8
by @pherty001
Washe gari....
Ta shirya ta fito bayan ta sanar da mahaifiyarta, ta nufi harabar gidan tana sanye da custom made silk blazer mai launin navy blue, paired da tapered trousers na cream satin, qafafun ta sanye da stiletto heels ɗinta na Gianvito Rossi, launin midnight blue da gold accents, suna taka marbles cikin ɗaukar hankali, duk inda ta bi sai an kalle ta saboda yanayin tafiyar ta da takalmin cikin jan hankali.
Hannunta ɗaya ɗauke da custom Vertu phone mai launin platinum da ƙaramin ruby a gefen logo, ɗayan kuma ɗauke da Chanel classic flap bag mai launin ivory, duk sun dace da kayan jikinta, kuma sun fito da ita sosai cos ba qaramin kyau tayi ba.
Kai tsaye aka buɗe mata motar ta ƙirar Rolls-Royce Ghost Extended Wheelbase, mai launi Pearl White da chrome accents, babu Bata lokaci ta shiga batare da ta saurari gaisuwar da ake mata ba.
Guards ɗinta uku, sanye da black tailored suits da sunglasses, suka nufi ɗaya motar suka bi bayan motar da take ciki, sun fara tafiya cikin quiet roads zuwa Millennium Park, basu dauki dogon lokaci ba suka isa Millennium Park.
Motar ta tsaya a private parking zone kusa da quiet section da take so. Aka buɗe Mata motar ta fito cikin takunta na izza zuwa gurin da ta saba zama duk sanda tazo, quite corner da take samun peace da kuma kallon kowa a gurin abinda yake matuqar burge ta kenan, duk wani motsin ta yana kan idon su.
Tayi kusan one hour da zuwa kafin motar su TYCOON ta iso gurin, Yusuf ya nuna masa inda take zaune yana faɗin "tabbas itace a gurin a zaune, cos wadannan guards ɗin saboda ita suke tsaro, and look at the plate number of the cars NB".
Eshraq yayi shiru, kafin ya fito daga motar, Yusuf da Rayhaan suka bishi da idanu suna qara boye kansu acikin motar kada a hango su a ciki.
Yana sanye da custom tailored midnight black suit na Brioni, silk shirt mai launin ivory, cufflinks na platinum da ƙaramin diamond inset, leather Oxford shoes masu sheƙi, da tie mai subtle pattern mai haɗe da gold accents.
Bluetooth ɗinsa yana maqale a kunnen sa, kai tsaye ya nufi gurin da take zaune, guards ɗin na ganin haka su ka taso da sauri suka tare sa, kowane fuskarsa a murtuqe cikin seriousness duk da wani kwarjini da suka gani a tare dashi.
Ya bata fuska yana jin wani bacin rai domin guards basu taba tare sa haka ba, ganin haka Rayhaan yace in a low voice da Eshraq kaɗai ke jin sa, "please control yourself, fatan mu ka sami haduwa da ita a yau, if not bamu san ranar da zamu sake samun wannan damar ba tunda bata tare da qawayen ta yau".
Eshraq ya ja numfashi kaɗan, yace "I want to meet her", ɗaya daga cikin guards ɗin yace "who are you, did you have any appointment?
Eshraq ya girgiza kansa, guard ɗin yace" then get out bazaka ganta ba", Eshraq yace "just 5 minutes bazan jima ba, and banzo dan na cutar da ita or to disturb her.....
Ya katse sa cikin tsawa, " I say get out please, bazaka ganta ba", ya qarasa maganar tare da ɗora hannunsa a ƙirjin Eshraq yana qoqari turesa.
Bai janye hannunsa ba yaji saukar mari a kuncin sa wanda ya gigita sauran guards ɗin guda biyu suka qaraso da sauri, hankalin Yusuf da Rayhaan ya tashi matuqar gashi basu zo da nasu guards ba kada wani abu ya sami Eshraq saboda zafin ransa.
Shima guard ɗin me zai kai shi taba jikin Eshraq, suna kokarin balle murfin motar su fito domin bashi agaji suka ga ya nuna sauran da yatsa cikin tsanani bacin rai kwance a fuskar sa, yace “Anyone among you who dares to touch me again the way he just did I swear, I’ll make sure his hand is cut off today.”
Wanda aka mara ya ɗaga murya cikin bacin rai "idan aka taba ka me zaka yi, cutt off my hand lemme see", Eshraq ya dube sa yace "then try it again, Ina ji marin bai gama ratsa jikin ka ba".
Hayaniyar su ya saka ta cira kai daga video call da take da Ruma tana kallon su, bata iya hango ko da waye suke faɗa amma ta san something wrong is going on yanda taga guards ɗinta suna gyara guns dake hannunsu like they want to shoot.
Da hannu tayi wa ɗaya daga cikin su alamar yazo, da gudu kuwa ya qarasa inda take, tace "hayaniyar me kuke yi, and who do you want to shoot?
Cikin girmamawa yace" Hajiya wani ne yazo ya gan ki muka hana sa zuwa shine ya mari Lizby " ta buɗe idanu cikin mamaki tace" like serious, bai ji tsoron ganin ku ko bindigar hannun ku ba har ya iya marin ɗaya daga cikin ku, waye shi?
Yace "nima ban sani ba, shi din ba qaramin mutum bane daga kallo ɗaya Balarabe ne", ta sauke numfashi kaɗan tace "allow him to come" yace " angama" ta cigaba da video call ɗin ta.
Yana zuwa ya sanar dasu tace a barshi yazo, Eshraq ya dube su da idanunsa dake nuna gargadi gare su, kafin ya daidaita nutsuwar sa ya nufe ta, Yusuf da Rayhaan suka sauke numfashi kusan lokaci ɗaya.
Tun kafin ya qaraso ƙamshin turaren sa na Dior oud ya ziyarci hancin ta, tayi saurin cira kai tana kallonsa, idanunsu suka sarqe dana juna, lokaci ɗaya taji wata irin fargaba ta ziyarce ta.
Ta kafe shi da manyan idanuwanta tana kallon yanda yake tafiya cikin izza, yana zuwa dab da ita ta kashe wayar da take tare da qoqari dai dai ta nutsuwar ta.
Daga can Yusuf yace "kayi mata sallama and ka nemi izinin zama in a stylish way", Cikin dakewa da son danne abin dake taso masa a qirji na baqin ciki haduwa da ita yace "Salam, can I have a seat?
Yusuf ya dafe goshin sa," oh not like this", karo na biyu ta sake cira kai tana kallon sa a inda yake tsaye, yayi mata kwarjini sosai da ta kasa yi masa musu, abinda bata taba yi ba, bawa stranger daga waje izinin zama a kusa da ita bayan Jibril kawai.
Da hannu ta nuna masa inda zai zauna batare da tayi magana ba, babu musu ya zauna har lokacin idanunsa akan ta kamar ya rufe ta da duka, yanda yake ji ma a haife zai haifi wannan yarinyar.
Yusuf yace "introduce yourself to her". yayi jim kafin ya ɗauke idanun sa akan ta yace "Sunana Eshraq Qumair...... yayi jim cikin tunani.
(Rayhaan yace, kace ka jima kana ganin ta a gurin..... Yusuf ya katse sa," a'a kada yace hakan", sai suka dauki rigima", Eshraq ya cire Bluetooth ɗin daga kunnen sa kaɗan tare da runtse idanunsa "calm down pls" yayi mgnr in a low voice da ya saka ta sake kallon sa ba shiri.
Dai dai lokacin ya buɗe idanunsa, ya mayar da Bluetooth ɗin yana qago murmushi yaqe, "sorry na amsa waya ne", har lokacin bata yi magana ba, yace "can we be friends?
Ta girgiza kanta da sauri, ya buɗe idanunsa kaɗan har bai san sanda yace" Why? batare da ya jira su Yusuf ba, cikin calmness muryar ta tace "I don't make friends with boys", bashi ba ko su Yusuf sai da suka ji muryar ta har cikin ransu.
Ya gyara zaman sa yana fuskantar ta, yace "you only want to marry them? tayi murmushi a wannan karon tana kallon wani guu kafin tace" already I have choose him and I love him".
Yayi shiru cikin rasa abin faɗa, yaji Rayhaan yace "tell her kai masoyinta ne tunda jimawa ka dade kana bibiyar ta, ko engagement ɗin da tayi kasan dashi wannan dalilin ya saka kayi approaching ɗin ta domin kana matukar son ta, and dan tayi engage da wani that doesn't mean shine mijinta".
Ko da Eshraq yayi mata wannan maganar, murmushi ta sake yi a karo na biyu har lokacin bata yarda sun sake hada ido ba saboda idanunsa dake kassara jikinta a duk lokacin da ta kalli cikin su, abinda take ji akan sa bata taba jinsa a tare da kowa ba.
Tace " Am engage already, bazan iya cin amana ko yaudarar sa ba cos I don't want to fall too, yana matuqar sona a yanda nake and ya shirya zama dani da dukkan sharuɗɗan da na gindaya masa", yace "tell me what's that?
Tace" our secret, baka buqatar sanin hakan", Yusuf yayi caraf yace "tell her, you are ready to do more than him? Eshraq ya faɗa cikin takaicin su.
Tace" wannan sirrin mu ne bazan faɗa ba, you are like a stranger to me, even my friends bazan iya faɗa masu sirrin dake tsakani na da Jibril ba",.
Eshraq yayi shiru, Rayhaan yace "kace ta baka lokacin ta and ka mata alqawarin bata kulawa da nuna mata kauna fiye da Jibril wanda da kanta zata so kasancewa da kai" Eshraq ya runtse idanunsa cikin takaici, yayi maganar batare da ya dube ta ba.
Murmushi ta sake yi, tana son juyowa ta dube shi tana jin tsoro, ta cira kanta sama kaɗan har lokacin da murmushi a fuskarta, tace "what do you do for a living?
Yayi Jim, daga can Yusuf ya dubi Rayhaan kafin kusan a tare su ce" business ", Eshraq yace" business ", tace" business.... sai kuma ta tabe baki, bata qara magana ba, yace "bakya son ɗan kasuwa", tace " ni ina son wanda nake so ko waye shi, I don't care da kuɗin shi".
Yayi caraf yace "ballantana ni bani da kuɗin ma, am mummy's boy", ta juyo tana kallon sa, idanunta akan pink lips ɗin sa, suna haɗa ido tayi saurin dauke kanta tana jin numfashi ta na neman ɗauke wa, gabanta na cigaba da faduwa.
Suka yi shiru na ɗan wani lokaci, daga can Yusuf yace "ask for her digit, Sai kazo mu tafi". ya bata wayar sa ƙarama alamar ta saka number ta, ta tsurawa hannunsa ido batare da ta karbi wayar ba, hasken fatar sa mai ɗaukar ido, hasken da kallo ɗaya zaka masa ka gane arab ne.
Ya juya wayar cikin tsokana yace "kin ga wayar qarama ko, that's my friend phone, nawa ma bai yi tsadar wannan ba". tace "then meyasa ka karbi wayar friend ɗin ka", kai tsaye yace "to impress you", ta girgiza kanta kaɗan, "ƙarya bata impressing ɗina, I will love who you are.....
Ya katse ta" kina sona? Kai tsaye tace "nop", ya sauke numfashi kaɗan, ta karbi wayar ta saka number tana faɗin "count yourself among the luckiest man on earth for having my number kai tsaye haka kuma a rana ta farko da haduwar mu", yace "Allah ko? ta gyada kai, yace" kema count yourself among the luckiest woman on earth ".
Cikin mamaki tace" meyasa? Rayhaan yace "kece mace ta farko dana taba tsayuwa da ita har nayi mata magana" (Eshraq ya maimaita mata) ta sake kallonsa fuskarta dauke da tsanani mamaki, tace "ni? Tana nuna kanta.
Ya gyada kansa cikin tabbatarwa, tace " don't you have a girlfriend? ya girgiza kansa, Yusuf yace tell her "ban taba ƙawa mace ba, ban taba soyayya ba sai akan ki dana soma yanzu", (Eshraq ya maimaita) taji wani iri a jikinta, duk da har lokacin ta kasa boye mamakin ta.
Tace "to baka son mata ne? Yace" ban sami wacce nake so ba sai dana fara ganin ki", tace "are you serious? Yusuf yayi magana," kace very serious" Eshraq ya faɗa cikin qaguwa, tayi shiru cikin tunani.
Kai tsaye ya tura number zuwa ga wayar Yusuf, nan take Yusuf yayi dialing ya kira, ta dube shi tana faɗin "your number? Ya gyada kansa, ta tashi, shima ya tashi yana faɗin " duk na takura ki ko? ta girgiza kanta tana faɗin "np lokacin tafiyata yayi".
Yusuf yace "sai kuma yaushe zamu haɗu? Eshraq ya faɗa yana kallonta, ta soma tafiya tana faɗin" I will let you know ", tana isa motar ta, guards suka buɗe mata da sauri, Eshraq har zai fara tafiya.
Rayhaan yace" ka jira ta wuce kada kayi gaggawa hakan zai nuna mata da gaske kana son ta", Eshraq ya harari motar da suke ciki kafin ya ja guntun tsaki, dai dai lokacin da motar ta tazo wucewa ta gaban sa, ta sauke glass kaɗan tana kallonsa.
Suna haɗa ido sai kuma ta saukar masa lallausan murmushi tare da ɗaga masa hannunta, (ka ɗaga naka mana, Rayhaan ya faɗa cikin zafi), ba shiri ya soma waving hannunsa shima har suka bacewa ganin sa, kafin ya juyo da kallonsa ga hannunsa cikin takaici.
Ya furzar da iska cikin takaicin abinda yayi yau wanda ko a mafarki bai taba tunanin zai yi hakan ba, Yusuf da Rayhaan suka fito daga mota suna dariya sosai har da riqe ciki, yana tsaye yana kallon su cikin takaici.
Rayhaan yace "wlhy she can't reject handsome man kamar ka, I swear she will fall for you, kaga yanda take kallon ka kuwa", Yusuf yayi caraf yace "kuma kun yi matuqar dacewa da juna I swear".
Ya soma tafiya cikin takaicin su batare da yayi magana ba, Bluetooth dake maqale a kunnen sa ya cire tare da jefarwa, Yusuf yaje ya ɗauka suka shiga mota, har suka isa gida baiyi magana ba saboda yanda zuciyarsa ke ƙuna.
#IZAYA
#Pherty
#Nihal
#Tycoon
#Jibril
#CG BILAL
#Yusuf
#Rayhaan