers na cashmere (slippers dake tare da kayan barcin), nasan will make me feel comfort and stylish at same time,

​but wait wait waye zan nunawa kwalliyar Idan na saka a gobe, we are not married just engagement? tayi tambayar cikin fiddo idanu tana kallon su,

​suka kyalkyace da dariya, Rumah tace "we are having fun tomorrow night, mu ma zamu saka namu daban, but yours is different you are the bride",

​ta jinjina kanta tana faɗin "oh nagane, na fahimta yanxu", ta cigaba da duba kayan, makeup pallettes, skincare kit, scented candles, designers scarves,

​Kuma haka tabi tana comment akan colors, quality da yaba kyawun kayan suna dariya da expressions of excitement.

​Bayan ta gama duba kayan suka sauka daga bed, suka nufi dinning, hayaniyar dariyar su kawai kake ji a sashen ta wanda ke tabbatarwa da masu kula da ita tana tare da friends ɗin ta,

​kusan a tare suka zauna suna hira da dariya, suka ci, pastries, sandwiches da fresh fruits,

​duk hirar tasu akan auren ta da Jibril ne suke da Planning ɗin da zasu yi idan lokaci yazo,

​bayan sun gama dama lokacin skincare ɗin ta yayi, ta kira lawee ta soma mata skin routine, cleansing, toning, moisturizing, da face mask,

​Rumah na tsaye tana gyara mata gashin ta suna cigaba da hira cikin excited tone.

​CG Bilal dawowar sa Kenan daga office yaji dariyar su, duk bacin rai da yake ciki akan abinda TYCOON yayi masa a yau yaji bacin rai yana gushewa kaɗan kaɗan saboda dariyar NIHAL da yake ji tare da friends ɗin ta,

​ya tsinci kansa da son zuwa ya ganta, ya nufi part ɗin ta, suna haɗa ido yaji wani farinciki a zuciyarsa,

​kawai annuri da yake gani a tare da ita yake jin komai na zuciyarsa ya gushe na bacin rai da ya dawo dashi,

​da sauri ta tashi ta nufe sa, ya buɗe hannuwa sa ta faɗa jikinsa ya mayar da hannun ya rufe tare da lumshe idanunsa,

​qawayen sanin irin soyayyar dake tsakanin su ya saka sai murmushi suke suna kallon su, kafin su soma gaida shi cikin girmamawa,

​ya amsa da farin ciki a fuskarsa kafin ya dubi NIHAL yana faɗin, "gyaran jikin ake yi kenan",

​ta gyada kai tana kallon shi da murmushi, kafin tace "you sound worried daddy akwai abinda yake damun ka?

​Ya girgiza kansa a hankali yana mata kallo mai cike da so da qauna, yana qara son tane saboda irin yanda take saurin gane idan yana cikin damuwa ko da ya boye mata hakan,

​ta san shi sosai fiye da mahaifiyarta, yaji ta riqo hannunsa tare da langabar da kanta tace "please Daddy",

​yace "yunwa kawai nake ji, tun safe babu abinda na saka a cikina",

​tace "zo na baka abinci kaci, muna da pastries da sandwich me kake so?

​ya girgiza kansa yana faɗin, je ki zauna a cigaba da gyara maki skin, I will eat with your mum",

​tace "sure? Ya gyada kansa in affirmation yana kallonta da murmushi,

​kafin ya saka hannu yana cire mata mask ɗin da aka saka mata a fuska da ya soma tashi da kanshi,

​ta yatsina fuska kaɗan tace "da zafi fa", cikin kulawa yace "kullum abinda kike cewa idan nazo cire miki, and ni ina jin daɗin cire wannan mask ɗin",

​ita da friends ɗin ta suka soma dariya, tace "kaje kaci abinci yau zaa saka ma ka pls Daddy kada kace Noo",

​ya gyada kansa alamar ya yarda, ta soma murna kafin ya juya ya bar wurin cikin murmushi", suka cigaba da hirar su cikin Nishadi bayan taje ta zauna.

​WASHE GARI

​An tashi da shirye shirye karɓa manyan baqi a gidan, iyayen Jibril da zasu zo tambayar aure,

​duk da gidan babu hayaniya kamar ko yaushe, amma yanayin sa kawai zai tabbatar maka da alamar zaa yi baqi,

​har sanda iyayen sa suka iso NIHAL tana barci bata tashi ba, motocine manya guda biyu suka shigo harabar gidan, Black Prado TXL da Mercedes Maybach S-Class, ceasar black,

​DCG Abdallah da manyan abokan sa guda biyu acikin motar farko da ta shigo, sai ɗayar kuma yan uwansa ne na jini guda uku aciki.

​Kusan lokaci ɗaya suka fito, kowane da shiga ta alfarma a jikinsa, kuma kowane da murmushi a fuskarsa,

​cikin girmamawa security dake gurin ya gaida su, “Sir, this way please, guest lounge has been prepared.”

​DCG ya dube sa kaɗan yace a nutse, “Alright Lead the way.” security na gaba suna biye dashi har guest lounge,

​sanyin ac da qamshin dake tashi a sashen ya ratsa su, suka zauna akan Italian leather sofa, milk color,

​sai raha suke da juna cikin dariya, basu jima ba CG Bilal ya shigo da hanzarin shima cikin shigar sa ta kamala,

​fuskar sa dauke da tsantsan farinciki, shima ƴan uwansa a bayan sa, suka soma musayar hannu cikin girmamawa suna gaisawa,

​sun ci sun sha, kafin su soma magana akan ya'ƴan su, komai suna yi cikin raha da barkwanci,

​DCG Abdullah da mutanen sa sun nemi auren NIHAL, CG Bilal da mutanen sa sun bashi,

​nan take aka yanka sadaki suka biya, aka sa lokacin auren nan da wata uku, kuɗin komai da komai duk nan a take suka biya komai.

​Sanda zasu tafi har harabar gida wajen motocin su CG suka raka su, sai bayan tafiyar su suka juya cikin nutsuwa suna tattauna karamci mutanen.

#IZAYA

#Pherty

#Nihal

#Tycoon

#Jibril

#CG BILAL

#Yusuf

#Rayhaan