Kuncin zuci
by @bintuuu
Kwanansu su daya suka juya zuwa Kano bayan sun cika su Ayuba da abubuwan arziqi, daga nan ma kwana biyu suka qara sannan suka koma Abuja, a komawarsu da sati biyu ne Na'ima ta fara ganin changes a jikinta da lamuranta, misali kamar yanda soyayyarta da nama ta qaru, naman ma ba kowanne ba sai silale, ta yanda tun tana ci da daya ko biyu har abun ya fara girma in the sense that tun kafin ta gama dafawa zata diba ta rinqa ci sannan ta zuba wanda zataci later, ko yanda zata rinqa jin zafi babu dalili ko da kuwa ta qure Ac bata jin enough satisfaction, a wani yammaci Ahmad ya dawo daga aiki ya shigo falon kenan ya dakata dalilin jin sanyin da ko Ina ya dauka, bai fi seconds a tsayen ba ta sauqo daga upstairs tana welcoming dinsa, sai ya qaraso tareda hugging dinta amma sai ya danyi baya yana kallon yar rigan dake jikinta, duk yanda tayi masa kyau a idonsa ya yabetan saida ya taba wuyanta yana fadin "Babe amma bakyajin sanyin nan? Falon is freezing" sai ta kamo hannusa suka nufi stairs din tana murmushi tace "Sanyi kuma?, naga ana zafi ne shiyasa na qure" dan murmushi yayi sannan yace "Kinajin zafi dai, amma weathern garin is normal babu zafi" tace "Toh muje ka huta in mun sake fitowa sai in rage" da haka suka wuce part dinsa yayi wanka ya shirya cikin qananun kaya na shan iska sannan ya sake samota a falonsa tana kwance akan kujera nan din ma ta sake qure Ac, ai da wuri ya koma dakinsa ya dauko safan kafa sannan ya dawo gurinta ya zauna, sai ta miqe zaune ganin yana saka safan tace "Bari na rage toh" da sauri yace "A'a yi zaman ki Babe, I'll manage" sai tayi murmushi tace "Allah da zafi, ko dai bakada lafiya?" dariya ma ta bashi amma beyin ba sai kawai yayi murmushi yace "Ko dai bakida lafiya ba, ni damuwa na ma kar mura ya kamaki" tana kokarin zuba masa juice a cup tace "Nidai banaji" ya karba tareda gyada kansa kawai.
Bayan Maghrib da sukazo cin abinci ma nan tace ta qoshi, sai ya ajiye spoon din yana kallonta yace "Me kikaci?" tace "Nama" sannan ta bude flask din dake gurin wanda ke dauke da papper soup ta fara zuba masa a plate yana kallonta, ganin wannan papper soup din sai Ahmad yayi tsammanin shi taci har ta qoshin sai beyi pressing zancen ba amma duk da haka sai da ya sata taci fried rice din kadan kafin su tashi, a daren ne ta sake bashi wani mamakin da suka kwanta, dan tashi tayi ta cire kayan baccinta gaba daya ta koma ta kwanta hakan bayan kuma ta kusan qure musu Ac'n dake dakin, nan ma bai isheta ba daga qarshe ta tashi zata fita sai ya miqe shima yace "Babe Ina zakije, ga ruwan naki na ajiye miki fa" ya qarasa maganan yana nuna mata bottle watern dake kan side drawer saboda yawancin dare tana farkawa ta sha ruwa sai ya zamo habbit dinsa ne shigo mata da ruwa kafin su kwanta, amma this time sai tace "Zan je dakina" yace "Nan din fa, meya faru?" ahankali tace "Zafi nakeji" nan kuma ta fara basa tsoro sai ya miqe tareda isa gareta yace "Bari in qure miki na nan din toh, basai kinje can ba, kinsan banason baccinmu a guri mabanbanta Babe" da haka ya jata suka koma gadon sannan ya qure mata Ac'n shikuma ya nemo safa ya saka tareda shiga blanket sannan ya matsa gareta yayi cuddling dinta suka koma baccin, washegarin ranan yace suje asibiti sai ta qi, dan cewa tayi batajin rashin lafiyan komai a jikinta banda wannan zafin kuma zai yiwu shi ba mai jin zafi bane kamarta, dan ko aranta bata kawo craving namanta a wani abu ba, haka suka tafi for two days tana jin zafin nan har Ahmad ya fara sabawa da sanyin gidan, a dare na uku ne ta farka while yana bacci ta fice daga part dinsa, da saurinta ta tafi kitchen ko kunna wutan batayi ba ta nufi fridge ta dauko white transparent robanta da tayi preserving silalen namanta aciki, sai ta koma gurin kitchen island din ta ajiye sannan ta fara ci batareda tayi heating dinsa ba, sai da tayi nisa da ci aka kunna wutan kitchen din ta dago kai da sauri tana kallon Ahmad dake tsaye a bakin kofan yana kallonta, fuskarsa cike da mamaki ya qaraso gurinta, sai ya kai hannu yana duban cikin roban yace "Babe menene wannan din?" a kunyace tace "Nama ne fa" sai ya kalleta yace "Wannan din?, kuma kiji sanyin fa" tace "Ai darene shiyasa banyi re-heating dinsa ba" sai ya tsaya kallonta kawai, nan kuma ta dauki daya zata cigaba da ci duk bai dena kallonta ba, sai can yace "Toh kawo in miki heating dinsa ko sama sama ne" ta girgiza kai tace "Na koshi ma" da haka ta rufe roban ta nufi fridge ta maida yana kallonta da mamaki, da ta dawo gurinsa sai ya miqa mata bottle watern da ya bude mata ta karba ta fara sha duk yana kallonta, sai da ya jira ta gama sha sannan yace "Wannan ne naman da kikeci din these days?" tana kallonsa ta gyada kai, sai ya sake cewa "Silale ne fa Babe" tace "Ji nayi yafi min dadi kwanannan" sai taji yayi shiru yana kallonta sannan ya fara murmushi, sai kuma ya matso daf da ita tareda kamo waist din ya fara yawo da hannunsa a kan cikinta, ganin haka sai ta dago tana kallonsa tace "What?" sai yayi burying fuskarsa a wuyanta bai bar murmushin ba, cikin kwantar da murya yace "Did my little angel finally arrived?" dan stiff Na'ima tayi jin abunda ya fada sai ta ja baya tana jin nauyin maganarsa, dan dariya ya fara sannan ya sake dawo da ita jikinsa yace "Gobe zamuje asibiti kinji Babe" tace "Nifa lafiyata qalau" yace "Naji, amma sai naje an dubamin ke zan samu nutsuwa, this.." ya nuna fridge "This right here is not normal" da haka ya sunkuceta yayi dakinsa da ita, amma madadin su koma bacci sai suka bude wani fagen soyayyar kuma, Ahmad bai barta ta rintsa ba sai kusan karfe biyun dare sannan ya qyaleta ta samu bacci, yana kwance a gefenta yayi ta kallonta cikin dim light na dakin tana baccinta hankali kwance, cike da kaunarta yakai hannunsa yana shafa gefen fuskanta ahankali, wani irin so da kaunarta ne suke dawainiya dashi da bazai iya misaltasu ba, bai bar kallontan ba ya cigaba da shafa fuskarta cike da muradin samun kyautar ubangiji daga gareta..
A washegarin ranan ko breafast beyi ba ya jira ta gama cin silalenta da sassafen ya dauke ta suka tafi Windscare hospital, dan zuwa lokacin Anty Amnah ta koma London sai ya zamto daya daga cikin manyan likitocin da suke aiki anan din ne ze gansu, kasancewan akwai sanayya a tsakani Ahmad da likitan sai basu wani dauki lokaci ba gurin ganinsa, bayan ya gama yiwa Na'iman tambayoyin da ya kamata ya buqaci yi mata tests dan tabbatar da abunda ya hango shima, da ya tashi basu test result din sai ya hau murmushi yace da Ahmad "Bani goro na tukunna" sai Ahmad ya fara murmushi yace "Doc, kar kajamin rai dayawa, I can't take it" nan kuma Na'ima ta hau murmushi itama dan ta harbo jirgin likitan, aikuwa sai ji sukayi yace "Congratulations, Amarya na dauke da juna biyu na kimanin sati hudu" ya qarasa maganan yana miqowa Ahmad result din, da sauri ya karba cike da farin ciki sannan ya juya ga Na'iman yana murmushi, aikuwa agaban likitan ya miqe sannan ya dagota daga zaunen ya rungumeta, sai itama tayi burying fuskarta a kirjinsa tana murmushi jin yana fadin "Alhamdulillah, Alhamdulillah".
Ranan Na'ima taga gata gurin mijinta, kamar wanda zai maida ita ciki haka ya rinqa tarairaiyarta da suka koma gidan, abinci ma sai order ya musu wai baza tayi girki ba kar ta wahala tunda doctor yace kar ta rinqa yawan stressing kanta, sai tace "Nifa banajin koma dear, I'm totally fine, ba jiya ma nayi girki ba" yana kallonta yace "Jiya kinyi girki cikin rashin sanin Babynmu na kwance a cikinki" sai ya kai hannu yana shafa cikin, ahankali yace "It's okay little one, Daddy got you..Maama won't be stressing you anymore" nan kuma Na'ima ta kasa riqe dariyanta tana kallonsa, sai tayi baya akan kujeran da suke zaunen bata daina dariyan ba duk yana kallonta, sai shima ya fara dariyan bai bar shafa cikin nata ba, sai da tayi me isarta sannan tace "This is going to be a long and dramatic journey" cikin kwantar da murya yace "And we'll go through it together in sha Allah, I love you Na'eemah, thank you for this" sai ta shafa gefen fuskansa ahankali tace "I love you too".
Da yammacin ranan Ahmad ya nemi zuwa gidansu dan ya sanar da su Mamma amma sai taqi barinsa, tace "Please karka fada musu, yayi wuri.. besides, ni kunya nakeji gaskiya" sai yace "Babe hakan fa ba komai bane, kowacce mace haka tayi" shiru tayi batace komai ba sai ya kamo hannunta, cikin nutsuwa yace "Ki bari mu fada musu, Mami will be there too, ita zata iya doraki akan abubuwan da baki sansu ba along the way" sai ta gyada kai ahankali tace "Hakan yayi" yace "Yauwa Babe" .
Time dinda news din cikin nata yayi breaking a cikin familyn sai kowa ya fara kiranta ana tambayan halin da take ciki dan a tsammaninsu irin ciki me laulayin nan ne take fama, Mami ce ta fara kiranta kafin su Mamma da Anty Amnah su kirata, bayan ta dauka sai taji tace mata "Habibti ya dai, ya kikejin jikin naki" a kunyace tace "Lafiya" tace "Talk to me kinji, yana baki wahala ne?" ta amsa da "A'a Mami, babu abunda nakeji" sai Mamin tace "Sannu ko, zanzo in dubaki in sha Allah, Allah ya sauqeki Lafiya, daga kinji wani Abu karkiyi shiru fa" tace "Toh Mami, in sha Allah" da haka ta fara tambayan lafiyan su Abba, aikuwa washegari da safe tana kwance a falonta Nafisa ta doka mata kira, tana dauka taji tace "Me ciki, me zaki ci a dafo miki in zan zo anjima" tana murmushi tace "Allah ya shiryeki Nafee" sai tace "Allah dagaske Mami tace in tambayeki me za'a miki, dan tasan in Itace zakice Aa" sai Na'ima ta danyi dariya tace "Babu komai, kawai kizo da wuri muyi hira" da haka suka dan taba maganganunsu sannan sukayi sallama, tananan zaune Ahmad ya shigo falon hannunsa riqe da tray na breakfast, sai tayi murmushi ta fara kokarin miqewa yace "Yi zaman ki Babe" ya ajiye tray din akan glass table ya sake cewa "There... it's all set" tana dariya tace "Sannu" sai ya zauna a gefenta yace "Anything for you Baby" da haka ya fara serving dinta abincin da yayi order, Yes ordern abinci ya koma yi musu akai akai ko kuma su fita zuwa eatery a wasu lokutan, Na'ima dai ta zuba masa ido yana pampering dinta kamar wata kwai..suna tsaka da yin breakfast din Anty Amnah ta kirata, a kunyace ta dauka suka gaisa, sai tace "Ya jikin naki daughter" ta amsa da "Lafiya Anty, ya boys suke?" Tace "Sunanan Lafiya, kinajin wani changes ki fada masa fa ba'a shiru kinji" tace "in sha Allah Anty" sai ta tambayeta ko Ahmad din na kusa, nan ta miqa masa wayan suka cigaba da magana.
A lokacin da Nafisan tazo bayan ta gaisa da Ahmad sai ya fita zuwa office ya barsu suna hiransu a falon qasa, da sauri Nafisa ta dauko remote na Ac ta rage tana fadin "Bobo banzo gidan nan dan in daskare ba wallahi" Na'ima na murmushi tace "Zafi nake ji dai Nafee, yanzu zakiga na fara gumi" sai tace "Kefa you're not normal yanzu" sai ta danyi dariya kawai batace komai ba, ganin Nafisan na kallonta yasa tace "Meye haka?" sai ta amsa da "Oh su Bobo da ciki, ya kikeji kuma?" tace "Nafee bakida dama wallahi" sai tace "Allah kuwa, mamaki nakeyi sosai wai zamuyi da" nan kuma Na'ima tayi dariya tace "Nima nayi mamaki, jiya a gaban madubi nayi ta kallon cikin dai" sai Nafisa tayi dariya tace "Dan ma naga kamar bakya laulayin da akeyi, kinga Ummin gidan Daddy saida tayi wata hudu tana jinya sosai kamar zata mutu wai duk ciki" Na'ima tace "Ayya wai ance wasu sunayin haka daman, nidai banajin komai" sai Nafisa ta gyara zamanta tace mata "Ni kinji labarin su Mummy zasu koma gurin Daddy da zama a Cairo?" ta amsa da "A'a bai fada min ba" Nafisa tace "Inaga next week zasu tafi, zasu bar nan din gaba daya sai dai zuwa occasionally" a sanyaye Na'iman tace "Allah sarki" sai Nafee ta dan harareta tace "Ba abun Allah sarki, suje can Umma ta gaida Aisha, mutanen nan abun tsoro ne gwara suyi nesan yafi" jin Na'ima tayi shiru yasa ta sake cewa "Next month su Al'ameen zasuyi graduation" tace "Har ya gama, aikuwa zamu je in Allah ya kaimu" sai Nafisa tayi dariya tace "Zamu je dai, ke yanzu ai ba zuwa ko Ina, Abba ma yace babu maganar zuwa Umrah yanzu" cikin sanyinta tace "Ayya Nafee banajin komai dangane da rashin lafiya in ba zafin nan da cravings ba" sai Nafisan tace "Aito ana guje miki matsalan ne Bobo, Allah dai ya sauqeki Lafiya" "Kuma gashi Lamin ya fara min maganar turo iyayensa, yanzu da cikin zamuyi hidiman auren nawa?" Ai da sauri Na'ima ta miqe daga kujeran da take ta dawo kusa da ita, sai ta dan tureta tana dariya tace "Ya haka? dama Ina ta tunanin ta inda zan fara fada miki tun dazu" cike da murna Na'ima tace "Dan Allah fa? Zuwa yaushe ne auren?" Tana murmushi tace "Sai iyayensa sunzo za muji actual date din, amma yace indai akazo tambaya kuma su Abban suka bayar to baza'a dauki lokaci ba" nan kuma Na'ima ta hau murna sosai tana fadin "Allah ya sanya alkhairi besty" ganin yanda take ta gumi yasa Nafisan yin dariya tareda daukan remote ta qara gudun Ac'n tace "Kinganki kuwa, kamar wadda aka saka cikin oven" sai tafara goge fuskanta da rigan dake jikinta tace "Ai na fada miki" Nafisa na dariyan ta miqa hannu ta zaro tissue dake kan table sannan ta fara tayata goge gumin kamar wadda aka zubawa ruwa ajiki.
Ana tafe Na'ima ta shiga wata na biyu da cikinta, kuma har zuwa wannan lokacin Allah baisa ta fara wani rashin lafiya ba, dan sai ciye ciye ne da ta qaro da kuma yawan jin yunwa kamar taci babu, duk da yanda garin yake da sanyi a wannan time din kasancewan raining season ya shigo amma har zuwa lokacin bata daina jin wannan zafin ba dan har Ahmad ya saba da sanyin gidan, komawa yayi yawo da safa acikin gidan saboda yanda tiles din suke daukan sanyi sosai, a farko har yana saka auduga a kunnensa in zasuyi bacci amma kuma ana tafe sai ya saba da hakan dan shi da kansa yake qure mata the more yaga ta fara gumin nan, dakyar ya barta ta cigaba da dafa musu abinci amma duk da hakan time to time sai ya siyo musu a wajen, mai aiki kuma tun wuri Mamma ta nemo musu me zuwa da komawa, takan zo da sassafe tun kafin Ahmad ya tashi daga bacci ma zata gama dan gyare gyare da mopping dinta anan downstairs sannan ta tafi, sai ya zamto pregnancy journey'n Na'ima har sannan babu wasu obstacles acikinsa, acikin wannan watan ne graduation din Al'ameen yazo amma Ahmad ya hanata zuwa, ranan da yace bazata je ba wuni tayi tana kumbure kumbure agidan har ya dawo daga gurin aiki bata sauqo ba, kasancewan da wuri yake dawowa sai ya zamto zuwa bayan azahar ma ya dawo gidan tana zaune a falo, a madadin ta tarosa kamar yanda ta saba sai ta juya kanta ma tana qara hade fuska, sai hakan ya basa dariya dan yasan me ya mata nan kuma ya wuce kitchen bai dade ba ya fito hannunsa riqe da bottle water yana kurba, ganin har sannan taqi kallonsa yasashi fara dariyan kuma, aikuwa da taga yana dariyan sai ta fara hawaye wanda yasa shi qarasowa gurinta da saurinsa yana fadin "Subhanallah, Babe menene na kuka kuma" ya zauna daf da ita tareda juyo da fuskarta yace "Abun har yakai haka?" sai ta gyada kai tana share hawayen tace "Kowa zaije fa bandani" yace "Toh ai ke da naki uzurin dear, it's a sixteen hours flight fa" da sauri tace "Ai zanyi bacci sosai" yana kallonta anutse yace "Banason risking lafiyanki da na babyn nan Na'eemah, da ma ace watannin sunyi nisa ne da sauki" nan ma ta cigaba da hawayen yana kallonta, sai ya jawo ledan da ya shigo dashi ya bude tareda ciro mata burgern da ya siyo mata a hanya, miqa mata yayi yana murmushi yace "Kici abinci tukunna sai mu cigaba da maganan" sai kuwa ta karba ta fara ci yana kallonta kamar zeyi dariyan amma ya danne sannan yace "My baby is toying with your emotions love, small things sai kuka yanzu kuma" bata kulasa ba ta cigaba da cin abincin ta har tana wani ajiyan zuciya kamar wadda tayi awanni tana kukan.
One more chappy to go darlings 😊❤️
Don't forget to follow my account and give a thumbs up by liking this story.
Bintu Musa✍️📖