Kuncin zuci
by @bintuuu
Washegari da safe bayan sun gama breakfast Na'ima ta tusa Ahmad agaba suje yin sallama da Abu da zai tafi karatu a qasar Germany, simply ta shirya cikin maroon jalbab da ya haska ta sosai, while Ahmad ya fito sanye da casual qananun kaya suka tafi, isarsu Airport din suka tadda iyalan Abban dukansu zazzaune a waiting area har Abban amma banda Al'ameen dan ya kwana biyu da komawa makaranta, Nafisa ce ta fara hangosu ta dago musu hannu sai Na'ima ta nufesu da saurinta Ahmad na biye da ita, saida suka gaggaisa sannan Na'ima ta kalli Abu tace "Zamuyi missing dinka Abu" jiki a sanyaye Nafisa ta kamo hannunsa tace "I'll call you...Everyday kaji" sai yayi dariya, sunanan zaune ana hira sama sama aka kira jirginsu sai duk suka mimmiqe jiki a sanyaye Mami ta rungume autan nata tace "Ka kira mu akan duk wata damunwanka kaji" ya gyada tareda riqe mahaifiyar tashi, sai da Nafisa tayi hugging dinsa sannan ta fara kuka Abba yace "Banda kuka Baby, bazai dade ba ai" sai Faruk yayi murmushi yace "Kuka kike wa abokin fadan naki kuma yau" Na'ima da duk jikinta yayi sanyi itama ta fara hawayen, sai Mami yace "Mai tafiyan ma fa baya kuka saiku" sai duk akayi dariya, Ahmad yace "He's a big man" ya qarasa gurin Abun yace "Give me shake" sai Abu yayi murmushi tareda miqa masa hannu sukayi shake sannan Ahmad ya sake cewa "Ka kula sosai kaji" ya gyada kai yana fadin "In sha Allah Yaya, thank you" da haka Faruk yace "Muje Abu, in ka biye biyun nan sai suce afasa tafiyan ma" ai nan Nafisa ta qara karfin kukan ta Abba na bata baki, Na'ima na hawaye ta cigaba da daga musu hannu har suka bace wa ganinsu sannan ta koma gurin Nafisa tana bata baki itama, Saida suka tashi tafiya tace mata "Kizo muje mu wuni yau tunda gidan zai zama shiru" asanyaye Nafisa tace "Sai gobe zanzo, it's weekend Abba yana gida yau" sai ta gyada kai da haka sukayi sallama harda su Mamin sannan kowa ya nufi gida, jikin Na'ima a sanyaye har suka koma gida Ahmad na lura da ita, saida ya faka motan a cikin gidan nasu sannan ya kalleta yace "Babe it's just school, kamar yanzu ma zakiga ya dawo hutu fa" tace "Abu is so lively ne in yana gidan especially in Al'ameen yananan shima, yanzu Nafisa zataji ba dadi dukanmu bama nan" sai yayi murmushi yace "Nafisa fa tasan gurin having funs sosai a garin nan, besides ga Husna ma tananan, sannan ga shagon ta data maida hankali akai yanzu" sai tace "Duk da haka dai please ka amince in rinqa zuwa akai akai" nan kuma yayi dariya tareda bude cab din motan ya fita, sai itama ta fito tana kallonsa, cike da shagwaba tace "Dan Allah fa" nan ma yana murmushin ya kalleta baice komai ba, sai taqi motsawa daga parking space din bayan yace su shiga ciki, ganin taqi tahowa yace "Abu me sauqi, sai in dauke ki" da haka ya duqa zai ciccibeta tayi qara tana dan dukan bayansa tace "Allah wataran zaka kada mu gaba daya" bai saurareta ba ya qarasa cikin gidan da ita a jikinsa, anan falon ya musu masauqi a kujera sannan ya cire mata hijab din yana kallonta har lokacin bai dena murmushi ba, sai ta kwabe fuska ta juya kai, duqowa yayi gareta ahankali yace "Toh saidai in zaki yarda kullum nayi" nan kuma ta fara murmushi tana qoqarin turesa ya fara dariya yace "Dagaske nake, and it starts from now" sai tace "Yau bazan je ba ai" da sauri yace "Da bonus zamu fara, sai mu fara na asalin daga gobe" batasan lokacin da ta fara dariya ba sai shima ya rungumota zuwa jikinsa suna dariyan tare ya hade bakinsu waje daya.
Daga wannan lokacin kuma suka dinqe da juna, Ahmad ya gane she's weak ta wannan fannin kamarshi, the more ya tabata take yin la'asar sai ya rinqa amfani da hakan gurin gyara hanyarsa da kyau wanda hakan ya zamto basuda gurin shiriricewa sai gadonsa ko nata, sune falonta, sune falonsa, sune dakinta sune dakinsa, sune under showernta sannan aje ga showernsa, su kitchen island duk ba'a bari a baya ba, sai a wannan lokacin suka fara dirzan amarcinsu dan soyayya ana shanta sai abunda suka manta ne kawai basayi, burin Ahmad ya maidata ita yanda yakeson kuma ya fara nasara akan hakan, a wata safiya bayan sunyi breakfast Ahmad ya ritsata a falon qasa ta bada kai suka shiririce akan kujera, sunyi nisa gurin badakalansu Na'ima ta dago kai idanunta suka fada cikin na Simba dake tsaye a matakalan stairs yayi quri yana kallonsu, ai batasan lokacin da tayi qara tana ture Ahmad ba, sai ya dago adan firgice yace "Babe what's wrong?" da sauri ta fara kokarin jawo riganta dake yashe a qasa tace "Kaga yanda yake kallonmu fa, dan Allah ka koresa" sai ya juya ya kallesa, yana murmushi yace "Babe dabba ne dai, mema ya sani" ta girgiza kai tace "Kaga idanunsa fa, he's freaking me out, please ka koresa" sai ya miqe yana dariya yadan kada hannunsa ga Simban dake tsaye har sannan, nufansa yayi yana fadin "Attaa boy" sai Na'ima tayi saurin wulla masa short dinsa ya karba ya saka sannan ya bi Simban daya koma falon Na'ima da gudunsa, saida ya kullesa acan sannan ya dawo yana dariya kadan, tana kallonsa tace "Wallahi keji zaka siyo masa" nan ma yana dariya qasa qasa yace "You're so silly Babe, kayan da ya gani babu a jikinmu ne ya basa mamaki amma bawai yasan me akeyi ba" tace "A'a nidai ka rinqa kullesa" sai ya zauna daf da ita yace "Angama Baby, Now...where were we?" tace "Mun gama" yana murmushi ya riqo waist dinta yace "Naa.. we're just getting started".....
Bayan sati uku da kwanaki suka shirya tafiya Kano da Adamawa, ranan da zasu tafin tunda asuba ta fara shiri, Ahmad na bacci da safe ya farka ganinta ta fito daga cikin closet dinsa tana hada masa kaya a qaramin box, sai ya miqe zaune a gadon yana kallonta yace "Babe, inada kaya acan gidan namu fa" tace "Naga baka zama acan shine nayi tsammanin babu" yace "Ina zuwa time to time" sai ta ajiye box din tace "Toh ka tashi kayi wanka ga breakfast can kar mu makara please" sai ya fara murmushi ya koma ya kwanta har da jan duvet din zuwa kansa, qarasowa tayi ta fara jan duvet din shikuma ya riqe ta ciki, sai ta kwabe fuska kamar zatayi kuka tace "Kar rana ta mana fa tunda kace da mota zamuje" bai fito ba yace "Babe ki bari in qara kadan, ke fa kika hanani baccin jiya" sai ta sake duvet din ta juya zata fita tana fadin "Ni ba abunda na maka, nice ma ya kamata in fadi hakan" tana jiyo dariyarsa harta fice daga dakin bata juyo ba.
Saida ta gama shiryawa tana fesa turare ya shigo dakin nata yana maqala link din hannun blueblack jamfan jikinsa, tsayawa yayi kallonta ganin yanda tayi kyau cikin maroon lace din jikinta, sai yayi kissing goshinta yace "You look so breathtaking" tana murmushi tace "Kaima haka, kayan nan sun maka kyau" sai yayi murmushi yana maida hankalinsa kan kayan daya gani shimfide akan gadonta yace "Wannan fa..kayan waye?" ta juya tace "Na Amina ne" yace "The nurse?" ta gyada kai sannan ta qarasa gurin kayan ta dauka zata saka a cikin wani leda dake gefen dan qaramin box dinta, sai da ta dago sannan ya riqo hannunta yace "Gurinta zamu fara zuwa kinji" a sanyaye ta amsa da Toh.
Suna daukar hanya Na'ima ta fara hamman bacci sai ya juyo yana kallonta yace "Wato plan dinki kenan" tayi murmushi tace "Ni ka hana baccin ai daman" da haka ta fara gyara zamanta ta kishingida, sai yayi dariya kadan tareda miqa hannu ya kwantar mata da seat yace "Zan rama" batace komai ba tana murmushin ta gyara kwanciyarta..
Sai karfe goma suka isa cikin garin Kano, sai Ahmad ya dauki hanyar hospital din da Aminan take, suna isa yayi parking a bakin wata bishiya dake wajen asibitin sai Na'ima ta nemi ta fara shiga dan ta fara nemanta tukunna, da haka ta fito ta shige cikin asibitin Ahmad na kallonta sai can kuma ya fito ya tsaya shima, sai da ta fara zuwa section din da tasan Aminan ke duty tayi tambaya sai abokan aikin Aminan suka fada mata anyi referring dinta zuwa section din masu awon ciki, anan din kuwa ta sameta ta fito kenan daga wani office hannunta riqe da folders sai ta tsaya tana kallon Na'iman da mamaki a fuskarta at the same time tana murmushi kuma ganin yanda Na'iman ta koma, sai Na'ima ta qarasa gareta tana murmushi tace "Anty baki ganeni bako" tace "Na ganeki mana Na'ima, Ina kika shiga?, ranan muka yita nemanki a asibitin nan, da fatan kina lafiya yanzu" sai Na'ima ta amsa da "Alhamdulillah Anty" nan Aminan ta jata suka zauna a wani resting chair dake wajen tana sake tambayanta inda ta tafi ranan, sai tace "Anty na koma Abuja ne da zama, kuma nayi wani auren yanzu haka ma tareda shi nake" cike da farin ciki Amina tace "Ma sha Allah Na'ima, Allah ya baku zaman lafiya, Allah ya kare duk wani tashin hankali da zai shiga tsakaninku" ta amsa da Amin sannan ta miqa mata ledan kayanta, amma da Amina ta bude sai taga harda sabbin atamfa masu tsada guda biyu da laces biyu harda su sarqa aciki, da mamaki ta dago kai tana kallon Na'iman amma kafin tace komai sai ta riga ta da fadin "Kayan ki ne Anty, akwai wanda kika bani ranan shima aciki na dawo miki dashi, nagode Allah ya biya miki buqatunki na alkhairi" tana murmushi ta amsa da Amin sannan tace "Ayya basai kin kawomin komai ba Na'ima, na taimaka miki ne saboda Allah" tace "Nasani wallahi, ni ma nasan babu abunda zan baki dan biyanki alkhairin da kikamin, amma nagode, nagode sosai Anty, dan Allah kizo muje ki gaisa dashi yana waje, shima yanason ku hadu yace yanason zai miki godiya" sai Amina ta fara girgiza kai cike da jin nauyi, da kyar Na'ima ta jata suka fice taren suka samu Ahmad har sannan a tsaye jikin motansa, Na'ima ce tace masa "Ga Anty Amina" sai shima yace "Anty Ina wuni" tana murmushi tace "A'a banda Anty, ya gida, kunzo Lafiya" ya amsa da "Alhamdulillah, mungode fa sosai, Allah ya saka da alkhairi" tace "Babu komai dai yiwa kai ne ai, Allah ya bada zaman lafiya" bayan ya amsa da Amin sai ya bude motarsa ya ciro leda mai dauke da kudi in cash ya miqa mata a ladabce sai taqi karba da fari har sai da Na'ima ta karba ta saka mata a hannunta sannan, sai yace "Ki bamu numbern ki sai a rinqa zumunci please" Na'ima tace "Na karba" yace "Toh, in sha Allah wani lokacin zamu zo har gida Anty, thank you once again" ta amsa da Allah ya kaimu tana murmushi sannan suka fara sallama, sai Na'ima ta samu kanta da dan hugging dinta cikin sanyin jiki tace "Bazan taba mantawa da alkhairinki ba Anty, nagode" da haka sukayi sallama ta shige motan suka tafi.
Misalin qarfe daya suka isa gidan Alhaji, sai Ahmad yayi horn maigadin ya bude musu suka shiga har compound din yayi parking, a nutse Na'ima ta fito tana dan bin gdan da kallo sannan ta fara shigewa gidan ta bar Ahmad a tsaye yana jiran iso, shigarta ta samu Hajiya na sauqowa daga stairs dalilin jiyo qarar mota da tayi acikin gidan, ganinta yasa ta fara murmushi tana fadin "Sannu da zuwa, manyan baqi mukayi a gidan haka" murmushi Na'ima tayi ta nufi kujera zata zauna sai Hajiyan tace "Tare kike dashi ne?" tace "Eh yana waje" sai tayi saurin cewa "Mazah je kice ya qaraso", bayan Ahmad ya shigo sai Na'ima ta jira ya zauna sannan ta zauna a kujeran dake nesa dashi dan tasan tsaf zai iya zaunawa a gefenta, sai da suka gama gaggaisawa bayan tasa shafa ta kawo musu refreshment har da abinci amma sai Ahmad yasha ruwan kawai sannan ya tambayi ko su Alhajin na nan, sai tace "Yananan, sunje masallaci ne amma yanzu zasu dawo" da haka shima ya nemi yin sallahn amma anan falon yayi while Na'ima ta tafi sama itada Hajiyan, bai dade da idar da sallahn ba Alhajin ya shigo falon tare da Bilal dake tafe a bayansa yana sanye cikin milk jallabiya har da tasbaha riqe a hannunsa, sai Ahmad ya dago kai yana kallonsu tareda da dan bin Bilal din da kallo wanda shima ya danyi stiff a tsayen dalilin ganin Ahmad zaune a falon.