ALIYU HAYDAR

Chapter 6

by @nieemartullah

Kallon kanta tayi a jikin madubi yadda dinkin yayi mata dass a jikintasanya take cikin wata atampa anyi mata dinkin riga da skirt tace kinyi kyau safiyyah sai yanxu na samu damar qare mata kallo sosai safiyyah yarinyace da Idan ana lissafin kyau toh fah ba xata wuce ta uku ba,baqa ce amma baqinta ba mai muni ba tana da siririn hanci wanda yayi dai dai da fuskar ta,idanun ta masu kalar birgewa da dan mitsitsin bakin ta bayan ta gama kallon kanta a jikin madubi lafaya ta daura saman kayan Ta sannan ta dauki makullin mota tayi ficewar ta daga gidan baki daya a hanya ne ta turama HAYDAR text cewa zata je gida ta gaida su momma kamar jira yake dama tana tura masa text yace a dawo Lpia............................

Jaiy ki xo muje kiga boutique din nan because kin dade baki je ba kullum Idan na kira ki muyi lissafi sai kice Tass na yadda dake kiyi abinda ya dace toh ni na gaji,kin fiye mita wlh tashi muje kamar dama jira take ta miqe ta dauka veil din abayar ta nada shi tare da daukar makullin mota suka fita a parlour suka samu ummah ita da baquwa suka mata sallama suka fita Jaiyana ita da Ayaanah a mota sai Tasneem tana driving nata motar.........................

Oyoyo Aunty safiyyah mi yelwima (nayi missing dinki) tayi hugging dinta dama I'm bored Allah ya kawo man ke ni daya a gida kamar mayya dariya tayi tace kinfa girma auta keda xa'ayi ma aure a baki gida gaba daya ina momma tana dakinta oya let's go,dakin momma suka tafi hannun su maqale da juna saboda kaf cikin gidan babu wanda auta take so kamar safiyyah haka safiyyah ma kaf cikin siblings dinta babu wanda take so kamar auta,su hudu ne kadai iyayen su suka haifa babban yayan su ibraheem wanda suke cewa khaleel yana da mata da kuma yara uku sai addah Fatima wacce take da yara biyu sai safiyyah sai kuma auta wato maryam babansu ya rasu lokacin da auta take da shekaru biyar a duniya,suna shiga suka tarar da momma a kan prayer mat daga gani sallah ta idar take adhkar gefen momma ta zauna ta dora kanta akan cinyar momma,tace ina yini momma mun same ku lpia,lpia qlau ya mijin ki yace ma a gaishe ki yana lagos ne shiyasa bamu zo tare ba toh madalla Allah yayi muku albarka Ameeen momma me kuka dafa yau don banci komai ba na fito saboda ina daukin naci abincin ki sai Kije kitchen ki duba Allah ya taimake ki favourite dinki muka dafa wani tsalle tayi ta kama hannun auta suka sauka qasa kitchen suka shiga ta dauko plate tace auta tare zamu ci abinci ko nayi kewar ki sosai kamar nasan zaki xo naqi naci abinci yawwa food flasks din da ta gani ta bude masa ce ta diba iya wanda zasu ci sai kuma ta diba miyan taushe wacce taji nama dining suka dawo suka zauna suna cin abinci suna ta hirar yaushe gamo........................

Bayan sunje boutique din Tasneem ta gama yi mata bayani sun kuma yi lissafin ribar da suka samu da kuma abubuwan da basu da shi Jay tayi listing abubuwan da babu tace za'a kawo basu bar boutique din ba sai da aka fara kiran sallar maghrib,Tasneem ta koma gida ita ta dauki hanyar da zai kaita gida,a hanya ta ga wani mai gashin kaza neman guri tayi ta gyara parking sannan ta sauka ta qarasa gurin mai naman kasancewar gurin maza ne sosai shiyasa bata qarasa ba tana tsaye har aka sallami mutanen gurin qarasawa tayi tace a bata gasassun kaji manya guda uku tana nan tsaye wata dalleliyar mota tayi parking a gurin sakkowa mutumin yayi ya qaraso gurin sallama yayi aka amsa mai naman ne yace sannu da zuwa alhaji yawwa ya aiki Alhamdulillah alhaji dayan yaron gurin ne ya  fara hada na wannan bawan Allah kusan tare aka gama hada masu kowa aka miqa masa nashi ledar mota duk suka koma Jay ta dauka hanyar komawa gida.........................

Sanin halayyar HAYDAR yasa zannur biyo shi a baya yana zuwa gurin motar yaga HAYDAR har yayi ma kanshi guri a passenger seat baice masa komai ba ya zagaya driver seat ya tada motar suka harba kan titi hankalin shi na kan tuqin da yake yi yace kai kana wani abu kamar wani dan qauye,kana ganin kyawawan yan mata suna kula ka amma kana wani mazewa,yana magana yana danne dariyar dake shirin kwace masa a fusace ya juyo kaga malam Idan kasan iskanci zaka man toh ka sauka a mota na ka hau taxi kai shikenan duk lokacin da mutum yake cikin fushi sai ka nemi abinda zaka qara batawa mutum rai,mcheeeeeew Allah ya baka haquri ba ni na kar zoman ba rataya aka bani ko ci kanka bai qara ce masa komai ba................................

Bayan sun ci abinci suka koma wurin momma sun dan taba hira gaskiya momma zan shirya next week naje gidan Hamma rabona da gidan shi fah an kusa shekara nan fah momma ta fara fada kamar zata ari baki yanxu tun da raina bakwa zumunci me kuke tunani bayan babu raina kiyi haquri zamu gyara in shaa Allah ni ba wai ina san yi maku fada bane amma babu wanda zai fada maku gaskiya duk dacin ta sama da ni kun sani baku da gata sai Allah haka ne kuma zamu gyara in shaa Allah yawwa Allah yayi maku albarka gaba dayan ku ameen momma kinga sai ki tashi kiyi shirin tafiya gidan ki kinga maghrib yayi tohm momma kuma kar ki manta don Allah ku riqe zumunci kunji ko bayan qasa ta shafe man idanu nasiha momma tayi ma safiyyah mai ratsa zuciya akan zumunci da kuma biyayyar aure sosai jikin ta yayi sanyi tace nagode momma Allah ya qara maki tsawon kwana ameen safiyya kema naga yaranki da na auta kamar yadda naga na yan uwanku ameen momma Sai da suka kaita har bakin motar ta suna daga mata hannu har ta fita daga premises din gidan..........................

Zaune take kan dadduma bayan ta idar da sallah hajiya mama ce ta shigo dakin bakin ta dauke da sallama gefen gadon ta zauna har Jay ta gama abin da take ta linke daddumar ta ajiye,ke yanxu kin kyautawa kanki kenan duk wanda kika gani yau toh saboda ke yaxo amma tsakani da Allah kisa qafa ki fice daga gida sai maghriba ki dawo ai shikenan kin kyauta Allah ya baku haquri amma bana son na zauna ne a saman ciwon kai kuma kinfi kowa sanin Idan na shiga hayaniya kaina ciwo yake man tun tana mata fada har suka koma hirar rayuwa kasancewar lokacin dinner yayi suka fito,suna zuwa suka tarar da mom,dad da kuma Ayaanah daga gani suma yanxu suka fito,kujera duk suka ja suka zauna jollof din taliya ce sai qamshi take Jay ce tayi serving dinsu baka jin komai a gurin sai qaran cutlery,parlour suka dawo bayan sun gama cin abincin aka zauna ana dan hira dama hakan al'adar su ce bayan sunyi sallar maghriba sunyi dinner sai su zauna suyi hira saboda da rana kowa ya fita Jay ta tafi asibiti mom ma ta tafi office shi dama dad bai cika zama ba amma duk sanda yake gari Toh fah za'a yi da shi,hira suka fara ana ta raha sosai mom ce ta kalli JAY tace ya maganar school din Ayaanah har yanxu baki ce komai ba eh haka ne mom da nayi tunanin zuwa yau Toh kuma yau kinga ban zauna ba amma gobe in shaa Allah Idan xan fita aiki zan tsaya nayi mata registration ina ma dai ta contemplating ne a cikin biyun nan ko Roberto school ko Nigerian Turkish saboda sune a kusa kinga duka su a wuse suke bamu da nisa eh hakan ma tunani ne Allah yayi maki jagora dad da hajiya mama ne suka hada baki gurin fadin ameen dama tun lokacin da JAY ta kawo ayaanah gidan ta fada ma dad suna ta hira har aka fara kiran sallar isha'i alwala dad yayi ya tafi masallaci su kuma matan kowa ya nufi hanyar dakin shi domin gabatar da sallah....................

Taje can ta dawo ta qara komawa ta kasa zama guri daya tun da ta dawo daga gidan su ta kasa samun sukuni maganganin momma ne keta maimaita kansu a cikin kwakwalwarta,musamman da tace kiji tsoron Allah safiyyah,kiyi ma mijin ki biyayya ki nemi aljannah,nasan kekam banda shakku akan ki Allah ubangiji ya albarkace ki,jikin ta ne ya qara yin sanyi kamar wadda ruwa ya cinye tana cikin duniyar tunani taji wayar ta na qara cikin sanyi jiki ta dauka tare da karawa a kunne tace hello daga dayan bangaren shema'u tace A'a qawata Lpia nake jinki haka ajiyar zuciya ta sauke sannan tace anya nayi ma kaina da kuma wanda suka amince dani adalci kuwa? A zuciyar ta tace qarya kike yarinya amma sai kawai tace qawata nifa har yanxu ban gane me kike nufi ba safiyyah tace rayuwar da na daukar ma kaina nake nufi kinga qawata ki kwantar da hankalin ki gobe zan zo gidan naki kinji,kamar wata qaramar yarinya tace toh,bayan sun gama waya shema'u tayi wata irin dariya sannan tace haba yarinya bahaushe ma cewa yayi ta yaro kyau take bata qarko dani kike magana Sai da nake ganin na kusa cimma nasara sannan ki bijiro man da wannan maganar,ai baki isa ki bata mun abinda na dade ina shiri ba mu xuba mu gani............................

Magana suke yi amma sai ka saurara sosai sannan zaka ji mai HAYDAR yake cewa zannur ne yace kaga Idan ka gama rashin kirkin naka ni zan tafi kuma dole na fada maka ko kana so ko baka so saboda baka da wani abokin da zai fada maka ya kamata ka rage wannan damuwar ka fuskanci rayuwar ka yawan damuwa da kake saka kanka ba shine ba ka tashi cikin dare ka fada ma mahaliccin mu damuwar ka pour your heart out to him I assure you he will find solutions to your problems shiru HAYDAR yayi kamar me nazari sannan ya budi baki cikin sanyin jiki yace thank you so much buddy Allah ya barmu tare banxa yayi da shi bai ce masa komai ba saboda ba qaramin haushin sa yake ji ba miqewa zannur yayi yace masa ni na tafi Sai da safe shima tashi yayi ya bi bayanshi suka fito har bakin mota ya raka shi suna ta hira kamar ba su ba yawwa HAYDAR ya kamata ka shirya wannan weekend din muje Abuja kaga mun dade bamu je ba tohm shikenan ka siya mana tickets sai mu tafi Saturday da safe tohm Allah ya kaimu ka gaishe man da su Areef toh zasuji in shaa Allah......................................

Wai me kake nufi ne sooraj kwana biyun nan Baka san zama a gida da ka dawo daga office zaka qara shirayawa ka fita Idan nayi maka magana sai kace kana bincike ne akan wani abu kaga fah niba qaramar yarinya bace Idan ma aure kake nema bari kaji na fada maka wallahi tallahi ba'a haifi wata ya macen da zanyi kishi da ita ba kinga Layla bana son wannan shirmen banxa wai yaushe ma kika raina ni da har kike fada man duk wani Abu da ya zo bakin ki,kuma bari nayi maki albishir aure zan qara nan kusa ba da dadewa ba,kuka ta fashe da shi tayi hanyar dakin ta tana sambatu na shiga uku na ni Raj zai tonawa asiri,tsaki yayi ya ma fita daga gidan,bayan ta shiga daki waya ta dauka tayi dialling number maman ta,tana dagawa ta qara sautin kukan ta har tana shasheqa sosai hankalin mahaifiyar ta ya tashi tace kinga Layla kiyi shiru ki man bayani ko wani abu ya samu Sooraj ne ai tana Jin an ambaci Sooraj ta qara sautin kukan ta,ji tayi hankalin ta yayi qololuwar tashi ending call din tayi ta ziri key din motar ta ta fito text ta yi ma babansu kasancewar ba a gidan ta yake ba,irin gudun da tayi a hanya Allah ne kadai ya kawota Lpia ko gaisuwar mai gadi da sauran ma'aikatan gidan bata iya amsawa ba sai hannu da ta daga masu,bata ganta a parlour hakan yasa ta wuce dakin ta direct,har yanxu kukan take amma ba mai sauti ba tana ganin mahaifiyar ta ta qara fashewa da wani sabon kukan kinga Layla bana son shiririta kinga daga man hankali na dauka wani Abu ne ya same ki ko mijin ki,kibar kukan nan kiyi man bayani tun kafin raina ya baci sanin halin mahaifiyar ta yasa ta tsaida kukan cakk kamar anyi ruwa ya dauke tambayar ta ta qarayi Lpia kika kira ni kina kuka Ammi Sooraj ne me ya faru da shi Ammi aure fah wai zaiyi ji tayi kamar ta rufe ta da duka yanxu akan mijin ki zai qara aure kika tasa man hankali Layla Toh kin kyauta aure fah nace Ammi eh ai na ji ki amma kinsan zai iya auren mace sama da daya ko,nasan bawai sanine bakiyi ba amma ya kamata na tuna maki Allah (S.W.T) ya fada mana a cikin littafin shi mai tsarki cikin suratul Nisa'i aya ta uku da tace

وَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تُقْسِطُوا فِي الْيَتَامَىٰ فَانكِحُوا مَا طَابَ لَكُم مِّنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْمَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا

Transliteration

Wa'in kiftum allā tuqsitū fīl-yatāmā, fankihū mā ṭāba lakum minan-nisā'i, mathnā wa thulātha wa rubā'a. Fa'in kiftum allā ta'dilū, fawāḥidatan, aw mā malakat aymānukum. Dhālika adnā allā ta'ūlū.

Don haka ina son ki kwantar da hankalin ki kiyi ma mijin ki biyayya bana son Jin labari mara dadi kinji tohm shikenan Ammi tashi tayi ta dau makullin motar ta ta fita rakiya tayi mata har bakin mota sannan ta koma ciki..........................

Kamar yadda yadda nayi maka alqawari baba na Toh na samu sauran iyayen naka munyi magana dasu kuma Alhamdulillah mun tsaida ranar da zamuje wurin shi mahaifin yarinyar yanxu abinda nake so da kai sai ka fada ma ita yarinyar ta sanar da mahaifinta zuwan mu tohm shikenan Abbah zan fada mata nagode sosai Allah ya qara girma ameen Allah ya albarci rayuwar ka ka shiga cikin gida ki gaisa da maman naka ina jinta tana ta mita wai jiya kayi ficewar ka bata ganka ba tohm shikenan xan shiga in shaa Allah na bar ka lpia...............

Kamar yadda shema'u ta fada ma safiyah washe gari da safe taje gidan ta don ita safiyyah ma bata tashi a bacci ba,tashin ta tayi tace qawata kin daga man hankali jiya shiyasa kika ganni da safiyar nan wani Abu ya faru ne da har kike tunanin ki watsar da rayuwar da kike yi ta Jin dadi kinsa dai idan har kika watsar da komai shi kanshi HAYDAR din da kike yi don shi zai ce baisan ki bane toh koma waye ya baki wannan gurguwar shawarar tun wuri ki sake tunanin don ba abu bane mai yiwuwa nan fah ta qara dora safiyyah kan wasu mugayen shawarwari Sai da ta tabbar ta hau sannan tace kinga ni tafiya zanyi don mutane ke jira godiya sosai safiyyah tayi mata tace ban san ya zanyi ba idan babu ke qawata muje na rakaki fita suka yi suna hira har ta raka ta parlour ita ta tafi ita kuma ta fara qwala kiran barira,jiki na rawa ta qaraso tace hajiya gani ina kwana wani kasqantaccen kallo tayi mata sannan tace ki hada man breakfast kafin nayi wanka jikin ta tsuma tace toh hajiya a fito lpia.............................

Bayan ta koma dakinta zuciyar ta sai radadi take ta dauki wayar ta ta kira aminiyar ta ta fada mata duk abinda ke faruwa wata ashariya tayi sannan tace yaushe shi Sooraj har wuyan shi yayi kauri da yake tunanin yi maki kishiya,amma ba laifin kowa bane sai ke tun tuni nake fada maki kishiya tashi tsaye mazan nan ba'a nade hannu ace za'a zauna tace toh Hafsat ya kike ganin za'a yi tace kar ki damu yanxu bana qasar amma ina dawowa zan zo musan yanda zamuyi ma tufqar hanci tohm shikenan godiya nake daga haka suka yi sallama anan ta dan samu nutsuwar zuciya..........................

Bayan ya bar parlour Abbah direct part din mahaifiyarsa ya wuce yana shiga ya tarar da qannensa su biyu a parlour gaishe da shi suka yi ya amsa sannan yace Zulaikha ina mama tana kitchen yaya ko gama rufe bakinta bata yi suka ji muryar mama na fadin kamar muryar sadeeq naji ko eh shine mama cewar Hannatu dayar qanwar sadeeq sannu da zuwa tayi mashi ya amsa sannan yace mama Ga yaran nan kike shiga kitchen da kanki,kai rabu da su yara sai shegen son jiki wai Abbah ku ne yace yana son cin kwadon zogale shine na sa daure ta nemo man nake hada masa,yawwa ni jiya Abban ku ya same ni da wata magana dama ina ta neman ka muyi magana kace masa ka samu matar aure har kana so aje nema maka auren ta,dan sosa kai yayi sannan yace eh hakane da akwai wata yarinya da nake so aje a nema man aurenta A'a Toh masha Allah ai wannan abin farin ciki ne Allah ya sa albarka ya kaimu lokacin Ameen qannen shi ne keta murna mama kice mun kusa Shan shagali a gidan nan,nan su Hannatu suka koma hirar irin abubuwan da zasuyi lokacin bikin mama da sadeeq sai dariya suke masu suna zaune har aka fara kiran sallar azahar alwala yayi a toilet din dake parlour sannan ya fita ganin da dan sauran lokaci yasa ya shiga part din step mom din shi bayan sun gaisa tace kuma jiya ko a leqe ba'a ganka ba wallahi Aunty jiya aiki ne yayi man yawa shiyasa ban dawo da wuri ba da na dawo kuma duk kunyi bacci toh haka ake so Allah yayi jagora,ameen aunty ni banji motsin Nafeesah ba wannan ina da bikin tana family house din mu sister na zata aurar da yar ta nayi ma ta ja to sai next week amma taqi ai shikenan Allah ya sa alkhairi bari na tafi masallaci kar a fara sallah,toh a dawo Lpia............................

Mai aiki ce tayi sallama a qofar dakin JAY izini ta bata na ta shigo barka da hutawa hajiya yawwa aunty Naja ya aka yi eh cewa akayi wai kina da baqo a waje dan tsayawa tayi nazari tace kuma baki sanshi ba ko ya taba zuwa gidan nan gaskiya ban sanshi ba, toh ki kai shi parlour baqi sai a kai masa ruwa Toh shikenan a fito Lpia ranki ya dade a cikin ranta take ta tunanin waye kuma tasan ba sadeeq bane tashi kawai tayi ta saka wata jallabiya ta mata tayi rolling veil sannan ta fito ta wuce dakin mom ta fada mata tayi baqo zata je ta fa waye basu fada maki waye ba eh mom har sai da na tambayi aunty Naja tace bata san shi ba toh shikenan ki kula Allah ya tsare amma fah kar ki dade kinji in shaa Allah mom bye,direct parlour da suke sauke baqi ta wuce sallama ce a bakinta ta shiga ciki a tsaye ta tarar da wani matashi sanye cikin shigar sa ta yadi fari ya dora baqar dara a kanshi kana kallon irin tsayawar da yayi kasan shidin ya cika namiji juyowa yayi ya fusakance ta saboda a lokacin da ta shigo ya bawa qofar baya Masha Allah fari ne sosai kana kallon matashin kasan cewa kudi fa hutu sun zauna tayi masa duk wannan kallon ne cikin yan daqiqu kadan,you can have a seat thank you yace kafin ya zauna akan daya daga cikin kujerun dake  parlour ina yini ta gaishe da shi cikin muryar ta mai dadi da sanya nutsuwa ga duk zuciyar mai sauraro amsawa yayi sannan yace nasan kina da tarin tambayoyi da kike san jin amsar su daga baki na eh haka ne toh da farko dai suna na..........................