MASARAUTAR KAIZUR

MASARAUTAR KAIZUR 15

by @nusybee143

🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 





✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 




Page 15




*SHEKARU ASHIRIN BAYA*

*DAULAR BARUDA*



Garin Baruda yana ɗaya daga cikin daulolin da suka kafu suka tsaya da ƙafarsu dalilin yaƙe-yaƙe, duk da cewa yaƙi yana kassara daula kamar yadda ya zamo sanannen abu a duniya,amma ga Baruda abin ba haka yake ba

Ƙasar Baruda ta ɗauki shekaru sama da ɗari biyar tana gina kanta don ganin bayan abokan gaba,ko kuma na ce don ta yi zarra ga duk wata daula da ke makwabtaka da ita

Ta yi nasara!inda daular ta shahara a ɓangaren horar da matasanta don zama mayaƙa,hakan bai yi ba sai da suka ƙara da koyar da tsaface-tsaface,a taƙaice ma, daular Baruda tana daga cikin manyan dauloli uku da suka shahara da tsafi a duniya,sannan kuma aka zo fannin yaƙi ba'a taɓa cin nasara akansu,idan ma basu yi nasara ba suna yin ragas da abokan gaba 

Mafi akasari daular Baruda bata cika yin yaƙi da ƙananan ƙasashe ko waɗanda ba su da komai ba,suna yaƙi ne da ƙasar da take da dukiya,su yi nasara akan ƙasar su kwashe dukiyar 

Ba su da wani abin bauta a duniya sama da rana,sai kogin Baruda da suka ɗauka abu mai tsarki da zai taimaka musu ga ibada,tsawon shekaru aru-aru sun yi imani da hakan,kuma akan hakan suke tafiya har zuwa sanda daular Tayaar ta rusa su

Babban sirrin garin Baruda kuwa ba sa amsar baƙo,ba su yarda da baƙo ba duk tsanani,ko da kuwa baƙon ɗan kaza ne,ba su yarda ɗan ƙasar ya rinƙa barin ƙasar yana ɗaukar lokaci bai dawo ba,a cewar su duk Waɗannan idan aka samu a Baruda za'a iya yi musu shigo-shigo babu zurfi,ko dai a yi amfani da baƙo mai shigowa ko kuma a yi amfani da ɗan gari da yake barin gari,hakan zai iya sakawa watan watarana a ci su da yaƙi 

A dalilin wannan tsatstsauran ra'ayi irin na su ya sa ko baƙo ne ya yada zango a Baruda matuƙar bai je ya nemi izinin Sarkin garin ba suke kashe shi a take da zarar sun kama shi,idan kuma ya nemi iznin sarki za'a saka masa abin da bai wuce kwana uku ba,ko dai ya bar garin ko ya bar duniya 

Wannan kenan!!!




💫


Mafarauci Murad mazaunin ƙasar Baruda ne,a wani ƙaramin ƙauye da ake kira da kalaar,ya shahara sosai akan sana'ar shi ta noma,sannan kuma babban matsafi ne wanda a duk ƙauyen nasu har ma da ƙauyukan maƙwabta babu wanda ya kai shi ƙarfin tsafi 

Saboda ƙarfin tsafinsa da yadda yake sarrafa aljanu yana iya barin ƙasar ya je wata nahiyar ya dawo a yini guda ko kuma a cikin dare,sannan kuma gwani ne a fannin farautar manyan namun daji,kama daga kura,kyarkeci,kada,damisa, da sauran su, dama ba'a maganar maciji da waɗanda ba su kai shi ba, Waɗannan ma bai ɗauke su wani abu ba

Abu ɗaya ne tawayarshi a rayuwa, tsawon shekaru sama da ashirin da aurenshi har yanzu bai taɓa haihuwa ba,duk dabara da surkulle na tsafi ya yi,amma babu wani cigaba, matarsa Hasa,bata gajiya da yawace-yawacen wajen bokaye da malaman tsibbu ba don su samu haihuwa,amma amsar ɗaya ce,ba shi da rabon haihuwa 

A dalilin haka ne Hasa ta canjawa mijinta,ya daina gane kanta,ta tayar da rikicin ita lallai sai ya sake ta, hakan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba,amma ya cigaba da lallaɓa ta ko don shekarun da suka ɗauka suna zaman tare

Sanadin haka ya sa ya ɗan mayar da hankalinsa kan farautar shi ta ɗan lokaci,sau tari idan ya bar nahiyar ta su bisa umarnin da yake bawa aljanunsa sai ya kwashe kwanaki bai dawo ba, musamman da Sarkin lokacin wato Jiyaaz ya yarje masa, kasancewar ana amfana sosai da farautar shi,har Giwa ya kan farauto ya feɗe ta, ba'a maganar su damisa,kura da sauran dabbobin daji,yana kawo fatocin dabbobi iri-iri a duk lokacin da aka buƙata a Baruda, hakanan kuma ya iya haɗa dafin macizai kala-kala musamman waɗanda ake shafawa makamai da wanda ake yiwa abokan gaba izaya 

Tsawon lokaci bai ziyarci dajin kalaar ba, saboda akwai isassun namun dawa a dazukan kewayensu,amma yau yana son ziyarar yankin 

Dajin Malug yana a wani yanki ne wata daular Musulmai mai suna JASUS, saboda yadda Baruda bata shiri da musulmai ya sa ko da ace Murad zai ziyarci wannan dajin sai cikin dare,ya je ya yi uzurinsa kafin ketowar alfijir ya dawo Baruda 

Yau ma kamar yadda ya saba ya kammala farautarsa,ɓauna ya samo, saboda ita yake buƙata yana son amfani da fatarta,ya dafa kujerar tsafinsa don ya koma Baruda kenan ya fara jin kukan jariri 

Ba yau ya saba shiga dazuka ba,yana iya bambance muryar jaririn mutum da ta aljani idan suka kwaikwaye shi, don haka ya yi matuƙar mamakin samun mutum mai rai a cikin wannan ƙungurmin dajin,mutum mai rai ɗin ma jariri,don haka ya bazama yana duddubawa 

Ai kuwa ya yi dacen samun jaririn a cikin wani buhu,an yasar da shi a bakin hanya,ya yi saurin ɗaukar buhun ya kwance yana ƙarewa jaririn da ba zai haura watanni uku ba a duniya kallo

Tsananin kyan jaririn ya shagaltar da shi ya yi ta kallonsa,daga baya ya yi tunanin nemar masa abinci,don da gani yunwa yake ji,bai yi wata wata ba ya koma baya inda ya gano wasu masu kiwon raƙuma a daf da dajin,suka ba shi nonon raƙumi ya ba wa jaririn,sannan ya hau kujerar tsafinsa don komawa Baruda 

Ya riga ya san dokar Baruda,ko ɗan tsako ne muddin ba nasu bane ba sa ƙaunar ya raɓe su ballantana ɗan mutum,shi kuma yana da tunani mai kyau akan jaririn,ya san tunda ya ganshi a gefen daular Jasus to tabbas ɗan cikin garin ne,tunda su musulmai ba sa sonshi shi zai raine shi ya koya masa yaƙi,ya nuna masa soyayya ya ba shi makami ya yaƙi Musulmi 

Iya wannan tunanin da ya yi kawai ya saka shi murmushi,a ranshi ya fara wassafa yadda zai mayar da wannan jaririn,ya yi nasara akan dukkan abokan hamayya,da ƙarfin tsafi da ƙarfin tuwo

Kai tsaye daga nan fadar sarkin Baruda Jiyaaz ya wuce,duk da kasancewar shi sananne a fadar,kuma ana girmama shi da mutunta shi amma sai da ya jira aka yi masa iso,sannan ya shiga

Bayan ya gaida sarki Jiyaaz kamar yadda ya zama al'ada,ya gabatar da jaririn da ya tsinta a dajin kalaar 

Ɗif fadar ta yi,wannan ya kalli wannan,wancan ya kalli wannan, Yarima Akaal, ɗan sarki Jiyaaz a wancan lokacin ne ya fara hasala,ya dubi mafarauci Murad a fusace ya ce"kai tsoho!

Da alamu ka rikicin tsufa ya fara mantar da kai dokoki da iyakokin ƙasar Baruda ko?

Na san ka sani,kuma ka tabbatar babu wani baƙo da yake zuwa Baruda ya zauna a matsayin garinsu,kai kuma ka kawo jariri,a wanne dalilin?"

Rissinawa Murad ya yi, cikin ladabi ya ce"abin bauta ya albarkaci zamaninka ya shugaba na,ina da kyakkyawar niyya da cigaban Baruda a zuwan wannan jaririn 

Niyya ta na tsaface shi, tunda musulmai sun yar da shi ba sa so,ni zan raine shi,na koya masa al'amuran yaƙi da tsafi,idan ya so sai mu rinƙa amfani da shi yana yi mana yaƙi,da zarar ya kai shekaru goma zan kai shi wajen Sarkin yaƙi ya koya masa al'amuran yaƙi,Ni kuma na cigaba da koya masa al'amuran tsafi,idan ya kai wasu shekaru a fara fita yaƙi da shi,amma ya ka gani?"

Tuni fuskar Sarki Jiyaaz da ta fadawanshi ta washe,suka jinjina wa wannan shiri na mafarauci Murad 

Bayan Sarki ya sallame shi kai tsaye gida ya wuce,Hasa tana zaune tana saƙar tufafin da yake sana'ar ta Murad ya shigo rungume da jaririn fuskarsa a washe

Da kallo Hasa ta bi shi tana mamakin inda ta samo jariri,ya miƙa mata shi ya ce"maza yi masa wanka Hasa,ki ba shi nonon akuya bayan ya ƙoshi ki zo za muyi magana "

Babu musu ta yi duk yadda ya ce,don so take yi su yi magana ya gaya mata inda ya samo wannan yaron

Bayan ta gama shirya shi,har ya koma bacci,ta dawo wajen mijin nata da jaririn, Murad ya amshe shi yana murmushi, sannan ya ce"tsintarshi na yi a dajin Jasus,sai na ɗauko shi,kin ga dama bamu da ɗa,ga shi kuma ina so ya zama mayaƙi tunda ni ban zama ba"daga nan ya yi mata bayanin yadda suka yi da mutanen fada da kuma niyyarsa akan jaririn 

Sam bai kula da irin mugun kallon da take aika masa ba sai da ta ya gama bayani,tana yi masa kallon banza ta ce "yanzu duk yaran da ake haifa a Baruda Babu wanda ka tsinta sai wanda aka haifa a wata duniyar?

To gaskiya ba zan iya ba,ni ba don ma ka ce Sarki ya yarda da zamansa ba da babu abin da zai hana ya baƙunci lahira yau ɗin nan"

Murad ya ce"ai ba kyauta za ki kula da shi ba, za'a biya ki,har sai ya kai shekaru goma"

Sai a lokacin ta sassauta fuska tana kallonsa ta ce"me za'a biya ni da shi?"

Murad ya ce"duk wata za'a biya ki dirhami biyu"

Hasa ta yatsina fuska ta ce"gaskiya bai yi min ba,dirhami. ......"

"Zan ƙara miki da mudun alkama biyu"

Hasa ta yi murmushi ta ce"yanzu na san ka shirya na yi maka rainon yaro"

Murad ya yi ɗan murmushi sannan ya ce"a don haka na zaɓi suna na nasara a garin Baruda,na sanya masa suna KAZUZI,daga yau har zuwa ranar da zai bar duniya zai amsa sunan KAZUZI IBN MURAAD!"




💫

Wata iriyar zabura gimbiya Hayat ta yi tana nuna Kazuzi da yatsa amma ta gagara magana,ya yi ɗan murmushi kawai ba tare da ya yi magana ba,da ƙyar ta iya faɗin"dama kai ba ɗan mafarauci Murad bane?

A'a,dama kai ba haifaffen garin Baruda bane?

Ya aka yi ka san da hakan?"

Kazuzi ya ce "za kiji yadda aka yi na sani"daga nan ya cigaba ba tare da ya damu da yadda take kallonshi da tsananin mamaki ba




💫

"Rayuwar Kazuzi a cikin garin Baruda rayuwa ce mai wahala tun yana jariri,Hasa bata damu da shi ba,bata kula da shi sai abin ya ba'a rasawa saboda kuɗin da ake biyanta 

A haka ya kai shekaru biyu, shi kanshi Murad ba damuwa ya yi da shi sosai ba,sai idan al'amuran asirin ko na tsaface shi da yake yi, bai taɓa damuwa ba idan ta ga yana kuka,bai taɓa jin ya kamata ya lallashe shi ko ya ji damuwarsa ba, ballantana kuma a kai ga yi masa maganin damuwarsa 

Ga yara kuwa abin babu sauƙi, sanannen abu ne a cikin Baruda cewa Kazuzi ɗan tsintuwa ne, ba'a san asalinshi ba,amma abu mafi rinjaye da ka iya yiyuwa shine Kazuzi ya kasance yana da alaƙa da musulunci,shi kuma musulunci shine abu mafi zama abin tsana da ƙyama a Baruda 

A dalilin wannan abu ko wasa ba'a barin Kazuzi ya yi da sauran yara,tun bai shekara biyar ba a duniya yake fuskantar tsangwama,har ta kai shi ga daina shiga yara shima 

Tun Kazuzi yana ɗan ƙarami ya taso da izza,da ji da kai,da nuna isa,sannan bashi da tsoro ko kaɗan,gashi baya ɗaukar raini,hakan ya farantawa Murad sosai,don a zatonsa aikin shi ne yake tasiri fiye da yadda yake zato 

Tun Kazuzi yana da shekaru biyar Murad ya fara ɗaukarshi zuwa farauta, abin da shi kanshi Murad ɗin ya ɗimauta shi ya firgita shi shine kashe maciji mai dafin gaske da Kazuzi ya yi yana da shekaru shida kacal,wannan abu ne ya sa Murad jin alfahari,ranar da ya dawo daga farauta washe gari ya ɗauki Kazuzi zuwa fada 

Bayan an yi masa iso cikin farin ciki ya sanar da sabon sarkin da aka naɗa babu jumawa bayan murabus da sarki Jiyaaz ya yi,cewa yana son a fara koyawa Kazuzi al'amuran yaƙi tun daga yanzu, saboda duba ga rashin tsoron shi da jarumtarshi tun yanzu,sarki bai yi musu ba,ya amince,aka kai Kazuzi wajen Sarkin yaki Anudu, don ya fara koya masa al'amuran yaƙi 

Ko a wajen koyon yaƙin ma Kazuzi yana ganin rayuwa, saboda irin horon da ya kamata a ba shi ba irin shi ake ba shi ba,ba iyaka horon yaƙi ba,ko laifi ya yi ake so a hukunta shi ana gana masa azabar da ta fi ƙarfin shekarun shi

Bai taɓa ɗaukar abin da aka yi masa a matsayin zalunci ba, asalima yana ƙoƙarin ganin cewa ya kiyaye dokokin da aka kafa masa,sannan yana ƙoƙarin ganin cewa ya iya abubuwan da aka koya masa a wajen horon yaƙin 





#Nusy_bee