Chapter 3
Kasancewar Yau Monday kowa da abinda yake yi ma'aikata na shirin fita wajen aiki yan makaranta suna shirin tafiya school hakan ne ya kasance a gidan air marshal Farouq ,Jaiyana sai sauri take gudun kar ta makara duk da kasancewar ta MD acikin asibitin,bata son latti ko kadan komai nata tana yin sa ne Akan tsari wannan yana daya daga cikin babban dalilin da ya saka sadiq ke son ta,cikin qanqanin lokaci ta gama shiryawa cikin silver ash abaya tayi rolling mayafin abayar,clutch da sabuwar iPhone 16 pro max ta dauka tare da mukullin mota tayi hanyar waje har lokacin ayaanah bacci take yi direct dakin mom ta shiga suka gaisa sannan ta fada mata ayaanah na bacci tana dakin ta addu'a mom tayi mata sannan ta tafi,a hankali take driving cikin nutsuwar da ta gama xama a jinin jikin ta har ta shigo cikin harabar asibitin wurin parking ta nema ta yi parking motar ta sannan ta zuro fararen qafafun ta qasa ta fito Subhanallah gaskiya duk inda ake neman kyau Toh tabbas dole xa'a saka jaiyana cikin sahun farko,sleepy eyes din ta masu daukar hankali,dogon hancin ta kamar ita tayi ma Kanta dan qaramin pinkish bakinta dai dai fuskanta tana da tsayi dai dai gwargwado,hourglass shape din ta mai daukar hankalin duk wani da namiji mai cikakkiyar Lpia,kasancewar bata saka matsatsen kaya amma hakan bai hana kyakyawar baiwar halittar da ubangiji yayi mata ta bay yana,a hankali take taka qafar ta kamar wacce aka yi ma dole har ta shiga cikin asibitin ma'aikata ne ke ta gaishe ta har ta xo qofar office din ta a hankali ta turo qofar ta shiga ba tare da tunanin da mutum aciki ba ta fara har ta kusa xuwa gurin xaman ta taji murya daga bayan ta ance surprise da sauri ta juya saboda Jin muryar sadiq,shi din ne kuwa da gaske sleepy eyes din ta ta xare masa sosai gaba daya ma ta kasa magana dariya yayi Toh xare idon ya isa haka dan murmushi tayi mai daukar hankali amma Baka fada man xaka dawo ba eh ina son nayi surprising dinki ne amma Yaushe ka dawo jiya cikin dare amma baka huta ba ka fito office ba office nazo ba kawai naxo naga wannan Kyakyawan fuskan naki ne ita kan ta tasan sadiq na Santa ita ma kuma ta na son ta sama masa gurbi ko kadan ne a xuciyar ta amma ta riga da ta bama wani xuciyar ta baki daya ba ita keda iko da xuciyar ta a yanxu ba maganan sadiq ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta fada me kike tunani haka love babu komai sadiq kawai nayi mamakin dawowarka ne yanxu dai kasan lokacin aiki ne xamuyi magana later kaje gida ka huta saluting din ta yayi sannan yace your wish is my command madam bye take care of yourself for me and don't stress yourself too much please dariya tayi tace you are so funny sadiq,anyway bye bayan fitar sadiq files din gabanta ta fara dubawa........
Mom ce ta shiga dakin jaiyana domin duba ko ayaanah ta tashi daga bacci akan gadon Jay ta ganta daga gani yanxu ta tashi a bacci saboda sai taba idon ta take yi a hankali ta mom ta qarasa bakin gadon ta xauna sannan tace good morning ayaanah a binka da yaro sai taji dadi an gaishe da ita sai Tace morning aunty mom ce Tace A'a ki ce man granny toh granny yawwa good girl muje ayi wanka da breakfast,toilet suka wuce sabon tooth brush ta dauko ta yi mata brush sai kuma ta yi mata wanka towel din Jay ta saka mata suka fito bayan ta gama shirya ta wani jersey din jay ta dauko mata da wani three quarter jeans ta saka mata duk da haka Kayan sunyi mata yawa sosai,riqe hannun ta tayi sannan suka fito domin yin breakfast suna fitowa suka tarar maids sun gama jera komai kasancewar Idan dad baya nan maids ke girkin gidan sandwich,cinnamon rolls,waffles and veggie omelette with apple juice shine yau breakfast din su bayan ta diba ma ayaanah ita ta diba wanda xata ci cikin nutsuwa take suke cin abinci su amma duk wani motsin ta akan idon mom yake,kasancewar mom na son yara yasa bayan sunyi breakfast ta saka driver ya kaisu mall yin siyayya kayan sawa ta siya Wa ayaanah kamar bata son xafin kudi ba kaya sosai Ta siya mata sannan suka dawo bangaren ciye ciye shima ta daukar mata chocolate da yawa sai kuma teddy shima ta siya mata manya teddy bear gud uku gurin biyan kudi suka je aka Ciri kudin kayan aka yi musu packaging sannan aka kai musu mota daga mall din kuma Tace da driver ya kaisu Central Park,ayaanah tana ta murna sunyi wasanni sosai da mom har xuwa qarfe biyu na rana sannan suka fito xasu koma gidan su dake Asokoro,suna shiga gida mom tayi al'wala sannan ta saka ayaanah tayi al'wala ita ma suka yi sallah tare lunch suka fito xasu yi mom ta zuba brown spaghetti with mango juice,ayaanah kuma Tace fried rice take so with watermelon smoothie bayan sun gama lunch suka wuce dakin mom suka zauna mom tana bama ayaanah labari wayar mom ne ya fara ringing sunan aminiyar ta hajia Aisha tagani murmushi tayi sannan ta daga wayar tare da yin sallama daga dayan bangaren aka amsa gaisawa suka yi kowa ya tambayi yara sannan suka shiga hirar duniya tsawon lokaci suna waya kafin suka yi sallama kowa xuciyar sa cike da qaunar dan uwan sa..........
Zaune yake saman daya daga cikin lafiyayyiyan kujerun da ke parlour,kallo ɗaya zakai masa kasancewa shidin namiji ne sbd yanayin murɗewar jikinsa ga wasu six packs da suka bayyana, baƙi ne sosai irin dark-skinned ɗin nan wacce har Shining takeyi, Amma kana kallonsa kasan cewa hutu da jin daɗi sun zauna masa, sbd yadda dark-skin ɗinsa tai fresh gwanin sha'awa . Babu wani abu mai haske a fuskarsa sai jajayen laɓɓansa da fararen idanunsa _He's dark and handsome_ ga kwantacciyar sumar kansa abin sha'awa tai luff har bayan wuyansa, gefen Arms ɗinsa akwai zanan Tattoo wanda a tsakiyarsa akai rubutu amma duhun fatarsa ya hana aga abinda aka rubuta, yana da ƙira irinta mazan Jiya, Black handsome guy na ajin ƙarshe domin kalar fatarsa abar so ce musamman yadda gargasa tai kwance a jikinsa, a hankali ya miqe daga xaunen da yake ya rage kayan jikin shi domin shiga wanka a hankali yake komai nashi cikin nutsuwa kamar mace har sai da ya gama shiryawa gaba daya cikin wasu sky blue suit,kayan sunyi masa kyau sun matuqar amsar jikin sa,bayan HAYDAR ya gama shiryawa ya dawo parlour da xama yana yan dube duben shi a waya,
Kamar yanda zannur yace karfe takwas da minti goma sha biyar ya je gidan gaisawa suka yi sannan suka dauki hanyar airport a hanya suka danyi yi hira amma rabi duk akan aikin su ne basu dauki lokaci ba suka qarasa murtala Muhammed international airport bayan ya gama komai su kayi sallama shi kuma zannur ya koma gida..........
Kamar yadda safiyyah da qawarta shema'u suka tsara jiya hakan ne ta kasance ana gama sallar asuba ta xo suka dauki hanyar wani qauye dake tsakanin Abuja da kaduna bayan sunyi tafiya mai tsayi suka qaraso wani jeji babu gida gaba babu gida baya haka suka tsaya saboda mota bata shiga cikin jejin suka fara tafiya da qafar su sunyi tafiya mai nisa sosai kafin suka zo wata bukka safiyyah ce ta fara shiga shema'u na biye da ita faduwa tayi gaban mutumin dake zaune daga shi sai wani kyalle da ya rufe jikin shi dashi siffar mutumin abin tsoro kirari safiyyah ta shiga yi masa,shi kuwa sai wata dariya yake yi,tsuke fuska yayi kamar bai taba dariya yace fadi abinda ke tafe da ke batacciya wacce sukayi hannun riga da aljanna da sauri shema'u Tace mallam da akwai wani alhaji ne da yake nema na Toh kwatsam kuma sai naga ya dena kira na Idan na kira shi ma sai ya ga dama zai dauke shiyasa nazo nan saboda a dawo man da hankalin shi kaina ya daina ganin kowa sai ni hahahahahahahahaha yayi wata irin dariyar har hayaqi na fita ta cikin bakinsa wani qullin magani ya bata yace wannan ki zuba a cikin ruwan wankan ki sanan ki kaiwa tsohuwar ki ruwan ta sha godiya suka yi masa suka ajiye masa rapper din yan dubu dubu guda biyar suka fita..............
Tafiyar one hour fifteen minutes ya kawo su Nnamdi Azikiwe International Airport bayan jirgin su yayi landing taxi kawai ya shiga ya kaishi gidan shi dake Garki,yana xuwa ya tarar babu kowa a gidan yayi tunanin princess tana school sai kawai ya tafi dakin shi ya xauna yana kiran layin safiyyah amma not reachable har ya gaji ya daina kira.............
A gajiye ta dawo daga aiki babu wanda yasan da shigowar ta saboda dakin ta kawai ta shiga ta watsa ruwa ta canja kaya xuwa na Shan iska marasa nauyi sai alokacin ta fito xata ci abinci ta tarar da mom ita da ayaanah a parlour suna kallon cartoon xuwa tayi ta kwanta a cinyar mom tana wash mom na gaji sosai yau gashin kanta mom ke shafawa a hankali sai da taga tana shirin yin bacci sannan Tace a'a yamma tayi kar kiyi bacci tashi ma Kije ki ci abinci miqewa tayi tareda daukar wayar ta tayi hanyar kitchen salad ta hada ta fito ta xauna yana ci yana karanta wani English novel 28 February, tana zuwa inda saurayin ke kiran budurwarshi da wani suna taji gabanta ya fadi saboda tunowa da tayi da wasu shudaddun memories da suka wuce amma har yanxu sunan nan rubuce a cikin kwakwalwarta................