IZAYA

6

by @pherty001

IZAYA

©️Fertymerh Xarah 💞

6

Cike da murna CG ya shiga gida ya tarar da sauran ƴan uwa sa mata aka soma gaisawa tare da Allah ya sanya alheri, masu aikin gida sai faman hidima suke da baqi,

​ya dubi Hajiya salima cikin murmushi yana faɗin "sadaki yana gurin Alhaji Fu'ad, nasan zai shigo maki dashi sai ki bata, tukunna wai ina shalele ni fa bangan ta ba?

​Ta tabe baki kaɗan tace" na aika aka ce tana barci, har zuwa wannan lokacin bata tashi ba, jira nake na gama da baqin nan naje da kaina na tayar da ita wannan karon dukan ta zanyi",

​yace "ba sai kin je ba bari ni naje da kaina, akan me zaki dake ta saboda kawai bata tashi da wuri ba?

​Yana qoqari juyawa tace" ka barshi zanje na tayar da ita, idan kaje kuma bansan ranar fitowar ka ba zaka biye mata ne, dan Allah kaje gurin baƙin ka",

​yace "kimin alqawarin babu duka ko faɗa? Taja numfashi kaɗan tace shikenan naji".

​Cikin gentle anger irin na uwa mai tarbiya ta janye duvet daga jikinta tare da buga qafafuwanta, "NIHAL barci kike har yanzu baki tashi ba, gamu da baqi a gidan kuma saboda ke suka zo amma baki fito kin gaida su ba, anya kin yi sallah kuwa?

​Ta ƙarasa mgnr cikin bacin rai kamar zata kai mata duka saboda takaici, Hannu tasa tana murza idanuwanta, ta buɗe idanunta kaɗan, cikin calm voice ɗin ta tace "Mamee I’m sorry, I slept late wallahi bansan time ya tafi har haka ba”

​Hajiya salima taji fushi ta na sauka a hankali, tace" kin yi sallah? NIHAL ta gyada kai idanunta akan fuskarta tace "bayan nayi ne na kwanta ai, makara ma da nayi cos na kwanta late ne muna ta fira da friends yesterday night".

​Hajiya salima taja tsaki kaɗan tace “Late or not late, you should’ve respected the people that came for you, ga cousins naki are eager to see you, iyayen sa ma sun zo har suka tafi baki je kin gaida su ba, haka zaki je kina wannan shashanci a gidan miji?

​“Sorry mamee please don’t be angry, I promise it won’t happen again.” ta faɗa cikin gentle tone kamar wacce bata son hayaniya",

​Hajiya salima tace "kije kiyi wanka ki shirya su na jiran ki", ta gyada kai tana kallonta har ta juya ta fice, kafin ta mayar da hankali ga wayar ta da ta ganta tana haske,

​sunan da tagani yana yawo a screen ya sakata jan numfashi kaɗan kafin ta ɗauki wayar tana kallon screen kasancewar video call ne, ta lumshe idanuwanta, yayi murmushi kaɗan yana faɗin “Finally! You’re awake, tun ɗazu Ina kira baki ɗaga ba na kira Daddy na tambaye shi ko lafiya yace kina barci mummy zata zo ta tayar dake”.

​Ta buɗe idanunta a hankali, tace "yh am awake, ashe kaine ka saka aka katse min barcina mai daɗi?

​Yace" Allah yasa kina mafarkin muna tare da juna a..... ta katse shi, "kamar baka da abin fada kullum sai mu kasance da juna, so irritating", ta bata fuska kaɗan,

​yace "everything went perfect, su Abba sun zo sun tambaya an basu, I’m relieved now, At least it’s confirmed, we have only three months left and you’ll be mine completely, Idan bama irin wannan maganar wacce iri kike so muyi fisabilillah.”

​ta yatsina fuska kaɗan tace "enjoy your morning, Ina da guest yanxu na tashi daga barci, zan je nayi wanka".

​Yace "take care my love, zan shigo da dare, zamu fara planning akan bikin auren mu, kin ga is getting closer, 3 months Kamar gobe ne", ta gyada kai kaɗan kafin ta tsinke wayar,

​tashi tayi ta shiga bayi, ta jima sosai kafin ta fito, kai tsaye gaban dresser ta nufa ta zauna, ta shafa simple glam skinlike foundation, nude lip gloss, light eyeliner, nothing heavy.

​Tuni Hadiya ta fito mata da kayan da zata saka, tsadaddiyar atamfa, simple amma expensive.

​Jewelries ɗinta silver ne ƙanana ba wani ado mai yawa, bata ko tsaya breakfast ba tasan idan mahaifiyarta ta sake riskarta zata iya dukan ta cos ba lallabata take kamar abbanta ba,

​kai tsaye ta bawa Lawee umarni ta same ta sashen mummy da breakfast ɗin ta.

​Sanda ta nufi sashen Hajiya salima cike da baqi manya da yara mata sai maza cousins, ta saki fuska tana murmushi sosai, ta soma gaida su cike da girmamawa, ​wasu cousins suna tsokanar ta, tana ramawa wasu kuma tana murmushi kawai, ta jima sosai acikin su tare kafin ta fito tayi breakfast, zuwa wani lokaci kuma sai ga friends ɗin ta sun shigo.

​Yana zaune a tangamemen falon sa, akan Italian leather armchair, a gaban sa marble top table ne daya ɗora ƙafafunsa akai yana kaɗa su a hankali,

​Air purifier ɗin falon yana wani soft hum, yana ba da ƙamshin oud & bergamot, dake kashe jikin mai shaqa, idanunsa akan modern art pieces dake rataye a bangon falon,

​ya lumshe idanun cikin kulawa yace, "Idan jikin bai yi sauqi ba kada ki boye min umma, zan zo na kai ki wata asibiti daban, koma me nake anan bai kai ki muhimmanci ba kin sani".

​Tace "na sami sauqi sosai na gayamaka, mai martaba da kanshi yazo ya duba ni shima yayi farinciki da yanda na sami sauqi, gobe zasu bani discharge",

​yace "waye yake tare dake a asibitin? Kai tsaye tace" Diyana".

​Yace "why her, wannan yarinyar ta yaya zata iya kula dake, yaushe ma ta iya kula da kanta ballantana ke, meyasa Anna bata zo ta zauna dake ba?

​Tace" Eshraq na gayama observation ne kawai, Diyana tana qoqari akai na sosai, ba qaramin ciwo zai saka Anna zuwa ta zauna dani asibiti ba, bafa wani babban ciwo bane, and yarinyar nan is trying, yanda take qoqari a kaina na tabbata zata iya kulamin da kai".

​Ya yatsina fuska yana jin tsikar jikinsa yana tashi, fuskarsa ta sauya nan take zuwa bacin rai, tace "kayi shiru, lafiya?

​Yace" zamu yi mgn anjima", tace "tun da nayi mgn akan mace ko, dan Allah me yake damun ka, na tambaye ka ba sau adadi, ni mahaifiyar kace zan shiga damuwa sosai idan ka cigaba da zama a irin wannan yanayi na baka son kasancewa da mace, idan baka da lafiya lemme know pls Eshraq",

​yanda tayi mgnr cikin rawar murya kamar zata yi kuka ya saka shi sassautowa daga fushin da ya soma,

​yace "zan yi aure ummi, kin damu da yawa kin manta auren lokaci ne dashi?

​Tace" kai da baka kallon mata, baka zance akan su kuma baka so ayi maka yaushe zaka yi auren, idan ma baka da lfy ne kake boyewa zan gane domin zaa ɗaura maka aure da Diyana, ranar da kazo ƙasar nan a ranar zata tare, zan ma mai martaba mgn da kaina da zarar an sallame ni",

​cikin rawar murya yace "saboda me.. Why? ni nace maki babu wacce nake so ne, ummi kada kimin haka, zaki batawa yarinyar rayuwa cos bana son ta... ,

​ta katse shi " zaka so ta domin Diyana tana da kirki, tana da tarbiya da nutsuwa, kuma ga tsabta irin yanda kake so, and ita jinin sarautar khobar ce kamar kai".

​Yace "ummi dan Allah kiyi hakuri ki bar zancen, ni dai bana so, ki barni idan lokaci yayi zan yi auren at any time".

​Tace "idan kana so na sami kwanciyar hakkali, kayi aure Eshraq",

​cikin son katse zancen ganin zuciyarsa na zafi zafi da zancen auren nan da take masa, kai tsaye yace da ita "zan zo da matar, amma ki bar mgnr Diyana",

​kafin tayi magana ya tsinke wayar dai dai lokacin da aka buɗe sensor slide door, ya ɗaga idanunsa yana kallon masu shigowa, Rayhaan da Yusuf,

​a gajiye suka zauna bayan sun bashi hannu sun gaisa, ya zuba masu idanuwa yana mamakin yanayin su, "wannan gajiyar dake tare daku a ina kuka kwaso ta?

​Rayhaan yace" from office, ka manta yau Monday? Eshraq ya jinjina kansa batare da yayi magana ba,

​Yusuf yace "mun gama bincike akan CG fa", Eshraq ya ɗauki cup ɗinsa na black coffee, ya ɗan juya shi, yana kallon su da cold calmness. “Tell me.”

​Yusuf ya jingina gaba, voice ɗinsa a zurfi yace “CG is dangerous, he’s strict, he’s resourceful, he’s connected,abin da yake cewa Container ɗin mu ba zai sake zuwa Nigeria ba idan har muka cigaba da ɗauko cocaine, wannan ma da gaske yake bzai bayar ba, he’s that type of man, ni mamakin sa ma nake yi".

​Rayhaan yace “Yeah, nothing’s hidden a binciken da muka yi, We know his routines, his people, even how he handles his work, conflict, everything".

​Eshraq ya ɗan jinjina kai, ya murmusa cikin slight challenge in his eyes,

​Yusuf yace “Honestly Eshraq, CG is a tough man, Strict, very meticulous, da ƙyar ne ya bamu kayan mu".

​Eshraq ya kwantar da cup ɗin, yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kafin yace “And his weakness?”

​Rayhaan ya ɗan jinjina kai, kamar yana tattara kalmomin da zai yi amfani dasu yace “Mun gano it's his daughter (NIHAL).”

​Eshraq ya zuba masu idanu cikin neman qarin bayani, Yusuf yace “Yes. She’s everything to him. He shields her from the world. He’s overprotective beyond normal. And rumor says there’s a planned engagement baiko, actually with son of his childhood friend. The wedding is three months from now.”

​Murmushi Eshraq yayi yana faɗin "interesting" ya jingina Yana kallon su ɗaya bayan ɗaya kafin yace "let's kidnap her".

​A tsorace suke kallon sa, Rayhaan yace “What? Eshraq no, this is not a solution.”

​Yusuf yace “Yeah, absolutely not. Idan mun yi haka, CG will trace it straight to us. He has connections, he has security clearance. He can get us charged, arrested, finished!”

​Rayhaan yace “Ba zamu yi haka ba, It’s reckless, It’s suicidal.”

​Eshraq ya tashi tsaye yana kallon su, "idan anyi kidnap ɗin ta sai kawai yace mu ne, akan wane dalili, idan muka bar qasar da ita fa?

​Yusuf ya tashi yana faɗin" dole zai gane mune tun da zamu nemi container ɗin mu hannunsa kafin mu bashi yarsa, ka janye wannan mgnr kidnapping pls, we are not kidnappers Kuma bazamu fara akan wannan yarinyar ba, kada tsautsayi ya ja mu....

​Eshraq ya katse sa, “Then what is the solution?” Duk suka yi shiru na ƴan dakiku, kafin Yusuf ya ce cikin nutsuwa “Fake love.”

​cikin rashin fahimta Eshraq ke kallonsa "fake love Kamar ya, kuma da waye zaa yi?

​Kai tsaye Yusuf yace" fake love kai da yar gidan CG I mean you and h.... bai bari ya qarasa ba ya ɗauke sa da mari cikin bacin rai,

​nan take idanunsa suka sauya, dama ran nasa a bace yake da mgnr mahaifiyarsa, kuma a kanta kadai yake iya controlling temper ɗin shi akan mace,

​Yusuf ya dafe kuncinsa cikin mamaki, Rayhaan kuwa a tsorace ya tashi daga inda yake zaune duk suna kallon Eshraq da mamaki,

​Yusuf yace "ka mare ni? Cikin bacin rai Eshraq yace “You want me to get close to a woman?”

​shima Yusuf ransa a matuqar bace yace “Yes. It’s the only safe Ko kana so ko baka so in dai kana son wannan billions of naira,”

​Eshraq ya girgiza kansa Idanun sa sun yi ja, harshness ɗinsa ya fito baki ɗaya, “KADA KA SAKE YI MIN MAGANAR MATA!!!”

​jikinsa ya dauki kyarma, ya nuna Yusuf da yatsa "Do you hear me? If there’s one thing I despise more than betrayal, it is women, don’t ever suggest that again.”

​Sai a lokacin Rayhaan yayi magana, yace “Eshraq… calm down. But you know he’s right. That’s the only safe way, kidnapping will destroy us, Fake love is the only path that leaves no fingerprints.”

​Cikin bacin rai Yusuf ya dubi Rayhaan yace "dalla barshi, har zai ɗaga hannu ya mare ni dan kawai na gayamishi gsky, if not fake love menene mafita, ko cewa akayi dole sai ya so ta da gaske, darajar wannan yarinyar dai dai yake da darajar wannan container ɗin, idan har da gaske yana son 500billions ɗin sa dole sai kayii fake relationship da ita, ka shiga rayuwarta, ka janwo hankalinta ka yi manipulating ka sa ta fall for you, so that we get leverage then CG will return the container just to save her reputation and avoid scandal saboda kasan babu ta yanda mahaifin ta zai yarda ka aure ta kana wannan sana'ar da yake yaqi da mai yin ta a ƙasa.”

​yana gama fadar haka ya fice a fusacce, Rayhaan ya bi bayan shi cike da damuwa domin bashi hak'uri, Eshraq kuwa wani bacin rai yaji yana lullube shi again.

#IZAYA

#Pherty

#Nihal

#Tycoon

#Jibril

#CG BILAL

#Yusuf

#Rayhaan