KUNCIN ZUCI

Kuncin zuci

by @bintuuu

Cike da fara'a Alhaji ya fara qarasowa cikin falon tareda fadin "Ah, malam Ahmad yau kaine a garin namu, sannu da zuwa" sai Ahmad ya miqe ahanzarce shima ya qarasa garesa a ladabce, yana dan duqar da kansa sukayi musbaha da Alhajin cikin raha, Bilal dai yana tsaye a bayan mahaifin nasa jikinsa duk a sanyaye amma ga mamakinsa sai yaga Ahmad din ya miqo masa hannu da nufin suyi musabaha, casually Ahmad ya masa gaisuwar kamar babu abunda ya taba shiga tsakaninsu sai Alhaji ya sake yiwa Ahmad din iso suka qarasa ga kujerun falon suka zazzauna, nan Alhaji ya fara tambayansa lafiyan mahaifansa da al'amura yana amsawa a ladabce, da ya tambayesa ya iyalin nasa sai yace "Tare muke, taje yin sallah gurin Mama" kafin Alhajin ya amsa suka juyo takun sauqowar Na'iman tareda Hajiya, sai Alhajin ya juya yace "Mamana ashe tare kuke" sai Na'ima ta sunkuyar da kai tana murmushin dole ta qaraso falon a sanyaye dan ganin wanda ke zaune a gurin yasa ta yin sanyi kuma, asannu Ahmad ya juya yana kallon Bilal da ya sunkuyar da kansa ba tareda ya dago ba tun fitowar su Hajiyan, Na'ima kuwa daman tun kallo dayan da ta masa bata sake kai idonta inda yake zaune ba, da ta zo zaunawa a falon ma sai ta tafi far end from inda Bilal din yake ta zauna tana gaishe da Alhajin, bayan ya amsa sai ta dan kauda kanta tace da Bilal din "Ina wuni" ba tareda ya kalleta ba shima ya amsa da "Lafiya" kawai. sannan ta juya kanta tana kallon Tv duk Ahmad na lura, da farko shiru akayi a falon sai can kuma Alhaji da Ahmad suka fara hiran su da ta shafi ayyuka, hankali kwance Ahmad yake maganarsa kamar baisan da wani Bilal a wajen ba, cikin hiran ne Alhajin ya ke tambayansa  "Naji labarin kunata expanding har zuwa United States ko" ya amsa da "Eh Abba, we're still working on that, dan munason mu matsa har zuwa New York and Seattle in the next 8 months in sha Allah" sai Alhaji yace "Hakan yana da kyau sosai, investing there is a good idea, Allah yayi jagora son" ya amsa da Amin sai Hajiya tace "Bakaci abincin ba dai Ahmad" sai yace "Naqoshi Mama" Alhaji yace "Tafiya kuka yo fa son" sai yayi murmushi da haka ya fara miqa flask da plates din zuwa gaban Na'ima yace "Baki ciba" dan qaramin murmushi tayi a kunyace ganin su Alhajin na kallonsu sai Hajiya tace mata "Ko zaki tafi sama kici toh" tace "A'a zancin" da haka ta fara zuba abincin kanta a sunkuye, sai Hajiya ta juya gurin Bilal da tun dazun bai dago kansa ba yana danna wayarsa yayi shiru kamar baya falon, tace "Babana a kawo maka abincin" sai ya girgiza kai bai dagon ba yace "Na qoshi" da haka kuma ya miqe yace "Bari na dauki kira" ya nufi kofan fita daga falon suna kallonsa.
Sai da sukayi sallahn la'asar bayan sun dawo falon banda Bilal sannan Na'ima ta miqawa iyayen nata takardun gidan man ta da ta taho dasu, nan suka nuna faricikin su tareda godiya wa Ahmad din, da ta sake fada musu adadin kudin da take dasu a qasa regarding App dinta sai da Hajiya ta kama baki saboda mamaki tana kallon Ahmad din, nan ma Alhaji ya hau saka masa albarka suka hau yi masa wani godiyan yana sunkuyar da kai cikin jin nauyin godiyan da suke masan, sai can kuma ya fadawa su Alhajin zasu tafi, Hajiya na kallonsa tace "Ba'a nan zaka barta ta kwana ba?" sai yayi murmushi baice komai ba, sai Alhaji yace mata "Ai yana da gidansa anan cikin Kano shima" tace "Ayyaa", Ahmad na qoqari miqewa yace "in Allah ya kaimu gobe zamuje can Adamawan" sai Alhaji yace "Ma sha Allah, hakan yayi kyau, ku basu gaisuwa da Allah" Ahmad ya amsa da "In sha Allah" sannan ya fita daga falon, sai sannan Alhaji ya kalli Na'ima dake zaune bata tashi ba, yace "Da fatan kuna Lafiya daughter?" ta amsa da  "Alhamdulillah Abba" yace "Ma sha Allah, Allah ya baku zaman lafiya, ki kula sosai kinji, ki masa biyayya sosai Mamana" sai ta sunkuyar da kanta tana amsawa da "Toh Abba" ya sake cewa "Ki gaishe da su Ayuban in kunje" tace "Zasuji, nagode Abba" sai kuma tayi shiru bata tashin ba, ganin haka yasa Alhajin cewa "kinada abun fadi ne Mamana" tace "Abba menene shawaranku akan kudin" yace "Kin fadawa su Abbanki Ina fatan?" tace "Eh" nan ta fada masa yanda sukayi da Abban sai shima yace "Hakan daidai ne daughter, in hakan ya kwanta miki arai sai kiyi din" ta amsa da "Toh Abba nagode" da haka Alhajin ya ciro kudi masu yawa daga aljihusa ya miqa mata, a kunyace ta karba tana godiya sai Hajiya ma tace ta jira ta tana zuwa, da haka ta tafi sama bata dade ba ta dawo hannunta riqe leda me dauke da kwalban turarukan wuta guda biyu da kuma na shafawa masu kamshi, a ladabce ta karba tana godiya sannan sukayi sallama ta fice daga falon kanta a sunkuye, fitarta compound din ta hango Ahmad tsaye jikin motarsa sannan a gefenta kuma Bilal ne zaune akan resting chair dake varendan yana danna wayarsa bai dago ba, sai itama ta nufi Ahmad din batareda ta kalli Bilal din ba tace "Sai anjima" shima ciki ciki yace "Allah ya kiyaye" sai kuma ya kasa jurewa ya dago kadan, nan kuma yayi dana sani bawai dan Ahmad zai masa wani abu ba sai dan ganin yanda Ahmad din ya taho gareta ya karbi ledan hannun nata tareda kamo hannunta suka karasa motan tare, saida ya bude mata front seat ta shiga ya rufe cab din sannan ya zagaya driver's part shima, da sauri Bilal ya maida kansa ga wayarsa ganin Ahmad din ya dan kallo gurinsa. Bai sake dago kansa ba har Ahmad yayi reversing motan megadi ya bude musu gate suka fice.

Sai yamma lis suka isa gida, Na'ima ta yaba da kyawun gidan sosai da suka shiga cikinsa, ganin yanda ta zube a kujeran falon cike da gajiya yasa Ahmad sunkuyawa ya dago kafafunta yana zaunen a gefenta ya dorasu bisa cinyarsa sannan ya fara mammatsa mata su, sai hakan ya mata dadi ta nuna masa gefen babban yatsanta tace "Boo nan yafi ciwon" sai yakai hannu gurin yadan danna mata tana rufe ido, kwanciya tayi ya cigaba da matsa mata kafan suna hira jefi jefi, can yace "Babe inason Inda hali muje a goben mu dawo, kuma naga kin gaji" sai ta dago tace "Da nisa fa, I thought zaka bari nayi kwana biyu ma" ya girgiza kai yana kallonta sai ta sake cewa "Kaddai ranan da kukaje kwanaki a ranan kuka dawo?" yana murmushi yace "Waya fada miki munje?" sai itama tayi murmushi tace "Da sukazo bikin sun fada min ai, amma me kukaje yi ne?" bai bar murmushin ba yace "Naje gaida surukaina" dariya ta fara tace "I'm not buying that" yace "Dagaske fa" sai ta miqe zaune tareda janye kafafunta daga jikinsa, tace "Please tell me" sai ya tsaya kallonta, can ya sauqe numfashi yace "Laila ce ta aikawa Baba wasu shitty takardu akanki, saying bad things and believe me...you don't want to know cos it's dirty, Baba kuma yace zai tura a bincika masa in gaskiya ne, plus that warning comes with our marriage at stake, so..I had to go and settle things with them" sai Na'ima ta tsaya kallonsa at the same time zuciyarta na sanyi akansa, jin tayi shiru sai ya kamo hannunta ya sake cewa "At that time, I had no choice but to go to them, banason wani magana mara dadi akanki ta dawo kunnen Baba" sai gani yayi kawai ta kwanto jikinsa tareda sarqe hannunta a bayansa sannan ta kwantar da kanta a kirjinsa, shima sarqo hannunsa yayi a bayanta sukayi shiru ahakan, sai can ta dago kai tana kallonsa tace "Thank you Ahmad, thank you for loving me no matter how many odds that came along with it" murmushi yayi ya hade karan hancinsu, yace "Even if I had to go back, I'd choose you all over again and again ..Thank you for loving this grumpy man Na'eemah" tana murmushi tace "You're not grumpy Ahmad, you're kind, honest man, and....Haaandsome" sai yayi baya da kansa yana dan dariya sai ta matso da kanta ta fara masa rain kisses a fuskansa, dariyan ya cigaba da yi sannan yace "Babe, are you planning to turn me on while you're tired?" nan kuma ta fara kokarin barin jikinsa tana dariya, sai ya riqota yace "I'm kidding dear, me zaki ci in mana order" tace "Let's eat outside today" yace "Angama, Ina kikeson zuwa?" sai ta tsaya kamar me tunani sannan tace "Calido?" yace "it's settled then, bari muyi sallah sai muje anjima" da haka suka cigaba da hiransu har aka kira sallahn maghrib.
Da wuri suka kwanta bacci bayan sun dawo daga eatry din dan su samu bacci isasshe kafin su tafi, aikuwa 7'oclock suka kama hanya, da yake yawancin motocin Ahmad manyan jeeps ne sai ya zamto wadda suka tafi da itan tana gudu smoothly ba bumps sosai, sai da ya siya musu abinci kafin su bar garin sannan suka dauki hanya, har Na'ima tayi dogon bacci ta farka basu isa, sai ta gyara zamanta ta juya tana kallonsa ganin ya miqo mata bottle watern da ya gama kurba, bayan tasha ta dauko abincin taci kadan sannan suka cigaba da hira har suka isa wajejen qarfe biyu na rana, a kofar gidan Kawu Ayuba yayi parking suka fito cike da gajiya sai Na'ima ta dan tsaya kallon gidan ganin gyaran da ya sha kamar ba gidansu da ta sani a baya ba, ita kadai ta fara shiga gidan sai ta tadda su Umma da yaranta a tsakar gidan suna ayyuka, aikuwa suna ganinta suka fara murna, Umma na murmushi tace "Lale lale 'yataa, sannu da zuwa" da haka tasa aka kawo mata tabarma suka gaisa, sai bayan sun gama gaisawan ta fada mata da wanda take tare, nan Umma ta hau bude falon dake sashen Ayuba cikin hanzari sannan aka masa iso cikin gidan, sai da sukayi sallah sannan kawu Ayuba ya dawo gidan tareda kawu Nasir, nan ma aka hau gaggaisawa Umma ta kawo musu jellof din spaghetti lafiyayye da yaji kifi wanda akan gudu ta dafa musu shi, anan ne kuma Ahmad yasa chokali ya dan ci abincin hankali kwance, sai bayan maghrib yace musu zai tafi masauki, da Na'ima ta same shi a mota lokacin da zai tafi sai yace su tafi tare amma taqi, nan kuma ya matso tareda cewa "Then give me a goodnight hug" sai ta ware masa hannunta tana murmushi, da haka ya rungumeta a jikinsa sannan ya mata rada a kunne da "Please muje mu kwana tare Babe" sai ta dago tace "Yau ne fa kadai, kaida kaqi yarda muyi kwana biyun ma" yace "Toh gobe da safe zanzo" tace "Naji, kazo kayi breakfast anan din ma" da haka sukayi sallama da kyar dan nema yake su shiririce a cikin motan kuma, sai da kyar ta zille masa ta nufi cikin gidan tana murmushi tareda juyowa tana kallonsa time to time while yana zaune cikin motan yana kallonta har ta shige ciki.
Daren ranan ta sha hira da kawunta Ayuba a falonsa, anan ne take tambayarsa labarin Anty Amarya dan rabonta da ita tun lokacin da tazo gidan kawo qarar abunda Bilal ya mata kuma zuwanta gidan yanzu ta dauka zata samota, sai ranan ya sanar da ita rabuwansu, dan da yace taje gida tun wannan lokacin da suka samu sabani akan Na'iman bata sake neman dawowa ba acewarta bazata iya zama da mai hali irin na Ayuba ba, jin wannan batun sai da Na'ima tayi hawaye, Ayuba na kallonta yace "Tana da gaskiya Na'ima, nima kaina bana alfahari da halina na baya, na koma yin bikonta yafi a qirga amma taqi dawowa, danta Hamisun ma gashican Jummai na riqonsa, yanzu haka naji labarin tayi wani auren acan gaba da garinsu" sai Na'ima tace "Dan Allah Baba a Ina zan samu ko da layin wayarta ne" yace "Sai dai in tambayi Yayanta da yake zuwa cin kasuwa a cikin garin nan duk ranan alhamis, zan tura miki, dan Allah ki qara bata hakuri a madadi na, kema kiyi hakuri da duk abubuwan da suka faru a baya" tace "Ba komai Baba in sha Allah komai ya wuce" sai yace "Amadun yace gobe zaku koma ko" ta amsa da Eh sannan ya sake cewa "Kafin ku tafin sai kuje ku gaisa da mamanki Lubabatu, da kuma iyalan Nasiru" tace "Toh Baba, har gidan Salame nakeson inje mu gaisa" ya gyada kai "Hakan yayi, Allah yayi albarka" sai da ta tashi zata tafi dakin Umma kwanciya yace mata "Na'ima ki tayamu godiya a gurinsa, kinga irin alkhairin da ya mana, kuma dukanmu uku harda kurma ya sabuntawa gidaje, qannenki ma duk sun koma makaranta yanzu, ki masa godiya sosai dan Allah" sai tayi murmushi tana sunkuyar da kai tace "in sha Allah" da haka ta fice da falon. Da maganar Anty Amarya ta kwanta aranta rannan, ashe shiyasa bataje Abuja ba lokacin aurenta da Ahmad, kuma duk wanda ta tambaya acikinsu sai suce mata ta tafi garinsu ne, Allah sarki Anty Amarya.



Bintu ✍️ 📖