IZAYA

7

by @pherty001

*IZAYA*

©️Fertymerh Xarah 💞

7

Washe gari haka ya tashi sukuku cike da damuwa da neman mafita tun da yake a rayuwa bai taba shiga damuwa irin wannan ba, bai taba sanin zafin rasa abu irin wannan ba.

​Babu abinda ya taba bashi wahala ko caja mashi kai irin container nan, tun a daren jiya yake tunanin mafita ya kasa samu kuma yaqi yarda da mgnr Yusuf.

​Ya lumshe idanunsa zuciyarsa na masa zafi, ya buga gabas da yamma ya kasa samun wata hanyar samun wannan container daga hannun mai taurin ran tsiyar nan.

​Da shi mugun mutum ne wanda bashi da imani tabbas zai iya kashe CG ko ya saka a kashe shi kuma ya tabbata waɗanda zai saka su kashe shi zasu iya aikin batare da an kama su ba.

​Matsalar ko kwaro bazai iya kashewa da gangan ba balle mutum ɗan adam mai daraja kuma mai iyali irin sa, yana ji wayar sa na ƙara bai duba ba.

​Da aka matsa da kiran ya ɗauki wayar, ganin sunan dake screen sai ya tattara hankalin sa sosai kan wayar, ɗaya daga cikin manyan mutanen dake son siyen kayan da suka maƙale a hannun CG, I mean abokan kasuwanci sa.

​Ya lumshe idanunsa a hankali kafin ya daga wayar, cikin calm voice dake nuna babu kuzari a tare dashi yace "Assalamu alaikum", ɗayan bangaren aka amsa kafin cikin girmamawa suka soma gaisawa da juna.

​Yace "Esh, Any update about the container, muna ta zuba idanuwa kullum ko zamu ga kaya sun sauka shiru kasan gurin ka kawai muke iya siya cikin kwanciyar hankali amma naga wannan karon kamar baka son siyarwa?"

​Eshraq yaja numfashi kaɗan kafin yace" anyi seizing container shiyasa har ynxu bata iso ba",....

​Cikin hanzari da tashin hankali mutumin yace" seizing kamar ya, waye ya karɓa?

​Eshraq yace "Comptroller Bilal, haka naji suna kiran sa, naje har office ɗinsa muka yi magana face to face, amma yaqi saurarena, har percentage nace zan bashi aciki, but he refused".

​Cikin kwantar da murya dake nuna tsantsar tashin hankali, mutumin yace "kuma shine tuntuni baka kira ka sanar damu ba, tukunna kasan waye CG kasan hatsari irin nasa da har zaka je ka same shi da kanka kuma ya barka, wannan mutumin bashi da sauqi akan gsky da bin doka a nigeria, bashi da sassauci kuma baya son sasanci, nayi mamaki da har ya tsaya ya kula ka".

​Eshraq ya yatsina fuska kaɗan, yace "that's the power of TYCOON, Ina da kuɗi kuma ina da girma a idon mutane, kasan yanda sunana yayi fice a qasar nan, mutane da yawa suna son ganina basu sami damar hakan ba, ciki kuwa har dashi, bai taba ganina ba sai a wannan karon, and he reject my offer, bazan iya sake zuwa gurin sa ko neman wata alfarma a gurin sa ba bayan tattakin da nayi har office ɗin sa ya watsamin ƙasa a ido kawai mu haqura da container ɗin ".

​Muryar mutumin ta canza gabaki ɗaya daga damuwa xuwa tsoro da fargaba sanin halin Eshraq" a bar container ɗin? Esh are you hearing yourself? We are loosing billions of naira And kana mgnr mu haqura, meyasa?

​Eshraq ya dafe goshinsa yace "shikenan I understand, amma ni for now bani da wata dabara, and I want to go back to Saudia Umma ba lfy, I don't have luxury to be stuck here endlessly."

​Duk suka yi shiru cikin tunani kafin mutumin cikin shigar rarrashi da kwantar da murya yace, Esh listen pls, try everything and get the container, you are the only one da zai Iya shawo kan wannan matsalar, zaka iya neman wata dabara mu sami container ɗin cos the money is huge, and the risk is bigger, don't give up on the container pls Esh ".

​Suka sake shiru ganin Eshraq ɗin bai yi magana ba sai ya cigaba da faɗin" in fact I will increase your sale, I will raise your share to 700 billions, just get the container and see nayi maka alqawari haka zamu siye ta zan ma ubangidana magana yanzu".

​Eshraq ya numfasa kaɗan, "Alright (Cikin seriousness), zan nemo hanyar".

​Ya kashe wayar a hankali cikin tunani, nan take idanunsa suka sauya suka qara qanqancewa, ba shiri ya danna call ɗin Yusuf, bugu ɗaya ya ɗauka da ƙyar yace "kana fushi dani?

​Yusuf ya numfasa kaɗan kafin yace" da bazan ɗauki wayar ba, I will ignore ", Eshraq ya lumshe idanunsa tare da shafa sumar kanshi, yace" call Rayhaan ku zo da gaggawa yanzu please", Yusuf yayi jim yana duba time, kafin yace "shikenan".

​Kusan 2hours da wayar su sai gasu sun iso, suka miqa masa hannu suka gaisa kafin su zauna, yace "na rasa mafita, and kuɗin sun qaru fiye da tunanin ku, ɗaya biyu ne, ko na nemi hanyar samun Container ɗin na cimma burina ko kuma na biya kuɗin container ɗin kuma nayi asarar maqudan kuɗi, cos I don't have that huge amount, cos 700billions zasu siye container ɗin kuma 60% ne fa, me kuke tunani a kuɗin container ɗin gabaki ɗaya tun da har suka matsa suna so harda qaramin wasu kudi akai?

​"like serious (Rayhan ya tambaya yana kallon Eshraq da mamaki) you mean 60% ne dama duk wannan kuɗin haka?

​Eshraq ya gyada kai yana kallon su, Rayhaan yace" lallai bazaka iya asarar kuɗin container ɗin ba, cos you will loose everything, all these luxury life you are living duk zaka qara darajarsu fiye da hakan",

​idanunsa masu rikitarwa ya zuba masu a karo na biyu, kafin yace "ko zamu tura a sace container ɗin?

​Yusuf ya kece da dariya, yace" kada kayi wannan mistake ɗin Esh cos zaa kama yaran ka duka, may be harda mu a nemo mu a haɗa damu, wannan ba mafita bace, container da ba'a san inda ya boye ta ba, Ina zaa je a ganta har a sace?, wannan mafitar da ta saka ka mare ni a jiya wlhy ita kaɗaice hanya mafi ɗorewa, use his daughter and get your container, shine kawai".

​Eshraq ya lumshe idanunsa, zuciyarsa na bugawa da qarfi da qarfi saboda tashin hankalin da yake ji a yanzu, ya buɗe idanunsa jawur kamar wanda zai yi kuka yana qara kallon Yusuf, yace "how do I approach her, ni da ban taba soyayya ba, ban taba zama da mace ba, ban taba magana mai tsayi da mace ba how do I confront her da fake love, a wannan fanni na yarda ni ba namiji bane domin bani da wannan jarumtar".

​Rayhaan yayi qasa da muryarsa, yace "sorry Esh, wannan kaɗai ce mafita, pretend to be her best man, Idan ta kamu sosai use her as the weapon",

​Eshraq ya yi shiru cikin tunani, yace "how old is she? Yusuf yace" Kamar 18yrs aka ce", ya ja qaramin tsaki, "and I hate childish, I want maturity",

​Rayhaan yayi murmushi yana faɗin "duk yanda take ba abin damuwa bane mu dai container kawai zaka kalla akan idanunta",

​Eshraq ya dube sa yace "bansan me zan ce ba, bansan yanda zan fara mata magana ba",

​Yusuf ya gyara zama yace "duk mu zamu yi wannan",

​Eshraq ya buɗe ido yana kallon su cikin mamaki yace "How?

​Yusuf yace" you will use Bluetooth, Idan kaje gurin ta koma menene zamu fada maka abinda zaka ce da kuma amsar da zaka bayar kafin kaje ka bayar da maza ta gane mu, mun san baka iya confronting mace shiyasa muka nemi wannan hanyar and it will surely work insha Allah ",

​sai a lokacin Eshraq yaja numfashi mai qarfi yana jin wani sassauci kaɗan a zuciyarsa, ya sani duk abinda zai fito bakin sa ba daga xuciyarsa bane daga bakin friends ɗin sa ne, idan hakane ya amince, ya jingina kansa yana kallon su in affirmation da cewa ya Amince da hakan.

​Eshraq shiru yayi cikin tunani a lokacin, yanda zai tsaya a gaban mace abinda bai taba ba a tsayin rayuwarsa, ta yaya ma zai isa gare ta, da wace jarumta, da wane ido zai kalle ta kuma da wane baki zai mata magana har ya furta yana son ta?

​Rayhaan ya taba hannunsa kaɗan yana faɗin "is not something big Eshraq, kasa a ranka duk abinda zaka faɗa is not you yin kan mu ne nida Yusuf, kuma ai ba daga zuwa kawai zaka ce I love you ba, maza masu aji basa furta I love you a fatar baki, sai dai idanu da gangar jikin su ta nuna hakan, as far as you don't love her babu wani abu dake tare da kai da zai nuna hakan, just pretend we only want her to fall for you then we use her to get what we want, kagane?

​Eshraq ya jinjina kansa a hannkali, amma har lokacin jikinsa a sanyaye, babu abinda ya taba bashi tsoro kamar wannan da zai hadu da mace.

​Yusuf yace "gobe zaku fara haduwa da ita a millennium pack, mun sami every info about her, can ne take xuwa a kowane sati, tare da friends ɗin ta wani lokacin ita kaɗai, ance tana son zuwa gurin dan kawai ta zauna tana kallon mutane it makes her happy shiyasa a sati ta zabi rana biyu da take zuwa hutawa acan, kuma ranar anyi sa'a rana ɗaya tazo a gobe we don't have to wait long, gobe zamu zo mu dauke ka mu tafi, zamu hada conference call, koma menene mu zamu faɗa maka duk abinda zaka gayamata, please Eshraq".

​Yace "shikenan, Allah ya kai mu", suka amsa da amin kafin su cigaba da hirar su.

#IZAYA

#Pherty

#Nihal

#Tycoon

#Jibril

#CG BILAL

#Yusuf

#Rayhaan