IZAYA

11

by @pherty001

Shiru CG yayi bayan ya dawo gida cike da tunanin al'amarin NIHAL, shi kansa shaida ne akan yanda ta canza ko daga yanda take kula dashi, da kuma walwalarta.

​Ya dubi mahaifiyarta sanda take shigowa sanye da kayan barci, tana ƙoƙarin kwanciya ya gyara murya kaɗan yace "za muyi magana Hajiya".

​A natse take kallon sa kafin ta zauna kusa da shi cikin girmamawa tace "lafiya dai Alhaji, na gan ka kamar acikin damuwa?

​Yace " eh, magana ce akan yarinyar nan, ɗazu Jibril ya same ni office tare da qorafi akan NIHAL da kuma irin yanda ta canza masa, kuma nima nagane hakan ko kirana da take yawan yi duk ta daina a yanzu sai idan nine na kira ta".

​Hajiya salima ta sauke numfashi kaɗan kafin tace "ni kaina bansan me ke damun ta ba, kafin yaje office ɗin ka sai da suka yi faɗa akan zasu fita tace bazata je ba, na zauna da ita tun ba yau ba ko bata da lafiya ko tana da wata damuwa tace duk babu".

​Ya tsura mata ido na ɗan wani lokaci, kafin ya duba time, dare bai yi sosai ba kuma ya tabbata bata yi barci ba, ya dauki waya ya kira ta akan ta same shi bedroom ɗin sa.

​Bata dauki lokaci mai tsawo ba sai gata ta shigo, sanye da rigar barci marar nauyi, kallon su tayi yanayin su ya nuna ba lafiya ba, ta yatsina fuska tana jin she is ready to face any challenges in dai akan TYCOON ne.

​"you called me" ta faɗa kai tsaye idanunta akan mahaifinta, ya dubi mahaifiyarta dake kallonta cike da mamakin yanda take masa magana wanda shi baya ganin hakan a matsayin komai tunda shine ya sagarta ta.

​Kafin ya dubi NIHAL yana faɗin, "wannan ne karo na biyu da zan tambaye ki akan me yake damun ki, meyasa kika canza lokaci ɗaya".

​Ta yatsina fuska kaɗan kafin tace "ni fa nace ba komai, I just need some rest, kawai yanxu bana son hayaniya ne".

​Yace "saboda hakan zai sa ki dinga wulaqanta wanda zaki aura, ki canza mishi bakya jin maganar sa kuma baki basa kulawa yanda ya dace, ko da ni ace kin daina kula ni amma shi da yake mijin da zaki aura fa".

​Kai tsaye tace dashi "Daddy ni bana son sa yanzu, am sorry to say.... Duka su biyu suka zaro ido cikin tsananin mamaki da faduwar gaba suna kallonta.

​Ta qara tunzuro baki da ganin yanayin su, tace " da gaske Daddy bana son sa".

​Ya tashi daga inda yake zaune cikin rawar jiki ya nufe ta, Salima tayi tunanin ko dukan ta zai yi har taji sanyi a ranta, sai ta ganshi ya zauna kusa da NIHAL tare da riqo hannunta alamar rarrashi.

​"bakya son sa, laifin me yayi? ta qara shagwabe fuska kamar zata yi kuka," dama can bana son sa saboda kai ne na amince da auren sa, yanzu kuma na sami wanda nake so".

​"Waye shi? Ya tambaya kai tsaye yana zare farin eyeglass ɗin idanun sa, tace " sunan sa Eshraq".

​Yace " na tambaye ki waye shi not his name".

​Tayi Jim kaɗan cikin tunani kafin ta qara matse hannun sa dake maqale da nata, tace "mun haɗu dashi a millennium park, daga kallo ɗaya naji ina son sa Dad, he's tall, handsome, da ka ganshi zaka ga kamala a tare dashi, acikin muryarsa akwai maturity da intonation and every word da zai fito bakin sa mai daɗi da ma'ana ne.

​In short daddy ban taba haduwa da namijin da nake so kamar sa ba, Ina matuqar sonsa da gaske, idan kaqi aura min shi wallahi zan iya mutuwa saboda shi".

​Dukan ƙirjinsa ya tsananta, ya juya yana kallon Salima dake kallonsa cikin takaici cos da itace take gayawa haka da tuni ta dauke fuskarta da Mari.

​Kafin ya juya yana kallon NIHAL da ta kafe shi da manyan idanuwanta tana sauraren me zai faɗa, tace "please Daddy, jiki a sanyaye yace " I want to meet him tomorrow ".

​Ta saki wani murmushi farin ciki tare da rungume shi," that's my dad", ta bashi peck a kumatu kafin ta tashi da sauri ta bar ɗakin.

​Cikin takaici Salima tace "Alhaji me kake yi haka? Maimakon ka tsawata mata ko ka dake ta amma kake son biye mata?

​Ya dube ta yana faɗin," abinda take so shi zan mata, so kike na aurar da ita ga mutumin da zabina ne ba nata ba, ko baki ji ta fada dan kawai ni nake so ne ba, and so kike na rasa ta saboda son zuciya na, ni da ke dole aka mana ne ba auren soyayya muka yi ba? Meyasa itama bazan mata auren da zata ɗore a farinciki ba?

​Cikin takaici Hajiya salima tace "Sam Alhaji baka kyauta wa a yanda kake tafiyar da yarinyar nan am sorry to say, yarinya bata jin maganar kowa and sai abinda taga dama take yi kuma sai abinda take so zaa mata, fisabilillah duk soyayya da kauna da yaron nan ya nuna mata zaku masa haka? Yaro ya je neman mafita a gurin ka akan ta canza mashi maimakon ka zauna da ita ka mata fada ko ka fahimtar da ita sai ka biye wa abinda take so?

​Cikin bacin rai ya tashi daga inda yake zaune yana kallonta yace "Salima kina so kice bani da tarbiya shiyasa na sagarta ƴata bana bata tarbiya, yarinya ƙwaya guda da Allah ya bani ita kaɗai a duniya sai na hanata yin yanda ta so a rayuwarta, na hanata farinciki saboda son zuciya irin naki, ki gayamin menene take yi da bata jin magana, yaron da kike magana tunda kin zabi farincikin wasu akan na ƴarki ina ce yaron abokina ne kuma nine na kawo shi and yanzu na janye na fasa tunda mai zaman auren bata so, sadakin su zaa maida masu shikenan".

​Taji wasu hawayen baqin ciki sun cika idanunta, cikin ɗacin zuciya tace "Idan kayi haka baka kyauta wa yaron nan ba wallahi babu adalci a wannan sai son zuciya wanda zai kai ku ga dana sani daga kai har ƴarka", ta juya a fusacce ta bar falon cikin ƙunci.

​Tana isa bedroom ɗin ta, ta kira shi cike da ɗoki, yana ɗauka ba bata lokaci tace dashi "Daddy want to meet you tomorrow", Yusuf ya juya da sauri yana kallon TYCOON dake sipping coffee, shima kallonsa yayi cos wayar is on.

​Tace "why are you silent? Ina ce Abinda kake jira ne, ban yi tunanin ya amince haka da sauri ba duk da nasan ko me nake so a rayuwa zai min shi".

​Yusuf ya daidaita nutsuwar sa kafin yace "Da wuri haka, har kin sa naji tsoro.... Tsoro, tsoron me? Ta katse sa cike da mamaki.

​Eshraq ya girgiza masa kai, kafin ya ɗaga kansa alamar amincewa, Yusuf yace" shikenan I will try my best naga nazo gobe".

​Ta sauke numfashi kaɗan tare da faɗin "kada kaji tsoron sa, duk abinda nake so shi yake min, my daddy is simple, and na tabbata zai mana aure.....

​Yusuf yace " NIHAL bamu gama fahimtar juna sosai ba, baki gama sanin koni waye ba, kika amince da aurena haka da gaggawa akan wanda kika jima dashi har aka maku baiko?

​Ta sauke numfashi kaɗan tace " I trust you, nasan bazaka cutar da zuciyata ba saboda adalcin da tayi maka akan son da kake min, and ni banji a jikina cewa zaka iya cutar dani ba".

​Eshraq ya ɗauke kansa daga kallon Yusuf yana cigaba da abinda yake batare da ya damu ba, Yusuf yace "kina sona da yawa, same too", tayi murmushi batare da tayi magana ba.

​Yace "nasan baban ki comptroller ne, ni kuma business man ne, may be wata harqalla ta taba haɗa mu, may be ma bata taba haɗa mu ba, but Ina so nasani Idan har wani abu ya taba hada ni da mahaifin ki ya ganni gobe yace bazaki aure ni ba what will you do?

​Dariya tayi sosai, dariyar dana ƙara janyo hankalin Eshraq gare su duk da bai san me ya saka ta dariyar ba, yaji tace "whatever it's tunda Ina son ka, zai haqura ya yafe maka, na gaya maka duk abinda nake so shi yake min", Yusuf yace "shikenan, suka cigaba da hirar su kamar ko yaushe cikin shauqin juna.

​Washe gari da yamma suka nufi gidan, ba'a buɗe masu gate ba sai da Yusuf ya kira yayi magana da ita kafin ta basu izini, suka yi parking suka fito harabar gidan kowanen su ya jingina da mota.

​Bata dauki dogon lokaci ba sai gata ta fito sanye da doguwar rigar Egyptian mai sulbi, pitch colour, rigar ta manne jikin ta sosai, gaban rigar an ƙanwata shi da embroidery, hannayen rigar dogaye ne, ​Sheer lace kaɗan a gefen hannu, wanda ya ƙara mata classy femininity, A ƙasan rigar kuma akwai pleats, shape ɗin ta sosai a ya fito acikin abayar tayi matuqar kyau sosai.

​Yau ne karo na farko da ta soma ganin shi tare da friends ɗin sa duk da tana jin labarin Yusuf da Rayhaan ɗin a bakin Yusuf mai qaryar shine TYCOON.

​Suka gaisa cikin girmamawa, jin muryar Yusuf sai ta juya tana sake kallon sa, kallo mai cike da tuhuma, muryar da take ji a waya babu banbanci da wannan da taji a yanxu.

​Ganin irin kallon da take wa Yusuf ya daidaita nutsuwar sa tare da gyara muryarsa yana qara gaida ta kamar bai fahimci halin da take ciki ba, saura qiris Eshraq ya kwashe da dariya saboda wata irin murya da Yusuf yayi amfani da ita a yanxu.

​Rayhaan kuwa kau da kai gefe yayi yana hadiye dariyarsa, a hankali tace "muje daga ciki", kafin Eshraq yayi wani yunquri sai yaji saukar hannunta a nasa wanda ita a ganin ta yin hakan ba komai bane, nuna kauna ce gare sa.

​Ya zubawa hannunta da ta maqale da hannunsa ido, wannan ne karo na farko da hannunsa ya soma taba mace, macen ma ba ummi ba kuma ba Anna ba.

​Duk da bashi da plan akan mace kuma bai taba zama yayi tunani akan irin macen da yake so ya aura ba, wannan abin da tayi masa a yau yaji yana da plan akan mace.

​Yana son mace mai nutsuwa da kamun kai wanda ya lura sam wannan yarinyar bata dashi.... ta katse masa tunani let's go".

​A fakaice ya dubi Yusuf da suka tsura masa ido da kallon mamaki, sun sani abu ne da bai taba faruwa akan sa ba, tunanin su zai fisge hannunsa ko ya nuna wani action amma sai suka ga yabi bayan ta.

​Suna kallo a hankali ya zame hannunsa daga riqon da tayi masa yana qara bata fuskarsa, Yusuf yasan ire iren hirar da yake yi da itane a waya ya saka tayi hakan.

​Falon mahaifin ta tayi masu masauki, cikin lokaci qanqani aka cika su da cima kala kala, gogan yana zaune akan Italian Formal Armchair, har lokacin yana qoqarin danne bacin ran dake son taso masa.

​Tazo ta zauna kusa dashi tana kallonsa da murmushi, tace "like you are not happy, yau ranar farinciki ce a gare mu fa".

​Ya qanqance idanunsa dake boye a baqin madubi dake idanunsa, yayi murmushi kaɗan wanda iyakacin sa fatar bakin sa, yace "har yanzu my heart is telling me bazai amince ba saboda an miki baiko da wani".

​Tace "ka daina wannan tunanin, Daddy yana sona sosai kuma na tabbata tunda nake son ka shima zai so ka".

​Yace "kika amince dani haka bayan bamu gama sanin halin juna ba, kuma rayuwar aure zamu gudanar till eternity, baki san kowane mutum yana da tsarin rayuwarsa na abinda yake so da wanda baya so ba.

​Baki san Kowanne dan Adam yana da ‘hali’, wato dabi’a ta halitta da Allah ke halittarsa da shi, kuma a duniya ba kowa zai iya jure halin dan uwansa ba, in ka dauke iyaye.

​Iyaye ne kadai za su iya jure halin ‘ya’yansu. Ba kowanne miji ne zai jure halin matarsa ba, ba kowacce mace ce za ta iya jure halin mijinta ba.

​Shi ya sa ake son fahimtar juna kafin aure, da sanin hali da dabi’un juna, ba kawai don soyayya ta hada a yi (rushing) a shiga rayuwar aure ba.

​Shi aure ibada ne da ake yi da sanya ran cewa, ‘till eternity’ (har abadan-abadan) cikin kowacce ibada kuwa sai an sa juriya da hakuri da yafiya. Duk auren da babu wannan a ciki, duk kauna da soyayyar da ke cikinsa sunansa rusasshe".

​A sanyaye tace "kana so ka karya min zuciya, kana so na fara zargi akan ka?

​Yusuf da Rayhaan suka kafe shi da idanuwa domin a fakaice magana ce ya ke gayamata, yana ƙoƙarin magana CG ya shigo cikin shigar sa ta alfarma.

​Lokaci ɗaya Rayhaan da Yusuf suka tashi cikin girmamawa, CG yaji wani tsoro da mamaki ganin mutum biyu dake gaban sa.

​Kafin ya juya da sauri yana kallon Eshraq dake zaune NIHAL na zungurar sa akan ya tashi shima ya gaida mahaifinta.

​Murmushi Eshraq yayi mai cike da nuna tsantsan farincikin ganin CG kafin ya zare madubin idanunsa a hankali idanunsa akan sa, cike da izza ya miqa masa hannunsa alamar su gaisa wanda tsananin shock ya saka CG ya kasa miqa masa hannunsa.

#IZAYA

#Pherty

#Nihal

#Tycoon

#Jibril

#CG BILAL

#Yusuf

#Rayhaan