KUSKURE 13
*KUSKURE*
BY Maman Shaheed
shafi na sha'uku
"Around 10 :30pm aka Fara watsewa daga wajen dinner, masu tafiya da wuri.
Wasu sun tafi ,Amarya ma gdn su za'a kaita amata fad'a kawai sanan a wuce da ita gidan Ammy sai gdn mijin ta at last Dan haka aketa musu magana su fito haka dare yayi.
Daƙyar aka samu aka kwaso Amarya d 'yan uwan ta aka kaita gdn su , 20mnts olny abokanen ango sukaba dangin Amarya ,suka dinga uzira musu seda aka Basu ita tanata kukan gulma ,aka wuce d ita gdn Ammy wai ta sa musu Albarka , Nan ma 20mnts 30 kawai akayi sanan aka wuce d ita gdn ta.
"Yayin d momyn su Noor Bata bisu gdn Amarya ba sbd tajeje gidan , Dan haka Tana gdn Ammy su twins ne kawai sukaje har huzna ,har d su Indo hadiya ce ta jata dake ta d'anfi Indo wayewa kad'an , badan tanaso ba ta jata sukaje ganin kwakwaf,
Aiko sun Sha kallo ,sunga kayan more rayuwa na agani afad'a sun yaba ,har hadiya ta dinga cewa "Allahummah Arzukunah" Indo Ta Amsa da " Ameen Amman dakamar wuya gurguwa da auren nesa"
hadiya tace "karki Mana baki Abin yin Allah nefa ba yin mutum ba ,keda Kika catching station ma ,gayen dazu d Kika nunamin wlh kin gama sa 'a ki bashi dama kawai ya dama ki rabu d wata aunty NAWAL ,Auren ki zatayi ? Ne ko a mata bauta zaki ƙare?"
Indo ta zaro ido kafin tace" a Ina Kika taba ganin mace ta auri mace ?"
Hadiya tace" toh ,ba Auren ki zatayi ba Kuma ba dawwama zakiyi kina Aiki ba agidan ta,kin ga ko dole kiyi Aure wataran ga dama ta fara zuwar miki"
"uhum" kawai indo tace, hidaya taci gaba da cewa.
"Dan haka kima kanki karatun ta nutsu ,sai nayi mgn kice wai baki girma ba ,hmm koni yanzu n Sami miji aurena zanyi wlh na ƙarasa girman acan"
Indo t dinga dariya ,wani irin sabawa sukayi lokaci kankani d hadiya ,sunajin dadin kawancen su Kawai dai Basa haɗuwa akai-akai ne.
Anata shiga mota Dan komawa gida ,Suma suka shiga wata motar dan amaidasu ,sukaci gaba da hirar su ta samun ƴanci yau.
Bayan sun dawo gd ,Indo Bata yadda sun had'u d momyn su Noor ba , makwanci kawai ta nema dak'in d aka sauki bakin kyauye Nan suka kwanta Kan wata katifa karama ita da hadiya sunata hirar su Kamar Kar su rabu.
Suma su twins, huzna,Asmy,suhaima,da su Hindu da sauran 'yan Mata nasu d'akin daban.
Itama NAWAL ,Tana tare d matasan matan Aure kamarta 'yan uwan Ammy sunata Hira wasu ma sun nemi makwancin su ,yaude Noor d Haneef suna tare da gyatumar su yau Kam ..Indo t huta.
Wasu kwana sukayi suna Hira ,wasu ko sunyi baccin su lakadan harda munshari .
Ango da Amarya ma suna can suna gidan su ko sun Sami damar baccin yau ko Basu samu ba Dan murna da farin ciki ohonnn musu Dan basu ba maman shaheed Daman shiga sha'anin su na yau d'inan ba ,Nima Kuma banyi naci d ganin kwakwaf ba na rabu dasu su sha sha'anin su.
Washegari ,tun safe aka Fara aikin Abin Karin kumalo , ansha Aiki ,wasu harma sun sa ruwan wanka sunyi Dan Akwai masu komawa aranar 'yan uwan Ammy Dana baban su twins din maxa da Mata .
Su Asmy d suhaima dai sai gobe zasu koma ,huzna ko ma cewa tayi sai ta huta zata bar garin Hmmm, dan tana da manufar ta.
Momyn su Noor ma sai dare zasu koma Dan gidan be gama watsewa ba , su Indo d hadiyane suka dinga gyagyara wasu abubuwan d aka Bata d gdn dake anrage musu aikin ma sosai Dan Ammy sai d Tayo hayar masu Aiki ,Amman Suma sun gyara gdn yayi fes duk d ba a gama watsewa ba ,Ammy tayi ta sa musu Albarka ,da wasu datijai suna yaba kokarin su "Indo tl taji dad'in kalmar da Bata taba samu daga uwar d'akin ta ba ko d wasa a zaman su tare in ta mata hidima a gida ko da yaranta.
Tsakanin NAWAL d Indo kadaran kada han ,har yanzu Bata ce Mata komai ba tukunna jira take su koma gd .
Yamma tayi likis wasu ma duk sunkara tafiya gd na kusa Dana nesa
Bayan Isha 'i dadyn su Noor yazo d'aukan su NAWAL d iyalan ta har Indo .
Sukama kowa na gdn sallama ,Ammy nata shi musu Albarka Tana musu Addu'a Allah ya hutar da gajiya, haka suka bar gdn ,huzna ko ji tayi kamar ta bisu su tafi ,Amman ganin yau kanwar su Bata jiku ba ita d NAWAL yasa t fasa Dan indai ta Mata bazata kyaleta ba Kuma SAFWAN Tana nan tare dashi ai d'an uwanta ne ,ita Kuma Indo zasu gauraya ne ...can aka barta d lissafi dai .
Har bakin mota twins ,Su suhaima suka rakosu Noor , suka musu fatan Isa gida lpy , sukama Indo Allah y hutar da gajiya safwan yaja mota suka nufi gida.
Isar su gd keda wuya , Indo ta je ta kwantar da Haneef bayan t rage Mai Kaya haka ma Noor itama takaita ta kwantar da ita ta musu addu'a itama ta nufi d'akin ta Dan gujema haɗuwar ta da uwar d'akin nata a daren Nan.
Itako NAWAL dama itama d'akin ta ta Fara wucewa Dan watsa ruwa ko taji dad'i .
Bayan t fito shima safwan y fito , y sako jalabiya y fito falo zai d'auki Abu a fridge ....ya ji NAWAL na Kiran Indo cikin gadara d Isa .
Sanin halinta y fara tuhumarta" me zata Miki a baƙin adaren Nan ?"
Ta turo baki Tana yamutsa fuska tasan ze kawo Mata cikas tace ," yarinyar Nan fa Bata d mutunci wuyanta y fara kauri , bakaga kayan jikin t da tasa bane irin Ankon dinner d'in mu waya Bata ?"
Wata muguwar harara ya wurga mata, ba tare da yace komai ba.
" Ko Kai kasiya Mata Eye dadyn Noor? Tana tuhumar Shi.
Ganin Abin zai zama zargi yace" kirata ki tabmayeta "
" Kuma ki Mata tambaya cikin Nutsuwa ba yadda Zaki firgitata har t kasa baki amsa ba.
Aiko da kanta ta tafi kiranta ,sukazo har gaban dadyn su Noor d'in atare.
Cikin Isa d gadara ,NAWAL takema Indo magana.
"Indo"
Cikin sanyin murya tace" naam"
"Uban wa ya baki kayan jikin ki da Kika sa ranar dinner?"
"mugun kallo SAFWAN ya sake mata na gargaɗi"
Cikin kid'ima d rawar murya tace" Su hassana da hussaina ne suka siyamin suka dinkamin Kuma suka bani sukace nasa ranar kamu d dinner Kamar kowa"
wani wawan kallo NAWAL tabi SAFWAN dashi Kafin ta iya furta.
" Kan uban Nan ,au bama kala d'aya bane? Munafuka"
dadyn Noor ne y dakatar da NAWAL din.
"bana son hayaniya
Bari in Kira su twins d'in Naji" ,tace
" kirasu mu kure munafuka"
Yayi dailing number hassana ringing 1,2 aka d'aga ,ya fara magana yaji muryar Ammy nacewa wayar Tana hannu na su Kuma suna d'aki kasan k'anwar taka d ajiye waya duk inda ta samu.
Safwan y k'osa da bayanin Ammy , yace "hassana fa Tana kusa?"
Ammy "tace duk suna can tare"
Bata rufe baki ba sai g ussaina ta shigo ɗakin.
sanan Ammy tace "toh ga ussaina Nan ma ta shigo ta Mika Mata wayar.
Usaina n karba tace ," Yaya y kukaje gd? "da ta saurari muryar shi.
" lpy "kawai yace kafin" ya cigaba da magana
ke waya siyama indo kayan anko ?"
Duk sunajin hiran nasu har NAWAL d'in ,ussaina tace
"eh mu muka siya Mata Kuma d izinin Ammy Amman mu muka nemi hakan"
Wani kallo ya sake ma NAWAL.
Kafin Yayi ajiyar zuciya ,yace" kin tabata Kuma kala nawa kuka Mata ?"
Ussaina tace" kala biyu ne , mu muka Mata duka har d'inki Yaya indon CE ai Bata d matsala tanada kirki wlh kodan hidima d take dasu Noor ai ma Mata Abin da yafi haka ma"ta firta mai da ƙarfin gwiwan ta.
Ya ce "eh kuma haka ne , kin tabata dai ko?"
Tace "eh Yaya g Ammy ma ka ji daga bakin ta" ta sakama Ammy waya a kunne.
Yana Mata magana akan ai basai taba Ammy ba, Ina Ammy har ta Amshi magana "safwan wani abune Dan sunma Indo d'inki lefi sukayi naji Kanata tuhumar SU Kamar sun aikata zunubi babba"
Cikin inda inda yace "aa Ammy dama ,bamu San Wanda y Mata bane dagani har momyn su Noor shine muke tambaya"
Ammy tace "hakane ,inace sun Gaya muku ai ,hakan nada kyau , Nima d Amincewa ta hakan ta faru Dan sun tambayeni nace suyi Mata ai ta cancanta ,Mai hidima ga iyalanka dan sun mata ba laifi bane"
Yace" hakane Ammy Allah ya Kara girma ,sai da safe to dama kawai shine tambayar "
,Ammy tace" Allah ya tashe mu lpy Allah y hutar da gajiya ya bamu Alkhairi "
kafin y kashe waya NAWAL t tashi fuuuu ta nufi daki ta barshi a wajen da malolon baƙin ciki amsar Bata gamsheta ba gashi Ammy ta Mata katsalandan tashiga maganar tayi magana ace tama sirika rashin kunya.
A wajen tabar shi da indon ta tafi Abun ta shima y juyo y zubama Indo ido , ita Kuma ta sunkuyar da kanta k'asa ,Sai da ƙyar ya magantu " tashi kije ki kwanta Kinji?"
tashi tayi kafin ta firta "toh nagode" ...cikin himma ta mik'e ta nufi d'akin ta da sanyayoyar zuciya.
Shiko be bi NAWAL ba seda y shiga d'akin yaran shi ya musu Addu'a sanan ya bita d'akin ta Dan Mata tambayoyi Daga baya y shiga d'akin ta y sameta Tana kad'e shinfid'a ranan a jagule.
Y zauna Kan wata kujera 1siter cikin d'akin yace "Zo muyi magana NAWAL" ,seda gabanta y fad'i Amman ta dake taje ta zauna kusa dashi.
Ya kalle ta Yace "NAWAL baki gamsu da bayanin Ammy bane mahaifiya gareni ko me kike nufi d har Kika d'auki zafi akan 'yar maganar Nan?"
Cikin Jin kunya da fargaba tace "laa nifa ba manufata kenan Ba
Ya katse ta yace" bayyana min manufarki Ina Jin ki?"
Ta ce" aa wlh Abin ne y d'aure min Kai ,Kuma kaga su Hassana ma ai Basu kyauta min ba sun munafirce Ni sun daidaita level ɗina dana Mai aiki na"
Yace "shine kawai laifin su?
" y zasu saima Indo anko irin namu ,Kuma batare d sun bani na Bata ba , me yayi zafi haka d zasu min haka ? Y Dace hakan d suka min? "
Yayi murmushi ,yace" be dace ba uwar haneef da noor uwar ɗakin indo baiwar Allah zan musu maga Kuma ,saura me Kuma?"
Zaro ido tayi" ni baiwar waye? "
" dani dake da ita duk bayin Allah ne"shiru tayi bata son tsawaita magana Amman badan ta gamsu ba.
" har kwaliya fa sukasa aka Mata irin tamu.."
Bata karasa ba y katseta Yana dariya.
"Banda Abin momyn su Noor meye acikin kwaliya Kuma ? Ko kema sai da ta canja miki ne? Baki gane ta ba ko?"
"au wai kaima Kaga canjawar da tayi kake nufi har ma ka ƙare mata kallo kaga canjin?" ta firta cike da kishi.
"a'a haka nace miki, ni ina ganin ta nasan indon house girl ɗin NAWAL ce"
Sai ta ɗan sauke ajiyar zuciya, shi ko be shirya ma hayaniyar bane dan a hannu yake, yana buƙatar samun nutsuwa da ita.
Ta ƙara numfasa kafin tace " kasan kud'in kwaliyan kuwa?"
Yace "ko nawa ne yakai 100 thousand ne ?
haba saikace ..."
Ya sake katseta ,yace" to meye Dan anmata kwaliya irin taku, Yanzu ina kwaliyar take da taku da tata kai har ma ta amaryar bade asarar kuɗi bane Anyi an wuce wajen? Kawai dai , ta haskane na lokaci d'aya "
NAWAL t d'ago d sauri ta kalle shi" kaima ta haska ka kenan?"
" aa ki Bari in gama maganata Mana "
yaci gaba da cewa" kuma ma yanzu Ina kwaliyar take? Tun aranar fa duk kukayi asarar kudin d kuka biya kuka wanke ta ,yada tata ta goge haka ma ta kowa ta goge ,ko Akwai a fuskar ta har yau?"
Kai kawai t girgiza Mai Alamar hakane.
Yace" toh ,duk fa abinan ke Kika d'auka d tsanani yarinyar Nan Tana Miki biyaya ga hidima d take Miki d yaranki , kwanaki fa bakiji dad'in cewa da tayi zata bar Aiki a gdn nan ba d yanzu fa Bata Nan ,in Kika ci gaba d takurata ta tafi shikenan "
" Kayan d kike magana akai ,kinji dai Mai Ammy tace Kuma ,su twins nace zan yi musu maga ,shikenan ai ko? "
Badan taso ba sai dai Kar yace ta Raina maganar Ammy yasa ta hakura tabar zancen suka kwanta ,cike d faranta ran junan su, kuma jikin ta ya ɗanyi sanyi da yayi maganar barin indo gidan.