Chapter 5
Bayan fitar mom daga dakin hira suka shiga yi tsakanin hajiya mama da JAY kasancewar akwai shaquwa sosai a tsakanin su duk da cewa jay bata boyewa mom komai Na rayuwarta amma akwai abinda zata fada ma hajiya mama bata fadawa mom ba,tun suna hirar duniya har suka dawo kan shagalin gobe na bude eatery din JAY da za'a yi,bayan sun shafe lokaci mai tsawo suna hira hajiya mama ta fara gyangyadi dariya JAY ke yi har da qwarewa hajiya mama ta Kama fuska ta hade girar sama da ta qasa ta miqe Tace mata sai da safe JAY na dariya tace ai sai ki bari Na raka ki kar ki fadi a hanya saboda gyangyadi,itama miqewa tayi suka fita ta raka ta har bakin dakin ta sannan ta dawo nata dakin ayaanah ta kalla da ke ta bacci hankali kwance blanket din da ya yaye ta gyara mata sannan ta shiga wanka.....................
A bangaren mom kuwa bayan tafiyar ta daga dakin sallah ta tada saboda lokacin da hajiya mama ta zo dama al'wala tayi,ta dade sosai a sujudar qarshe tana addu'ar dawwamammen farin ciki mara yankewa a cikin ahalinta sannan ta kar kata akalar addu'ar tata zuwa kan tilon yarta bayan ta idar da sallar ce ta daga hannayen ta sama tace ya ubangijin al'arshe ina roqon ka kare man yata dama duk al'ummar musulumi daga duk wani abun qi ka dawwamar da farin ciki a rayuwarta sannan ka hada ta da abokin rayuwa wanda zai ji tausayin ta ya kula da ita wanda zai zama bango a rayuwar ta ya hana ta zubar da hawaye ko da kuwa bama raye,bayan ta gama addu'ointa ne ta nade prayer mat da hijabin da tayi sallah ta mayar da komai muhallinsa,mom wayayyiyar mace ce mai ilimi da kuma tsafta bata hada hanya da qazanta wayar ta ce tayi haske kasancewar wayar a silent take qarasawa tayi wurin drawer ta duba mai kiran,murmushi ne kwance kan fuskar ta ganin mai kiran Assalamu Alaika ya zawji,shima murmushi ne akan fuskar yace wa'alaikissalam warahmatullah ya zawja ya kadaici kamar yana ganin ta ta kwabe fuska tace kadaici kam akwai shi i just can't bring myself to stop missing you 😢 dan murmushi yayi mai kyau saboda yasan ta kwabe fuskarta don yasan halin kayarshi,sorry dear ai gobe zan dawo farin ciki sosai akan muryar ta tace dagaske kake zawji,eh you know i can't afford to miss tomorrow's events,daughter will be mad at me,even though i won't tell her I want to surprise her,hira suka ci gaba cike da farin ciki soyayya da kuma qaunar juna sai bayan lokaci mai tsawo sannan suka yi sallama cike da kewar junan su,bayan sun gama waya ne mom tayi addu'a sannan taja blanket ta kwanta.................................
Kamar ko wace rana yau ma ba wani canji tunanin ta da son zuwa gare ta kullum shike azazzalar zuciyar shi amma baya da wannan qwarin gwiwar ta zuwa ya fuskance ta kullum cikin saqe saqe yake yadda zai je gareta amma ya kasa samun hanya da kuma qwarin gwiwar yin hakan,zannur ya dade tsaye akan shi bai sani ba kasancewar yayi nisa cikin tunanin da yake kiran sunan shi da zannur yayi shi ya dawo dashi daga duniyar tunanin da ya fada HAYDAR ya kamata ka cire duk wani tunani dake ranka saboda hakan bazai haifa mana da mai Ido ba tabbas yasan abunda zannur ya fada haka ne amma shima baya da ikon hana kansa tunanin ta bashi ya saka ma kanshi tunanin ta ba shima da yasan hanyar da zai bi ya dena tunanin ta da ya dade bi don yana matuqar azabtuwa dan murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo yace buddy kawai ka taya ni da addu'a ita nafi buqata saboda ni kadai nasan irin radadin da zuciya ta take man,a hankali zannur ya tashi daga inda ya zauna ya dawo gefen HAYDAR ya zauna sannan ya dafa kafadar shi yayi masa murmushi mai qarfafawa mutum gwiwa saboda bayan HAYDAR babu wanda ya kai zannur sanin irin labarin soyayyarshi ba da kuma dalilin rabuwar su ba tare da zuciyoyin su sun shirya ba,sosai ya fada ma HAYDAR kalamai masu qarfafa gwiwa ganin dai he is still moody yasa zannur yace let's go somewhere please shima dama ya gaji da zaman gidan yace ok bari na shirya,bai wani bata lokaci ba ya shirya cikin plain white T-shirt da black trousers Na company bottega veneta kasancewar garin da sanyi ya ya dauki black leather jacket ya riqe a hannun shi,zannur kawai tsayawa yayi yana kallon shi,daga masa gira daya yayi yace kallon fah bai ce komai ba ya qaraso cikin parlour daya daga cikin keys din shi ya dauka suka fice daga gidan baki daya,bayan sun dauki hanya ne ya juya ya kalli zannur irin kallon nan na ina zamuje harara ya balla mai kamar wata mace yace ai ni na kawo shawarar fita don haka kai zaka kawo shawarar inda zamuje baice masa komai ba ya samu gefen titi yayi parking idan da sabo ya saba da hali irin na HAYDAR ganin haka yasa zannur ya hade rai ya fara danna waya ganin suna bata lokaci a titi yasa HAYDAR jan tsaki ya tada motar suka cigaba da tafiya,ko kallon inda yake zannur bai qara yi ba ya maida hankalin shi kan wayar da yake dannawa,bayan tafiya mai dan tsayi suka qaraso BOCOCHO BEACH (bococho beach guri ne na hutawa da kuma shaqatawa guri ne mai matuqar kyau da tsari yana daya daga cikin manyan gurin shaqatawa a Lagos) bayan HAYDAR ya dai dai ta parking ne suka fito tare suka shiga ciki,ganin kallon da yan matan dake wurin ke masa yasa shi jan tsaki ya kuma qara hade rai sannan ya duba aljihun jacket din shi cikin sa'a kuwa ya samo baqin shade ya saka a fuskar sa kamar mayu haka suka cigaba da kallon shi har ya bace ma ganin su,ya zama kamar al'ada agare shi idan har yazo bococho abinda yake fara yi shine hawan doki dan gaba yayi saboda yasan zannur bai fiye hawan doki ba,bai yi nisa ba yaji zannur yace wait for me yau dai mu tuna baya kuma ka sani yau baxan barka Kayi nasara akai na ba,dan murmushin mugunta yayi yace zamu gani ai...........................
Yau ma dai kamar kullum bata sauya zani ba tana kan sallaya ne bayan ta idar da sallar walha tayi addu'oi bata ma san lokacin da ta fada duniyar tunani ba,jiddarh ce ta zauna gefen ta tace Mamy don Allah ki rage wannna tunanin ko dan saboda lafiyar ki kin fi kowa sanin condition din ki,murmushi tayi irin na manya tace jiddarh wani lokacin ba mu ke tsara yadda rayuwar mu zata kasance ba nima bana son wannan tunanin amma ya zama dole amma in shaa Allah komai ya kusa zuwa qarshe in shaa Allah mamy,yanxu dai mun makara ki tashi ki shirya mu tafi idan har ba so kike mom ta zo har gida ta tafi da ke ba wayar ta ta duba taga tara har ta wuce Subhanallah ai bansan lokaci ya wuce har haka ba bari na hanzarta kema je ki shirya.........................
Babu abinda kake ji sai qaran spoons da fork gaba daya ahalin ne zaune suna breakfast mom na lura da yanayin jaiyana kamar wani abu na damunta saboda sosai ta lura jikin ta yayi sanyi ba kamar yadda take ta zumudin zuwan wannan rana ba so she decided that she would talk to her later,ohh my dear mun kusa makara kamar a mafarki taji muryar dad yayi sallama cikin parlour ai batasan lokacin da ta ruga da guda tayi hugging din shi ba ohhh my goodness dad i can't actually bring myself to believe this,am i dreaming, you are not my baby,dad is here with you,shesheqar kuka suka ji a bayan su gaba dayan su suka juya sai ganin hajiya mama suka yi ta riqe qasan zani tana matsar qwalla yar dariya jaiyana tayi sannan tace drama queen,dad ne ya qarasa yace haba hajiya me kuma ya faru eh lallai ummaru yanxu har ni kake kallon tsabar Ido na kake cewa meya faru ko zaka fada man tunda ka shigo gidan nan yar ka kawai ka gani mu duk ba mutane bane eyeee ummaru,Allah ya baki haquri hajiya in shaa Allah hakan bazai qara faruwa ba eh hakan dai yafi ai Toh ya hanya Alhamdulillah hajiya, kai kuma haka ake tafiya ba sanar wa ai sai ka fada man na saka ka a addu'a yanxu irin wannan tafiya ka biyo jirgi ummaru amma baka kira na maka addu'a ba anya ummaru,muje kunga mun bar mutane suna jiran mu dawowa yayi ta gefen mom ya bata side hug yace hope you are not angry with me zawja dan murmushi tayi tace why would i fitowa suka yi compound drivers din gidan ne suka taso tare da bude musu mota jaiyana ce ta riqe hannundad tayi kalar tausayi da fuska sannan tace I am going with you daddy dama mom tasan xa'ayi haka sai kawai ta shiga motar da su hajiya mama suka shiga,a hanya suna tafiya sai surutu take masa shi kuma yana biye mata dad i miss you so much,likewise dearest,sosai take ta mashi surutu har suka ji an staida motar su alamun sun qaraso kenen,daya daga cikin masu tsoron lafiyar shi ne suka bude mashi mota ya fito hannun sa na cikin na jaiyana suka nufi entrance din shiga wurin,daga kan ta tayi ta kalli symbol din da aka makala a hanyar shiga da aka rubuta you are highly welcome to the grand opening JAYHA wani sad smile ne ya kubuce mata underneath her breath tace i miss every single thing about you dauke kanta tayi daga kallon gurin tayi hanyar shiga ciki,sosai aka qawata gurin da simple decoration mai matuqar kyau da daukar hankali,lokacin da suka shiga ciki sun samu mutane sun dan zo don haka Sai da suka fara gaisawa da mutanen dake wurin kafin suka zauna akan wani table dake facing Jama'ar gurin kamar yadda aka tsara bayan an bude taro da addu'a MC ya fara gabatar da jawabi akan abinda ya tara su a gurin,bayan yayi dan taqaitaccen bayani ne ya juya ya miqawa jaiyana mic domin tayi bayani da kuma godiya ga mutanen da suke wurin,Assalamu Alaikum everyone,first of all i will like to thank each one of you here for honouring our invites we really appreciate,and i will like to thank my constant supporter for always being there for me Jazakhallah bi khair dad this is not just an achievement to me but a dream come true,lokacin da nake qarama Idan naga caterers suna matuqar burgeni,so na tashi ne da son abin a cikin rai na da na fada ma dad bai yi discouraging dina ba a lokacin duba da qarancin shekaru na sai ma encouraging dina da ya riqa yi yake ce man Idan kika girma in shaa Allah ni da kaina zan bude maki eatery and here we are today and my mom too ta bani qwarin gwiwa da kuma shawarwarin da zan iya cewa sune suka qarfafa min gwiwa har na kawo yanxu Allah ubangiji ya saka maku da mafificin alkhairi gurin yayi shiru ita kadai ake saurara a lokacin ko allura ce ta fadi xa'a ji qara Idon ta ne ya cika da qwalla sannan ta kalli kowa da yake gurin tace da akwai wasu mutanen da sun bada muhimmiyar gudummawa ganin na cika buri na amma yau basa tare damu,ubangiji baya barin wani don wani yaji dadi,Allah ya gafarta masu ya kuma yi musu rahama gaba daya gurin aka dauka da ameeen,thank you once again for coming may Allah reward you abundantly i think that all i can say,miqawa MC mic tayi ta koma ta zauna kamar yadda aka tsara an cigaba da taro inda aka fara gabatar da abinci kala-kala ga baqi a dai-dai lokacin kuma wayar ta ta fara ringing ganin mai kiran yasa ta dauka ta kai wayar kunnenta bayan tayi sallama ok kawai naji tace sannan tayi excusing kanta ta fita a hanya ta hadu da daya daga cikin ma'aikatan gidan su riqe da hannun ayaanah ta bata jikin ta da juice,bata wani tsaya sauraren bayanin ta ba tace mata tasa driver ya kaisu gida ta canja mata Kaya saboda kar tayi mura,tana gama fadin haka ta wuce gurin da aka yi parking motoci,bata sha wahalar ganin shi ba kasancewar babu mutane da yawa a gurin,sadeeq mai yasa baxa ka shigo ba ka tsaya a waje I'm really sorry my love yanxu haka ma jira na ake amma nace sai nazo babu komai ai hakan ma na gode dama I just want to say congratulations may this be the beginning of your success Ameeen thank you so much sadeeq never mind you deserve it yanxu dai bari na tafi na bar mutane na jira na ok dan bani one minute please take your time dear cikin hall din ta koma souvenir ta dauko bayan ta koma ta bashi karba yayi ya mata godiya sannan yama motar shi key ya bar gurin tana shirin juyawa ne aka ce good morning miss jaiyana,morning ta amsa tana juyowa,gabanta taji ya fadi saboda ta gane fuskar mutumin kamar koda Yaushe yau paper ya bata tayi signing sannan ya miqa mata wasu roses masu bala'in kyau da kuma wata qaramar takaddar write up a ciki,mutumin yana tafiya Tasneem ta zo gurin saboda ta ga jaiyana ta fita kuma ta dade bata dawo ba,eyyeh shi sadeeq din ne ya kawo maki wanann roses din masha Allah Amma fah sunyi kyau sosai ita kadai ke surutun ta saboda jaiyana gaba daya hankalin ta baya jikin ta ma tana ta tunanin da babu mai bata amsa,kula da Tasneem tayi hankalin jaiyana baya jikin ta ne yasa ta dan taba ta,a dan firgice ta juyo tace Tass Lpia? Jay ke zan tambaya lpia kin tafi tunani dole kiga na shiga tunani amma yanxu dai mu tafi gida idan muka je sai muyi magana Tohm shikenan muje sai ki fadawa mom,ciki suka koma ta fada ma mom xasu tafi gida da har ta hana Sai da ta ce mata kan ta ke mata ciwo sannan tace su tafi and kar ta manta da magani,Sai da ta qara jaddada mata Shan magani sannan ta kyale su suka tafi,a motar Jay suka tafi aka bar ta Tasneem a gurin,suna zuwa gida an gama shirya ayaanah xasu koma gurin taron ganin jaiyana ta dawo yasa suka fasa komawa maid din ta wuce domin qarasa sauran abubuwan da suka rage ita kuma ta riqe hannun ayaanah suka wuce daki,suna shiga ta wuce bathroom,wanka tayi ta qara shirya cikin wata light blue simple abaya ganin qarfe daya saura yasa tayi alwala sannan sa ayaanah ma tayi alwala suka yi salla ita ma Tasneem alwala tayi tayi salla bayan duk sun idar ta dauki makullin mota tace musu su zo suje wani guri,tayi haka ne saboda tasan yanxu mutane xasu fara dawowa a fara hayaniya,ita kuma bata san hayaniya shiyasa tace su fita,mota tayi ma key suka dauki hanya sunyi tafiya mai dan nisa kafin suka qaraso millennium park bayan tayi parking ne suka shiga cikin park din,sun yi yawo sosai bayan duk sun gaji ne suka dauki hanyar gida instead of tayi hanyar gida sai ta dauki hanyar gidan su Tasneem dake wuse suna zuwa bayan tayi parking suka shiga ciki su duka suka zube kan kujera da take zaune kasancewar three seater ce har suna hada baki wurin fadin ummah mun gaji cikin jikin ta ta shigar da su sannan tace Allah sarki yan biyun ummah sun gaji yanxu a shiga ciki ayi sallah kafin ku fito zan hada maku abinci don daga ganin wannan idanun naku baku ci abinci ba,cike da ladabi sukace Tohm sannan suka miqe don yi abinda aka umarce su,sai bayan sun tashi ne take ganin ayaanah da ta lafe jikin kujera kaii ku dawo ina kuka samo diyar mutane sai a lokacin ma suka tuna da ayaanah Tasneem ce tace ummah it's a long story zamuyi magana da dare komawa tayi ta kama hannun ayaanah suka wuce dakin ta,suna idar da sallah suka fito parlour ummah har ta gama shirya masu abinci,suna zuwa kowa yaja kujera ya zauna,wani lafiyayyen tuwon semovita sai tururi yake da egusi soup wanda yaji different varieties of fish cike da Jin dadi jaiyana ta fara cin abincin ta bata kula kowa ba har ta gama cin abincinta daga ummah har Tasneem sunyi mamakin yadda ta ci abinci da yawa saboda sun san ita din ba ma'abociyar cin abinci da yawa bace,ganin irin kallon da suke mata ne yasa tayi dan guntun murmushi tace kar kuga laifi na nima bansan na cinye ba ummah yayi dadi sosai Toh haka ake so tunda yayi maki dadi................................
Bayan dukkannin su sun dai-dai ta zaman su kowa ya riqe sirdin dokin sa aka fara tsere Sai da HAYDAR ya bar zannur yayi masa nisa sosai sannan yaja sirdin sa ya fara gudu yanayin yadda yake sarrafa dokin ne ya dau hankalin yan tsira-run Jama'ar dake gurin wasu suka fara daga wayoyin su suna video,cikin dan qanqanin lokaci ya cimmasa,yana zuwa dai dai inda yake ya daga masa gira irin ya dai sannan ya cigaba da tafiya Sai da yaxo gurin da zai tsaya yaja ya tsaya ya dade kafin zannur ya qaraso HAYDAR yace ta yaya kake tunanin zaka tsere man a kilisa bayan ni na riqe hannun ka na koya maka hawan doki suna cikin magana wasu yan mata suka qaraso inda su ke ko kallon iskar da ta dakko su HAYDAR be yi ba suka ce Hii zannur ne kawai yace masu hello mr.handsome gurin ka muka zo,keda kike gidan ki Idan kin amsa to HAYDAR ma ya amsa sai ma qara hade rai da yayi ko kallon inda zannur yake be yi yayi tafiyar sa.............................