Chapter 4
by @reza12
*YAN MATA*
_By S Reza...✍️_
*Whasop Channel*
***
*Chapter 4*
Jin sunyi shiru ne sun kasa magana ɗaya saurayin ya ce "Ina zaku je ne haka, ai da kun shigo mata mun rage muku hanya, wannan ba girmanku bane, ace kyawawan ƴan mata kamar ku kuna tafiya a ƙafa alhalin muna gari, ina hakan bai dace ba". Haura ta ce "Malam duk kun dame mu da surutu fa, to wannan ɗin da kake magana a kanta matar aure ce, saboda haka kaja abokinka ku ƙara gaba". Siyama ta zungureta da ƙafa. Samarin suka kwashe da dariya jin wai matar aure ce. Ya ce "Haba ke kuwa ƙawarmu, ko dai banyi kama da wanda zai iya zama saurayin kawar taku bane, ai ko makaho ya shafa yasan abun da kika faɗa ba haka bane, Ni dai yanzu kuyi hakuri kuzo muje Mota sai mu karasa maganar a cen". Ya na faɗa yayi gaba dayan ya bishi a baya. Siyama tayi saurin faɗin "Haba Haura, meye haka, ai sai kisa yayi tunanin ko gaba dayanmu ne muke da aure, kina jifa harda mota suke da ita, ko iya na yawon yau muka samu ai zamu huce haushin da wannan banzan angon ya ƙunsa mana". Amera ta ce "To tunda baki da hankali sai kije ki shiga motar tasu, haka kawai baki san mutane ba daga yin magana sai kawai ki amsa, to ni dai wallahi ba zan shiga ba, kuma ki daina zagar min miji haka ya isa bana san wulaƙanci, abu kaɗan kuma sai ki zage shi bayan kuma ai shima laifi aka yi masa". "Iyeeeee sannu matar aure Mai miji, Mijin da ya nuna dake da babu duk ɗaya a gurinsa, ɗan zumudin nan ma da angwaye keyi shi fa Kamar an kawo masa bazara wa". Siyama ta faɗa itama ranta a ɓace. Amera ta buɗe baki zatayi magana, haura ta ce "Dan Allah kuyi mana shiru akan hanya muke karku yarfa mu, yanzu abun yi kawai muke nema, tafiya ko kuma muje mu shiga motar?" Abida ta ja tsaki a fili ta ɗora da "Shima duk cikinmu ya rasa wacce tai masa sai wannan mai katon kan, ji fa yadda take yi kamar wata yar ƙauye, to wallahi dan sabo da auran ki da wannan Ƙasim ɗin ba zaki kashe mana kasuwa ba, dole ne Kiyi hakuri mu ci arziki mu barshi ko iya na yau ne". Ta ce "Me kuke nufi? Wai kina so nace masa ina sonsa ne alhalin ina da Aure?" "To idan kin faɗa auran kika sake yi, iya fa na yau ne, da mun rabu da su ba lallai mu sake haduwa ba". Haura ta ce "Kai gaskiya a'a hakan bai fa dace ba wallahi, gara dai a faɗa musu gaskiya..." Kafin ta karasa Siyama ta sake take mata ƙafa. Tayi shiru tana raba ido. Amera ta buɗe baki zatayi magana kenan sai ga motar samarin ta tsaya a gabansu. Hakan yasa tayi shiru. Ya sauke glass ɗin ya ce "Bismillah ƴan mata". Suka sake kallon juna. Siyama tayi wuff ta shiga, Abida ta bi bayanta. Haura tayi kamar zata shiga sai ta dawo ta jawo hannun Amera suka shiga. Gabanta na cigaba da faduwa.
"Ina muka dosa?" Ya faɗa yana hawa babban titi.
Siyama ta ce "Yanzu dai mun fito yawon buɗe ido ne, kawai ka kaimu wani guri mai ɗan Kyu mu huta sai mu dawo".
Ɗayan ya ɗan juyo ya kalleta ya ce "Amma daga ji kam ke bakanuwa ce ko?"
"Ta ɗan yi farr da ido ta ce "Gaba dayanmu duk Kanawa ne, ko dan kaga sunyi shiru, kawai bamu saba shiga motar wanda bamu sani bane shi yasa".
"Gaskiya ne, amma mai yasa ɗazu kuka ce mana wannan tana da Aure?"
"Kawai wasa muke yi".
"Amma kin san ba'a wasa da zuciya ko?"
"Har rai ma ana wasa da shi bare kuma zuciya".
"To idan aka rasa shi fa daga wasa?".
"Shikenan dama ba zai jure ba".
"Gaskiya ne, Ni sunana Faisal, Abokina kuma Hafiz, ko zamu iya jin sunayenku?". Ya faɗa yana satar kallon Siyama ɗin ta madubi, ko dai shima yayi kamu ne.
Ta ce "A haba kai kuwa Malam Faisal sanin sunayen mu da araha haka sai kace ba gaskiya bane abun da ka faɗa a kanmu ba". Ya ce "Gaskiya ne, to nawa ne farashin sunayen naku, naji ko zan iya biya a faɗa min". "Gaskiya da tsada bance zaka iya bafa". "Idan ma ban iya ba ko iya naki sunan sai na fansa, shi a bokaina sai ya ji da sauran". Ta ce "Da alama dai sai kun haɗa Giwa zaku iya". Faisal ya sake yin murmushi ya ce "Idan na bayar da dubu ashirin za'a iya faɗa min"? Take suka kalli juna jin tarkonsu ya kama. Siyama harda tafawa da Abida tana ƙara zuga ta. Ta ce "Lallai wannan sunayen namu da arahar tsiya suke, sai kace ana cinikin mangwaro". "Hafiz ya ce "Haka ne, to ku kawo account yanzu a fashi sunayen naku da dubu hamsin, duk da na san darajar sunan tafi haka". Ya ƙarasa yana dauko wayar sa ƙirar iPhone. Ya shiga cikin app ɗin ya mika musu wayar alamar su saka acont.
Hannunsu har rawa yake suka amshi wayar. Sai kuma aka shiga kallon juna jin ga garin dad'i amma yayi nesa, ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa, ga harka ta samu amma tazo da sigar zubar da aji. Amera ta kawar da kai gefe kamar tayi musu dariya jin sabon salo wai liman a gidan gala. Na farko dai gaba dayansu ba mai acont, na biyu kuma ita kanta iPhone ɗin ba taɓa rikewa sukayi ba. Babbar magana wai amarya da ciki!. Kafin su samu mafita suka ji an tsaya da motar, gashi wayar ma ta mutu, wato ta shiga ki. Faisal ne ya fara fita ya zagayo ya buɗe musu. Shima Hafiz ya Fito yana kallon gurin da ya kawo su. Ya ce "Ina fatan nan gurin zai burge ku ko?" Abida ta ce "Ba laifi yayi kyau". Ya ce "ina wayar kun saka acont number ɗin?" Siyama ta saki wata murmushin yaƙe ta ce "A haba ga wayar ka, wasa nake maka, Sunana Siyam, wannan Haura wannan Abida, sai Amera". Ta karasa tana nuna kowacce da hannu. A ranta kuwa ta tsinewa rashin acont ya fi cikin carbi. Ya amshi wayar ya na faɗin "Nice name's, sunayen yan gayu, dole wannan sunayen su samu tukuici fa, kuma na riga nayi niyya, dan haka sa min acont ɗin, wannan ra'ayin kai na ne". Siyama ta sake amsar wayar tana tuno ko tana da acont ɗin Umma akanta, tun ma kafin ta gama amsar wayar ta tabbatar da bata da ita. Hakan yasa tana amsa ta mikawa Abida ta ce "Saka masa acont ɗin ki, wayata ta ɗauke". Ta faɗa tayi fuska abunta. Abida ta waro ido jin za'a zubar mata da mutunci. Ta yi murmushi mai kama da kuka ta amsa tayi kamar ta fara sawa sai ta ce "Sorry wayata fa na baro ta a gida, kawai Haura sa masa Naki". Itama ta mikawa Haura da take ta ƙunshe dariya. Ai tuni ta tsayar da dariyar tana kallon Abida da take mata murmushi. Itama tana amsa ta mikawa Amera ta ce "To kawai Amera ta saka tunda naga ita ce take tare da waya yanzu. Amera ta amshi wayar tayi shiru tana tunani. Ai kuwa a ranta tace bari nayi maganin ku". Ta ce "Wayar ta mutu cire ki ɗin?". Hafiz ya cire yana sake miƙa mata. Su dai suna ta kallon su, suna son ganin yadda zata kaya. Amera ta miƙa masa bayan ta gama sawa. Ya amsa ya sake nuna mata sunan da ya fito. Ta ce "Eh shine. Ai kuwa take ya tura mata 100k successful ya nuna mata. Dukkanin su suka turo kai domin ganin sunan da aka Turawa kuɗin. Gaba ɗaya suka bita da kallon mamaki, to ina aka tura kuɗin. Suka nufi cikin gurin Siyama dai hankalinta naga Amera, su kansu sauran ma sun san kaf cikinsu ma babu wacce take yin abu Kamar yar ƙauye Kamar ta, haka zaluka gara ma su suna da yayye masu account ba ita da take shiru ba. Bayan sun zauna aka kawo musu yorgot da figza da ruwa. Suna ci suna ta jansu da hira. Gaba ɗaya hankalin Amera yayi gida, gabanta nata faɗuwa idan ta tuno da Ƙasim. Hakan yasa ta yanke shawarar kawai ta tafi gida ba tare da su Siyama sun sani ba. Ana cikin hira ta mike tsaye tace tana zuwa minti biyu. Abida ta ce "Ina zaki je kuma, karfa kiyi nisa". Ta daga mata kai tana barin gurin cikin sauri. Siyama ta bita da kallo Kamar bata yarda da fitar ta ba, ita dai kuɗin su ne abun jin ta, so take ta faɗa musu ina aka tura. Haka shiru-shiru zata dawo zata dawo amma babu labarinta har kusan minti goma, hakan yasa Abida ta fita waje amma babu ita. Ta dawo ciki tace musu bata ganta ba, nan fa suka runtuma gaba ɗaya amma babu Amera babu dalilin ta. Take suka bari akan gida ta tafi gurin mijinta, suka ci-gaba da hirar su amma dai hankalin Amera ya kasa kwanciya, hakan yasa duk ta rage surutu. Haura da ita ma ta kasa natsuwa ta ce musu gaskiya ya kamata subi bayanta su tabbatar da cewar gidan ne taje. Hakan yasa misalin ƙarfe huɗu suka haɗa yadda zasu gudu su bar wannan samarin. Ɗaya bayan ɗaya suka fara fita har suka gama. Mai keke Napep suka tare suka faɗa masa sunan unguwar suna tafiya suna ayyana abun da zasuyi mata idan suka isa gidan. Abida harda cewa kawai ta basu kuɗin su sai su tafi su barta da mijin da ta zaɓa tunda ita bata san kare mutuncin ta suke son yi ba. Ana sauke su suka ga Ƙasim da abokinsa Nura tsaye da sauran matan da basu tafi ba a ƙofar gidan kamar dai su ake jira.
A bangaren Ƙasim kuwa. Bayan ya sauke wayar daga kunnensa ne ya ce "Kasan Allah Nura, Matar nan bata san waye ni ba, Naso ace ita muka samu a gidan Allah da sai ta faɗa min uban da yasa suka kai min Mata gidan su, ina ruwa na dasu, tunda aka fara shagalin bikin nan kaga kafar ɗaya daga cikinsu a Kano? Amma tsaɓar rainin hankali wai sune da riƙe min mata wai wani an kaita gidan mu wai haka alada tace, al'adar uwarsu". Nura ya ce "Ko ba Komai dai itama ai uwa take a gurin ka, sannan meye a ciki badan ma kai ɗin da zuciya ba, kuma ita Amarya ina ruwanta da kake ta huce haushi akanta da yan rakiyar ta, wannan abun banga abun tada hankali ba wallahi". Ƙasim yayi masa wani kallo ya ce "uwata ko? Kuma babu abun tashin hankali ko?". Yana faɗa ya ja tsaki ya na huci. Nura ya sake faɗin "To dan Allah dai kayi hakuri, kuma zuwa anjima muje a sallami baƙi kowa ya tafi gida haka muma mu sarara". Ya ce "Wallahi babu shegiyar da zan sallama, kuma zuwa anjima idan naje duk ƴar iskar da na samu a cikin gidan na Allah sai dai ta kwana a waje". "Ai kuwa wallahi karya kake yi, amma kasan ba yan gari bane ko, a ina zasu samu kuɗin motar, sannan ko baka sallami kowa ba ai a kwai wanda suke kamar iyayenta ga kuma ƙawayenta". Nura ya sake cewa "Sai kuma kayi idan nine na kawo su". A haka suka koma cikin gidan da suke zaman angwancin nasu. Misalin ƙarfe biyu yauma Nura ya ɗibar musu abinci zai kai musu. Sai kuma Ƙasim ya tashi yana shirya wa domin dai tare zasu je ya faɗa musu cewar kafin yamma kowacce ta tafi haka, kuma yana ta kiran number Amera ɗin bata shiga. Duk yadda Nura yaso da ya hana shi zuwa amma yace to sai yazo ya hana shi shiga gidan sa. Koda suka iso gidan har yanzu a kwai mutane sai dai wasu sun kara raguwa. Bayan sun gaisa Nura ya miƙa musu abincin yana tambayar lafiya dai suke ko?" Suka amsa a tsorace domin dai har yanzu Yan Mata basu dawo ba. Da yake a ƙofar gidan suka tsaya basu shiga ciki ba Nura ya ce "Dan Allah amarya muke son gani zamuyi mata magana?" Matar ta ɗan diririce ta ce "Eh tana wanka ne idan ta fito za'a faɗa mata kazo". "To ina ɗaya daga cikin ƙawayen nata magana angon zaiyi da su?" "Matar ta ce "Ai duk tare suke wankan basu fito ba tukunna?" Ƙasim ya ce "Tare suke wankan kuma?" "Kafin tayi magana wata daga baya ta ce "Maganar gaskiya fa amarya da ƙawayen ta basa cikin gidan nan, wai sun tafi yawon ganin gari tun ɗazu, gara ma a faɗa maka gaskiya kafin ma wani abu ya faru kace baka sani ba". Nura ya buɗe baki da hanci da ido yana kallon Ƙasim da shima yake ta kallon matar. Tuni aka shiga basu labarin yadda suka fita ɗin da kuma yadda aka yi da su akan karsu fita amma suka ƙi. A fili Nura ya ce "Matsalar auran Ƙwaila kenan mai ƙawaye irinta, sam basu da hankali. "Ƙasim ya ce "Kuma ku fissabillahi sai ku barsu su fita da ita idan su basu da hankali, haba dan Allah, meye amfanin ku, ko sunfi ƙarfinku ne". "Matar tace "To so kake mu kama su da dambe bayan mun faɗa musu sunki ji?" Wata ta ce "To mu yaya batun tafiyar mu, dan Allah ko zuwa anjima ne a samo mana Mota mu tafi, mun gaji da wannan zaman haka". Ƙasim ya ce "Idan har sai an kawo muku mota zaku tafi kar Allah ma yasa ku tafi, su kuma wannan yaran Allah ya dawo dasu, wallahi sai na koya musu hankali, ba su basu da hankali suna yin abu Kamar yan iska ba, nifa dama gaba ɗaya yaran nan haushin su nake ji, tun ma ba wannan shegiyar Siyaman ba mai dogon ƙafa kamar yar raƙuma, duk nasan ita zata shirya musu wannan abun, Allah yasa wani abu ya samu mata ta, wallahi ba zan yarda ba". "Nura ya ce "To wannan fatan tsiyar da kake yi fa, kai ba zaka ce Allah ya dawo dasu lafiya ba sai wani fatan samun matsala. Gaba ɗaya Ƙasim ya shiga damuwa ya samu guri ya zauna yana kiran dawowarsu, har karfe Uku, har karfe huɗu babu yan mata. Bayan sun yi Sallah sun dawo kenan sai gasu an sauke su a keke Napep, sai dai ganin babu Amera ne yasa ya zuba musu ido ganin ta ina zata baiyana...✍️
Yan Mata masu abun mamaki