9
by @pherty001
Yinin ranar bayan ta dawo gida sukuku tayi shi cike da tunani, abinda bata taba yi akan wani namiji ba, Jibril ma bata taba bata lokaci akan tunanin sa ba ballantana sauran masoyan ta.
Meyasa ya tsaya mata a rai, meyasa tunanin sa ke neman hanata sukuni, tayi tsaki yafi a qirga, sai ga idanunta sun yi rau rau kamar zata yi kuka.
Dai dai lokacin aka turo qofar ɗakin ta, Lawee ce, da sauri taje gaban gadonta tare da kai gwiwowinta kasa cikin girmamawa, tace "Hajiya tace kizo yanzu".
Batare da ta dube ta ba ta gyada kai, Lawee ta fice da sauri, ta dauki dogon lokaci cikin tunani kafin ta sauko jiki a sanyaye ta nufi bangare Hajiya Salima.
Hajiya ta zuba mata idanu tana kallon yanayin ta, yanda ta san NIHAL da rashin nutsuwa abin ya bata mamaki, kafin NIHAL ta zauna taji Hajiya Salima na faɗin "baki da lafiya ne?
Tayi saurin girgiza kanta kafin ta zauna kusa da ita, tace" then meke damun ki naga duk kin yi sanyi", ta dubi mahaifiyarta tare da shagwabe fuskarta tace "ba komai".
Hajiya ta tabe bakin ta tare da faɗin "idan tayi wari maji, nasan Idan mahaifin ki yazo shi da gudu zaki gayamasa ko menene batare da ya tambaya ba", NIHAL bata ce komai ba sai kallon ta take.
Ta miqa mata wayar ta tana faɗin "duba kiga designers ɗinnan, sun iya kayan amare sosai daga Thailand suke, ko zamu je can tare acikin satin nan?
NIHAL ta yatsina fuska kadan kafin ta karɓa tana kallo, sai da ta gama ta miqa mata wayar tana faɗin " sun yi kyau Mamee, ni ba sai naje ba, ke kaɗai ma zaki iya zuwa ko kawai ayi order, ki tura min duka sai na zaba wanda nake so aciki".
Hajiya salima tayi murmushi cikin farinciki cos ba komai take so wanda NIHAL ke so ba sai wannan karon, shima ɗin bata san dan tana cikin damuwa bane, kafin Hajiya tayi magana ta juya ta fice.
Ta bita da kallo cikin mamaki tabbas akwai abinda yake damun NIHAL, tana shiga bedroom ɗinta wayar ta na soma ringing, tunanin ta ko su Rumah ne, sai taga baƙuwar number.
Kuma ta tabbata wannan number itace TYCOON ya kira ta da ita a daxu daya saka number ta a wayar sa, gabanta ya soma faduwa, gab da wayar zata tsinke ta ɗauka.
Yusuf dake maqale da wayar yayi ajiyar zuciya kaɗan yace "ranki shi daɗe, wannan kira shine na uku kafin ki ɗaga kin tayar da hankalina sosai".
Ta cira wayar daga kunnen ta tana sake kallon number, kamar ba muryar da taji a daxu ba, waccan tafi nutsuwa da zama calm kuma waccan muryar kowane kalma yana fita cikin izza ba kamar wannan ba, tace "who are you?
Yusuf yaji yana neman nutsuwar sa, suka hada ido da TYCOON dake sauraren su yana kallo, da yake ya saka wayar a hands-free, Yusuf ya gyara murya cikin son kwaikwayon Eshraq yace" Ashe har yanzu baki bani matsayin ko girman dabino a zuciyar ki ba tun da har kike tambayar ko waye".
Tayi shiru batare da tayi magana ba, ya cigaba da faɗin "tun da nadawo gida nake tunanin ki, komai na kasa aiwatar wa sai tunanin ki, Ina jin tsoro ranar da zan rasa ki, ranar da zaki auri wancan da kike so, wallahi zan iya rasa rayuwa ta saboda ke.
Bugun zuciyarta ya tsananta, kamar ta tambaye shi meyasa yake son ta, ko kuma yaushe har ya san ta, ya fara son ta, kamar bazata yi magana ba, tace "har yanzu baka mayar da wayar hannun abokin ka ba?
Hankalin sa ya tashi, ya dubi Eshraq da shima shi yake kallo, Yusuf yace " mayarwa fa? Tace "ɗazu kace wayar abokin ka ce a hannun ka?
Yace " oh wannan ai karama ce a hannuna, Ina dawowa na bashi wayar shiyasa nake tunanin wace wayar kike magana", tayi shiru a ranta tana tunanin may be saboda qaramar wayar ce ta sauya muryarsa".
Yace "ina so na sake ganin ki", tace "not now", yace "when? Tayi jim kafin tace " I will let you know, Ina so na huta yanxu".
Yace "shikenan take care, sai anjima", batare da tayi magana ba ta tsinke wayar, Yusuf yaja dogon numfashi da ƙyar yana kallon Eshraq.
Yace "may be ta gane ba kai bane shiyasa tayi cutting conversation ɗin". Eshraq yayi shiru kaɗan kafin yace "zata saba da muryar ka with time, cos ni bazan iya bata lokacina waya da ita ba gsky I can't, ko haduwa ta da ita har yanxu xuciyata xafi take min da raɗaɗi".
Yusuf yayi murmushi kaɗan yace "zaka manta da wannan zafin ranar da duk ka sami container ɗin ka saboda ita, insha Allah I will make her fall for you, I will be disturbing her with calls and messages".
Eshraq bai ce komai ba ya cigaba da kallon sa, a ransa yace ɗan wahala. Tun daga lokacin kullum shi yake tayar da ita da asuba da zafafan kalamai masu ratsa zuciya akan tayi sallah.
Messages kala kala haka ma call tun bata sakin jiki dashi har ta soma sabawa dashi, wani lokacin ma ita take kiran shi da kanta, Eshraq yana gefe yana kallon su, wani lokacin ma sai yayi tunanin anya ba da gaske Yusuf ya kamu da son yarinyar ba kuwa? Sun shaqu a waya cikin kwana biyar tamkar wadanda suka shekara tare.
Yau ce ranar da zasu sake haduwa a karo na biyu, ranar zuwa millennium ko da friends ɗin ta suka yi mgn zasu zo suje tare sai ta nuna masu a'a, ita kaɗai take son zuwa.
Bayan ta gama shirin ta sai ta tsaya gaban madubi tana kallon kanta, karo na farko a rayuwarta da taji tana son tayi kyau dan ta burge wani, ta qara kallon kanta, tana sanye da white applique lace mai ratsin red, babu makeup a fuskarta dama bata fiye yi ba.
Kallon ta Hajiya salima tayi lokacin da taji takun takalmin ta tana shigowa, wani boyayyan annuri ne a fuskarta wanda ya kasa boyuwa, tace "Ina zaki je? Kai tsaye tace da ita," millennium park".
Salima tayi shiru, NIHAL ta soma tafiya tana faɗin "sai na dawo", wannan karon ko da suka zo gurin tuni Yusuf da Rayhaan sun ajiye Eshraq sun je nesa dasu kaɗan sun yi parking inda zasu din ga hango su.
Tana ganin sa sai da ta saki ajiyar zuciya, guards ɗin ta suka fita da sauri suje su ga waye ya zauna a gurin da gimbiyarsu take zama, sai suka ji tace "ku barshi".
Tana nufar gurin yana juyowa, takaicin kansa yaji da yasan zai ganta da bazai juyo ba, ya qago murmushi da iya labbansa yana kallon ta, a yau sai ta tsinci kanta da matsinanciyar kunyar sa, saboda irin kalaman da yake kashe ta dasu a waya.
Ta sami guri ta zauna bayan sun gaisa, yace "na ɗauka baza ki zo ba", tayi far da ido tana kallonsa, idanunta suka sauka akan abinda ke qara burge ta da shi, pink lips ɗin sa, ta kau da kanta da sauri tana murmushi.
Yusuf yace "tell her you miss her a lot", Eshraq yayi shiru cikin tunani yanda kalmar zata fito bakin sa, Rayhaan ya kai hannu bakinsa yana dariya sannu sannu yasan da ƙyar Eshraq ɗin ya faɗi haka.
Ga mamakin sa sai yaji yace "Nayi kewar ki", murmushi tayi a karo na biyu, tana jin wani sonsa na shiga kusurwa kusurwa na zuciyarta, kai tsaye tace da shi, "nima nayi kewar ka sosai fiye da tunanin ka".
Ya buɗe idanunsa a hannkali cikin mamakin ta, Yusuf yace "tell her zaka bar ƙasar cos bazaka jure ganin ta auri wanin ka ba, zaka je Saudia inda mahaifiyar ka Sai bayan auren ta may be ka dawo".
Da Eshraq ya faɗi haka, sai ta tsayar da komai nata tana kallon sa kai tsaye, tace "you mean all the care, messages, phones da muke yi kana gayamin how you love me ashe zaka iya haqura dani, kazo ne kawai dan mu saba na wani lokaci kaje ka barni?
Yusuf da Rayhaan suka kece da dariya cikin tsananin farinciki, daga yanda take magana zaka fahimci bitterness a kalamanta, da gaske tana son Eshraq.
Eshraq yayi shiru yana sauraren wace amsa zai bayar amma Yusuf ɗin sai dariya yake shi da Rayhaan, ya kasa ɗaga ido ya dube ta saboda yanda ta kafe shi da idanuwanta tana jiran me zai ce.
Cikin kiɗimewa yace "a'a ni ban shigo rayuwar ki haka kawai dan na tafi na barki na wani lokaci ba, kin gayamin ranar da muka soma magana bakya so ki yaudari kowa saboda kada a yaudare ki, kina da wanda kike so kuma iyayen ki sun amince ki aure shi".
Ta ja numfashi kaɗan tana dauke kanta gefe, "dama shi zabin mahaifina ne, and Daddy zai iya min duk abinda nake so a rayuwa, idan nace bana son Jibril bazai min dole ba".
Eshraq yaji wani sanyi a ransa yana ji kamar har ya karbi container ɗin ma, yaji wani ƙwarin gwiwa sosai.
Ya cire Bluetooth ɗin kunnen sa dan ya batawa su Yusuf rai yanda suke dariya ya katse connection ɗin ya fuskance ta, "just tell me how your Dad zai amince to cut off your engagement bayan ba qananun mutane suka zo neman auren ki kuma ya bayar ba, ina ce har sadaki an biya?
Tace" wannan ba abin damuwa bane, Daddy bazai min dole ba, zai kira su ko yaje da kansa ya basu hak'uri matuqar nace bana son sa".
Yace "amma ina jin tsoron mahaifin ki kada ya tsaneni saboda na zama silla raba ki da wanda kike so, and am not that wealthy man irin Jibril, ni ummy's Boy ne, ita take min komai", ya qarasa maganar cikin murmushin shaqiyanci domin gwada yanayin ta.
Tace "Daddy zai iya baka aiki babba since you are educated and ko gidan da zamu zauna zai iya baka, ni kaɗai ce ya haifa a duniya, that's why yake matuqar sona kuma yake min duk abinda nake so".
Eshraq ya jinjina kansa a hankali, yayi jim kaɗan kafin yace "shikenan idan kin je ki masa mgn ina so nasan matsayina, idan ya karɓe ni na sanar da mahaifiyata".
Tace "kada ka yaudare ni ko kaci amana ta, saboda zuciyata ta gama aminta da kai, idan kaci amana ta..... sai kuma tayi shiru.
Yayi jim yana kallon ta, ta ɗauke kanta gefe a hankali tace" bazan taba yafe maka ba", ya gimtse dariyar dake son taso masa, dan bata yafe masa ba sai me, wannan tsakanin ta da Yusuf ne dashi take sosai, yace "bana fatan hakan ko a mafarki".
Tace "ina da ƙa'idoji a auren, idan ka amince zan aure ka, kuma kome kake so zan saka Daddy yayi maka", ya zuba mata idanunsa wannan karon yana mata kallon mamaki kafin yace "ina jin ki".
Tace " yara biyu kawai zan haifa and I will not breastfeed them, again bazaka mayar dani sex machine ba".
Bai san sanda ya tallabe kumatunsa da hannuwa sa ba saboda tsananin mamaki, yana kallon ta head to toe, yarinya ƙarama ke mgnr sex, what did she know about sex?
Jin yayi shiru tasan tunani yake, ta kasa ɗago kai ta kallesa tana tsoron kada yaqi yarda kamar yanda Jibril yake gudun zuciyarta akan kome tace.
Jin yayi shiru na tsawon wani lokaci bai ce komai ba, cikin rawar murya tace "we can cuddle na yarda da wannan", kamar ya hau ta da duka yake ji, saboda baqin ciki.
Fisabilillah duk manyan matan dake son sa, masu kyau da diri, cikakkun mata ya rasa wacce zai nema sai wannan abar, me ma take dashi? Me ta sani a abinda take magana, ko dai ko dai ita da Jibril.....
Sai yayi shiru baya son zargi a zuciyarsa amma Sam yarinyar bata da kamun kai tun da har zata iya faɗa masa wannan magana.
Ganin yaqi magana har lokacin sai ta bata rai, tana ƙoƙarin ɗaukar handbag ɗin ta taji yace "na yarda", ta dube shi da manyan idanunta, bacin rai kwance a kyakkyawar fuskarsa, wanda a tunanin ta saboda ta hana masa sex ne bata san tsabar haushin tane ya cika sa ba.
Taja numfashi kaɗan tasan is not easy for men's but with time zai saba har abin bazai dame sa ba, tace "am sorry", bai ce komai ba har lokacin, itama tayi shiru cike da fargaba bata ga wani abu acikin wannan mgnr da tayi ba a yanda tasan aure ba bauta bane, is all about love, care, and sacrifices.
Sai da yayi controlling kansa sosai yaja numfashi kaɗan yace "let's go". A raunane ta dube shi "kana fushi? Yace" no, duk abinda kike so shi zan yi kada ki damu".
Ta tashi suka soma tafiya har wajen motar ta, da sauri guards ɗin suka buɗe mata ta shiga, ta juya tana kallon shi, ya qago murmushin yaqe da Iya labbansa sanin duk abinda zai yana yi akan container ɗin sa, ya ɗaga mata hannu har suka bar gurin.
Kafin su Yusuf su kara so cikin mota da sauri dama suna kallon su, yace "why meyasa zaka kashe, and...... yayi shiru ganin fuskar Eshraq ta sauya cike da bacin rai, bai yi magana ba ya buɗe motar ya shiga.