46
by @zahrabmrs02
BAYAN MURMUSHI
Page 46⌨️💬
Tun daren jiya AK ya buga waya zuwa ga Gwamnan jihar Kwara, wanda babban aminin mahaifinsa ne, kuma babban yaya a wajen AK.
"Your Excellency, zan shigo Ilorin gobe da sassafe tare da iyalina. Za mu gaishe da kakaninta na wajen uwa ne kafin mu wuce Amurka," AK ya fada cikin girmamawa.
Gwamna ya amsa cikin murna, "Barka da zuwa Abdulkadir! Kar ka damu, komai ya kammala. Zan sa a gyara maka Government Guest House, sannan motoci da jami'an tsaro za su jire ku a Airport."
Ranar Tafiya (Abuja Airport)
Farhana ta fito cikin shiga ta alfarma, sanye da wata tsadaddiyar lallausar laffaya mai kalar sararin samaniya. Tana ganin yadda motocin tsaro (Security Escorts) suka jera a harabar gidan, gabanta ya fadi.
"AK, duk wannan saboda mu ne?" Ta tambaya da muryarta kasa-kasa.
AK ya yi murmushi ya kamo hannunta. "Ba komai ba ne wannan, Wifey. I want you to feel like the Queen you are."
Suna isa sashin jirage masu zaman kansu (Private Wing) na Airport din Abuja, aka kwashe akwatunansu cikin sauri. Ba a fi minti arba'in da tashi ba, jirgin ya sauka a garin Ilorin.
A can ne Farhana ta ga jerin gwanon motoci kirar Lexus da Land Cruiser Prado baki-fata, dauke da tutar jihar Kwara. Jami'an sanya-ido (Protocol) na Gwamna, sanye da bakaken kaya, suka bude musu kofa cikin girmamawa.
"Welcome to Ilorin, Sir!" babban jami'in ya fada yana sara wa AK.
Haka suka dauki hanyar gidan su Mami dake Taiwo Road. Lokacin da motoci hudu na tsaro suka shigo unguwar tare da karar jiniya kadan-kadan, mutane suka fara fitowa daga gidajensu don ganin wanene ya zo.
Mami, wadda take tsakar gida tana gyara egusi, ta ji jiniyar jerin gwanon motocin. Ba a jima ba ta ga AK da Farhana sun shigo.
"Maryama ce wannan?" Mami ta fada tana tafa hannu cikin mamaki da farinciki. "Sannunku, sannunku! Ai jiya Habibu ya ce mijinki ya kira shi, ya ce kuna tafe. Bismillah, ku karaso!"
Farhana ta rungume Mami tana kukan farinciki, yayin da AK ya durkusa har kasa ya gaishe da tsohuwar. Suna cikin gaisawa, Uncle Habib, Uncle Ismail, da Bafa suka shigo gidan. Aka sake barkawa da sabuwar gaisuwa, Baffa yana ta tsokanar Farhana.
Ba a dade ba, Mami ta kawo musu Amala da miyar Ewedu da naman zuku-zuku. AK ya saki jiki ya ci Amalar Mami, sai santi yake yi.
Bayan sun gama hira, AK ya bukaci su wuce Guest House din da Gwamna ya ba su domin su huta, sannan gobe za su dawo su kara ganawa kafin su wuce Matazu.
Farhana ta fito daga wanka, tana kokarin shiryawa cikin kayan baccinta. AK yana zaune a kan kujera mai siffar L-shape, yana waya da su Kausar. Ko ba komai, AK ya faranta mata rai da ya kawo ta Ilorin; hakan zai kara masa girma da mutunci a idon Diddi.
AK ya rungume ta ta baya. "Wifey, tunanin me kike yi haka?"
"Ba komai, Honey. Kawai nagode sosai da ka kawo ni wajen su Baffa. It means a lot to me."
Cikin mamaki da shauki AK ya kalli Farhana. Wai yau Farhana ce ta kira shi da "Honey"? Kara rungume ta ya yi tsam a jikinsa, kamar wani zai kwace masa ita. Farinciki ya ratsa zuciyarsa.
"Wifey, kin iya irin Amalar Mami?"
"Eh, na iya. Me ya sa ka tambaya?"
"Me ya sa ba ki taba yi min ba?"
Murmushi Farhana ta yi. "Ina zan sani? Ina tunanin kai 'Big Boy' ne, ba za ka ci Amala ba. Shiyasa ban taba yi maka ba."
Ya ja hancinta cikin wasa. "Ai ke ce Big Boy din!"
Hannunta ya ja a hankali har zuwa kan babban gadon su (Royal Bed). Tana kwance a jikinsa, ta ji alamun tashin sha'awarsa (junior dinsa), amma abin mamaki, har suka yi bacci bai neme ta ba.
Zata iya rantsuwa AK baya bin mata, domin wayarsa ko password babu, kuma kullum yana makale a gida, sai dai idan zai leka kamfaninsa, shi ma ba kowane lokaci ba. Ba ta taba ganin wata mace ta kira shi ba. Kamar yadda Halima take fada mata, iya danginsa ne kawai suke da lambarsa, shi din mutum ne mai matukar sirri (very private person).
"Amma farkon aurensu ba haka yake ba... to me yake faruwa?" Farhana ta yi ta wasika a ranta. Ko so yake ta sake sosai ne?
A haka har bacci ya dauke ta, ba tare da ta gano hakikanin abin da AK yake nufi ba.
Washegari, sararin samuniyar garin Ilorin ya waye da wani irin sanyi mai ratsa jiki. Farhana ta fito cikin wata shiga ta alfarma da ta amsa sunanta, kyan fuskarta ya kara fitowa fili, kwarjininta ya ninka na kullum.
Bayan sun kammala shiri, jerin gwanon motoci ya nufi Government House, inda Gwamna ya bukaci su hadu don yin karin kumallo (breakfast), kasancewar an dade ba a hadu da AK ba.
Tarbar da aka yi musu ta musamman ce; jami’an tsaro da ma’aikatan kowa na girmama su. Matar Gwamna (First Lady) ta tarbi Farhana cikin mutuntawa da karramawa. An dauki hotuna na tarihi, inda First Lady ta nuna wa duniya cewa Farhana ba surukar suce kasancewar Kawar mummy ce kuma ta zo bikinsu.
Farhana ta kalli yadda kowa yake durkusawa yana kiran sunansu cikin girmamawa. Wata zuciyar ta ayyana mata, “Ashe haka masu kudi da mulki ke ji? Dole ne wanda ya hau mulki ba zai so sauka ba.” Ta ji wani irin kwarjini da dan girman kai na lokaci guda ya ziyarci zuciyarta, ganin yadda ake taku ana zuba kamshi a cikin fadar gomnati
Bayan sun kammala sallama da Gwamna, suka koma gidan Baffa don kammala sallama da sauran dangi.
Kafin su isa, tuni mami ta riga ta sanar da dukkan ’yan uwan diddi cewa su taru a gidan Baffa, don kada a wahalar da Farhana wajen bin gidaje daya-bayan-daya. Gidan ya cika ya yan uwa , kowa na son ganin Maryama da mijinta.
AK ya nuna halin kwarai da ladabi wanda ya ba kowa mamaki. Duk da cewa shi dan Gwamna ne, bai nuna wata isa ba. Ya durkusa har kasa ya gaishe da Baffa da su Mami. Abin da ya fi taba zuciyar Baffa shi ne yadda AK ya zauna a kan kafet, ya sanya hannu yana cin Sakwara da miyar Egusi tare da su, girman kai.
Baffa ya gyara zama, fuskarsa dauke da murmushin jin dadi. "Abdulkadir, mun gode sosai da ka kawo mana Maryama. Mun ji dadin yadda kake kula da ita. Allah ya bar zumunci."
AK ya sunkuyar da kai cikin natsuwa. "Baffa, ai Maryama amana ce a gare ni. Mun zo ne mu nemi tabarau da addu'o'inku kafin mu bar kasar nan zuwa Amurka."
Baffa ya kalli Farhana, ya ga yadda fatar jikinta ta yi luwai-luwai, fuskarta ta yi bul-bul, ya tabbata tana cikin kwanciyar hankali. "Allah ya yi muku albarka, ya kiyaye hanya. Maryama, ki kasance mai yi wa mijinki biyayya a kowane lokaci."
Daga nan, Farhana ta shiga daki inda Inna Jamila da sauran mata suka taba ta da hira da nishadi. Mami ta fito da manyan kayayyaki, tsaraba niki-niki ta ba Farhana.
Kafin su tashi, AK ya dauko wasu dunkulan kudade (bundles) ya ajiye wa Baffa. Farhana kanta bata san nawa ne a ciki ba, amma kudin sun yi yawa. Da kyar, cikin mutunci da rarrashi, Baffa ya amsa kudin bayan AK ya nuna cewa alheri ne na neman addu'a.
Bayan sun yi bankwana mai ratsa zuciya, suka nufi filin jirgi na Ilorin kai tsaye. Ba a dauki lokaci ba, jirginsu ya karkata zuwa sararin samaniyar jihar Katsina.
Suna sauka, Farhana ta leko ta taga, ta ga jerin gwanon motocin gidan Gwamnan Katsina su ma suna jiran su. Gwamnan Katsina, wanda ya san darajar mahaifin AK, ya tura babban jami'in tsarinsa (ADC) ya tarbe su.
"Welcome to the Home of Hospitality, Sir," jami'in ya fada yana bude musu kofofin Bulletproof Land Cruisers.
Haka aka dauki hanyar Matazu. Isarsu garin ke da wuya, jiniya ta fara kuka wee-wee-wee, yara suka fara bin motocin suna ihu. Farhana ta gyara zamanta, tana jin wani irin kwarjini.
Suna isa kofar gidan Nene, motocin suka dandalala. Nene dake tsakar gida tana fitsarin fako (tsantsar fura da madara), ta ji karan jiniya. Ta mike da sauri ta fito tana sanye da tsohon mayafinta mai kalar toka.
Ganin AK da Farhana sun fito daga cikin motocin alfarma, Nene ta saki baki, ta tafa hannu. "Iye! Lallai Maryama kin yi miji! Wato yanzu har da motoci masu jiniya ake yawo da ke? 'Yan garin Matazu yau sai sun kusa mutuwa da kishi!"
Ta karasa wajen AK, ta shafa jikin motar tana gyada kai. "Abdulkadir, yanzu na yarda lallai kai dan Gwamna . Don kasan Bayan na dawo daga habuja na fadawa yan garin nan dan gomna maryama ta aura suka karyata ni, Yanzu dai sun shaida!"
dariya Ak yake dan nene Tana bashi nishadi .karasowa sukayi cikin gidan Ak ya durkusa har kasa. "Nene barka da gida."
"Barka dai babban bako! Shigo ciki akwai magana," Nene ta ja hannunsa.
Suna zama a falo, Farhana tana ta faman rarraba idanu saboda kunyar yadda Nene take kallon AK. AK ya sa aka shigo da manyan ledoji na tsaraba. Nene ta fara duba su daya bayan daya.
"Wadannan atamfofin sun yi kyau, amma dai Abdulkadir, kasan tsohuwa ba ta cika cin abinci mai yawa ba."sai dan Kayan kwadayi , Ta rage murya tana rada, "Kasan dai yanzu rayuwa ta yi tsada, kuma ni ce na raine ta. Don haka, kada ka mance da 'na goro' na musamman wanda zan boye a karkashin katifata don 'yan tsegumi su gani."
Farhana ta rufe fuska. "Nene! Don Allah ki bari mana."
"Ke rufa min baki!" Nene ta daka mata tsawa Tinda kuka zo kike bakin Hali Kina fushe fushe ,In ban karba yanzu ba, yaushe zan kara ganin sa tunda guduwa zaku yi Amurka?"
AK ya kwashe da dariya, ya zura hannu a aljihu ya fito da wata damin dari biyar-biyar sabbi fil. "Nene, gashi wannan naki ne na musamman. Kuma duk watan duniya za a dinga turo miki wani abu."
Nene ta karbi kudin ta fara kirgawa nan take, tana taba yawu a harshe tana kirgawa "Daya, biyu, uku... kai kai ban taba rike kudi masu yawa irin wanan ba ,Nagode sosai dan gomna Allah yasa gomna ya zama shugaban kasa watarana ,Maryama, lallai kin yi miji!"
Ta fito tsakar gida rana kiran surukain ta"Luba! Inno! Ku zo ku gani! Mijin Maryama ya kawo min kudin fure! Kun ga motocin da suka zo dasu kuwa?
Tsabar son abun dunia nene ko ruwa bata basu ba,haka ta yafa mayafi ta tafi kiran yan unguwa suzo suga dan gomna ,farhana tayi nadamar zuwa matazu ,inda Ak yayi ta rabon kudi ,nene sai washe Baki take .
Haka dai sukayi yi sallama sai hanyar sokoto Wajan mommy .
Ya Haduwar mummy da farhana zai kasance a sokoto?
Don’t forget to follow share your thoughts on the comment section