2
*KUNDINA*
*NAFISATU SASAAL*
2
Jikina a mace na isa sashen da ni kaɗai nake rayuwa a cikinsa.
A ɗaya daga cikin kujerun parlon na yada zango, na yi shiru a zaune ina kallon waje ɗaya.
"Menene zai ba ni ƙwarin gwiwar cikawa Baba alƙawarin da na ɗaukar masa?" Na tambayi kaina a sarari.
Sanin babu wanda zai ba ni amsa ya sa na miƙe.
Inda na ɓoye Takardun makaranta na je na ɗauko, na dawo inda na tashi na zauna.
Takardun shaidar kammala Firamare ne da sakandare, sai kuma wasu takardun da ke nuna shaidar Jami'ar da na fara zuwa a shekarun baya.
Cikin rauni nake binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, kafin a hankali na zamesu takardar da take ta ƙarshe ta bayyana.
Takardar shaidar korar da a kayimin daga Jami'a ce, ɗauke da sunana ɓaro-ɓaro.
Ƙuri na yiwa Takarda, hannuna ya fara rawa, na fashe da kuka.
Na ɗauki tsahon lokaci a haka, kafin na share hawayena.
Na tattara takardun na ajjiye a gefe.
Ban motsa ba, tunda na zauna sai da aka fara kiran sallar magriba.
Tashi na yi na ɗoro alola anan Washroom ɗin dake cikin parlon.
Ban tsaya yin Sallah Parlo ba, na wuce ɗaya daga cikin ɗakunan da yake mallakina.
Anan nayi Sallah, ban miƙe ba har sai da nayi Sallah Isha'i, da na idar kafin na miƙe na jima ina addu'o'in neman yafiya a wajen Ubangiji, da daidaito cikin al'amurana.
Ina miƙewa wayata da tun kafin naje wajen Baba, na kasheta na ajjiye akan bedside drawer na ɗauko.
A hankali na kunna, zuciyata tana rayamin na kira Mahaifiyata ko zata jiƙaina a wannan karon ta ɗaga ta saurarenu.
Na jima da wayar a hannuna, wata zuciyar tana gargaɗina da kar na kirata, na bari sai na fara zuwa Makaranta, naga dagaske na canza tukunna.
Shawarar da ɗaya sashen na zuciyata ya ke ba ni na bi, don haka na mayar da wayar inda na ɗaukoshi, na dawo zauna haɗe da jingina da fuskar gadon da nake zaune a kai.
Tambayar da na yiwa kaina lokacin dana dawo Sashena daga wajen Baba na ƙara yiwa kaina,;
"Menene zai ba ni ƙwarin gwiwar cikawa Baba alƙawarin da na ɗaukar masa?"
"Sake maimata karanta labarin KUNDINKI da kanki, hakan zai farkar dake ya kuma baki ƙwarin gwiwar da kike nema Fatima"
Zuciyata ta bani amsa..
Kaina na girgiza alamar bazan iya ba.
"Zaki iya Fatima" zuciyata ta ƙarfafeni.
A take ƙafafuwana da jikina sukayi nauyi.
Kamar ba ni ce Fatima mai son karatu da rubuta duk abinda ya dameta a cikin littafi ba.
Daƙyar na ƙarfafi kaina na miƙe.
killataccen wajen da muke ajiye littattafai, da takardun makaranta tun daga kan na Nursery har zuwa sama na nufa.
Idanuwana da suka fara sauya kala zuwa Jajaye sosai, na farawa rarrabawa ina neman inda na ɓoyeshi.
Dogayen siraran yatsuna na kai kan inda nake kyautata zaton anan na ɓoyeshi.
A take na zaƙulo ƙaton littafi Mai tudu da tsahon da akayiwa gidan ɗan ƙarami kwaɗo. Ɗauke da rubutun maka a jikinsa an rubuta *KUNDINA*
Kamar ba zan taka ba, haka nake motsa ƙafafuna har na iso bakin gado na zauna ɗauke da littafin.
A gefena na ajjiyeshi, na matsa na buɗe drawer na ɗauko wani ɗan ƙaramin mabuɗi, na matsa na ɗauko littafin nasa mubuɗin na buɗe ɗan kwaɗon dake jiki.
A hankali na zame kwaɗon zuciyata na tsananta bugu, idona a runtse na buɗe littafin, shafin farko ya bayyana.....✍🏻