ALIYU HAYDAR

Chapter 4

by @nieemartullah

Wajajan qarfe goma da rabi na safe safiyyah ta dawo gida,tafiya take tana yan waqe waqen ta har ta wuce HAYDAR bata son yana xaune a parlour,kamar me jin tsoron wani abu ya bude baki yace sweetheart ina kika je haka da mamaki Ta juya dan ta ji muryar shi, shidinne zaune yana kallon ta hade rai tayi Tace inda ka aike ni kiyi haquri kin san bana san naga ranki ya baci Toh shikenan yanxu me ya dawo da kai ba tare da ka sanar da ni ba,dama ina ta kiran number princess ne bata dagawa shine na xo naga ko Lpian ta qlau dummmm taji xuciyar ta ta buga amma sai ta hade rai Tace kawai saboda ka xo kaga ko ayaanah tana Lpia shine ka kashe kudin jirgi ko Toh ka kyauta ayaanah kuma na kaita gurin family na zasuyi zumunci suna ta damu na akan bana kai masu ita ko dan naga ba ni na haife ta ba waya kuma tana nan abuja bata tafi da ita ba,hakan ma yayi dai dai sweetheart amma makaranta fah,na fahimci dai ka gama raina ni HAYDAR ni nake fada kana maida min da amsa kuma yanxu ka tashi ka koma gurin aiki bana son ka qara ko da minti talatin ne a garin nan fuuuuuuuuuuuuuuu ta wuce dakin ta kamar xata tashi sama sau dayawa idan safiyyah tana mashi rashin mutunci sai yaji kamar yayi ta dukan ta amma sai ya kasa ce mata komai tunawa yayi Tace kar ya qara minti talatin a garin miqewa yayi da 

sauri ya fita daga gidan yayi hanyar airport……….

Tayi nisa cikin tunani har bata lura da xuwan mom gurin ba sai da ta dafa kafadarta sannan ta juyo ta kalli mom cikin damuwa Tace Jay me yake damunki please ki fada man kin san bana son ganin ki cikin damuwa murmushi jay tayi wanda iya karsa leben ta Tace mom ba komai fah kawai ina tunanin duniya ne kin tabbata ta jinjina mata kai alamar tabbatarwa,if you say so,ni yanxu xan shiga ciki ina son na saka a gyara dakin hajiya mama Tace man tana hanya cikin qaramin lokaci mood dinta ya sauya zuwa farin ciki Tace don Allah dagaske,kiji man yarinya da qarya xanyi sai kuma ta hade rai Tace shine bata fada man xata xo ba ni nama bata da ita dariya mom tayi sosai ganin tilon yar tata har ta dawo yadda take so lively,kunfi kusa ke da ita idan Taxo sai ku qarata wucewa tayi domin saka yan aiki su gyara dakin da hajiya mama ke sauka duk lokacin da ta xiyarce su jay a hankali ta cigaba da cin abincin har ta gama a parlour ta samu ayaanah tana ta kallo,kashe kallon tayi ta riqe hannun ta suka je daki suka xauna ta fara koya mata karatu saboda jay macece mai tsauri akan tarbiyar yara bata yadda ace kullum yaro yana kallo ba idan yaro yayi kallo Toh sai yayi karatu suna karatu har aka kira sallan maghrib bayan sunyi sallah suka tafi dakin mom a nan take ganin iyayen kayan da mom ta siya ma ayaanah godiya tayi ma mom sosai sannan Tace ma ayaanah ma tayi ma mom godiya mom tace jay ki dauki kayan nan sai ki gyara mata gadon JAS tayi amfani da shi suna cikin hira ne suka ji muryar hajiya mama na ta surfa bal’ai a parlour ai da ubanki ne ummaru yaxo baxa ki barshi a parlour ba yana ta sallama ba kema bilkisu wannan figaggiyar yar taki ta koya maki fi’ili ko ai da ba haka kike ba wallahi idan kika yi wasa ummaru Xansa ya qara aure inga ta tsiya dariya mom tayi ta miqe xuwa parlour turo baki jay tayi sannan ta riqe hannun ayaanah suka fita parlour mom na qarasawa parlour ta durqusa har qasa ta gaida hajiya mama ciki ciki ta amsa sannan ta dora da fadin ai da uwarki ce baxa ki barta a parlour ba yana ta sallama kai Allah dai ya jiqan hajiya mero mutuniyar kirki ke kam dai bilkisu ban san inda kika samu wannan mugun halin ba alhaji aminu ma ba haka yake ba,mom dai kanta na qasa bata ce komai ba idan da sabo ai ta saba kuma dama ai duk wanda xai xauna da tsofaffi ai dole yayi haquri bare kuma ita da ba gida daya suke ba sai irin haka idan ta kawo masu ziyara,Jay da ta gaji da surutun Tace har kin fara ko daga xuwanki xaki fara takurawa mutane wallahi ni dama baki xo ba mom cikin bacin rai Tace jay bana san rashin kunya fah hajiya mama ta saki can kuma Ta fara tafa hannu tana salati,yanxu Bilkisu saboda rashin imani duka yarinyar nan nawa take da kike ta surfa mata masifa haka kamar kin samu qato dai dai ke,mutane yanxu duk ba tsoron Allah a ransu Kai turr da wannan xamani,a’uzubilahi billahi minash shaidanirrajim innalillahi wa’inna ilaihi raji’un me nake gani haka bilkisu badai haihuwa kika qara yi ba har yarinya ta girma bani da labari mom da kanta ke qasa ta dago ta kalli hajiya mama sannan ta ce muje ciki ki huta sai na miki bayani,yawwa shiyasa ni dama da kika ganni ai nama fi sonki akan shi ummarun saboda kin fishi sanin abinda ya kamata Allah dai yayi maki albarka ameen hajiya,bayan tafiyar su mom jay ta wuce ta dauki kayan kamar yadda mom tace haka aka yi dayan gadon dake gefen nata ta gyara sannan ta dora mata teddies dinta akai…………..

Sadiq ne xaune gefen Abban shi suna magana,Abbah dama magana nake so muyi idan ba damuwa jaridar hannun shi ya aje yace ina jin ka babana emm dama sai ya fara sosa qeya dama Abbah don Allah akwai wata yarinya ce da na gani nake son a tambayan man auran ta,murmushin manya yayi yace masha Allah babana yayi hankali yanxu xan kira sauran iyayen naka sai mu tsaida ranar da xamuje gidan su yarinyar,ita yarinyar yar ina ce,Abbah yarinyar ita ce MD a asibitin mu kuma babanta shine Air Marshal,Masha Allah yar gidan alhaji farouq ce kenen ai mun taba haduwa da shi a jirgi ya dawo daga Russia,in shaa Allah idan munyi shawarar lokacin da xamuje sai na sanar da kai ka fadawa ita yarinyar toh Abbah nagode Allah ya saka da alkhairi ameeen Allah yayi maka albarka……….

Mom ce xaune kan carpet din dake gefen gadon hajiya mama bayani take yi mata akan maganar ayaanah Allah sarki ta sha wahala yarinya qarama ace ana mata irin wannan zalincin Allah zai saka mata mom dai shiru tayi saboda kar ta qara fadin wata maganar hajiya mama ta qare mata tasss,cikin dabara tace hajiya mama bari na je naga me yan aikin nan suke yi kar suyi ba dai dai ba,eh gaskiya tashi Kije don mutane yanxu ba tsoron Allah a ransu sai su maka ba dai dai ba Toh a huta lafiya fita tayi ta wuce dakin ta,bangaren jaiyana kuma tana zaune a kan gadonta tana duba wasu takkadu na wurin aiki ayaanah kuma na ta wasa da sababbun kayan wasan da mom ta siya mata har bacci ya dauke ta wayar jay ce ta fara ringing,answering call din tayi ganin best friend din ta ke kira,hello Tasneem kina lafiya Lpia qlau Alhamdulillah JAY,ya yan gidan  duk Lpian su qlau wlh ya shirye shiryen azumi,Alhamdulillah wlh Masha Allah ki gaishe man da ummah kafin naxo,kamar da gaske ummah dai har ta gaji da complain ta qyale ki ai Allah dagaske xanxo kin san aiki ya man yawa ne shiyasa Tohm ina jiran xuwanki a haka suka yi sallama jay ta cigaba da abinda take yi…………….

Sai da taga fitar HAYDAR daga gidan sannan taji hankalin ta ya kwanta duk da asirin da take yi masa amma Tana matuqar tsoron shi saboda wani lokacin idan ya juya bata gane kan shi ma baki daya,kan gadon ta kwanta tana ta tunani nan wata xuciyar Tace mata meyasa baxa ta sa boka ya qara sa masa tsoron ta ba wata xuciyar kuma Tace mata ki saka ya manta yana da wata “ya a duniya da wannan shawarar ta amince baccin da bata samu yi ba daxu ta kwanta ta fara yi…….

Hajiya mama ce xaune tana ta fada ita daya yanxu bilkisu hana yarinyar nan tayi ta xo dakina ai shikenan taje don kanta ai ni ina da qafar xuwa,miqewa tayi tana tafiya a hankali saboda tsufa don a qalla hajiya mama za tayi shekara tamanin a duniya hutu ne da jin dadi ya ke boye shekarunta,har ta qarasa dakin jay sababi take ita daya,ko sallama bata yi ba ta dora yanxu ke wannan yarinya mai sunan aljanu me kike nufi da ni ne eyeee tun daxu kin barni a daki ni daya kamar wata mayya ai baxa ki yiwa uwar ki haka ba ko ita bilkisun ce ta hana ki xuwa daki na,kinga  tsohuwa Idan kina abin ki ki daina saka iyaye na ehe sallalahu sallalahu ni yanxu kike fadawa wannan maganar ai shikenan baxan qara xuwa dakin ki ba ta juya har ta kai qofar dakin ta dawo ni nasan tsakanin mu aka shiga Idan ba haka ba duk duniya wa kike da shi sama da ni ai ko ita bilkisun baxa ta fada man sonki ba lokacin da aka haife ki fah gaba daya na tattaro Kaya na dawo gidan ku da xama a lokacin ummaru dai gashi nan dai ba wani kudi ne da shi ba,haka kishiyoyi suka rinqa gulma ta wai na tare gidan Suruka babu ko kunya toh ni da Allah yaga zuciya ta taimako nake son yi ko kula su banyi ba har suka gaji suka daina,jay har ta gaji da jin wannan labarin saboda kullum sai hajiya mama ta bada labarin nan,bayan iyayen ta babu wanda take so kamar hajiya mama shiyasa ko sunyi rashin kirki da anjima xasu shirya kansu babu mai shiga fadan su saboda kai xaka ji kunya,guri hajiya mama ta nema ta zauna jay Tace ki bani labarin kano da abubuwan da suka faru hmmmmm ina fada miki Ina wata yarinya nan da aka kawo gefen gidana eh toh ina fada miki yanxu dai kinga shekarar ta uku a unguwan amma “ya “yan ta hudu duk shekara sai ta haihu wata shekara ma biyu ta Haifa, toh ni dai Wlh mijin tausayi yake bani dan yaro da shi ta tara mashi bataliya a gida cikin shekara uku wa yasan me xata yi xuwa shekara goma,ni dai ranar nan na kasa haquri ya fito xai fita na tare shi na mai Jaje bawan Allah murmushi kawai yayi yace ai babu komai,toh irin wannan Idan banyi masa jaje ba ai sai ya dauka tsohuwar banxa ce ni ya qullaceni,jay tunda hajiya mama ta fara magana take dariya har tana neman qware wa,A’a fah ya xaki maida ni mahaukaciya ina baki labari kina mun dariya jay da ta qara tuna labarin sai ta qara sa dariya hajiya mama ce ta miqe da gudu ta fita xuwa dakin mom har tana tuntube bilkisu toh ga yar ki cen dai ta haukace sai dariya take yi ita daya dan murmushi mom tayi  tace wani irin hauka kuma hajiya mama muje na gani suna xuwa dakin jay suka tarar har yanxu dariya take yi mom ce ta shiga hajiya mama cewa tayi baxa ta shiga ba kar taje a shaqe ta tambayar jay tayi meyasa take ta dariya a hankali ta daina dariyar ta bawa mom labarin da hajiya mama ta bata murmushi mom tayi tace yanxu hajiya mama ke meyasa xaki yiwa bawan Allah magana shida iyalinsa,a matsayi na na tsohowar arziqi naga ba daidai ba ai dole nayi magana Allah ya kiyaye Tace tare da miqewa tayi waje………….

Wuraren qarfe uku na rana safiyyah ta tashi daga bacci dama babu batun sallah a tsarinta sai lokacin da taga dama take yi parlour ta fito tana qwallawa barira kira,jiki na rawa barira ta fito daga dakin ta saboda ta san halin safiyyah,durqusawa tayi ta gaishe ko amsa bata bata ba Tace ina abinci,xare ido ta farayi saboda tasan a cikin littafin rashin mutum cin safiyyah babu babin da bata karanta mata ba cikin jin tsoron abinda xai biyo baya Tace hajiya jiya ke kika ce ke xaki fadi abinda xa’a gir..kafin ta rufe bakin ta taji saukar mari har biyu a quncinta saboda baki da hankali da ban fadi me xa’a dafa ba sai nace ki barni da yunwa ko ubanku ke kawo abincin ne ban sani ba barira bata ce komai ba sai haquri da tai ta bata Tace bari na hada maki yanxu in shaa Allah,hanyar kitchen ta wuce don hada mata abinci mai dan sauqi,cous-cous jollof ta hada mata wanda yaji hanta,gyada,carrot,green beans, da peas ……………………..