BADAƘALA

Part 10

by @chefmuaysh


BADAƘALA 

✍️ 
A'isha Hamza

ABUJA 

WUSE

Manyan motoci ne guda uku suka tunkaro unguwar daidai wani hadadden gida wanda ganin farko saika ɗauka wata tsararriyar Hotel ce akayi saboda kyawunsa tundaga kan jibgegen get ɗin gidan kafin mu shiga ciki na tantance muku 

 faskeken Glass ne da yake kawo haske yake daukewa wanda saika ɗaga kanka zaka iya gane da akwai shi an rubuta SHAUBAN FAMILIES HOME

Motar dake gaba ce ta danna horn da karfin gaske daga ciki sai ga get ɗin na zugewa alamar mai gadi ne ta ciki yake buɗewa suka shiga danna kai cikin gidan 

Parking space ɗin gidan suka nufa wanda shi kansa abin kallo ne a jere suka tsaya bayan a ƙalla akwai motoci kusan bakwai a cikin parking space ɗin ga kuma uban filin da zai iya daukar wasu mota goman 

Motar farko aka buɗe driver ne ya fito ya buɗe bayan motar saiga wasu yan mata kyawawa masu ji da aji sun fito suna faman yauki kamar miyar kubewa ɗaya sanye take da bakin wando sai rigarta da bata ƙarasa gwuiwa ba tasha Kitson attachment har gadon bayanta sai wata yar ƙaramar hula data sanya mai kama da p.cap tana danna waya a hannun ta kirar iPhone 

Wadda ta biyo bayanta daga gani basu wuce Sa'anni don zaka iya kiransu da twins ma saboda suna kama saidai dan bambancin wasu abubuwan na jiki ta farkon batada kiba ta biyun kuma tanada yar kiba itama ba sosai ba ita kuma sanye take cikin Pakistan sky-blue da alama waya take don tana manne ne a kunnenta itama dai iPhone dince ta yan mata 

Mota ta biyun data ukun ne suma aka buɗe suka fara fitowa saidai ta ukun ba driver ne ya buɗe ba saɓanin ta farkon data biyun suma dai wasu yan matan ne kowace biyu biyu kuma duk kusan Sa'annin juna Saida na farkon zasu kai 21 years na biyun kuma 17 na karshen ne yara da alama kuma daya zata girma dayar duk da bada nisa ba 
Suma dai kusan duk shigar tasu ɗaya ce sai daya ce da tasaka Abaya maroon tayi rolling mayafin ta cikin wanda zasu kai 17 years ɗin 

Wanda yake tukin motar ta uku ne ya fito cikin shigar kananun kaya saurayi ne zaikai 23 da haihuwa fatarsa irin black beauty dinnan Sai dan sajensa na samartaka daya fara fitowa ya kwanta luff yayi bala'in yi masa kyau 

Hanyar shiga suka nufa su dukan su hada saurayin da yake ta faman cin magani daga gani ransa a bace yake 

Wata kofa suka nufa mai dan girma karamar cikinsu ce tayi gaba tana kiran Mommy I'm back Mommy I'm back Kamar mai raira waka 

Da gudu ta ƙarasa wajen kofar ta murda handle ɗin ta faɗa ciki 

Haɗuwar parlour Bazan iya kwatanta muku ba don kujeru manya manya na alfarma parlour saiti biyu ya dauka da farko idan ka shigo zaka dauka parlour biyu ne a hade saboda yanayin da aka kawata shi gefen dama green ne ga wata tv kamar a jikin bangon aka gina wajen da'ita sai daga hagu kuma Black da wani faskeken Glass table a tsakiya daga can gefe kuma ga wani dan step kamar sabon gini za'ayi wajen matattakalar bata wuce hudu zuwa biyar wajen yana dauke da wasu manya manyan dining table guda biyu duk ɗaya yana daukar mutum takwas gefe da gefe huɗu huɗu kowane da design dinsa 

Stairs uku ne a parlour left right and middle da alama kuma kowane da reshen nasa sai corridor daga gefen middle stairs ɗin mai ɗauke da dakuna shida uku na kallon uku 

Wata babbar macece zaune saman 2 seater ta sauko da ƙafafuwan ta ƙasa sai wata yar matashiya duke tana danna mata su da alama tausa ta sanya ta a hakan 

Sanye take cikin atamfa tasha daurin nan wai shi ture kaga tsiya sai glass fari manne a fuskarta da computer a hannunta da alama wani aikin takeyi mai muhimmanci 

Muryar yarinyar ne yadan sanyata dagowa tana sakin Murmushi oh my daughter I miss you da gudu takaraso har tana tunkude mai tausar ta faɗa kanta tana faɗin miss you more my Mommy 

Peck Mommy din tayi mata a goshi kafin takai dubanta ga yan matan dake shigowa gaba ɗaya tana ƙara gyara zaman glass ɗin nata akan fuskar ta 

My babies welcome ya duk kunyi laushi da alama kun gaji ta faɗa tana yar dariya tare da janye yarinyar data manne mata tana ma mai aikin nuni data tashi ta tafi 

Kamar jira suke kuwa ɗaya daga cikinsu itama ta karaso tare da dan rungumar Mommy din tana faɗin wallahi Mommy akwai gajiya gashi Saida su Anty samrita da Anty Anisah suka batawa yaya Farouk rai a wajen 

Wadda aka kira da Samrita da Anisat ne suka galla mata harara Samrita bata tsaya ba tayi middle stairs dama tunda ta fito a mota take wayar har yanzu kuma bata gama ba 

Anisat kuma karasowa tayi itama ta rungume Mommy ɗin tana faɗin Mommy kinsan yaya Farouk dai basai na faɗa miki ba zuciya kamar kuturu ba wani abu fa akayi masa ba shine yaketa faman dacin rai har muka baro wajen.

Da guda guda suka rungume ta ita kuma tana musu sannu da gajiya biyu suka ƙara nufar middle step suma wai sunaso suje suyi wanka parlour ta zama daga Anisat sai Mommy da yaran nan guda biyu autar Mommy sai wadda ta ɗan girme mata 

Suma basu wani dade ba suka mike kowa yayi hanyarsa dama wannan saurayin da yaketa ɗacin rai tun shigowar su ya fice bai karasa shiga parlour ɗin ba ma 

Wajajen karfe biyu na rana wata yar matashiyar budurwa ta nufa stairs ɗin farko mai ɗauke da parlour sai kofofi a cikinsa da alamu kowace kofar bedroom ne da koman sa a ciki 

Kofa ɗaya ta danna wani madanni a kofar dakin bata jira ba da yake akwai hanyar da zata sada ka da dayan stairs ɗin ta cikin kowane, nan tabi sai gata a middle stairs sabanin stairs ɗin farko wannan babban parlour ne yafi na farkon sai wani stairs ɗin jikinsa alamar akwai wata saman kenan a cikin gidan, kofofi ukune a tsakiyar parlour duka kusa da juna sai wasu biyu a daga corridor wajen stairs ɗin kowace kofa Saida ta danna madannin kofar ta wuce batareda ta tsaya ba har zuwa biyun corridor daga nan kuma ta bullo ɗayan ɓangaren wato stairs ɗin karshe nan kuma iri ɗaya ne komai da komai dana farkon kofa ɗaya ta danna tayo kasa abinta sai kuma ta tuna ashe ta last stairs ɗin ma tafita unguwa batanan tadan taɓe baki tawuce

Tana saukowa ta hango Farouk zai hau sama murmushi ta danyi sai kuma tace ehemm alamar ya juyo kenan 

Har yadan wuce da sauri yana hawa ta middle sai ya juyo shima murmushin ya maida mata sai ta daga hannu tana masa magana dashi 

Shima hannun ya daga irin na kurame yana maida mata sai ta ɗan bata rai tana make kafada sai ya sake yin magana da hannun kafin tayi murmushi alamar taji daɗi hannu ya daga mata alamar yana saukowa yanzu ta girgiza kai kawai ta wuce 

Dakunan da suke ta corridor ta nufa na biyu daga hannun dama ta shiga tare da sallama wata budurwarce a ciki kamarta wadda take ma hajiyar nan tausa a parlour dazun tana cin abinci ta amsa sallamar tare da faɗin Indo kindawo

Eh ta amsa tana ya mutse fuska sai kuma tace ina fatan dai nima kin zubomin abincin don bazan yi miki aikin banza ba Allah ya taimakeni ma ban haɗu da kowa ba sai yaya Farouk tana murmushi alamar jin daɗin hakan data kasance 

Mai cin abincin tace ohni zubaida Indo wai me kike so kizama a gidan nan bakida zance saina yaya Farouk wallahi ba ruwana keda Hajiya Mommy 

Yar dariya tayi tace haba zubaida daɗi na dake kenan daga faɗa miki Abinda yafaru zaki kaini inda Allah bai kaini ba kuma idan ma nayi zancen nasa ai ba laifi bane saboda ya Farouk yanada matuƙar muhimmanci a gareni 

Taɓe baki Zubaida tayi kedai kika sani don wallahi iska na wahalar da mai kayan karane tanajan siririn tsaki 

Itama Indo ɗin tsaki taja tana aika mata da harara tare da faɗin falyaqul khairan dai kuma inshaa Allah bakinki bazai kama ni ba zakiga yanda za'a sha shagalin bikinmu da yaya Farouk a gidan nan 

Shakewa zubaida tayi da abincin tuni ta nemo ruwa Saida ta dawo dai-dai kuma ta babbake da dariya tana faɗin wallahi Indo bantaba sanin haukan naki yakai haka ba wato ke har mafarkin auren yaya Farouk kike to sannu kinji ta faɗa tana ƙara kurbar ruwan hannunta 

Mikewa Indo ɗin tayi tana faɗin aike Zubaida mutum bazai taba kawo zance ba kiyi mashi fatan Alkhairi dan masifa sai na tsiya ki canja hali ta nufi toilet ɗin dakin tana bambami itadai zubaida tanata cin dariya abinta 


Da guda guda suka fara saukowa daga saman stairs din da alama kowace ta canja shiri don duk ba kayan dazu bane a jikinsu 

Dining table suka nufa saidai kowa da inda ya nufa uku suka nufi dining mai green colour Sai uku da Mommyn da itama ta sauko yanzu suka nufa dayan dining ɗin 

Mommy Samrita Suhailat sai yar autar ta wato sofiya yar ƙaramar yarinyar gidan baki daya suna zaune a dining ɗaya biyu suna facing biyu sauran kujerun bakowa 

Sai dayan kuma Anisat ramlat da karamar su mai shekara 15 wato raudat sukuma duk a jere suka zauna 
Wata babbar macece don zata haura hamsin a duniya ta karaso dining ɗin tana faɗin ranki ya dade ayi hakuri dan Allah ina can lokacin Sallah ne ya kubuce man shi yasa ban iso da wuri ba 
Samrita ce taja uban tsaki kafin tace waike iyah bakida aiki ne sai komai kice sallah sallah kamar ke kaɗai ce musulma gidan nan 
Suhailat ta katse ta da faɗin kinga yaya samrita rike zancenki tukun nidai iya zubamin fried spaghetti da naman kan da nafada Miki xanci yau 

Matar da aka kira da iya bata saurari Samrita ɗin ba ta cigaba da abinda ya kawo ta Saida kowa ya fadi abinda zaici tayi serving dinsu uwar tareda ya'yan ta kuma 

Su kuma su Anisat ramlat da raudat da kansu sukayi serving duk abinda suke so dan dama inda sabo sun saba saboda gidan kowa da mai aikinsa kuma Meeymeey wato mahaifiyar su tace ba wanda zai dinga musu wani serving su dingayi da kansu duk da da farko sun so bata ransu amma ta nuna musu dalilin yin hakan kuma bai dace suce duk abinda yaran Mommy sukayi suma sai anyi musu ba hakan ba dai-dai bane ta nuna musu duk da kuwa itama tana iya kokarinta akan komai donta faranta ma yaran nata Duk da mai kula da gidan baki ɗaya mutum ɗaya ne shi yake ma yaran komai a yanzu bai kuma banbanta su ko kadan 

Bakajin komai sai karar spoon a wajen kwas kwas kwas Anisat ce data ɗan fara ture plate ɗin gabanta wai ta koshi ta zuba juice tana dan kurba tareda duban inda Samrita take zaune tace waini Samrita baki dai manta da sakon mutumin nki ba 

Kamar jira take dama a tambaye ta ɗin tace ban manta ba Anisat don order nayi masa inajin zuwa anjima za'a kawo gashi bansan jirgin karfe nawa zamu bi ba goben 

Taɓe baki Mommy tayi tace to ai gara dai wani cikinku ya kirashi yaji karfe nawan zaku tafi sai kunsaki jiki gobe yace jirgin 9 ko 10 zaku bi kuma kuce baku shirya ba yace shirin ubnmi zakuyi ta faɗa tana ƙara tabbatar musu da hakan 

Ajiyar zuciya Samrita ta sauke kafin tace Mommy ke ya Kamata ki taimaka mana dan wallahi Ni fushi ma yake dani kwana biyun nan 

Mommy data mike tace kanku akeji dai gara ma ku kirashi da kanku ko kuma kawai kuzama cikin shiri a koda yaushe 

Autar Mommy tace Mommy nima dana gama primary za'a kaini school din su yaya Suhailat Koh

Mommy tajuyo tana faɗin ah ah sofiya bazakije boarding ki barni ba 

Sofiya tadan taɓe baki Suhailat tace keda rigimar nan waxai kaiki boarding kwana ɗaya kice ke Mommy zaki raudat ta amshe da faɗin wallahi yaya Suhailat Bama sai ankwana ba indai sofiya ce zatace gida take so 

Mommy dai tawuce saman dakinta sai ga Farouk ya sauko inda Mommy ɗin ta tashi nan yasamu waje ya zauna bai tanka ma kowa ba ya fara zuba abincin sa yanaci har suka gama suka tashi suka barshi anan zaune 

Zaune suke su kusan biyar a dakin yan mata uku ne sai babbar macen nan wato iya tana zaune sun saka ta a tsakiya tana basu labaran su nada 

Indo ce tace wallahi iya sai inji dama zamanin ku nazo komai gwanin ban sha'awa amma wannan zamanin bawani jin daɗi ta faɗa tana yamutse fuska 

Zubaida ta katseta da faɗin ke wallahi Indo muma zamanin nan akwai daɗi don dai ke kawai ba'a ƙauye kikayi rayuwa ba amma ƙauye akwai daɗi in faɗa maki ta faɗa tana murmusawa alamar ta tuna wani abu mai muhimmanci da take dashi a kauyen nasu 

Wata babba ce a cikinsu don duk ta girme masu Indo tace to wai iya ni abinda ma ke bani mamaki shine lokacin yarintar baya iyaye basu damu da inda yaransu zasu shiga ba saboda sun san ko ina sukaje da sunyi ba dai-dai ba za'a nuna musu amma banda wannan zamanin kowa nashi yasani 

Iya tace ai mardiyya zamanin da ko ina akwai iyaye saboda dakayi ba dai-dai ba za'a gyara maka amma yanzu ba wanda yake gyarawa dan wani kuskure idan ka gyara iyayen yaro suce ka takurawa dansu idan kuma ka kyale shi kuma wasu suce don ba danka bane abin ne sai a hankali gaskiya Allah yasa mu dace dai amma duk abinda zakayi bazaka taɓa burge mutane ba shi yasa ake cewa kayi don Allah saboda shine kaɗai yasan zahirinka da kuma badininka 

Indo ce ta zunguro ta kusa da'ita tana faɗin wai ni jalila lafiya kike kuwa anata magana kinyi tagumi hankalin ki baya kanmu 

Zumbur wadda aka zunguro ta mike tsaye tana wuƙi wuƙi da idanu kamar an kwashewa karya ya'ya agogo ta daga kai ta kalla ta cikin ɗakin bata tanka musu ba kawai tafice 

Zubaida tace waini iya jalila ko lafiya kusan kwana biyu kenan a gidan nan ina ganinta cikin damuwa ko me ya faru 

Mardiyya ce tayi murmushi irin na tantirancin yan bariki tace tagano abinda yafi ƙarfin tane wajen sa ido 

Iya dai batace komai ba sai Indo ce tadan tsurawa mardiyya ido don tagane ina zancen nata ya dosa da tace ta gano abinda yafi karfinta wajen sa, ido to mekenan take magana akai Indo ta faɗa acikin zuciyar ta sai kuma tadan taɓe baki itama ta mike tace zataje ta gyara ɓangaren Meeymeey don tasan takusa dawowa daga unguwar data fita yau 

A parlour ta iske jalila tsaye bakin stairs da faranti a hannunta mai ɗauke da tea cup Sai tiriri yake kuma ba tafiya take ba ta tsaya tana sharar ƙwalla 

Jin tafiyar mutum a bayanta yasa ta miki hanya ko waigowa batayi ba tana ƙara share kwallar data ɗan silalo mata 

Indo tayi turus tana kallon ikon Allah 🤔 ita kuma jalila meyake damunta a gidan nan haka ne, gaskiya dole sai naji ta faɗa tana juyawa ta nufi stairs ɗin da zai kaita ɗakin Meeymeey

Tunda tadawo dakinsu take kai kawon ko jalila tadawo ɗakunan su da yake suna kallon juna amma idan ta leka sai taga batanan tun tana tsammanin ta har ta fidda rai har Meeymeey tadawo yan gidan suka fito sukayi dinner dukda bakowa ya fito ba saboda basu cika damuwa da abincin dare ba amma shuru ba jalila ba labarin ta 

Shirin kwanciya tayi har tahau gadonta sai kuma ta mike ta buɗe kofa ta nufa dakin jalila ɗin knocking tayi jin shuru ya sanya tadan buɗe kofar ta leka amma bataga kowa har toilet Saida ta buɗe yanzu dai amma babu jalila agogon dakin nata ta kalla taga 11:30pm 

Tana shirin fita taji an turo kofar an shigo nunfashi ta sauke da tunanin jalila ce tadawo amma sai taga saɓanin hakan mardiyya ce ta shigo tana taunar chewing gum a bakinta tana wani far far da idanu daga ƙasa har sama tagama kalle Indo da ruwan mamaki ya daskarar da'ita kafin tace 

Indo kenan na lura yarinyar nan kinfiye shisshigi yanxu me ya kawoki dakin jalila ko kinzo ne lallai sai kinji abinda yake damunta yar sa,ido 

Indo fa ba Kanwar lasa bace ba don haka ta shiga bata amsa ai yan sa,idon da bin sahun mutane sunada yawa dan naga alamar kema shisshigin ne yakawo dakin jalila ɗin Koh 

Yar dariya mardiyya tayi kafin tace dama tunda nazo gidan nan ina lura dake bakida kunya ko kaɗan Indo saboda haka Karki bari musa kafar wando ɗaya dake 

Tsoki Indo taja kafin tace ai indai tsoho baiji kunyar hawa jaki ba haka jaki bazaiji kunyar tumoshi da ƙasa ba ta ƙare maganar a zafafe tare da bin gefen mardiyya ɗin tayi ficewar ta abinta 

Mardiyya ta cije kunburarren lips dinta tace lallai yarinyar nan da alama zan saita maki zama a gidan nan dan idan kinsan wata bakisan wata ba ita kanta shugabar taku iya ai nan taganni nan tabarni nasan yanda zanyi dake ja'ira kawai fuuu itama ta fita tabar dakin jalila ɗin 

Zagaye indo tafara yi cikin ɗakin ta da yake kowa na yan aikin da dakinsa su biyar daki ɗaya ne acikin shidan babu mutum a ciki 

Ta kwance wannan ta saka wancan don zata iya cewa tunda mai aikin yaran Meeymeey ta gudu duk wadda aka kawo basa zama suke guduwa saidai a nemesu a rasa gashi yanzu tunda mardiyya da jalila suka zo sun dade amma ita jalila kwana biyu tana cikin damuwa kuma da alama ita mardiyya ɗin tasan menene yake faruwa shi yasa take nuna ko in kula akan jalila ɗin bayan da sukazo lokacin bazata manta ba cewa akayi jalilan kanwar mardiyya dince amma daga baya ta lura jalilan ma bata sakewa idan mardiyya na waje jin motsin mutun daga waje yasa ta dawo daga duniyar tunanin data shiga kasancewar a buɗe tabar kofar dakinta yasa tajiyo motsin mutun wajen ma 

Hanyar fita ta nufa saidai kafin ta ƙarasa anja kofar jalilan da alama kuma itace tadawo a gigice 

Tofah ga wani gidan mai kunshe da nashi tarin tambayoyin amma muje gaba dan idan akace za'a tsaya tambaya babu ranar gama amsata har sai mun shiga sabon babin BADAƘALA tukunna 




Tunda asuba saboda dokin tafiya makaranta basu koma bacci ba suka hau wanka da shirya kansu cikin materials iri ɗaya duka green da red flowers 🌻 a jikinsa sunyi kyau sosai don a parlour suka dawo suka zauna sunata kallo kuma suna ɗan taɓa fira kaɗan kaɗan 

Wajen karfe takwas Imran yazo gidan gaishe shi sukayi ya amsa cikin kulawa yace yan makaranta har anyi me kun shirya kenan suka gyada kai alamar eh 

Murmushi yayi sai yace to yanzu bari in kawo maku breakfast tunda bai kamata ayi tafiya anajin yunwa ba 
Khairiyya tadan rike ciki tareda faɗin wallahi kuwa kamar kasan nafara jin yunwa 
Ayrah tadan harare ta tare da taɓe baki Imran cikin zolaya yace ya naga kina hararar ta Ayrah ai gaskiya ta faɗa Murmushi sukayi baki ɗaya kafin ya kuma fita daga dakin 

Bai dade ba yadawo musu da breakfast hada nashi anan parlour shima ya zauna kowa yaci nashi suka cigaba da kallo yana ɗan jansu da fira 

Kiran wayar sane yasa mike ya fita waje bai dade ba sai gashi sun dawo da biyu daga cikin masu kula da gidan 
Akwatinan su Ayrah yace su fita dasu kafin ya dube su yace su tabbatar basu manta komai ba yanzu zasu tafi 
Murna wajen Khairiyya ba'a magana itama ayrah ɗin tana farin ciki sosai saidai ba yabo ba fallasa zakaga fuskar ta 

Basuyi mamakin ganin babu uncle Sameer ba don suna tunanin kila a hanya ko a makarantar zai iske su aikuwa hakance tafaru amma sabanin tunanin su kallo fa ya koma sama Ayrah tafara girgiza domin yanzu ɗin ma suda suka shirya zuwa makaranta a kano saigasu a airport 

Mamaki ne ƙarara kwance a fuskarta don har takasa cewa uffan sai baza idanu take ta ko'ina abinda ya ƙara bata mamakin ma shine ganinsu a private jet zasu tafi 

Hajiya Khairiyya kuwa sai Murmushi ake xa'a hau jirgi anan suka haɗu da uncle Sameer yana jiransu basu ɓata lokaci ba suna zuwa suka tashi tiiiii sai sai birnin tarayya Abuja 🛫🛫🛫

Tofah wannan makaranta dai ta cika tsawo amma dai bari inyi shuru mu ci-gaba 

Rana bata ƙarya ✍️

Misalta girman makarantar ba mai yiwuwa bane dan da ka shigo garden zaka fara cin karo dashi irin hadadden nan wanda yasamu kula sosai korayen ganye sai karkadawa suke ga mosque a gefen hagu daga can nesa zaka fara hango manya manyan offices na malamai da principals duka kasancewar makarantar akwai bene wasu na saman wasu 

Sudai tunda motar su ta danno kai cikin makarantar fa suka fara leke ta window Allah yasa ma a rufe glass ɗin yake da mutuniyar taku Khairiyya ta zura kai 

Jefi jefin wasu motocin ne da suka rigasu shigowa sai wasu kuma daga bayansu suke shigowa kasancewar Sunday ce da alamu hutu akayi yau ake dawowa saboda students su kimtsa komai kafin gobe a shiga class kenan 

Wajen wani office daga gefe sukayi parking uncle Sameer ne yafara fitowa da yake suna baya shida Khairiyya sai Ayrah dake kusa da driver itama ta fito uncle Sameer ne yace su biyo shi 

Cikin office ɗin suka shiga wanda daga waje an rubuta Principal office akwai parlour daga ciki mai ɗauke da kujeru guda uku da table a tsakiyar su sai Center carpet dan madaidaici sai tv anan yace musu su zauna shi kuma ya karasa ciki 

Ƙasa ƙasa ake magana daga cikin office ɗin wajen minti sha biyu kuma sai gashi ya fito hannusa rike da wasu takardu guda biyu 

Gaba yayi yace su biyo shi ɗan waigawa Ayrah tayi kasancewar sunzo fita ne zaka iya hango cikin inda ya fito kuma bai jawo kofar ba da alamu babu kowa a ciki ta ayyana a ranta sai kuma tace kila kuma bayan wannan din can ciki ma akwai wani 


Suna fita sai ga wata yar tsohuwa ba sosai ba sanye take cikin uniform blue black babu ko mayafi akanta ƙoƙarin dukawa take ta gaishe da uncle Sameer yayi saurin dakatar da'ita cikin girmamawa da kuma mutuntawa suka gaisa kafin ya nuna mata su Ayrah yace ga sabbin daliban naku nan a kula mana dasu dan Allah 


Inshaa Allah ranka ya dade karka damu za'a kula sosai mungode ta faɗa suka nufi wajen mota baki ɗaya shida driver suka fara fiddo musu da kayansu sai wannan tsohuwar tace tana zuwa bata dade ba sai gata da wasu matan daga ganinsu basufi 32 years ba su biyu kowace taci bleaching da alama dai basuji irin uniform ɗin ta ne a jikinsu kayan aka nuna musu nasu Ayrah suka shiga dauka 


Saida suka gama kwashe kayan suka tafi basu sake dawowa ba Khairiyya fa kuka aka fashe dashi wai ita uncle Sameer bazai tafi yabarta ba daƙyar ya rarrashe ta har Saida ya kira mata Abbanta suka gaisa har yace zaizo shima idan an kwana biyu kafin suka rabu ya shiga mota suna daga masa hannu ita kuma Khairiyya tana sharar ƙwalla 


Sun shagala da kallon motar su uncle Sameer harta ɓace maganar tsohuwar nan ta dawo dasu hayyacinsu ku wuce muje koh juyowa sukayi gareta sukabi bayanta 


Wannan fa shine suda suke tunanin da anzagaya baya zasuje inda zasu sai sukaga ta nufi wata ƙatuwar mota wai su shiga suna ƙoƙarin shiga saiga wata yarinya sanye cikin riga da wando sun kama jikinta itama tazo zata shiga Khairiyya tasaki baki tana kallonta Saida ta ja tsoki mai karfi kafin tace ke mayya ce ne kike kallo na 


Ayrah ce ta juyo tana duban wadda tayi maganar don ita a tunanin ta ma yarinyar batajin Hausa sai gashi tayi hausar Khairiyya dai ta kasa tankawa sai dukar da kanta datayi ƙasa tare da matsa ma budurwar tawuce kafin suka bita ciki 


Doguwar mota ce sosai sai kujeru biyu hade daga gefen dama haka ma daga gefen hagu kamar dai ka shiga jirgin ƙasa waje ɗaya suka samu suka zauna duk wani iri sukeji kasancewar su baƙi a wajen dakuma yanayin yan makarantar gaba ɗaya ya birkita su gashi da sun daga ido zasu ga su ake kallo a cikin motar alamar anga bakin fuska da kuma yanayin yadda suke takure kansu ya nuna su 


Wata budurwarce ta taso daga kujerar ta taxo inda suke saida ta ƙare musu kallo daga sama har ƙasa tana tauna chewing gum kafin ta taɓe baki sai kuma tace "Are you new here at this school?” (Ku sabon zuwa ne a makarantar nan ) Ayrah ce tadan daga mata kai alamar eh dan ta fahimci abinda tace ɗin 


Ok ta faɗa tana karkada kai what's your name ta nuna Ayrah da yatsanta da yasha uban jan farce ga akaifa zako zako 


Ayrah ta fada kai tsaye ba tareda takara kallon inda take ba ta dukar da kanta don tagaji da kallon da yan cikin motar suke musu Khairiyya kuwa kamar jira take a tambaya sunanta 


Budurwar tadan taɓe baki tare da maimaita kalmar Ayrah a iya labbanta ba tareda kaji sauti ba ta juya kan Khairiyya tace kefa Khairiyya ta daure fuska tamau kafin tace sunana uwarki tana zare mata idanu alamar kinada abunyi ne 


What budurwar ta faɗa da ƙarfi tare da daga hannu zata wanka ma Khairiyya mari taji an rike hannun juyowa tayi taga wace isasshiyar ce ta rike mata hannu sai taga Ayrah ɗin ce 

Ayrah bata kalleta sai yarfar da hannun ta tayi a ƙasa tare da faɗin karki fara wannan kuskuren ta buɗe baki zatayi magana saiga wannan tsohuwar data rako su ayrah mota ta shigo tana faɗin ke Hamdiyya me kukeyi nan dan juyawa tayi taja dogon tsaki kafin ta koma mazaunin ta 

Group suka haɗa daga baya suna kuskus sudai su Ayrah basu bi ta kansu ba tsohuwar ce ta karaso inda suke kafin tace kuyi hakuri kunji yan mata ku sabbin zuwa ne amma a sannu zaku saba da dabi'un yan makaranta kuma saidai koda wasa karku bari wasu su rainaku domin zaku zama mujiyoyi a cikinsu dukkan wanda kuka gani a makarantar nan to mahaifinsa fa Saida ya tara kafin don haka ku kula sosai tana kai ayah tafice tabarsu sun saki baki suna kallon ta 

Khairiyya ta dubi Ayrah tace wai Ayrah kenan nan makarantar ta yaran masu kuɗi ce koh 

Ayrah tace eh Khairiyya tun daga zubinta Nima na fahimci hakan amma ai kinga su uncle Sameer sunada kuɗi sosai shiyasa suka kawo mu nan ɗin 

Dan jinjina kai tayi kafin tace haka ne Ayrah amma kinsan mu dole zasu dinga gane cewa ba ya'yan masu kuɗi bane ba koh 

Ayrah tace ah ah Khairiyya ba dole sai sun yarda munada kuɗi ko bamuda kuɗi ba mudai karatu mukaxo saboda haka mu maida hankali akan karatun kawai zaifi mana kuma komai dai-dai gwargwado ba abinda ba'a kawo mu dashi ba dan ina ganin har wani abun yayi mana yawa ta kare zancen tana ƙara jaddada wa, 

Khairiyya tace haka ne suna zaune sai gashi kamar wasa motar ta cika da yan makarantar duk yawanci daga Sa'annin su sai wanda suka girme su kusan dai duk kansu ɗaya yan makarantar wanda suke shigowa motar tunda motar ta tashi kuma sai kowa yayi tsit kamar bakowa a ciki sai wadannan masu uniform ɗin ke kaiwa da kawowa cikin motar tana tafiya 

Abin mamaki bai karewa dan tafiyar tasu batada nisa amma Saida suka shiga wani get kuma da dan nisa kafin suka fara ganin wasu gine ginen sama da ƙasa sama da ƙasa 

Tsayawar da akayi wasu suka fara sauka har sun mike saiga ɗaya daga cikin masu uniform ɗin tace dasu ba anan zasu sauka ba hada wannan budurwar Hamdiyya itama ta sauka su kuma suka ɗan ƙara tafiya ta wani titin daga baya saiga wasu gine ginen anan akace su sauko duk basuda yawa kasancewar yawancin daliban sun san kan makarantar kowa yana fitowa yake nufa dakin da yake su kuma saidai suka tsaya suna kallon ikon Allah 🤔 


Daya daga cikin masu uniform ɗin ce tace su biyo ta ta wani corridor na middle step suka bi sai suka hau saman stairs ɗin daga gefen dama kofa biyu ce haka daga hagu ma kofa biyu ce daya daga hagu sukaga tasa key tana budewa kasancewar kofar a kulle take Saida suka shiga nan ma dai duk sai baza idanu suke ganin dan ƙaramin parlour mai ɗauke da dining mai daukar mutum huɗu sai fridge madaidaita guda biyu kowane da gefensa alamar na kowane dakin da nasu sai Center carpet iya haduwa amma ya haɗu parlour ɗin iya abinda ke cikinsa kenan sai kofa ɗaya daga dama ɗaya daga hagu 

Ta daman takara zura wani key ɗin ta buɗe sudai sunata binta suna baza ido 

Tofah nan kallo yaƙare musu gadaje biyu ne masu kyau a gyare suke kamar ba wanda yataba zama a dakin sai wardrobe madaidaita kowane gado daga gefensa sai kofar toilet sai mirror da dan ƙaramin stool komai dai yaji a ɗakin 

Khairiyya tace Ayrah kina ganin abinda nake gani kuwa sai kace ba makaranta mukazo ba matar ce tayi Murmushi tace to ke bakisan cewa makarantar haka take ba kenan ko gida ba'a miki bayani ba 

Ayrah ce ta katse su da faɗin don Allah Anty ya sunan makarantar nan sakin baki tayi sai kuma tace ikon Allah 🤔 waiku iyayen naku basu gaya muku komai bane gaku dai kamar masu wayau amma dai sai kuma ta yanke zancen da faɗin sunanta SHAUBAN INTERNATIONAL SCHOOL 

Ayrah tadan jinjina kai tare da maimaita kalmar shauban dan jimm tayi Saida sukaji matar tana musu sallama tace zata dawo yanzu za'a shigo musu da kayan su suka amsa da toh 


Tana fita Ayrah ta faɗa toilet alwala ta dauro ta fito domin lokacin Sallah ya gabato gaban mirror ta ƙarasa tana ƙara kallon kanta tana sakawa da warwara a cikin zuciyarta tare da faɗin sai nagano ku gaba ɗayan ku 


Khairiyya tace suwaye zaki gano kuma,

Ayrah kin juyowa tayi don batasan zancen nata yafito fili ba sai tace wannan makaranta nakeson ganin komai na cikinta 

Murmushi Khairiyya tayi tare da faɗin kamar kinsan abinda yake zuciya ta kenan Ayrah inaso nasan cikin makarantan nan sosai nima wallahi 

Ayrah tace zamu sani Khairiyya saidai na lura makarantar nan sai mun dage zamu iya zama a cikinta domin gaba ɗaya yaran makarantar nan yawancin su sangartattu ne kuma basuda mutunci sosai takare zancen tare da juyowa suna fuskantar juna kasancewar Khairiyya na zaune daga gefen gado ita kuma tana jikin mirror 

Khairiyya tace nima na lura da hakan Ayrah amma su ɗin yawancin su nasan yaran masu kuɗi ne ki duba fa kiga yanayin shigarsu ma kiga fa yanda suke wani saka riga da wando ga attachment akai ko kunya basuji 

Taɓe baki Ayrah tayi tace to dan sunada kuɗi ba hakan yana nufin zasu taka mu mu kyale su ba Khairiyya dole idan muka ce zamu dinga shuru to tabbas zasu ce zasu ci abinci akan mu ne 

Knocking kofar ne ya dakatar da firar da suke Saida suka bada izini kafin aka shigo wannan ce dai wadda ta fita sai wasu ma'aikatan masu irin uniform ɗin ta su biyu da kayansu suka shigo baki ɗaya 

Shirya musu suka farayi kowa suka tambaye ta wanenen trolley nata Ayrah tace su bari zasu gyara da kansu amma sukace aikin su ne ai 

Dole suka haƙura suka kyalesu saidai da lokacin da aka gama fitoda kayan Ayrah tass na sanyawa saiga ɗan buhun akwatin nan nata ƙoƙarin fiddo shi daga ɗan buhun matar nan keyi da sauri Ayrah ta ƙarasa kusa da'ita tana faɗin Nagode hakanan Anty bari in ƙarasa Ayrah bata jira taji me zatace ba ta mika hannu ta karba kayanta tayi gaban wardrobe ɗin ta saka ta daga saman kaya da tunanin idan sun fita saita sama mata wajen zama 

Matar dai tadan taɓe baki tare da faɗin meye haka yarinyar nan ta rikice akansa aiko saina gano menene a zahiri kuma tadan saki murmushi kafin ta nufi wata locker mai sama da ƙasa kamar hade take da bango a dakin ta saman aka buɗe aka shiryawa Khairiyya Provision ɗinta daga ƙasa kuma aka saka ma Ayrah nata akwatinan kuma da aka cire komai a cikinsu aka dora musu su can saman wardrobes ɗin ɗakin kowa da wajen nata juice dinsu kaɗai aka ware akace akwai fridge a parlour idan sunaso a saka a ciki idan kuma anan zasu barsu idan sun tashi sunaso sai su dinga sakawa lokacin da suke buƙatar 

Ayrah tace a barsu anan ɗin zasu dinga sakawa idan sun tashi bayan an kammala komai Ayrah ta shiga toilet ta watsa ruwa itama Khairiyya sai gashi sunbaje kowa kan gadonta ana huce gajiyar tafiya 

Knocking aka ƙara musu suka amsa saiga wannan tsohuwar ta shigo gaisheta sukayi daga gefen gadon Ayrah ta zauna gaba dayansu suka tashi zaune suna jiran jin me zatace dan gyaran murya tayi kafin tace nazo ne nadan wayar muku dakai dangane da makarantar nan domin nasan cewa bakusan komai game da'ita ba 

Jinjina kai sukayi alamar eh 

Ta cigaba da cewa nan makarantar SHAUBAN’S FAMILIES ce tana dauke da yara ne iya na gwamnoni shuwagabannin ƙasa da kuma ministoci sai shahararrun yan kasuwa da ya'yan sarakuna 


😳 gwalalo idanuwa Khairiyya tayi har zatayi magana tsohuwar ta cigaba da faɗin sai kundage zaku iya zama dasu domin kuɗin ba kamar su kuke ba kunada banbance bambancen rayuwa da kuma dabi'u saidai su basu cika hayaniya ba saidai daidaiku amma basuda fitina kuma saboda haka banaso a samu matsala daga gare ku domin kune na farko da kuka taɓa shigowa makarantar nan a matsayin bare batareda kunada alaƙa da kuɗi mulki ko sarauta ba 


Abubuwa da yawa sun cunkushe ma Ayrah kai don tafara tunanin yaƙin ba ƙarami bane kallo ɗaya tayiwa tsohuwar ta kauda kanta saidai tanajin duk wani abun da take faɗa a kunnen ta kuma tana ƙara warware wasu abubuwan data fara ganowa dangane da abinda take zargi saidai tana tunanin aikin nata ba ƙarami bane don saita shirya masa 


To 😲 ikon Allah 🤔 wai menene mutuniyar take kullawa ne nifa nafara tunanin tasan wani abu amma yawan shurunta yasa taki bari mu fahimta to mundai haƙura muje gaba Hajiya Ayrah ai dole mubiki tunda munaso muji ƙarshen labarin naki 


Mikewa tayi ta harde hannayenta ta baya ta cigaba da magana saidai Khairiyya bata gane inda ta fuskanta ba don tafara canja musu harshe tana magana da mutum biyu amma tana ambaton ɗaya 


Ki kasance a ankare dan komai zai iya faruwa nan ɗin ba kamar gida bane da kika baro fitinar da take anan tafi ta can saidai bambancin ilimi a tsakanin su waccan a bayyane take wannan kuma yaƙin sunkuru ne dole ki farka daga nannauyan baccin da kika faɗa……


Gaba ɗaya sun daskare don Ayrah har wani ƙara kallonta take taga ko ita take kallo amma idanuwanta suna ƙasa Khairiyya dai baki abin magana har takara bude baki xatayi magana aka ƙara katseta da faɗin yanzu ku shirya za'a kawo muku abinci kuci sai ku fito parlour anan zakuci gobe neighbours dinku zasu dawo suma ta faɗa tana nuna alamar ɗayan kofar da yake ta parlour ɗin 


Ficewa tayi tabar Ayrah cikin tantama da tunani dan koda tsohuwar nan batayi magana ba ta gama gane tana ɗaya daga cikin mutanen da take zargi saidai kuma ta ƙara buɗe mata kofar fahimtar haka amma meyasa tayi mata hakan kota lura cewa ta gane ta ne 


Khairiyya ce ta dawo da'ita hayyacinta tana faɗin Ayrah ki tashi yanzu za'a kawo mana abinci nidai bari in dauka lemuka na nakai wasu fridge su danyi sanyi bata jira amsar Ayrah ɗin ba ta fice 


Zagayen dakin tafara can kuma tadan tsaya tare da furta Meyasa suka haɗa Khairiyya dani a wasan nasu kuma wanene shugaban wasan nasu domin a cikin harkar anyi tane komai a shirye idan har Khairiyya taso fahimtar wani abu yanzu za'a mata zancen Abinci hakan tana faruwa sosai a duk lokacin da wani abun ya taso kenan dai Khairiyya ansan cewa ita akan abinci bata cika zurfin tunani ba ya Allah ni Ayrah ka kawoman mafita ta faɗa tare da zama gefen gadon ta zabga uban tagumi har Saida Khairiyya tazo takara kiranta akan ankawo abincin 


Abinci mai rai da lafiya suka ci suka sha suka koshi kafin suka koma daki haka har dare ma aka ƙara kawo musu wani abincin tare da wata leda Babba Saida suka zazzage sukaga kalan uniform ɗin makarantan me shegen kyau sun sha guga kowa kala uku da mini skirt Sai mai wando pencil sai doguwar riga iya gwuiwa da socks dogaye sai sneakers kala biyu duka iri ɗaya saidai damuwarsu ɗaya hijabs ɗin duka mini ne da kaɗan ma suka sauko musu kafada hada tag mai suna kowa da nata 


Zuwa dare suka kwanta da murnar zasu shiga class gobe Ayrah dai abin duniya duk ya isheta don tafara tunanin gaba ɗaya zuwan su makarantar nan shiri ne amma abubuwan suna daure mata kai to tayaya duk da wadanda suke a lissafin ta yanzu su uku ne amma ɗaya daga cikinsu yafi bata mamaki wato A-K kamar yanda ta saka masa suna 


To ikon Allah waye kuma A-K ɗin nan🤔❓

Su waye sauran biyun tayaya Ayrah har tafara gane wasu daga cikin yan wasan nata ❓ Wacece wannan tsohuwar wane yakin take nufi kenan ❓😳 waye shugaban wasan kuma ❓ 



Nidai nace bazan jira ba gara in cigaba da bibiyar Ayrah ta fada man kan zancen don ni nawa rudanin yafi nata tabarni a duhu da yawa wanda suke bayana suzo mutafi mujiyo kan zancen nan gaskiya 😆…………




Karki bari karku bari kar mu bari abamu labari top 3 Na A'ishatu Hamza wadda kuka fi sani da Muaysh graphics 🤟 🤗 basai na faɗa muku ba littafaine wanda daga jin sunayen su zaka gane cewa na musamman ne 


(UMMU OR SALMA) UMMU kO SALMA


(ORPHANAGE HOME) GIDAN MARAYU 


(MARYAM’S LIFE) RAYUWAR MARYAMA 


Wannan shine account details din mu 👇

3201868037 A'isha Hamza First bank

Ko kuma 9131096058 A'isha Hamza Opay bank

RAYUWAR MARYAMA akan 400 kacal GIDAN MARAYU akan 400 sai kuma UMMU KO SALMA akan 400  ga wanda yake buqatar duka zai biya 1000 instead of 1200 sana zaka tura receipt after payment a wannan number *** ta whatsapp